Ba Mu Ji Tsoro Ba Don Jehobah Yana Tare Da Mu
Egyptia Petridou ce ta ba da labarin
A shekara ta 1972, Shaidu da suke Cyprus sun taru a birnin Nicosia don su ji jawabi na musamman da Nathan H. Knorr ya bada, ya yi ja-gora a hidima ta Shaidun Jehobah shekaru da yawa. Ya gane ni ba tare da ɓata lokaci ba, kuma kafin na gabatar da kai na, ya tambaye ni: “Kina da wani labari daga Masar?” Na sadu da Ɗan’uwa Knorr shekara 20 da ta shige a garinmu Iskandariya, da ke Masar.
AN HAIFE ni a Iskandariya a ranar 23 ga Janairu, 1914, ni ce ta farko cikin yara huɗu. Mun yi girma kusa da teku. A lokacin, Iskandariya birni ce mai kyau inda mutane daga ƙasashe dabam dabam suke da zama, an san birnin don zane-zanensa da tarihi. Tun da yake Turawa suna cuɗanya da Larabawa, mu yara mun koyi Larabci, Turanci, Faransa, Italiyanci, da kuma yarenmu, Helenanci.
Bayan na gama makaranta, na samu aiki a gidan ɗinki na Faransa, inda na yi farin cikin koyon ɗinka tufafi masu kyau na bukukuwa na mata masu arziki. Ni mai bin addini ne sosai kuma ina son karanta Littafi Mai Tsarki ko da ba na fahimtar abin da na ke karantawa.
A tsakiyar shekara ta 1930 na sadu da wani saurayi mai kyau, ɗan Cyprus. A dā Theodotos Petrides yana yin kokawa, kuma ya koyi yin alewa da gashe-gashe kuma aka ɗauke shi aiki a wani sanannen gidan gashi. Theodotos ya soma so na, ni gajeriyar mace mai baƙar suma. Sau da yawa, yana zuwa wajen taga ta yana yi mini waƙar soyayya ta Helenanci. Mun yi aure a ranar 30 ga Yuni, a shekara ta 1940. Waɗannan kwanaki ne na farin ciki. Muna zama a gida kusa da na mamata. Na haifi John ɗanmu na fari a shekara ta 1941.
Koyon Gaskiyar Littafi Mai Tsarki
Theodotos ba ya son addini da muke bi, amma yana tambayoyi game da Littafi Mai Tsarki. Ba tare da sani na ba, Shaidun Jehobah sun soma nazarin Littafi Mai Tsarki da shi. Wata rana, da nake gida da yaronmu, wata mata ta ƙwanƙwasa ƙofarmu kuma ta ba ni kati mai ɗauke da saƙon Littafi Mai Tsarki. Don in nuna ladabi, sai na karanta. Sai ta ba ni wasu littattafai masu bayyana Littafi Mai Tsarki. Abin mamaki, ashe irin littattafai da Theodotos ya kawo gida ne!
Sai na ce, “ina da irin waɗannan littattafai. “Ki shigo ciki.” Nan da nan, sai na yi wa Mashaidiya, Eleni Nicolaou tambayoyi masu yawa. Cikin haƙuri, ta yi amfani da Littafi Mai Tsarki ta amsa tambayoyi na. Na so abin da na ji. Farat ɗaya, na fara fahimtar saƙon Littafi Mai Tsarki. Lokacin da muka ɗan dakata da maganarmu, Eleni ta ga hoton maigidana. Ta ce: “Na san wannan mutumin!” Asirin Theodotos ya tonu. Na yi mamaki ƙwarai. Theodotos yana zuwa taron Kirista ba da sani na ba kuma bai ma gaya mini ba! Sa’ad da Theodotos ya dawo gida a ranan, sai na ce masa: “Wannan makon zan bi ka inda ka je Lahadi da ya wuce!”
A taro na farko da na je mutane goma suna tattauna littafin Mikah na cikin Littafi Mai Tsarki. Na fahimci kome! Tun daga lokacin, kowane Jumma’a da yamma George da Katerini Petraki suna ziyararmu don su yi nazarin Littafi Mai Tsarki da mu. Babana da yawancin ’yan’uwana ba sa so mu yi nazari da Shaidu, amma, ƙanwata ba ta damu ba, ko da yake ba ta taɓa zama Mashaidiya ba. Amma, mamata ta amince da gaskiyar Littafi Mai Tsarki. A shekara ta 1942, da ni da mamata, da Theodotos, mun yi baftisma a teku a Iskandariya don mu nuna alamar keɓe kanmu ga Jehobah.
Mun Sami Damuwa a Rayuwa
A shekara ta 1939, aka soma Yaƙin Duniya ta biyu, kuma ba da daɗewa ba ta yaɗu. A farkon shekara ta 1940, Janar na Jamus Erwin Rommel da rundunarsa suna kusa da birnin El Alamein, kuma Iskandariya na cike da sojojin Britaniya. Mun tara abinci. An ba wa Theodotos aikin kula da sabon wajen yi gashe-gashe na shugaban wajen aikinsa da ke Port Taufiq kusa da garin Suez, sai muka ƙaura zuwa wajen. Shaidu ma’aurata masu yaren Helenanci suka soma neman mu. Ko da ba su san adireshinmu ba, sun yi wa’azi gida gida har suka same mu.
Sa’ad da muke Port Taufiq, mun yi nazarin Littafi Mai Tsarki da Stavros da Giula Kypraios da yaransu, Totos da Georgia, kuma suka zama aminanmu. Stavros yana jin daɗin nazarin Littafi Mai Tsarki sosai har ya mai da dukan agogo da ke gidansa baya da awa guda don kada mu samu jirgi na ƙarshe na koma gida don mu daɗe sosai tare da su. Mun ci gaba da tattaunawa har cikin dare.
Mun zauna a Port Taufiq watanni 18 sai muka koma Iskandariya sa’ad da mamata ta soma rashin lafiya. Ta rasu a shekara ta 1947 tana da aminci ga Jehobah. Jehobah kuma ya ƙarfafa mu ta wurin cuɗanya da abokai Kiristoci da suka manyanta. Muna nuna wa masu wa’azi a ƙasashen waje karimci a hanyarsu ta zuwa inda za su yi hidima idan jirginsu ya tsaya na ɗan lokaci a Iskandariya.
Farin Ciki da Wahaloli
A shekara ta 1952, na haifi James, ɗanmu na biyu. Mun fahimci muhimmancin renon ’ya’yanmu a mahalli na ruhaniya, saboda haka muka sa gidanmu ya zama inda ake taruwa don nazarin Littafi Mai Tsarki, kuma sau da yawa masu hidima na cikakken lokaci suna zama a gidanmu. Da hakan, ɗanmu na fari John, ya so gaskiyar Littafi Mai Tsarki, kuma sa’ad da yake cikin tsakiyar shekarunsa na goma sha, sai ya soma majagaba. Yana zuwa makarantar yamma don ya gama makarantarsa.
Ba da daɗewa ba, aka gano cewa Theodotos yana da ciwon zuciya mai tsanani kuma aka ba shi shawara ya daina aikin da yake yi. Ɗanmu James yana shekara huɗu ne kawai. Menene za mu yi? Jehobah ya yi alkawari: “Kada ka ji tsoro; gama ina tare da kai.” (Isha. 41:10) Mun yi mamaki sosai da kuma farin ciki sa’ad da aka ce mu yi aikin majagaba a birnin Ismailia, kusa da Tabkin Suez a shekara ta 1956. Shekaru na gaba sun zama na wahala a Masar, kuma ’yan’uwanmu Kiristoci suna bukatar ƙarfafawa.
A shekara ta 1960 mun bar Masar, kowannenmu da jaka guda kawai. Mun ƙaura zuwa Cyprus, garin maigidana. A wannan lokacin, Theodotos yana ciwo sosai kuma bai iya yin aiki ba. Amma, wani ɗan’uwa mai kirki da matarsa sun ba mu wurin zama a gidansu. Abin baƙin ciki, maigidana ya mutu bayan shekara biyu, kuma aka bar ni kaɗai da James. Shi ma, John da yake Cyprus ya yi aure kuma yana da na sa iyalin da zai kula da su.
An Kula da Mu a Lokacin Wahala
Stavros da Dora Kairis sun ba mu gida a cikin gidansu. Na durƙusa na gode wa Jehobah don ya kula da bukatunmu kuma. (Zab. 145:16) Sa’ad da Stavros da Dora suka tsai da shawara su sayar da gidansu su gina sabon gida mai Majami’ar Mulki a ƙasa, cikin alheri suka gina mana ɗakuna biyu a cikin gidan.
Daga baya, James ya yi aure, kuma shi da matarsa suka yi hidimar majagaba har suka haifi ɗansu na fari, daga baya suka sami yara uku. A shekara ta 1974, shekara biyu bayan ziyarar Ɗan’uwa Knorr, an yi hayaniya ta siyasa a Cyprus.a Mutane da yawa, har da Shaidu sun bar gidajensu suka gudu suka koma wani waje. Ɗana John yana cikinsu. Ya koma Kanada da matarsa da yara uku. Ko da yake mutane sun ƙaura, mun yi farin cikin ganin cewa adadin masu shelar Mulki a Cyprus sun ƙaru.
Sa’ad da na soma karɓan fansho, sai na samu lokacin yin hidima sosai. Shekaru da suka shige, ɓangaren jikina ya ɗan shanye kuma na je na zauna da ɗana James da iyalinsa. Daga baya da ciwona ya yi tsanani sosai, sai aka kwantar da ni a asibiti na makonni da yawa kuma bayan haka aka kai ni gidan kula da tsofaffi. Duk da cewa ina jin zafi koyaushe, ina yi wa masu aikin asibiti, majiyyata, da baƙi wa’azi. Ina nazarin sa’o’i da yawa ni kaɗai, kuma da taimakon ’yan’uwana na ruhaniya, ina halartan taron Rukunin Nazarin Littafi na Ikilisiya da ke kusa da inda na ke zama.
Ƙarfafa a Lokacin Tsufata
Ina yin farin ciki sa’ad da na ji labarin waɗanda ni da Theodotos muka samu zarafin taimakonsu. Yawancin yaransu da tattaɓa-kunne suna yin hidima na cikakken lokaci, wasu suna hidima a Austariliya, Kanada, Ingila, Hellas, da Siwizalan. A yau, ɗana John da matarsa suna zama a Kanada da ɗansu. ’Yarsu ta fari da mijinta suna hidima na majagaba. An gayyaci Linda ’yarsu ta ƙarshe da Joshua Snape mijinta su halarci aji na 124 na Makarantar Gileyad.
Ɗana James da matarsa suna zama a Jamus. ’Ya’yansu maza biyu suna Bethel, ɗaya yana Atina, Helas kuma ɗayan yana Selters, a Jamus. Ɗansu na ƙarshe, da ’yarsu da mijinta suna hidimar majagaba a Jamus.
Da akwai labarai da yawa da za mu gaya wa mamarmu da mijina Theodotos sa’ad da suka dawo a tashin matattu! Za su yi farin ciki sosai idan suka ga gādo mai kyau da suka bar wa iyalinsu.b
[Hasiya]
a Ka duba Awake! ta 22 ga Oktoba, 1974, shafuffuka 12-15.
b ’Yar’uwa Petridou ta mutu sa’ad da ake shirya wannan mujalla tana shekara 93.
[Bayanin da ke shafi na 24]
Jehobah kuma ya ƙarfafa mu ta wurin cuɗanya da abokai Kiristoci da suka manyanta
[Taswira a shafi na 24]
ƘUBRUS
NICOSIA
BAHAR MALIYA
MASAR
CAIRO
El Alamein
Iskandariya
Ismailia
Suez
Port Taufiq
Tabkin Suez
[Inda aka Dauko]
Bisa ga NASA/Visible Earth imagery
[Hoto a shafi na 23]
Tare da Theodotos a shekara ta 1938
[Hoto a shafi na 25]
Ɗana John da matarsa
[Hoto a shafi na 25]
Ɗana James da matarsa