Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w01 6/1 pp. 13-18
  • Gina Iyali Mai Ƙarfi A Ruhaniya

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Gina Iyali Mai Ƙarfi A Ruhaniya
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ku Rifta Zarafi
  • Ka Koyar ta Magana da Kuma Misali
  • Ka Taimaki Yara Su Yi Girma a Ruhaniya
  • Ka Adana Ruhaniya
  • Ka Dogara Sosai ga Jehovah
  • Iyaye Ku Biya Bukatun Iyalinku
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Iyaye, Ku Koya wa Yaranku Su Ƙaunaci Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
  • Iyaye, Ku Koyar da Yaranku Su Kaunaci Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2019
  • Mene ne Zai Sa Iyaye da Yara Farin Ciki?
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
w01 6/1 pp. 13-18

Gina Iyali Mai Ƙarfi A Ruhaniya

“Ku goye su cikin horon Ubangiji da gargaɗinsa.”—AFISAWA 6:4.

1. Menene nufin Allah domin iyali, amma me ya faru maimakon haka?

“KUYALWATA da ’ya’ya, ku riɓu, ku mamaye duniya.” (Farawa 1:28) Da waɗannan kalmomi ga Adamu da Hauwa’u, Jehovah Allah ya kafa tsarin iyali. (Afisawa 3:14, 15) A hangar nesa, da ma’aurata na farko sun iya ganin duniya cike da ’ya’yansu—babbar iyali na mutane kamiltattu da ke zama cikin farin ciki a aljanna ta duniya kuma suna bauta wa Mahaliccinsu Mai Girma da haɗin kai. Amma Adamu da Hauwa’u suka fāɗa cikin zunubi, kuma ba su cika duniya ba da ’ya’ya masu adalci, mutane masu tsoron Allah. (Romawa 5:12) Maimakon haka, rayuwar iyali ta sukukuce da wuri, kuma ƙiyayya, mugunta da rashin ‘ƙauna’ suka cika ko’ina, musamman ma a waɗannan “kwanaki na ƙarshe.”—2 Timothawus 3:1-5; Farawa 4:8, 23; 6:5, 11, 12.

2. ’Ya’yan Adamu suna da wane iyawa ne, amma menene ake bukata don a gina iyali mai ƙarfi a ruhaniya?

2 Adamu da Hauwa’u an halicce su cikin surar Allah. Ko da yanzu shi mai zunubi ne, Jehovah ya ba Adamu ikon ya haifi ’ya’ya. (Farawa 1:27; 5:1-4) Kamar ubansu, ’ya’yan Adamu suna iya koyon su bambance tsakanin nagarta da mugunta. Za a koyar da su yadda za su bauta wa Mahaliccinsu da kuma muhimmancin ƙaunarsa da duka zuciyarsu, ransu, azancinsu, da ƙarfinsu. (Markus 12:30; Yohanna 4:24; Yaƙub 1:27) Ban da haka ma, za a koya musu su nuna ‘aikin gaskiya, da son jinƙai, yin tafiya da tawali’u tare da Allah.’ (Mikah 6:8) Amma, da yake su masu zunubi ne, za su bukaci su mai da hankali sosai don su gina iyali mai ƙarfi a ruhaniya.

Ku Rifta Zarafi

3. Ta yaya iyaye za su “rifta zarafi” a renon yara Kirista?

3 A waɗannan miyagun zamanu, za a yi ƙoƙari sosai don yara su zama “masu-ƙaunar Ubangiji” waɗanda da gaske sun “ƙi mugunta.” (Zabura 97:10) Iyaye masu hikima za su “rifta zarafi” don su yi wannan aiki mai wuya. (Afisawa 5:15-17) Idan kai mai yara ne, yaya za ka yi wannan? Na farko, ka kafa muhimman abubuwa, kana mai da hankali ga “mafifitan al’amura,” haɗe da koyar da kuma renon yaranka. (Filibbiyawa 1:10, 11) Na biyu, ka sauƙaƙa yayin rayuwarka. Mai yiwuwa za ka bar ayyuka da ba su da muhimmanci ainun. Ko kuma kana bukatar ka kawar da abubuwa da ke ɗaukan lokaci a kula da su da ba su da muhimmanci. Iyaye Kirista, ba za ku taɓa da-na-sani ba a ƙoƙarin da ake bukata da ku ka yi a renon yara su zama masu tsoron Allah.—Misalai 29:15, 17.

4. Yaya za a sa iyali ta kasance da haɗin kai?

4 Lokaci da ku ka ba da wa yaranku, musamman idan game da al’amura na ruhaniya ne, kwalliya ce da za ta biya kuɗin sabulu kuma hanya mafi kyau ce ta sa iyalin ta zama da haɗin kai. Amma kada ka bar wannan wai sai ka sami zarafin haka. Ka tsara wasu lokatai da za ku shaƙata tare. Wannan ba ya nufin zama a gida ɗaya kawai, kowanne yana abin da yake so. Yara suna girma da kyau in ana ba su lokaci kullum. Ana bukatar a nuna ƙauna sosai da kuma damuwa. Kafin ma su tsai da shawara za su haifi ’ya’ya, ma’aurata dole su yi la’akari da wannan muhimmin hakki. (Luka 14:28) Ta haka ne ba za su ɗauki renon yara aiki mai wuya ba. Maimako, za su ɗauke shi gata mai albarka.—Farawa 33:5; Zabura 127:3.

Ka Koyar ta Magana da Kuma Misali

5. (a) Koya wa yara su ƙaunaci Jehovah zai soma da me? (b) Wane gargaɗi aka ba iyaye a Kubawar Shari’a 6:5-7?

5 Koya wa yaranka su ƙaunaci Jehovah, tana somawa ne da ƙaunarka gare shi. Ƙauna mai ƙarfi ga Allah za ta motsa ka ka bi dukan umurninsa cikin aminci. Wannan ya haɗa da renon yara “cikin horon Ubangiji da gargaɗinsa.” (Afisawa 6:4) Allah ya gargaɗi iyaye su kafa misali wa yaransu, su yi magana da su, kuma su koya musu. Kubawar Shari’a 6:5-7 suka ce: “Za ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan ƙarfinka. Waɗannan zantattuka fa, da ni ke umurce ka yau, za su zauna cikin zuciyarka: kuma za ka koya ma ’ya’yanka su da aniyya, za ka riƙa faɗinsu sa’anda kana zaune cikin gidanka, da sa’anda ka ke tafiya a kan hanya, da sa’anda kana kwanciya, da sa’anda ka tashi.” Ta wajen gargaɗi a kai a kai da maimaitawa, za ka iya saka umurnin Allah cikin yaranka. Da haka, yaranka za su gane kana ƙaunar Jehovah, kuma za su motsa su matso kurkusa da shi su ma.—Misalai 20:7.

6. Ta yaya iyaye za su yi amfani da gaskiyar cewa yara suna koya ta misali?

6 Yara suna da marmarin koyar abu. Masu sauraro ne sosai kuma masu lura ne, yana da sauƙi su yi koyi da misalinka. In sun gani kai ba mai son abin duniya ba ne, wannan yana taimaka musu su koyi yadda za su bi gargaɗin Yesu. Ka koya musu kada su yi alhini game da abin duniya amma su ‘fara biɗan mulkin Allah.’ (Matta 6:25-33) Ta yin taɗi mai ginawa mai kyau game da gaskiyar Littafi Mai Tsarki, ikilisiyar Allah, da kuma dattawa da aka naɗa, koya wa yaranka ka ke su daraja Jehovah kuma su yi godiya ga tanadinsa na ruhaniya. Tun da yake yara suna da saurin lura da abu da ba daidai ba, gargaɗin baki dole ka haɗa da hali da ke nuna godiyarka sosai game da abubuwa na ruhaniya. Abin farin ciki ne yayin da iyaye suka ga cewa misalinsu mai kyau ya sa yaransu sun ƙaunaci Jehovah da dukan zuciyarsu!—Misalai 23:24, 25.

7, 8. Wane misali ne ya nuna amfanin koya wa yara daga yarantaka, kuma waye za a yaba wa don nasarar?

7 Ana iya ganin amfanin koya wa yara a lokacin da suke ƙanana cikin wani labari daga Venezuela. (2 Timothawus 3:15) Ya ƙunshi ma’aurata da su matasa ne, Félix da Mayerlín. Suna hidimar majagaba. Lokacin da suka haifi ɗansu Felito, sun yi iyakacin ƙoƙarinsu a renonsa ya zama mai bauta ta gaskiya ga Jehovah. Mayerlín ta soma karanta wa Felito Litafi Na na Labarun Bible, da Shaidun Jehovah suka buga. Tun yana yaro, Felito kamar ya waye da Musa da wasu mutane da aka nuna a cikin wannan littafin.

8 Da yake ƙarami har ila, Felito ya soma wa’azi da kansa. Ya cika sha’awarsa ya zama mai shelar Mulki, daga baya ya yi baftisma. Da shigewar lokaci, Felito ya zama majagaba na kullum. Iyayensa suka ce: “Yayin da muke ganin ci gaban ɗanmu, mun fahimci cewa hakkinmu ne ga Jehovah da kuma umurninsa.”

Ka Taimaki Yara Su Yi Girma a Ruhaniya

9. Me ya sa ya kamata mu yi godiya don koyarwa ta ruhaniya da muke samu ta ajin bawa mai aminci, mai hikima?

9 Akwai jaridu da yawa, ɗarurruwan littattafai, da dubban hanyar wasa sanarwa na Intane, da ke ba da shawara a yadda za a yi renon yara. Sau da yawa “waɗannan sun saɓa wa juna,” in ji wata jaridar Newsweek a batu na musamman a kan yara. “Kana ƙara rikicewa yayin da sanarwa da ka ke tunanin za ka amince da ita ta zama ƙarya ce zalla.” Muna godiya cewa Jehovah ya yi tanadi mai yawa don koyarwa da kuma girma a ruhaniyar iyalai! Kana amfani sosai da duka tanadi da aka yi ta wajen ajin bawa mai aminci, mai hikima?—Matta 24:45-47.

10. Ta yaya nazarin Littafi Mai Tsarki mai kyau na iyali ke da amfani ga iyaye da yara?

10 Bukata ɗaya da take da muhimmanci ita ce nazarin Littafi Mai Tsarki na iyali a kai a kai da ake yi a yanayi mai kyau. Don ya zama abu mai wayarwa, mai daɗi, na ban ƙarfafa, ana bukatar shiri mai kyau. Ta wurin yi wa yaransu tambayoyi, iyaye za su iya su san abin da ke zukatansu da azantansu. Hanya ɗaya da za su san ko nazari na iyalinsu yana nasara shi ne ta lura ko duka da suke cikin iyali suna sauraronsa.

11. (a) Waɗanne makasudai iyaye za su iya taimakon yaransu su tsara? (b) Menene ya faru lokacin da wata ’yar Japan ta nace wa makasudinta?

11 Makasudai na nassi ma yana sa iyali ya yi ƙarfi a ruhaniya, ya kamata iyaye su taimake yaransu su tsara su. Makasudai da sun dace sun haɗa da karanta Littafi Mai Tsarki a kai a kai, zama mai shelar bishara kullum, da kuma ci gaba zuwa keɓe kai da baftisma. Wasu makasudai za su iya haɗa da hidimar majagaba ta cikakken lokaci, hidima a Bethel, ko mai wa’azi a ƙasar waje. Yayin da take makarantar firamare, wata yarinya ’yar Japan da sunanta Ayumi ta sa ya zama makasudinta ta yi wa kowa a cikin ajinta wa’azi. Don ta ta da marmarin malamanta da ’yan ajin, ta karɓi izini ta saka littattafai na Littafi Mai Tsarki dabam dabam a laburaren. A sakamakon haka, ta gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki guda 13 a shekaru shida na makarantar ta na firamare. Ɗaya cikin waɗannan ɗaliban Littafi Mai Tsarki da wasu cikin iyalin ɗaliban suka zama Kiristoci da sun yi baftisma.

12. Ta yaya yara za su sami amfani mafi girma daga taro na Kirista?

12 Wani abin da yake da muhimmanci don ruhaniya mai ƙarfi shi ne zuwa taro kullum. Manzo Bulus ya gargaɗi ’yan’uwa masu bi ‘kada su fasa tattaruwansu kamar yadda waɗansu sun saba yi.’ Kada mu saba da wannan, gama yara da manya suna amfana sosai daga halartar taro na Kirista kullum. (Ibraniyawa 10:24, 25; Kubawar Shari’a 31:12) Ya kamata a koya wa yara su saurara sosai. Shirya taro yana da muhimmanci kuma, gama amfani mafi girma yana zuwa daga yin furci. Ko da yaro zai iya soma ta yin wasu furci ko kuma karanta layi kaɗan na izifi, zai fi amfani idan an koya wa yara su nemi amsoshi kuma su furta a nasu kalmomin. Iyaye kuna nuna misalin ta yin furci mai ma’ana ko yaushe? Yana da kyau kuma kowanne cikin iyali yana da nasa Littafi Mai Tsarki, littafin waƙa, da kuma littattafai da ake amfani da shi don tattaunawar Nassi.

13, 14. (a) Me ya sa ya kamata iyaye su fita hidima tare da yaransu? (b) Me zai sa hidimar fage ta kasance da amfani da kuma farin ciki ga yara?

13 Iyaye masu hikima za su ja-gorance yaransu ga bauta wa Jehovah da kuzari na ƙuruciya, suna taimakonsu su sa aikin wa’azi a muhimmiyar sashe na rayuwarsu. (Ibraniyawa 13:15) Sai ta yin wa’azi tare da yaransu ne iyaye za su iya tabbata cewa yaransu za su samu koyarwa da ake bukata su zama masu hidima ‘da babu dalilin kunya garesu, suna rarrabe kalmar gaskiya sosai.’ (2 Timothawus 2:15) To, kai kuma fa? Idan kai mahaifi ko mahaifiya ce, kina taimakon yaranki su shirya hidimar fage? Yin wannan zai sa hidima ta kasance na farin cikin, mai ma’ana, da kuma mai ba da amfani a gare su.

14 Me ya sa yake da muhimmanci iyaye da yaransu su yi wa’azi tare? A wannan hanya, yara za su lura kuma su bi misali mai kyau na iyayensu. A wannan lokacin, iyaye za su lura da hali, ƙoƙari, da iyawar yaransu. Ka tabbata ka tafi tare da yaranka a fannoni dabam dabam na hidima. Idan zai yiwu, kowanne yaro ya samu tasa jakar hidima, kuma a koya masa ko mata ta ko ya ajiye ta da tsabta kuma da kyau. Ta wajen koyarwa a kai a kai da kuma ƙarfafawa, za a gina son hidima da gaske, yara kuma za su ga aikin wa’azi hanya ce ta nuna ƙauna ga Allah da maƙwabta.—Matta 22:37-39; 28:19, 20.

Ka Adana Ruhaniya

15. Da yake adana ruhaniya ta iyali tana da muhimmanci sosai, waɗanne hanyoyi ne za a yi wannan?

15 Adana ruhaniya ta iyali tana da muhimmanci. (Zabura 119:93) Hanya ɗaya ta yin haka ita ce ta tattauna abubuwa na ruhaniya da iyalinka a kowanne zarafi. Kana tattauna ayar Littafi Mai Tsarki na kowacce rana da su? Halinka ne ka gaya musu labarai da ka samu a hidimar fage ko kuma darussa daga sababbin jaridun Hasumiyar Tsaro da Awake!, “in kana tafiya a hanya”? Kana tuna ka gode wa Jehovah cikin addu’a don rayuwa ta kowacce rana da kuma tanadinsa mai yawa “sa’anda kana kwanciya, da sa’anda ka tashi”? (Kubawar Shari’a 6:6-9) Idan yaranka sun ga kana nuna ƙauna ga Allah a kome da ka ke yi, wannan zai taimake su su mai da gaskiya ta zama tasu.

16. Wane amfani ne yake cikin ƙarfafa yara su yi nasu bincike?

16 A wasu lokatai, yara za su bukaci ja-gora don su sha kan matsaloli ko yanayin da ke tasowa. Maimako kana gaya musu abin da za su yi koyaushe, me ya sa ba za ka nuna musu yadda za su san ra’ayin Allah a kan al’amura ta wajen ƙarfafa su su yi nasu bincike ba? Koya wa yara su yi amfani mai kyau da dukan kayayyaki da kuma littattafai da ‘bawa mai aminci’ ke tanadinsu zai taimake su su gina dangantaka ta kusa da Jehovah. (1 Samu’ila 2:21b) Yayin da suka gaya wa waɗanda suke cikin iyali amfanin bincike na Littafi Mai Tsarki da suka yi, yana ƙara sa ruhaniya ta iyali ta yi girma.

Ka Dogara Sosai ga Jehovah

17. Me ya sa ya kamata iyaye gwauraye kada su fid da rai yayin da ya zo ga renon yaransu su zama Kiristoci?

17 Iyaye gwauraye kuma fa? Waɗannan suna fuskantar ƙarin kaluɓale in ya zo ga renon yara. Amma iyaye gwauraye, kada ku yi sanyin gwiwa! Za ku iya nasara, yadda iyaye gwauraye da yawa da suka dogara ga Allah suka yi, a yin biyayya sun yi amfani da gargaɗinsa, kuma sun yi renon yara masu kyau, masu ƙarfi a ruhaniya. (Misalai 22:6) Hakika, Kiristoci da su iyaye gwauraye ne suna bukata su dogara sosai ga Jehovah. Dole ne su kasance da bangaskiya cewa zai yi tanadin taimako.—Zabura 121:1-3.

18. Ga waɗanne bukatu na azanci da na jiki na yaransu ya kamata iyaye su mai da hankali, amma a kan menene za su fi mai da hankali?

18 Iyaye masu hikima sun gane cewa akwai ‘lokacin dariya da lokacin rawa.’ (Mai-Wa’azi 3:1, 4) A gina zuciyar yaro da jiki, ana bukatar hutu da nishaɗi mai kyau daidaitacce. Kaɗe-kaɗe masu ginawa musamman rera waƙoƙin yabo ga Allah zai taimaki yaro ya gina hali mai kyau da zai iya kasancewa da muhimmiyar matsayi a ƙarfafa dangantakarsa da Jehovah. (Kolossiyawa 3:16) Ƙuruciya lokaci ne na shirin zama mutum mai jin tsoron Allah, don jin daɗin rayuwa ya ci gaba har abada a cikin aljanna ta duniya.—Galatiyawa 6:8.

19. Me ya sa iyaye za su kasance da gaba gaɗi cewa Jehovah zai albarkace ƙoƙarin da suke yi wajen renon yaransu?

19 Jehovah yana son duka iyalai Kirista su kasance da ƙarfi a ruhaniya kuma su zama da haɗin kai. Idan muna ƙaunar Allah da gaske kuma muna yin iyakacin ƙoƙarinmu mu yi biyayya da Kalmarsa, zai albarkaci ƙoƙarinmu kuma ya ba mu ƙarfi da muke bukata don mu bi ja-gorarsa da aka hure. (Ishaya 48:17; Filibbiyawa 4:13) Ka tuna cewa zarafi da ka ke da shi yanzu ka koyar kuma ka yi renon yaranka kaɗan ne kuma ba za ka sake samu ba. Ka yi iyakacin ƙoƙarinka ka yi amfani da Kalmar Allah, Jehovah kuma zai albarkaci ƙoƙarinka don ka gina iyali mai ƙarfi a ruhaniya.

Me Muka Koya?

• Me ya sa rifta zarafi yake da muhimmanci sosai a renon yara?

• Me ya sa misali mai kyau daga iyaye ke da muhimmanci?

• Waɗanne hanyoyi masu muhimmanci ne za a taimaki yara su yi girma a ruhaniya?

• Yaya za a adana ruhaniya ta iyali?

[Hotuna a shafuffuka na 16, 17]

Iyalai masu ƙarfi a ruhaniya suna nazarin Kalmar Allah kullum, halartar taron Kirista, kuma suna fita hidima tare

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba