Kiristanci Na Gaskiya Ya Yi Nasara!
“Hakanan maganar Ubangiji ta yawaita da iko ƙwarai, ta yi nasara.”—AYUKAN MANZANNI 19:20.
1. Ka kwatanta haɓakar Kiristanci a ƙarni na farko.
CIKE da ikon ruhu mai tsarki, Kiristoci na farko suka yi shelar maganar Allah da ƙwazo da ba zai karaya ba. Wani ɗan tarihi ya rubuta: “Kiristanci ya yaɗu da sauri na ban mamaki cikin duniyar Roma. A shekara ta 100 wataƙila dukan yankin da ke kewaye da Bahar Maliya yana da tarayyar Kiristoci a cikinsa.”
2. Ta yaya Shaiɗan ya yi ƙoƙari ya yi hamayya da bishara, kuma ta yaya aka annabta wannan?
2 Shaiɗan Iblis ya kasa rufe wa Kiristoci na farko baki. Maimakon haka, ya yi hamayya da muhimmancin bisharar, ta—ridda. Yesu ya annabta wannan a cikin almararsa ta alkama da zawa. (Matta 13:24-30, 36-43) Manzo Bitrus ma ya yi gargaɗi cewa malaman ƙarya za su taso a cikin ikilisiyar, su kawo ɗarika mai halakarwa. (2 Bitrus 2:1-3) Hakazalika, manzo Bulus ya yi gargaɗi takamaimai cewa ridda za ta zo kafin ranar Jehovah.—2 Tassalunikawa 2:1-3.
3. Me ya faru bayan mutuwar manzannin?
3 Bayan mutuwar manzanni, koyarwar arna da falsafa suka zo suka lulluɓe bishara. Kamar yadda aka annabta, koyarwar ƙarya ta tanƙwasa kuma ta gurɓata tsantsar saƙon gaskiya. A hankali, jabun Kirista da ake kira Kiristendam ya lulluɓe na gaskiyar. Ajin limamai ya taso wanda ya yi ƙoƙarin ya hana wa talakoki Littafi Mai Tsarki. Saboda haka adadin waɗanda suka kira kansu Kirista ya ƙaru, bautarsu ba ta da tsarki. Kiristendam suka yaɗu a ƙasashe suka zama manyan ƙungiyoyi da kuma marinjaya a al’adar Yamma, amma ba su da albarkar Allah ko kuma ruhunsa.
4. Me ya sa ƙoƙarin Shaiɗan ya wargaza nufin Allah bai yi nasara ba?
4 Duk da haka, ƙullin Shaiɗan na wargaza nufin Allah ba zai yi nasara ba. Har ma a lokaci mai duhu na ridda, Kiristanci na gaskiya ya kasance tsakanin wasu. Mutane da suka kofi Littafi Mai Tsarki sun mai da hankali sun yi ta daidai. Saboda haka, Littafi Mai Tsarki kansa ya kasance daidai, ko da waɗanda suke da’awar suna da ikon fassara saƙonsa ba su yi shi daidai ba. A cikin ƙarnuka da suka shige da akwai manazara, kamar su Jerome da Tyndale, suka jarumtaka wajen fassara Littafi Mai Tsarki da kuma rarraba Kalmar Allah. Miliyoyin mutane suka sami Littafi Mai Tsarki da kuma iri na Kiristanci, ko da yake jabu ne.
5. Menene annabi Daniel ya annabta game da ‘ilimi na gaskiya’?
5 A ƙarshe, kamar yadda aka annabta a littafin Daniel, ‘ilimi na gaskiya kuma ya ƙaru.’ Wannan ya faru ne a “kwanakin ƙarshe”—lokaci da muke raye a ciki yanzu. (Daniel 12:4) Ruhu mai tsarki ya kai masoya gaskiya a dukan duniya ga sanin Allah da kuma nufinsa. Har bayan ƙarnuka na koyarwar ’yan ridda, maganar Allah ta yi nasara! A yau, ana shelar bisharar a ko’ina, ana kai mutane zuwa begen sabuwar duniya mai faranta rai. (Zabura 37:11) Bari mu bincika wannan haɓaka ta zamani ta maganar Allah.
Haɓaka ta Kalmar Allah a Yau
6. Waɗanne gaskiya ne Ɗaliban Littafi Mai Tsarki suka fahimta a shekara ta 1914?
6 A ƙarshen ƙarni na 19, gaskiyar Littafi Mai Tsarki ya motsa ƙaramin rukuni na Ɗaliban Littafi Mai Tsarki, da aka san su a yau da Shaidun Jehovah. A shekara ta 1914 Littafi Mai Tsarki ya kasance gaskiya gare su. Suka fahimci gaskiya mai ban mamaki game da nufin Allah. Ƙaunar Jehovah da ya aiko Ɗansa zuwa duniya da ta buɗe hanyar samun rai madawwami ya motsa su. Suka zo ga sanin kuma so sunan Allah da kuma mutumtakarsa. Ƙari ga haka, suka gano cewa “zamanan Al’ummai” sun cika, wannan yana nuna cewa lokaci ya yi kusa da Mulkin Allah zai kawo albarka ga ’yan Adam. (Luka 21:24) Wannan bishara ce ƙwarai! Waɗannan gaskiya masu ƙarfi don a gaya wa ko waye a ko’ina. Rayuka suna cikin haɗari!
7. Ta yaya gaskiyar Littafi Mai Tsarki ta yi nasara a zamanin yau?
7 Jehovah ya albarkaci waɗannan shafaffun Kiristoci da ba su shige cikin ludayi ba. A yau, adadin da suka rungumi Kiristanci na gaskiya sun shige miliyan shida. Kalmar Allah ta yaɗu a ƙasashe, domin ana samun Shaidun Jehovah a ƙasashe 235. Bugu da ƙari, Littafi Mai Tsarki ya nuna ƙarfi, domin ya yi nasara bisa dukan wata tangarɗa ta addini da dai sauransu. Wannan wa’azi a dukan duniya ya ƙarfafa tabbacin da ba za a yi musu ba cewa Yesu ya kasance da ikon mulki.—Matta 24:3, 14.
8. Menene wasu suka ce game da haɓakar Shaidun Jehovah?
8 Kamar yadda ’yan tarihi suka yi magana game da haɓaka na ban mamaki na Kiristanci a ƙarni na farko, manazarta da yawa suna magana a kan haɓaka na mutanen Jehovah a zamanin yau. A Amurka, manazarta biyu suka haɗu suka rubuta: “A shekara 75 da ta shige, Shaidun Jehovah suka riƙa ƙaruwa na ban mamaki . . . kuma sun yi haka a dukan duniya.” Wata jarida ta Gabashin Afirka ta ce Shaidun suna cikin “addinai masu haɓaka da wuri da aka sani a duniya kuma da ake daraja su domin bin koyarwar Littafi Mai Tsarki.” Jaridar Katolika na riƙe al’ada, da aka buga a Turai, ta yi magana game da “haɓaka mai girma na Shaidun Jehovah.” Menene ya tallafa aka sami wannan haɓakar?
Ruhu Mai Tsarki Yana Aiki a Yau
9. (a) Menene ainihin dalili da ya sa maganar Allah ta yi nasara a yau? (b) Ta yaya Jehovah ya jawo mutane gare sa?
9 Dalili na musamman da maganar Allah ta yi nasara a yau domin ruhun Jehovah yana aiki ne tuƙuru, kamar yadda yake a ƙarni na farko. Yesu ya ce: “Ba wanda ya iya zuwa wurina, sai dai Uba wanda ya aiko ni ya jawo shi.” (Yohanna 6:44) Waɗannan kalmomin sun nuna cewa Allah yana jawo a hankali waɗanda suke da zuciyar kirki, yana taɓa zuciya. Ta wajen ayyukan wa’azi na Shaidun, Jehovah yana jawo ga hidimarsa “muradin dukan dangogi”—masu tawali’u, mutane masu kama da tumaki na duniya.—Haggai 2:6, 7.
10. Waɗanne irin mutane ne suka yi na’am da maganar Allah?
10 Ruhu mai tsarki bai ƙarfafa mutanen Allah su kai maganarsa zuwa iyakar duniya kawai ba; ya motsa dukan iri-irin mutane su yi na’am da bisharar. Hakika, waɗanda suka rungumi maganar Allah sun fito daga “kowace kabila, da kowane harshe, da al’umma, da iri.” (Ru’ya ta Yohanna 5:9; 7:9, 10) Ana samun su tsakanin attajirai da matalauta, masu ilimi ƙwarai da jahilai. Wasu sun karɓi maganar a lokacin yaƙi da kuma na mugun tsanantawa, yayin da wasu sun yi haka a lokacin zaman lafiya da kwanciyar hankali. A ƙarƙashin kowace irin gwamnati, dukan al’adu, daga sansanin fursuna zuwa fada, maza da mata suna na’am da bisharar.
11. Yaya ruhu mai tsarki yake aiki a rayuwar mutanen Allah, kuma wane bambanci ne ake gani?
11 Duk da bambanci na ban mamaki tsakanin mutanen Allah, suna zama tare cikin salama da juna. (Zabura 133:1-3) Wannan ya ƙara ga tabbacin cewa ruhu mai tsarki yana aiki a rayuwar waɗanda suke bauta wa Allah. Ruhunsa iko ne mai ƙarfi da ke sa bayinsa suke nuna ƙauna, farin ciki, salama, kirki, da wasu halaye masu kyau. (Galatians 5:22, 23) A yau, mun gano ƙwarai abin da annabi Malachi ya annabta shekaru aru aru: “Za ku . . . rarrabe tsakanin adali da mugu, tsakanin wanda ya ke bauta ma Allah da wanda ba ya bauta masa.”—Malachi 3:18.
Kalmar Allah ta Yi Nasara ga Ma’aikata Masu Ƙwazo
12. Yaya Shaidun Jehovah suke ji game da aikin wa’azi, kuma yaya suke tsammanin za a karɓi aikin wa’azinsu?
12 Shaidun Jehovah a yau ba masu zuwa coci ba ne kawai. Suna aikin wa’azi ƙwarai. Kamar Kiristoci na ƙarni na farko, suna ba da kansu da son rai su yi nufin Allah, suna ƙoƙarin su taimake wasu su koyi game da alkawuran Mulkin Jehovah. Abokanan aiki ne na Allah, waɗanda cikin jituwa da ruhunsa mai tsarki, suna tara mutane ga hidimar Jehovah. A yin haka, suna nuna jinƙan Jehovah da kuma ƙaunarsa ga ’yan Adam marasa bangaskiya. Suna kuma yin hakan duk da ƙiyayya da ba’a da kuma tsanantawa. Yesu ya shirya mabiyansa ga yadda za a karɓi bisharar. Ya ce: “Bawa ba ya fi ubangijinsa girma ba. Idan suka yi mini tsanani, su a yi maku tsanani kuma; idan suka kiyaye maganata, su a kiyaye taku kuma.”—Yohanna 15:20.
13. Menene ake rashi a Kiristendam da yana da yawa a tsakanin Shaidun Jehovah?
13 Kamani tsakanin Shaidun Jehovah a yau da kuma waɗanda suka rungumi Kiristanci na gaskiya a ƙarni na farko yana burge mu. Wani abin lura shi ne bambanci da ke tsakanin Shaidun Jehovah da Kiristendam a yau. Bayan ya rubuta game da ƙwazo na wa’azi na Kiristoci na farko, wani manazari ya furta baƙin cikinsa: “Sai dai ko an canja rayuwar coci na yau, saboda a sake ɗaukar aikin wa’azi abin da ake gani dole ne ga kowanne Kirista da ya yi baftisma, kuma a goyi bayansa da rayuwa wadda ta fi kyau daga na marasa bangaskiya.” Abin da Kiristendam yake rashi yana nan da yawa tsakanin Shaidun Jehovah! Da akwai bangaskiya rayayya, bangaskiya ta gaske, kuma bangaskiya da take bisa Littafi Mai Tsarki da suke ji dole ne su gaya wa duka waɗanda za su saurara.—1 Timothawus 2:3, 4.
14. Yaya Yesu ya ɗauki hidimarsa, kuma wane hali almajiransa suke nunawa a yau?
14 Yesu ya ɗauki hidimarsa da muhimmanci ƙwarai, ya mai da ita damuwarsa ta farko. Ya gaya wa Bilatus: “Domin wannan an haife ni, domin wannan kuma na zo cikin duniya, domin in bada shaida ga gaskiya.” (Yohanna 18:37) Mutanen Allah suna ji kamar yadda Yesu ya ji. Da gaskiyar Littafi Mai Tsarki a zukatansu, suna ƙoƙarin su nemi hanyoyin da za su gaya wa wasu da yawa iyaka yadda za su iya. Wasu hanyoyin suna bukatar hikima ƙwarai.
15. Ta yaya wasu suka nuna hikima wajen yin wa’azin bishara?
15 A wata ƙasar Amurka ta Yamma, Shaidu suka yi tafiya har zuwa tabkin Kogin Amazon domin su gaya wa mutane gaskiyar. Duk da haka, da tarzoma ta ɓarke a shekara ta 1995, aka hana tafiye-tafiye na mutane a wajajen kogin. Da aniyyar su riƙa ba masu marmari littattafan Littafi Mai Tsarki, Shaidun suka tsai da shawara, suka zuba saƙon a kan ruwa. Suka rubuta wasiƙu suka haɗa da jaridun Hasumiyar Tsaro da kuma Awake! a cikin ƙwalaben roba. Sai su jefa ƙwalaben cikin kogi. Wannan ya ci gaba haka na shekara huɗu da rabi har sai da aka buɗe kogin wa sauran mutane. A dukan bakin kogin, mutane suka yi wa Shaidun godiya domin littattafan. Wata mace da take nazarin Littafi Mai Tsarki ta rungume su da hawaye a idanunta ta ce: “Ina tsammanin ba zan sake ganin ku ba kuma. Amma, da na fara samun littattafai a cikin ƙwalabe, na san cewa ba ku manta da ni ba!” Wasu da suke zama a bakin kogin suka ce sun karanta jaridun a kai a kai. Unguwa da yawa suna da “gidan waya”—inda abubuwa suke taruwa na ɗan lokaci. A nan ne masu marmari suke bincike duk wani “saƙo” daga tabki.
16. Ta yaya ba da kanmu wani lokaci yake buɗe hanyar almajirantarwa?
16 Aikin wa’azin bisharar Jehovah Allah ne yake ja-gorarsa kuma yake goyon bayansa da kuma mala’ikunsa masu ƙarfi. (Ru’ya ta Yohanna 14:6) Idan muka ba da kanmu, yanayi da ba mu yi tsammaninsa ba na almajirantarwa sai ya taso. A Nairobi, Kenya, ’yan’uwa mata biyu a hidimar fage suka gama wa’azi a gidajen da aka ba su. Wata mace ta tunƙare su da farin ciki ta ce: “Ina ta addu’a in haɗu da mutane kamar ku.” Ta kira Shaidun su zo gidanta ba tare da ɓata lokaci ba domin tattaunawa, sai aka fara nazarin Littafi Mai Tsarki da ita a wannan ranar. Me ya sa wannan matar ta tunƙare waɗannan Kiristoci biyun da irin saurin nan? Makonni biyu da suka shige ’yarta ta rasu. Da ta gani wani matashi yana ɗauke da warƙar nan “Akwai Bege ga Matattu Ƙaunatattu?” ta bukace ta ƙwarai, ta roƙi yaron ya ba ta. Ya ƙi, amma ya nuna mata Mashaidin da ya ba shi warƙar. Ba da daɗewa ba matar ta fara ci gaba sosai a ruhaniya kuma ta iya bi da baƙin ciki na yin rashin ’yarta.
Ƙaunar Allah Dole ne ta Yi Nasara
17-19. Wace ƙauna ce Jehovah ya nuna wa ’yan Adam ta wajen fansa?
17 Haɓakar maganar Allah a dukan duniya tana da alaƙa ta kusa da hadayar fansa ta Yesu Kristi. Kamar fansar, aikin wa’azi nuna ƙauna ce na Jehovah ga dukan mutane a ko’ina. An hori manzo Yohanna ya rubuta: “Allah ya yi ƙaunar duniya har ya bada Ɗansa, haifaffe shi kaɗai, domin dukan wanda yana bada gaskiya gareshi kada ya lalace, amma ya sami rai na har abada.”—Yohanna 3:16.
18 Ka yi tunanin ƙauna da Jehovah ya nuna wajen yin tanadin fansar. Allah ya more dangantaka ta kusa da makaɗaicin Ɗansa wanda yake ƙauna na shekaru aru aru, “farkon halittar Allah.” (Ru’ya ta Yohanna 3:14) Yesu yana ƙaunar Ubansa ƙwarai, kuma Jehovah yana ƙaunar Ɗansa, “tun ba a kafa duniya ba.” (Yohanna 14:31; 17:24) Jehovah ya ƙyale ƙaunataccen Ɗansa ya mutu domin mutane su samu rai madawwami. Lalle ƙauna ce mai girma da aka nuna wa ’yan Adam!
19 Yohanna 3:17 ya ce: “Allah ya aiko Ɗan cikin duniya ba domin shi yi ma duniya shari’a ba; amma domin duniya ta tsira ta wurinsa.” Saboda haka, Jehovah ya aiko Ɗansa saƙon ƙauna na ceto, ba na shari’a ba ko na halakarwa. Wannan ya jitu da kalmomin Bitrus: “[Jehovah] ba shi nufin kowa da halaka ba, amma duka su kai ga tuba.”—2 Bitrus 3:9.
20. A wace hanya ce ceto yake da alaƙa da wa’azin bishara?
20 Bayan ya yi tanadin yardajiyar hanyar ceto ta azabta wa kansa, Jehovah yana son mutane da yawa su yi amfani da wannan zarafin. Manzo Bulus ya rubuta: “Dukan wanda za ya kira bisa sunan Ubangiji za ya tsira. Ƙaƙa fa za su kira bisa ga wanda ba su bada gaskiya gareshi ba? kuma ƙaƙa za su bada gaskiya ga wanda ba su ji ba? ƙaƙa za su ji kuwa in ba mai-yin wa’azi ba?”—Romawa 10:13, 14.
21. Yaya za mu ji game da zarafi na saka hannu cikin aikin wa’azi?
21 Babban gata ce a saka hannu cikin wannan aikin wa’azi na duniya duka da kuma koyarwa! Ba aiki ba ne mai sauƙi, duk da haka Jehovah yana farin ciki idan ya lura cewa mutanensa suna rayuwa cikin aminci bisa gaskiyar kuma suna gaya wa wasu bisharar! Saboda haka, ko yaya yanayinka ya ke, ka ƙyale ruhun Allah da kuma ƙaunarsa da take zuciyarka ta motsa ka ka saka hannu cikin wannan aikin. Ka tuna cewa abin da muke gani ake kammala a duniya duka yana ba da tabbacin cewa Jehovah Allah zai cika alkawarinsa ba da daɗewa ba na kawo “sababbin sammai da sabuwar duniya” mai ɗaukaka inda “adalci ya ke zaune.”—2 Bitrus 3:13.
Ka Tuna?
• Me ya sa ridda ba ta sa masu wa’azin bishara su yi tsit ba?
• Ta yaya kalmar Allah ta yi nasara a zamaninmu?
• A waɗanne hanyoyi ne ruhun Allah yake aiki a yau?
• Ta yaya fansa take da alaƙa da wa’azin bishara?
[Hotuna a shafi na 25]
JEROME
TYNDALE
GUTENBERG
HUS
[Inda aka Dauko]
Gutenberg da Hus: Daga littafin nan The Story of Liberty, 1878
[Hoto a shafi na 25]
Ɗaliban Littafi Mai Tsarki suna shelar bishara a shekaru na 1920
[Graph/Hoto a shafi na 26]
Haɓaka a adadin masu shelar Mulki a ƙarni na 20
Matsakaicin adadin Masu Shela (miliyoyi)
6.0
5.5
5.0
4.5
4.0
3.5
3.0
2.5
2.0
1.5
1.0
0.5
1900
1910
1920
1930
1940
1950
1960
1970
1980
1990
2000
[Hotuna a shafuffuka na 26, 27]
A dukan duniya mutane suna martani ga bisharar
[Hoto a shafi na 28]
Kamar hadayar fansar Yesu Kristi, aikin wa’azin yana ɗaukaka ƙaunar Allah