Biyayya—Muhimmin Darasi ne na Yarantaka?
“IYAYE Suna Son Yara ne na Musamman, ba Yara Masu Biyayya ba Kawai.” Jigon wata jarida ke nan. Wannan ɗan rahoto sakamakon bincike ne da aka yi a New Zealand, wanda ya nuna “kashi 22 bisa ɗari ne kawai suka ga ya dace a koya wa yara biyayya daga gida.” Binciken kuma ya gano cewa iyaye sun ga ya fi muhimmanci a koya wa yara al’amura kamar su halin kirki, ’yancin kai, da kuma cika hakki.
A cikin wannan zamani na nuna ikon son rai da kuma son kai, ba abin mamaki ba ne cewa yawancin mutane suna tantama a kan ra’ayin biyayya da kuma koyar da yara. Amma anya, za a ɗauki biyayya daga yarantaka banza, cewa yayin dā ne kuma ba a yinsa kuma ba? Ko kuma yana cikin muhimman darussa da yara za su iya koya kuma su amfana? Mafi muhimmanci ma, yaya Jehovah Allah, Tushen iyali, yake ɗaukan yin biyayya ga iyaye, kuma menene wasu fa’idodi da ke zuwa daga irin biyayyar nan?—Ayukan Manzanni 17:28; Afisawa 3:14, 15.
“Wannan Daidai Ne”
Manzo Bulus ya rubuta zuwa ga ikilisiyar Kirista na ƙarni na farko a Afisas: “Ku ’ya’ya, ku yi biyayya da waɗanda suka haife ku cikin Ubangiji: gama wannan daidai ne.” (Afisawa 6:1) Saboda haka, dalili na musamman na yin biyayyar nan shi ne cewa cikin jituwa yake da mizanan Allah na abin da ke daidai. Yadda Bulus ya ce, “wannan daidai ne.”
Daidai da haka, mun lura cewa Kalmar Allah ta kwatanta horo daga iyaye cikin ƙauna sifar kyau ce, “kalankuwa mai-ado a kanka. Ƙungu kuma a wuyanka,” kuma “abin yarda ne cikin Ubangiji.” (Misalai 1:8, 9; Kolossiyawa 3:20) Idan aka saɓa wannan, rashin biyayya ga iyaye zai jawo rashin tagomashin Allah.—Romawa 1:30, 32.
“Domin Ka Sami Alheri”
Bulus ya nuna wani amfanin biyayya da ya rubuta: “Ka girmama ubanka da uwarka ita ce doka ta fari tare da wa’adi, domin ka sami alheri, ka yi tsawon rai kuma cikin ƙasan.” (Afisawa 6:2, 3; Fitowa 20:12) A waɗanne hanyoyi ne biyayya ga iyaye take kawo wa mutum alheri?
Da farko, ba gaskiya ba ne cewa iyaye sun girme mu kuma sun fi mu da hikima? Ko da yake ba za su san abubuwa da yawa game da kwamfuta da kuma wasu darussa da ake koyarwa a makaranta ba, sun san abubuwa da yawa game da rayuwa da kuma jimiri da matsalolin rayuwa. Amma kuma matasa, ba su da daidaitaccen tunani da ake samu ta wajen manyanta. Saboda haka, sukan yi hanzari wajen tsai da shawara, yawanci suna bin mummunar sha’awar tsararsu da ke jawo musu wahala. A zancen gaskiya, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Wauta tana nan ƙunshe a zuciyar yaro.” Menene maganinsa? “Sandar horo za ta kore masa ita nesa.”—Misalai 22:15.
Fa’idojin biyayya ya ɗara dangantakar yara da iyaye kawai. Domin a sami zaman jama’a mai kyau mai amfani, dole ne a sami haɗin kai, wanda yake bukatar yin biyayya. Alal misali, cikin aure, yana nufin kasancewa a shirye don a yarda da wani abu, maimakon kasancewa da yawan biɗa da kuma ƙin damuwa da yadda wasu suke ji, yake kawo salama, jituwa, da kuma farin ciki. Domin a sami nasara wajen kowanne irin aiki, ana bukatar yin biyayya da waɗanda suke da iko. A zancen dokoki da sharuɗan gwamnati, biyayya ba kawai takan ’yantar da mutum daga horo ba amma kuma za ta kāre mutum.—Romawa 13:1-7; Afisawa 5:21-25; 6:5-8.
Matasa da suke rashin biyayya ga iko sau da yawa ba sa dace da zaman jama’a ba. Bambancin, darasi da aka koyi daga yarantaka a kan yi amfani da shi a duk rayuwan mutum. Lalle yana da amfani a koyi wannan daga yarantaka!
Lada Mai Girma ta Yin Biyayya
Ba kawai biyayya tana kawo farin ciki ta iyali da wasu fa’idoji masu daɗewa ba amma kuma tana tanadar da tushen da za a gina dangantaka ta musamman—tsakanin mutum da Mahaliccinsa. Wanda shi ne ‘Mahalicci Mai Girma’ wanda shi ne “maɓulɓular rai,” Jehovah Allah ya cancanci biyayyarmu ta duka duka.—Mai-Wa’azi 12:1; Zabura 36:9.
Kalmar nan “biyayya” an ambata ta sau da yawa cikin Littafi Mai Tsarki. Ƙari ga haka, da akwai wasu nuni ga dokokin Allah, ƙa’idodi, umurnai, hukuntai, da kuma sharuɗa, da duka ana bukatar biyayya. Babu shakka cewa yadda Allah yake ɗaukar biyayya aba ce da ake bukata a gare mu don samun tagomashinsa. Hakika, biyayya mataki ne na gina dangantaka da Jehovah. (1 Samu’ila 15:22) Abin baƙin ciki ne, yadda mutane suke, nufinsu ba na yin biyayya ba amma na rashin biyayya. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Tunanin mutum mugunta ne tun daga ƙuruciyarsa.” (Farawa 8:21) Saboda haka, za a koyi darasin biyayya ba daga yarantaka kaɗai ba amma a duk rayuwa. Yin haka yana kawo lada mai girma.
Ka tuna, cewa manzo Bulus ya ce, umurnin a yi biyayya ga iyaye yana ɗauke da alkawari biyu, wato, “domin ka sami alheri, ka yi tsawon rai kuma cikin ƙasan.” An tabbatar da wannan alkawarin kuma a Misalai 3:1, 2: “Ɗana kada ka manta da koyarwata: amma ka bar zuciyarka ta kiyaye dokokina: gama za su ƙara maka tsawon kwanaki, da shekaru na rai, da salama kuma.” Lada mai girma ga waɗanda suka yi biyayya ita ce dangantaka da Jehovah yanzu da kuma rai na har abada a sabuwar duniya ta salama.—Ru’ya ta Yohanna 21:3, 4.
[Hoto a shafi na 31]
Biyayya tana kawo dangantaka ta farin ciki cikin iyali, a wajen aiki, kuma tare da Jehovah