“Maganar Allah Kuwa Ta Yawaita”
“Ya aike da umurninsa a bisa duniya; maganatasa ta kan yi gudu da sauri ƙwarai.”—ZABURA 147:15.
1, 2. Wane aiki Yesu ya bai wa almajiransa, kuma menene wannan ya ƙunsa?
ƊAYA daga cikin fitattun annabce-annabce na Littafi Mai Tsarki an same shi a Ayukan Manzanni 1:8. Ba da daɗewa ba kafin ya tafi sama, Yesu ya gaya wa mabiyansa masu aminci: “Za ku karɓi iko lokacinda Ruhu Mai-tsarki ya zo bisanku; za ku zama shaiduna . . . har kuma iyakan duniya.” Wannan lalle babban aiki ne!
2 A yi shelar maganar Allah a dukan duniya, kaluɓale ne ga almajirai da aka ba su aikin, su da kalilan ne. Ka yi la’akari da abin da wannan ya ƙunsa. Dole ne su taimake mutane su fahimci bisharar Mulkin Allah. (Matthew 24:14) Yin shaidar Yesu tana bukatar saka hannu tare da wasu a koyarwarsa mai ƙarfi da kuma yin bayanin aikinsa cikin nufin Jehovah. Bugu da ƙari, aikin ya haɗa da almajirantar da mutane da kuma yi musu baftisma. Kuma za a yi wannan a dukan duniya!—Matta 28:19, 20.
3. Game da menene Yesu ya ba wa mabiyansa tabbaci, kuma yaya suka amsa ga aikin da aka ba su?
3 Duk da haka, Yesu ya tabbatar wa mabiyansa cewa ruhu mai tsarki zai kasance tare da su wajen yin aikin da ya ba su. Saboda haka, komin girman aikin da kuma ƙoƙari babu karaya na ’yan hamayya su sa su yi tsit, almajiran Yesu na farko sun yi nasara wajen cika aikin da ya ba su. Rubutaccen tarihi ne wannan babu musu.
4. Ta yaya ƙaunar Allah ta bayyana a umurnin da ya bayar a yi wa’azi kuma a koyar da wasu?
4 Wa’azi da kuma koyarwa a dukan duniya nuna ƙauna ne na Allah ga waɗanda ba su san shi ba. Ya ba su damar matsowa kusa da Jehovah domin ya gafarta musu zunubansu. (Ayukan Manzanni 26:18) Umurnin da ya bayar a yi wa’azi da kuma a koyar ya nuna ƙaunar Allah ga waɗanda suke sanar da saƙon, tun da ya ba su damar furta ibadarsu ga Jehovah kuma su nuna ƙaunarsu ga ’yan’uwansu ’yan Adam. (Matthew 22:37-39) Manzo Bulus ya daraja hidimar Kirista da ya ce da ita “kaya mai-daraja.”—2 Korinthiyawa 4:7.
5. (a) A ina muka sami tarihi mafi tabbaci na Kiristoci na farko, kuma wace haɓaka aka kwatanta a ciki? (b) Me ya sa littafin Ayukan Manzanni yana da ma’ana ga bayin Allah a yau?
5 Tabbacaccen tarihi na aikin wa’azi na Kiristoci na farko an same shi ne a cikin hurarren littafin Ayukan Manzanni, da almajiri Luka ya rubuta. Tarihi ne na haɓaka kuma mai ban mamaki. Wannan haɓaka na sanin Kalmar Allah ta tuna mana Zabura 147:15, da ta ce: “[Jehovah] ya aike da umurninsa a bisa duniya; maganatasa ta kan yi gudu da sauri ƙwarai.” Tarihin Kiristoci na farko, da aka ƙarfafa su da ruhu mai tsarki, yana faranta mana rai, kuma yana da ma’ana a gare mu a yau ƙwarai. Shaidun Jehovah suna yin wannan aiki na wa’azi da kuma almajirantarwa, amma ya fi faɗaɗawa. Mu ma muna fuskantar matsala kusa da wadda Kiristoci na ƙarni na farko suka fuskanta. Yayin da muka bincika yadda Jehovah ya albarkace kuma ya ƙarfafa Kiristoci na farko, bangaskiyarmu ga goyon bayansa za ta yi ƙarfi.
Haɓaka a Adadin Almajirai
6. Wane furci ne game da haɓaka ya bayyana sau uku a littafin Ayukan Manzanni, kuma me yake nufi?
6 Hanya ɗaya ta bincika cikar Ayukan Manzanni 1:8 ita ce ta yin la’akari da furcin nan “maganar Allah kuwa ta yawaita,” furci da ya bayyana da ɗan bambanci kaɗan, sau uku kawai cikin Littafi Mai Tsarki kuma dukansu an same su cikin littafin Ayukan Manzanni. (Ayukan Manzanni 6:7; 12:24; 19:20) “Maganar Ubangiji,” ko “maganar Allah,” a waɗannan ayoyin tana nufin bishara—gaskiya ta Allah mai motsawa, rayayya, saƙo mai iko da yake canja rayuwar waɗanda suka karɓe shi.— Ibraniyawa 4:12.
7. Ga menene haɓakar kalmar Allah take da alaƙa a Ayukan Manzanni 6:7, kuma menene ya faru a ranar Fentakos na shekara ta 33 A.Z.?
7 Magana ta farko da aka yi game da haɓakar kalmar Allah a Ayukan Manzanni 6:7 ne. A nan mun karanta: “Maganar Allah kuwa ta yawaita; yawan masu-bi kuma cikin Urushalima ya riɓanɓanya ƙwarai; babban taro kuma na malamai suka yi biyayya ga imanin.” A nan haɓaka tana da alaƙa da yawaitar almajirai. Da farko, a ranar Fentakos na shekara ta 33 A.Z., an zuba ruhu mai tsarki na Allah a kan almajirai 120 da suka taru a ɗakin bene. Manzo Bitrus ya gabatar da jawabi mai motsawa, cikin waɗanda suka saurara, wasu 3,000 suka zama masu bi a wannan ranar. Lalle an yi hayaniya kam, lokacin da dubban mutane suka je tabki ko kuma tabkuna a ciki ko kuma wajen Urushalima domin su yi baftisma cikin sunan Yesu, mutumin da aka rataye kamar mai laifi kwanaki 50 da suka gabata.—Acts 2:41.
8. Ta yaya adadin almajirai ya ƙaru a shekarun da suka biyo bayan Fentakos na shekara ta 33 A.Z.?
8 Wannan mafari ne kawai. Ƙoƙarin shugabannan addinin Yahudawa su murje aikin wa’azi ya zama banza. Ga baƙin cikin waɗannan shugabannan, “Ubangiji kuma yana tattarawa yau da gobe [ga almajirai] waɗanda a ke cetonsu.” (Ayukan Manzanni 2:47) Ba da daɗewa ba, “yawan mutane ya kai wajen hamsa.” Bayan haka, “masu-bada gaskiya kuma suka ƙara daɗuwa ga Ubangiji, taro mai-girma ne na maza da mata.” (Ayukan Manzanni 5:14, 15) Game da abin da ya faru daga gaba, mun karanta: “Ikilisiya fa ta sami salama, tana ginuwa, cikin dukan Yahudiya da Galili da Samariya; tana tafiya cikin tsoron Ubangiji, bisa ga ta’aziyar Ruhu Mai-tsarki kuma, sai ta yawaita.” (Ayukan Manzanni 9:31) Bayan wasu shekaru, wataƙila kusan shekara ta 58 A.Z., an yi magana game da “dubban mutane waɗanda sun bada gaskiya.” (Ayukan Manzanni 21:20) A wannan lokacin kuma, akwai mutane na Al’ummai da yawa da suka ba da gaskiya.
9. Yaya za ka kwatanta Kiristoci na farko?
9 Wannan ƙarin adadin, yawancin domin waɗanda suka tuba ne. Addinin sabo ne—amma da akwai ƙwazo. Ban da zama mabiya kawai na coci, almajiran suna ba da kansu sosai ga Kalmar Jehovah, da yake wasu lokatai sun koyi gaskiya daga waɗanda aka tsananta musu ne ƙwarai. (Ayukan Manzanni 16:23, 26-33) Waɗanda suka karɓi Kiristanci sun yi haka ne bisa dalilai, shawara ce mai hujja. (Romawa 12:) An ilimantar da su a hanyar Allah; gaskiya tana tunaninsu da zuciyarsu. (Ibraniyawa 8:10, 11) A shirye suke su mutu domin abin da suka gaskata.—Ayukan Manzanni 7:51-60.
10. Wane hakki ne Kiristoci na farko suka karɓa, kuma wane makamancinsa muke da shi a yau?
10 Waɗanda suka rungumi koyarwar Kiristoci sun fahimci hakkinsu su gaya wa wasu gaskiyar. Wannan ya ƙara ga ƙarin adadinsu. Wani manazarin Littafi Mai Tsarki ya ce: “Yin bishara ba a ɗauke ta aikin mai wa’azi ba ko wani mai ƙwazo sosai da aka naɗa. Wa’azi aiki ne kuma hakki ne na dukan waɗanda suke Coci. . . . Yadda Kiristoci suke kai wajen dukan jama’a da nisa abin ƙarfafa addini ne tun daga farko.” Ya daɗa rubutawa: “Wa’azi ainihi shi ne ran Kiristoci na farko.” Haka yake ga Kiristoci na gaskiya a yau.
Yaɗuwa a Ƙasashe
11. Wace irin haɓaka ce aka kwatanta a cikin Ayukan Manzanni 12:24, kuma yaya wannan ya faru?
11 Magana ta biyu game da haɓakar maganar Allah an same ta cikin Ayukan Manzanni 12:24: “Maganar Allah tana daɗuwa, tana riɓanɓanya.” A nan furcin yana da alaƙa da yaɗuwa a ƙasashe. Duk da hamayyar gwamnati, aiki ya ci gaba da girma. Da farko an zuba ruhu mai tsarki a Urushalima, kuma daga nan kalmar ta yaɗu da wuri. Tsanantawa a Urushalima ta yi watsi da almajiran zuwa yankunan Yahudiya da kuma na Samariya. Menene sakamakon wannan? “Su fa da suka watse suka yi tafiya ko’ina, suna wa’azin kalmar.” (Ayukan Manzanni 8:4) An umarci Filibbus ya yi wa wani mutum wa’azi, bayan ya yi baftisma ya kai saƙon Habasha. (Ayukan Manzanni 8:26-28, 38, 39) Nan da nan gaskiya ta yi jijiya a Ludda da Ƙasar Sarona, da kuma Yafa. (Ayukan Manzanni 9:35, 42) Daga baya, manzo Bulus ya yi tafiye-tafiye na mil dubbai a ƙasa da kuma teku, yana kafa ikilisiyoyi a dukan ƙasashen wajajen Jar Teku. Manzo Bitrus ya je Babila. (1 Bitrus 5:13) Cikin shekara 30 bayan an zuba ruhu mai tsarki a Fentakos, Bulus ya rubuta cewa bishara “wadda aka yi wa’azinta cikin dukan halitta da ke ƙarƙashin sama,” wataƙila yana nufin duniya da aka sani a lokacin.—Kolossiyawa 1:23.
12. Ta yaya ’yan adawa da Kiristanci ma suka yarda da yaɗuwar maganar Allah a ƙasashe?
12 Har ’yan adawa da Kiristanci sun yarda cewa maganar Allah ta yi jijiya cikin dukan Daular Roma. Alal misali, Ayukan Manzanni 17:6 ta ba da labari cewa a Tasalunika, arewacin Hellas, ’yan adawa suka ta da murya suna cewa: “Waɗannan mutane waɗanda sun birkitarda duniya, sun zo nan kuma.” Bugu da ƙari, a farkon ƙarni na biyu, Pliny the Younger ya rubuta zuwa ga Daula Trajan na Roma daga Bithiniya game da Kiristanci. Ya yi ƙara: “Bai tsaya a cikin biranen ba kawai, amma ya yaɗa lalatarsa tsakanin ƙauyuka da ƙasashen da muke maƙwabtaka.”
13. A wace hanya ce yaɗuwa a ƙasashe ta nuna ƙaunar Allah ga ’yan Adam?
13 Wannan yaɗuwar a ƙasashe ta nuna ƙauna ce mai zurfi ta Jehovah ga ’yan Adam da za a iya ’yantarwa. Da Bitrus ya lura cewa ruhu mai tsarki ya bayyana a bisa Karniliyas mutumin Al’umma, ya ce: “Hakika na gane Allah ba mai-tara ba ne: amma a cikin kowace al’umma, wanda ya ke tsoronsa, yana aika adalci kuma, abin karɓa ne gareshi.” (Ayukan Manzanni 10:34, 35) Hakika, bishara ta kasance kuma saƙo ne ga dukan mutane, kuma haɓakar maganar Allah a ƙasashe ta ba mutane a ko’ina damar su yi martani ga ƙaunar Allah. A wannan ƙarni na 21, maganar Allah ta yaɗu a zahiri zuwa dukan ɓangarorin duniya.
Haɓaka da ta Yi Nasara
14. Wace irin haɓaka ce aka kwatanta a Ayukan Manzanni 19:20, kuma bisa menene maganar Allah ta yi nasara?
14 Magana ta uku game da haɓaka ta maganar Allah ta bayyana a Ayukan Manzanni 19:20: “Hakanan maganar Ubangiji ta yawaita da iko ƙwarai, ta yi nasara.” Ainihin kalmar Helenanci da aka fassara “nasara” tana nufin “yin amfani da ƙarfi.” Ayoyi na baya sun ba da labarin cewa mutane da yawa a Afisas sun zama masu bi, kuma wasu da suke yin sihiri sun ƙona takardunsu na sihiri a idanun dukan mutane. Saboda haka, maganar Allah ta yi nasara bisa koyarwar addinan ƙarya. Bisharar kuma ta yi nasara bisa wasu tangarɗa, kamar su tsanantawa. Babu abin da zai tare ta. A nan har ila, mun ga kamani da Kiristanci na gaskiya na zamaninmu.
15. (a) Menene ɗan tarihin Littafi Mai Tsarki ya rubuta game da Kiristoci na farko? (b) Ga wa almajiran suka yaba wa game da nasararsu?
15 Manzanni da wasu Kiristoci na farko sun yi shelar maganar Allah da ƙwazo. Game da su wani ɗan tarihin Littafi Mai Tsarki ya lura: “Idan mutane suna da nufin yin magana game da Ubangijinsu, suna samun hanyoyi da yawa na yin haka. Hakika, abin da ke motsa waɗannan maza da mata ne ya burge mu fiye da hanyar da suke yin haka.” Duk da haka, waɗannan Kiristoci na farko sun fahimci cewa nasara da suka yi a hidima bai dangana bisa ƙoƙarinsu kawai ba. Umurni ne daga Allah su yi aikin, kuma suna da goyon baya daga Allah su gama aikinsu. Haɓaka ta ruhaniya ta zo ne daga wurin Allah. Manzo Bulus ya yarda da haka a wasiƙarsa zuwa ga ikilisiyar Koranti. Ya rubuta: “Ni na dasa, Afolos ya yi ban ruwa; amma Allah ne ya bada amfani. Gama mu abokan aiki na Allah ne.”—1 Korinthiyawa 3:6, 9.
Ruhu Mai Tsarki Yana Aiki
16. Menene ya nuna cewa ruhu mai tsarki ya ba da ƙarfi ga almajiran su yi magana da gaba gaɗi?
16 Ka tuna cewa Yesu ya tabbatar wa almajiransa cewa ruhu mai tsarki ya yi aiki wajen haɓaka maganar Allah kuma cewa ruhu mai tsarki ya ba almajiran iko a aikinsu na wa’azi. (Ayukan Manzanni 1:8) Ta yaya wannan ya faru? Ba da daɗewa ba bayan an zubo da ruhun a kan almajiran a Fentakos, Bitrus da Yohanna aka yi sammacinsu gaban Kotun Yahudawa, babban kotu a ƙasar, waɗanda alƙalanta suke da hakkin kashe Yesu Kristi. Shin manzanni za su yi rawar jiki ne a gaban wannan babban taro mai hamayya? Ko kaɗan! Ruhu mai tsarki ya ƙarfafa Bitrus da Yohanna suka yi magana da gaba gaɗi, har masu adawa da su suka cika da mamaki, suka “ɗauki zobe a kansu dā suna tare da Yesu.” (Ayukan Manzanni 4:8, 13) Ruhu mai tsarki kuma ya sa Istafanus ya yi wa’azi da gaba gaɗi a babban Kotun. (Ayukan Manzanni 6:12; 7:55, 56) Da farko, ruhu mai tsarki ya motsa almajiran su yi wa’azi da gaba gaɗi. Luka ya ba da rahoto: “Sa’anda suka yi addu’a, wurin ya raurawa inda su ke a tattare; dukansu suka cika da Ruhu Mai-tsarki, suka faɗi maganar Allah da ƙarfinzuciya.”—Ayukan Manzanni 4:31.
17. A waɗanne hanyoyi ne ruhu mai tsarki ya taimaki almajiran a hidimarsu?
17 Ta wajen ruhunsa mai tsarki mai iko, Jehovah tare da Yesu da aka tashe shi daga matattu, suka ja-goranci aikin wa’azi. (Yohanna 14:28; 15:26) Lokacin da aka zuba ruhu mai tsarki bisa Karniliyas, ’yan’uwansa, da abokanansa na kusa, manzo Bitrus ya fahimci cewa mutanen Al’umma marasa kaciya sun cancanci su yi baftisma cikin sunan Yesu Kristi. (Ayukan Manzanni 10:24, 44-48) Daga baya, ruhun ya yi aiki wajen naɗa Barnaba da Shawulu (manzo Bulus) domin aikin wa’azi a ƙasashen waje da kuma gaya musu wajajen da za su je da inda ba za su je ba. (Ayukan Manzanni 13:2, 4; 16:6, 7) Ya ja-goranci shawarar da manzanni da dattawa suka tsai da ita a Urushalima. (Ayukan Manzanni 15:23, 28, 29) Ruhu mai tsarki ya kuma ja-goranci naɗa dattawa a ikilisiya ta Kirista.—Ayukan Manzanni 20:28.
18. Ta yaya Kiristoci na farko suka nuna ƙauna?
18 Ƙari ga haka, ruhu mai tsarki ya bayyana kansa a cikin Kiristocin kansu, yana ba da iri na ibada, irin su ƙauna. (Galatiyawa 5:22, 23) Ƙauna ta motsa almajiran su raba abin da suke da shi da juna. Alal misali, bayan Fentakos na shekara ta 33 A.Z., sun kafa asusu guda don su biya bukatun almajiran a Urushalima. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Daga cikinsu babu wanda ya rasa: gama iyakacin waɗanda su ke ma’abutan gonaki da gidaje suka sayarda su, suka kawo tamanin abin da aka sayar, suka ajiye a ƙafafun manzannin; aka rarraba ma kowane ɗaya, daidai bukatar kowa.” (Ayukan Manzanni 4:34, 35) Wannan ƙauna ba ga ’yan’uwa masu bi ba ne kawai amma ta kai ga wasu, ta hanyar yi musu bishara da kuma wasu ayyukan alheri. (Ayukan Manzanni 28:8, 9) Yesu ya ce ƙauna ta sadaukar da kai ce za ta bayyana mabiyansa. (Yohanna 13:34, 35) Babu shakka, hali mai kyau na ƙauna yana jawo mutane ga Allah kuma ya tallafa wajen haɓaka a ƙarni na farko kamar yadda take yi a yau.—Matta 5:14, 16.
19. (a) A waɗanne hanyoyi uku ne maganar Jehovah ta haɓaka a ƙarni na farko? (b) Me za mu bincika a talifi na gaba?
19 Furcin nan, “ruhu mai tsarki” a duka duka ya bayyana sau 41 a littafin Ayukan Manzanni. Hakika, haɓaka ta Kiristoci na gaskiya tana da alaƙa da iko da kuma ja-gorar ruhu mai tsarki. Adadin almajirai ya ƙaru, kalmar Allah ta yaɗu zuwa wajaje da yawa, kuma ta yi nasara bisa addinai da falsafa na wannan zamanin. Wannan haɓaka na ƙarni na farko yana da kamani a ayyukan Shaidun Jehovah a yau. A talifi na gaba, za mu bincika haɓaka mai ban sha’awa na maganar Allah a zamanin yau.
Ka Tuna?
• Ta yaya Kiristoci na farko suka ƙaru a adadinsu?
• A wace hanya ce maganar Allah ta yaɗu a ƙasashe?
• Ta yaya maganar Allah ta yi nasara a ƙarni na farko?
• Wane aiki ruhu mai tsarki ya yi wajen haɓakar maganar Allah?
[Inda Aka Ɗauko Hoto da ke shafi na 20]
A sama ta dama: Sabon fitar Birnin Urushalima a lokacin Haikali na Biyu - da ke wajen ƙasar Holyland Hotel, Urushalima
[Hoto a shafi na 22]
Filibbus ya yi wa Bahabashe wa’azi, yaɗa bishara a ƙasashe
[Hoto a shafi na 23]
Ruhu mai tsarki ya ja-goranci manzanni da dattawa a Urushalima