Littafi Mai Tsarki—Littafin Rayuwa
“MAGANAR Allah rayayyiya ce, mai ƙarfin aiki, ta fi kowane takobi kaifi, . . . tana kuma iya rarrabe tunanin zuciya da manufa tata.” (Ibraniyawa 4:12) Wannan kwatancin abin da Kalmar Allah za ta iya yi babu shakka ya nuna cewa Littafi Mai Tsarki ba littafi ba ne kawai mai kyau.
“Saƙonsa yana da muhimmanci a rayuwarmu kamar yadda numfashi yake da muhimmanci,” haka wani marubucin addini ya ce a taƙaice. Sai ya daɗa: “Idan ka yi la’akari da bukatarmu ta warkarwa a yau kuma ka karanta Littafi Mai Tsarki da wannan a zuci, za ka samu sakamako mai ban mamaki.” Kamar fitila mai haskakawa, Littafi Mai Tsarki yana haskakawa a kan abubuwa masu wuyan ganewa da kuma matsaloli na rayuwar zamani.—Zabura 119:105.
Hakika, hikima da aka furta a cikin Littafi Mai Tsarki tana da ikon mulmula tunaninmu, ta taimake mu mu magance matsaloli, mu inganta rayuwarmu, kuma ya cika mu da basirar yadda za mu bi da yanayi da ba za mu iya canjawa ba. Mafi muhimmanci, Littafi Mai Tsarki yana sa mu san Allah kuma mu ƙaunace shi.
Littafi da Yake ba da Ma’ana
Mawallafin Littafi Mai Tsarki, Jehovah Allah, ya ‘san dukan hanyoyinmu.’ Ya san bukatunmu na jiki, zuci da kuma na ruhaniya fiye da yadda ma mu muka sani. (Zabura 139:1-3) Da hikima, ya sanya iyaka ga halin mutane. (Mika 6:8) Hikima ce mu yi ƙoƙarin fahimtar waɗannan iyaka da kuma ja-gora domin mu koyi rayuwa ta hakan. Albarka ta tabbata ga mutumin da “yana jin daɗin karanta shari’ar Allah,” in ji mai Zabura. “Yakan yi nasara a dukan abin da ya yi.” (Zabura 1:1-3) Irin wannan damar babu shakka ta kai mu bincike ta.
Maurice, wani malamin makaranta da ya yi murabus, ya yarda cewa Littafi Mai Tsarki yana da amfani wajen tarihi da kuma adabi. Duk da haka, ya yi shakkar cewa hurarre ne daga Allah. Bayan ya ji bayani game da abin da ya sa Allah ya ba da rubucacciyar Kalmarsa ga mutane, Maurice ya bincika annabce-annabce na Littafi Mai Tsarki. Lokacin da yake saurayi ya karanta tarihin dā, adabi, kimiyya, da kuma ilimin yanayin ƙasa. Ya ce yana ganin yana da hikima da yawa a ganinsa da zai yarda da misalai da yawa da suka goyi bayan hurewar Littafi Mai Tsarki. “Na kamu cikin biɗan sukuni, arziki, da kuma nishaɗin rayuwa. Abin tausayi, na kasance babu sani da kuma jahili ga kyau da kuma gaskiyar littafi mafi girma da aka taɓa rubutawa.”
Yanzu a shekararsa ta 70, Maurice, da yake magana game da labarin bayyana da Yesu ya yi wa manzo Toma, ya ce cikin godiya: “An ja-goranci hannuna zuwa ‘ciwo’ wanda zai kawar da dukan shakka a zuciyata har abada cewa Littafi Mai Tsarki gaskiya ne.” (Yahaya 20:24-29) Manzo Bulus ya faɗi gaskiya da ya ce, Littafi Mai Tsarki yana fallasa manufar zuciya, kuma ya ba da ma’ana ga rayuwa. Littafi ne na rayuwa da gaske.
Ƙara Jimiri ga Rayuwa Mai Matsala
Littafi Mai Tsarki yana ba da gargaɗi da yake taimakon mutane su daina halin da ba shi da kyau. Daniel ya daina shan taba, har da yin dina da ba ta da kamewa da kuma maye. (Romawa 13:13; 2 Korantiyawa 7:1; Galatiyawa 5:19-21) A hakikanin gaskiya, a bar waɗannan halaye a “ɗauki sabon halin” yana bukatar ƙoƙari ƙwarai. (Afisawa 4:22-24) “Kaluɓale ne,” in ji Daniel, “domin ajizai ne mu.” Duk da haka, ya yi nasara. Yanzu Daniel yana karanta Kalmar Allah kowacce rana, kuma ta jawo shi kusa da Jehovah.
Lokacin da yake girma, Daniel yana ba wa Littafi Mai Tsarki daraja—ko da yake bai taɓa karanta shi ba—kuma yana yin addu’a ga Allah kowanne dare. Duk da haka, akwai abin da babu. Farin ciki ya yi nesa da shi. Lokacin canji ya zo da ya ga sunan Allah a Littafi Mai Tsarki da farko. (Fitowa 6:3; Zabura 83:18) Bayan haka, ya fara amfani da sunan Jehovah idan yana addu’a, kuma ya zama yana addu’arsa da kansa sosai. “Jehovah ya zama wanda ya fi kusa da ni, kuma har yanzu shi ne abokina mafi kusa.”
Kafin ya koyi game da Littafi Mai Tsarki, Daniel yana gani ba shi da wani bege a nan gaba. Ya ce, “Baya bukatar yawan ilimi kafin a ga abin da yake faruwa a duniya.” “Na tsorata, na yi ƙoƙari na shagala don in fid da shi a zuciyata.” Sai ya koyi cewa Allah zai kafa gaskiya a tsabtacacciyar duniya, inda mutane masu biyayya za su more salama ta har abada. (Zabura 37:10, 11; Daniyel 2:44; Wahayin Yahaya 21:3, 4) Yanzu Daniel yana da tabbacaccen bege. Wannan ikon kafawa na Littafi Mai Tsarki ya sa ya kasance da ra’ayi mai kyau game da rayuwa.
Taimako Wajen Magance Matsaloli na Zuci
George yana ɗan shekara bakwai lokacin da mamarsa ta mutu. Ya tsorata ba ya iya barci dad dare, don bai san idan ya kwanta ko ba zai farka ba washegari. Sai ya karanta abin da Yesu ya ce game da mutuwa da kuma tashin matattu: “Lokaci na zuwa da duk waɗanda ke kaburbura za su ji murya tasa [Yesu].” Kalmomin Yesu kuma sun taɓa shi: “Ai, ni ne tashin matattu, ni ne kuma rai. Wanda ya gaskata da ni, ko ya mutu zai rayu.” (Yahaya 5:28, 29; 11:25) Irin wannan tunanin yana da kyau, daidai ne, kuma da ban ta’aziyya. “Wannan gaskiyar,” in ji George, “ba kawai tana da kyau ga azanci ba amma kuma tana taɓa zuciya.”
Daniel, da aka faɗa da farko, shi ma ya razana. Mamarsa ba ta iya renonsa ba ita kaɗai, saboda haka aka tura shi ya zauna a gidajen renon yara. Ko yaushe yana ji shi bare ne kuma yana bukatar tsari da ke ga zama cikin iyali mai ƙauna. A ƙarshe, ya sami abin da yake nema ta wajen nazarinsa na Littafi Mai Tsarki. Daniel ya shiga tarayya da ikilisiyar Kirista na Shaidun Jehovah kuma ya zama cikin iyali na ruhaniya, inda ya ji an karɓe shi kuma wasu suna ƙaunarsa. Hakika, Littafi Mai Tsarki yana da amfani a zahiri kuma yana cika bukatar zuci.
Ka tuna, Jehovah yana ganin abin da yake zuciyarka kuma ya san abin da ka ke nema. Allah “ya san manufarka,” kuma yana sāka wa kowa “gwargwadon al’amuransa.”—Karin Magana 21:2; Irmiya 17:10.
Gargaɗi Mai Amfani Game da Rayuwar Iyali
Littafi Mai Tsarki ya ba da gargaɗi mai amfani idan ya zo ga hulɗa tsakanin mutane. George ya ce: “Bambancin ra’ayi ko kuma rashin fahimtar mutane suna cikin yanayi da ba su da daɗi a rayuwa.” Yaya ya magance su? “Idan na fahimci cewa wani ya riƙe ni a zuciya, ina amfani da gargaɗi da yake Matiyu 5:23, 24: ‘Ka je ku shirya da ɗan’uwanka.’ Gaskiyar cewa na yi magana game da abin yana kawo sasantawa. Ina da salama ta Allah da Littafi Mai Tsarki ya yi magana a kai. Lalle yana yiwuwa. Abu ne na zahiri.”—Filibiyawa 4:6, 7.
Lokacin da mata da miji ba su jitu ba, dukansu suna bukatar su yi “hanzarin kasa kunne, da jinkirin yin magana, da kuma jinkirin fushi.” (Yakubu 1:19) Irin wannan shawarar tana gyara ganawa. George ya daɗa: “Idan na yi amfani da gargaɗi na in ƙaunaci matata kuma in bi da ita kamar yadda zan yi da kaina, ina ganin amfanin wannan a take. Ba zai yi mata wuya ta ba ni daraja ba.” (Afisawa 5:28-33) Hakika, Littafi Mai Tsarki ya koyar da mu yadda za mu fahimci ajizancinmu kuma mu bi da namu ajizanci da kuma yadda za mu ci nasara a bi da na wasu.
Gargaɗi da Ya Jimre
Sarki mai hikima Sulemanu ya ce: “Ka dogara ga Ubangiji da zuciya ɗaya, kada ka dogara ga abin da kake tsammani ka sani. A cikin dukan abin da kake yi, ka tuna da Ubangiji, shi kuma zai nuna maka hanyar da ke daidai.” (Karin Magana 3:5, 6) Waɗannan kalmomi ba su da wuya, amma suna da zurfin basira!
Littafi Mai Tsarki abu ne mai kyau. Yana sa masu ƙaunar Allah su sa rayuwarsu ta jitu da nufinsa kuma ya samu farin ciki wajen “zamansu bisa ga dokar Ubangiji.” (Zabura 119:1) Ko yaya yanayinmu yake, Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da ja-gora da gargaɗi da muke bukata. (Ishaya 48:17, 18) Ka yi karatunsa kullum, ka yi bimbini bisa abin da ka karanta, kuma ka yi amfani da shi. Zai sa ka kafa zuciyarka bisa abubuwa da suke da tsarki kuma suke da kyau. (Filibiyawa 4:8, 9) Za ka koyi ba kawai yadda za ka rayu kuma ka more rayuwa ba amma kuma za ka koyi har yadda za ka ƙaunaci Mahaliccin rai.
Ta wajen bin wannan tafarkin, Littafi Mai Tsarki zai zama a gare ka—kamar yadda ya zama ga miliyoyin mutane—ba littafi ba ne kawai mai kyau. Da gaske zai kasance littafin rayuwa!
[Hoto a shafi na 6]
Littafi Mai Tsarki yana iya ƙarfafa ƙudurinka na magance miyagun halaye
[Hoto a shafi na 7]
Littafi Mai Tsarki yana koya maka yadda za ka matso kusa da Allah