Kiristoci Suna Samun Farin Ciki A Bayarwa
“Bayarwa ta fi karɓa albarka.”—AYYUKAN MANZANNI 20:35.
1. Wane mummunan hali ne ya cika ko’ina a yau, me ya sa yake da haɗari?
A SHEKARU na ƙarshe na 1900, ana yawan jin furcin nan “sai-ni.” “Sai-ni” yana nufin “ni ne farko” da ke nuna hali da ya haɗa son kai da kwaɗayi da rashin la’akari da wasu. Za mu tabbata cewa a shekara ta 2000, halin sai-ni yana ci gaba. Sau nawa ka ke ji ana tambayoyi, “Menene nawa a ciki?” ko kuma, “Me zan samu a ciki?” Irin wannan hali na son kai ba ya kawo farin ciki. Akasin ka’idar da Yesu ya faɗa ne: “Bayarwa ta fi karɓa albarka.”—Ayyukan Manzanni 20:35.
2. Ta yaya ake gani cewa bayarwa tana kawo farin ciki?
2 Da gaske ne bayarwa ta fi karɓa albarka? I. Ka yi tunanin Jehovah Allah. Shi ne “mafarin dukan rai.” (Zabura 36:9) Yana tanadin kome da muke bukata don ya sa mu farin ciki da kuma rayuwa mai ma’ana. Hakika, shi ne Tushen “kowace kyakkyawar baiwa, da kowace cikakkiyar kyauta.” (Yakubu 1:17) Jehovah, ‘Allah ne mai farin ciki,’ yana bayarwa kullayaumi. (1 Timoti 1:11) Yana ƙaunar halittunsa ’yan Adam, yana ba su abubuwa da yawa. (Yahaya 3:16) Ka yi tunanin iyalin ’yan Adam. Idan kana da yara, ka san yawan sadaukarwa, da ƙoƙarin da ake bukata don a yi renon yaro. Shekaru da yawa yaron bai san sadaukarwa da ka yi ba. Yana ɗaukansu da sauƙi. Duk da haka, kana farin ciki ka ga yaronka yana girma domin bayarwa da ka ke yi ba tare da son kai ba. Me ya sa? Domin kana ƙaunarsa.
3. Me ya sa abin farin ciki ne mu yi wa Jehovah da ’yan’uwanmu masu bi hidima?
3 Hakanan ma, sujjada ta gaskiya ta ƙunshi bayarwa cikin ƙauna. Tun da yake muna ƙaunar Jehovah kuma muna ƙaunar ’yan’uwanmu masu bi, abin farin ciki ne mu yi musu hidima, mu ba da kanmu gare su. (Matiyu 22:37-39) Duk wanda son kai ne yake motsa shi ya yi bauta, ba zai yi farin ciki sosai ba. Waɗanda suke bauta ba tare da son kai ba, suna damuwa sosai da abin da za su iya bayarwa fiye da abin da za su karɓa, suna samun farin ciki ƙwarai. Ana gane wannan gaskiyar ta wurin bincika yadda wasu kalmomin Littafi Mai Tsarki game da bautarmu aka yi amfani da su a cikin Nassosi. Za mu tattauna uku cikin waɗannan kalmomi a wannan talifi da kuma na biye.
Hidimar Yesu ga Jama’a
4. Menene “hidima ga jama’a” ta ƙunsa a Kiristendam?
4 A Helenanci na asali, kalma da take da muhimmanci da take da alaƙa da sujjada ita ce lei·tour·giʹa, da aka juya zuwa “hidima ga jama’a” a cikin New World Translation. A Kiristendam “liturgy” (hidimar addinai) ya fito daga kalmar nan lei·tour·giʹa.a Amma, hidimar Kiristendam ba ta amfani jama’a ba da gaske.
5, 6. (a) Wace hidima ce ga jama’a aka yi a Isra’ila, menene fa’idodinsu? (b) Wace hidima ga jama’a ce mafi girma ta sake wadda aka yi a Isra’ila, kuma me ya sa?
5 Manzo Bulus ya yi amfani da kalmar Helenanci da ya yi daidai da lei·tour·giʹa a yin nuni ga firistoci na Isra’ila. Ya ce: “Kowane firist yakan tsaya a kan hidimarsa kowace rana, [wani fasalin lei·tour·giʹa] yana miƙa hadaya iri ɗaya a kai a kai.” (Ibraniyawa 10:11) Firistoci Lawiyawa sun yi hidima ga jama’a da kyau a Isra’ila. Sun koyar da Dokar Allah kuma sun miƙa hadayu da ke rufe zunuban mutanen. (2 Tarihi 15:3; Malakai 2:7) Yayin da firistoci da mutanen suka bi Dokar Jehovah, al’ummar ta sami dalilan yin farin ciki.—Maimaitawar Shari’a 16:15.
6 Yin hidima ga jama’a a ƙarƙashin Dokar, gata ce ga firistoci Isra’ilawa, amma hidimarsu ba ta da amfani lokacin da aka ƙi Isra’ila saboda rashin aminci. (Matiyu 21:43) Jehovah ya shirya abu mafi girma—hidima ga jama’a da Yesu ya yi, Babban Firist mai girma. Game da shi, mun karanta: “Shi da ya ke madawwami ne, yana da matsayinsa na firist wanda ba ya komawa hannun wani. Saboda haka yana da ikon ceton masu kusatowa ga Allah ta wurinsa, matuƙar ceto, tun da ya ke kullum a raye yake saboda yi musu addu’a.”—Ibraniyawa 7:24, 25.
7. Me ya sa hidimar Yesu ga jama’a ta kawo amfani da babu irinsa?
7 Yesu ya ci gaba firist ne shi har abada, ba tare da magāji ba. Da haka, shi kaɗai ne zai iya ceton mutane ɗungum. Ya yi wa jama’a hidima da babu kamar ta, ba a cikin haikali da mutane suka yi ba, amma a cikin haikali na alama, tsari mai girma don sujjada da Jehovah ya yi da ya soma a shekara ta 29 A.Z. Yesu yanzu yana hidima a cikin wuri Mafi Tsarki na wannan haikali, a sama. Shi “mai hidima [lei·tour·gosʹ] a Wuri Mafi Tsarki, da kuma masujada ta gaskiya, wadda Ubangiji ya kafa, ba mutum ba.” (Ibraniyawa 8:2; 9:11, 12) Ko da yake Yesu yana da matsayi mai girma, shi har ila “mai hidima” ne. Yana amfani da ikonsa mai girma a bayarwa, ba a karɓa ba. Kuma irin wannan bayarwa yana kawo masa farin ciki. Ɓangaren “farin cikin da aka sa gabansa” ne, wannan ya ƙarfafa shi ya daure a duk tafarkinsa a duniya.—Ibraniyawa 12:2.
8. Ta yaya Yesu ya yi wa jama’a hidima don ya sake Dokar alkawari?
8 Akwai wani fanni kuma a hidimar Yesu ga jama’a. Bulus ya rubuta: “Almasihu ya sami hidima wadda take mafificiya, kamar yadda alkawarin nan—wanda shi ne matsakancinsa—yake da fifiko nesa, tun da ya ke an kafa shi ne a kan mafifitan alkawarai.” (Ibraniyawa 8:6) Musa ne matsakancin alkawari da ya kasance tushen dangantakar Isra’ila da Jehovah. (Fitowa 19:4, 5) Yesu ne matsakancin sabon alkawari, da ya sa ya yiwu a haifi sabuwar al’umma, “Isra’ilan gaske na Allah” da ya ƙunshi Kiristoci da aka shafa su da ruhu daga al’ummai da yawa. (Galatiyawa 6:16; Ibraniyawa 8:8, 13; Wahayin Yahaya 5:9, 10) Lalle wannan hidima ga jama’a ce mafi kyau! Muna farin ciki cewa mun sarƙu da Yesu, mai hidima da ta wurinsa za mu iya yin sujjada da Jehovah ya amince da ita!—Yahaya 14:6.
Kiristoci ma Suna Hidima wa Jama’a
9, 10. Wace irin hidima ce ga jama’a Kiristoci suke yi?
9 Ba mutumin da ya yi hidima da aka ɗaukaka kamar na Yesu. Amma, lokacin da Kiristoci shafaffu suka karɓi ladarsu na samaniya, za su zauna wajen Yesu kuma su yi hidima tare da shi, su zama sarakuna da firistoci na samaniya. (Wahayin Yahaya 20:6; 22:1-5) Duk da haka, Kiristoci a duniya suna yi wa jama’a hidima, kuma suna samun farin ciki mai girma a yin haka. Alal misali, lokacin da aka yi ƙarancin abinci a Palasɗinu, manzo Bulus ya kwashe kyauta daga ’yan’uwa a Turai don su taimaka a sauƙaƙa wahala da Kiristoci Yahudawa da suke a Yahudiya suke sha. Wannan hidima ce ga jama’a. (Romawa 15:27; 2 Korantiyawa 9:12) A yau, Kiristoci suna farin ciki wajen yin irin wannan hidima, suna ba da taimako nan da nan lokacin da ’yan’uwansu suke shan azaba, bala’i, ko wasu masifu.—Karin Magana 14:21.
10 Bulus ya yi maganar wata hidima yayin da ya rubuta: “Ko da za a tsiyaye jinina a kan hadaya da hidima na bangaskiyarku, sai in yi farin ciki, in kuma taya ku farin ciki, ku duka.” (Filibiyawa 2:17) Aiki mai wuya da Bulus ya yi domin Filibiyawa hidima ce ga jama’a da ya yi da ƙauna da kuma ƙwazo. Ana yin irin wannan hidima a yau, musamman ma ga Kiristoci shafaffu da suke hidimar “amintaccen bawan nan,” suna tanadin abinci na ruhaniya a kan kari. (Matiyu 24:45-47) Ƙari ga haka, su rukunin waɗannan “tsattsarkar ƙungiyar firistoci” ne da aka ce su “miƙa hadayu na ruhu, abin karɓa ga Allah ta wurin Yesu Almasihu” kuma su “sanar da mafifitan al’amuran wannan da ya kirawo [su] daga cikin duhu, [su]ka shiga maɗaukakin haskensa.” (1 Bitrus 2:5, 9) Kamar Bulus, suna farin ciki a irin waɗannan gata yayin da suke ‘ba da kansu’ a cika hakkinsu. Abokan tarayyarsu “waɗansu tumaki” suna bin su kuma suna toƙara musu a aikin gaya wa mutane game da Jehovah da nufe-nufensa.b (Yahaya 10:16; Matiyu 24:14) Lalle wannan hidima ce da take da muhimmanci kuma take kawo farin ciki!—Zabura 107:21, 22.
Yi Tsarkakkar Hidima
11. Ta yaya annabiya Hannatu ta tanadar wa duka Kiristoci misali mai kyau?
11 Wata kalmar Helenanci da ke game da bautarmu ita ce la·treiʹa, da aka juya zuwa “tsarkakkiyar hidima” a cikin New World Translation. Tsarkakkiyar hidima game da ayyukan sujjada ne. Alal misali, Hannatu gwauruwa ’yar shekara 84 da kuma annabiya an kwatanta ta da cewa “ba ta rabuwa da Haikalin, tana bauta wa Allah dare da rana [kalmar Helenanci da ta bayyana a nan ita ce la·treiʹa] ta wurin yin addu’a da azumi.” (Luka 2:36, 37) Hannatu ta bauta wa Jehovah cikin aminci. Misali ce mai kyau ga dukanmu—yara da manya, maza da mata. Yadda Hannatu ta yi wa Jehovah addu’a da himma kuma ta bauta masa kullum a haikali, tsarkakkiyar hidimarmu ta ƙunshi yin addu’a da kuma zuwa taro.—Romawa 12:12; Ibraniyawa 10:24, 25.
12. Wane fanni na tsarkakkiyar hidimarmu ya fi muhimmanci, kuma ta yaya yake shi ma hidima ne ga jama’a?
12 Manzo Bulus ya ambata fanni na tsarkakkiyar hidimarmu da ya fi muhimmanci yayin da ya rubuta: “Allah, wanda nake bauta wa a ruhuna ta yin bisharar Ɗansa, shi ne mashaidina a kan yadda kullum ba na fasa ambatonku a cikin addu’ata.” (Romawa 1:9) Hakika, wa’azin bishara ba hidima ba ce kawai ga jama’a waɗanda suke jin ta ba amma bauta ce ga Jehovah Allah. Ko an saurare mu ko babu, aikin wa’azi tsarkakkiyar hidima ce ga Jehovah. Ƙoƙarin da muke yi mu gaya wa wasu game da ingancin nufe-nufensa masu amfani na Ubanmu da muke ƙauna na samaniya babu shakka yana kawo mana farin ciki mai girma.—Zabura 71:23.
A Ina Muke Yin Tsarkakkiyar Hidima?
13. Menene begen waɗanda suke tsarkakkiyar hidima a farfajiya ta ciki na haikalin Jehovah na ruhaniya, kuma su wanene suke murna da su?
13 Bulus ya rubuta wa Kiristoci shafaffu: “Sai mu yi godiya domin mun sami mulkin da ba ya girgizuwa, ta haka kuma mu yi wa Allah sujada abar karɓa, tare da tsoro da tsananin girmamawa.” (Ibraniyawa 12:28) Da gabagaɗin tsammanin gādan Mulkin, ba a kawar da bangaskiyar shafaffu yayin da suke bauta wa Maɗaukaki Duka. Su kaɗai ne za su iya yi masa tsarkakkiyar hidima a wuri Mai Tsarki da kuma farfajiya ta ciki na haikalin Jehovah na ruhaniya, suna saurara da marmari ga yin hidima da Yesu a cikin wuri Mafi Tsarki, sama kanta. Abokan tarayyarsu, ajin waɗansu tumaki, suna murna da su a begensu mai girma.—Ibraniyawa 6:19, 20; 10:19-22.
14. Ta yaya ƙasaitaccen taro suke amfana daga hidimar Yesu ga jama’a?
14 Waɗansu tumakin kuma fa? Yadda manzo Yahaya ya gani, taro mai girma cikinsu ya bayyana a waɗannan kwanaki na ƙarshe, kuma “sun wanke rigunansu, suka mai da su farare da jinin Ɗan Ragon nan.” (Wahayin Yahaya 7:14) Wannan yana nufin cewa, kamar ’yan’uwansu shafaffu masu bi, su ma sun ba da gaskiya ga hidimar Yesu ga jama’a, hadaya da ya miƙa da kamilcaccen ransa domin mutane. Waɗansu tumaki ma sun amfana daga hidimar Yesu domin suna ‘riƙe da alkawarin Jehovah.’ (Ishaya 56:6) A’a, ba sa cikin sabon alkawarin, amma suna riƙe da shi ta yin biyayya da dokokin da ya ƙunsa kuma ta wajen haɗa kai da shirye-shirye da aka yi ta wurinsa. Suna tarayya da Isra’ila na Allah, suna ci a teburi ɗaya na ruhaniya da kuma yin aiki tare da waɗanda suke ciki, suna yaba wa Allah a fili kuma suna miƙa hadayu na ruhaniya da suke faranta masa rai.—Ibraniyawa 13:15.
15. A ina ne ƙasaitaccen taro suke bauta, ta yaya wannan albarka take shafan su?
15 A ta haka kuma, an ga ƙasaitaccen taro “suna tsaitsaye a gaban kursiyin, a gaban Ɗan Ragon kuma, saye da fararen riguna.” Ƙari ga haka, suna “gaban kursiyin Allah, suna bauta masa dare da rana a Haikalinsa. Na zaune kan kursiyin nan kuwa zai kare su da zatinsa.” (Wahayin Yahaya 7:9, 15) A Isra’ila, shigaggu suna bauta a cikin farfajiya ta waje na haikalin Sulemanu. Hakanan ma, ƙasaitaccen taron suna bauta wa Jehovah a farfajiya ta waje a haikalinsa na ruhaniya. Yin bauta a wajen yana ba su farin ciki. (Zabura 122:1) Bayan abokan tarayyarsu na ƙarshe ma sun karɓa gadōnsu na samaniya, za su ci gaba da bauta wa Jehovah su mutanensa.—Wahayin Yahaya 21:3.
Tsarkakkiyar Hidima da ba a Amince da Ita Ba
16. Wane gargaɗi ne aka bayar game da tsarkakkiyar hidima?
16 A zamanin Isra’ila ta dā, za a yi tsarkakkiyar hidima cikin jituwa da dokokin Jehovah. (Fitowa 30:9; Littafin Firistoci 10:1, 2) Hakazalika yau, akwai farillai da za a bi idan Jehovah zai amince da bautarmu. Dalilin da ya sa ke nan Bulus ya rubuta wa Kolosiyawa: “Ba mu fasa yi muku addu’a ba, muna roƙo a cika ku da sanin nufin Allah da matuƙar hikima da fahimta na ruhu, domin ku yi zaman da ya cancanci bautar Ubangiji, kuna faranta masa ta kowane fanni, kuna ba da amfani a kowane aiki nagari, kuna ƙaruwa da sanin Allah.” (Kolosiyawa 1:9, 10) Ba mu ba ne za mu ƙudura hanya da ta dace na bauta wa Allah. Cikakken sanin Nassi, fahimta ta ruhu, da hikima ta Allah suna da muhimmanci. In ba haka ba, abubuwa za su yi muni sosai.
17. (a) Ta yaya aka ɓata bauta a zamanin Musa? (b) Ta yaya za a iya kaucewa daga bauta a yau?
17 Ka tuna da Isra’ilawa a zamanin Musa. Mun karanta: “Allah ya juya musu baya, ya sallame su ga bautar taurari.” (Ayyukan Manzanni 7:42) Waɗannan Isra’ilawa sun ga ikon Jehovah dominsu. Duk da haka, sun juya ga wasu alloli yayin da sun yi tunanin cewa wannan zai amfane su. Ba su da aminci, kuma aminci dole ne idan bautarmu za ta faranta wa Allah rai. (Zabura 18:25) Gaskiya, a yau kalilan za su juya daga Jehovah su bauta wa taurari ko maraƙi na zinariya, amma akwai wasu irin bautar gumaka kuma. Yesu ya yi kashedi a kan bauta wa “Dukiya,” Bulus ya kira kwaɗayi, bautar gumaka. (Matiyu 6:24; Kolosiyawa 3:5) Shaiɗan na gabatar da kansa allah. (2 Korantiyawa 4:4) Irin waɗannan bautar gumaka sun cika ko’ina kuma tarko ne. Alal misali, ka yi tunani wanda yake da’awa shi mai bin Yesu ne amma makasudinsa na gaske shi ne ya zama mai arziki ko kuma wanda ya dogara a kansa da kuma ra’ayoyinsa. Wanene ya ke bauta wa da gaske? Yaya ne ya bambanta daga Yahudawa na zamanin Ishaya waɗanda suke rantsuwa da sunan Jehovah amma suna yaba wa gumaka mara tsarki don ayyukansu masu girma?—Ishaya 48:1, 5.
18. Ta yaya ake bauta da ba daidai ba a dā da kuma a yau?
18 Yesu ya yi kashedi: “Lokaci ma na zuwa da kowa ya kashe ku zai zaci bautar Allah yake yi.” (Yahaya 16:2) Shawulu, wanda ya zama manzo Bulus, babu shakka tsammani yake cewa yana bauta wa Allah lokacin da yake ‘goyon bayan kisan Istifanas’ yana kuma ‘tsananta kashedi gaba da masu bin Ubangiji cewa zai kashe su.’ (Ayyukan Manzanni 8:1; 9:1) A yau, wasu da suke kawar da kabilai ko kuma halaka dangi su ma suna da’awar bauta wa Allah. Akwai mutane da yawa da suke da’awar suna bauta wa Allah, amma da gaske suna bauta wa allolin wariyar al’ummai, son kabila, dukiya, kansu, ko kuma wasu alloli.
19. (a) Yaya muke ɗaukar bautarmu? (b) Wace irin bauta ce za ta kawo mana farin ciki?
19 Yesu ya ce: “Ka yi wa Ubangiji Allahnka sujada, Shi kaɗai za ka bauta wa.” (Matiyu 4:10) Yana wa Shaiɗan magana, amma yana da muhimmanci dukanmu mu yi biyayya ga kalmominsa! Yi wa Ubangiji Mai Ikon Mallaka na sararin samaniya bauta, gata ce mai girma, na ban sha’awa. Me kuma za a ce game da yin hidima da take haɗe da bautarmu? Yin wannan domin maƙwabtanmu aiki ne mai kyau da ke kawo farin ciki mai yawa. (Zabura 41:1, 2; 59:16) Duk da haka, irin wannan hidima za ta kawo farin ciki na gaske sai dai an yi ta da dukan zuciya kuma a hanyar da ta yi daidai. Su wanene da gaske suke bauta wa Allah daidai? Bautar su wanene Jehovah yake amincewa da ita? Za mu amsa waɗannan tambayoyi idan mun bincika kalma ta uku ta Littafi Mai Tsarki da take da alaƙa da bautarmu. Za mu yi wannan a talifi na biye.
[Hasiya]
a Hidimar Kiristendam bauta ce ko kuma bukukuwa na ainihi, kamar su Cin Jibi da ake yi a Cocin Roman Katolika.
b A Ayyukan Manzanni 13:2, an ba da rahoto cewa annabawa da malamai a Antakiya suna ‘hidima’ (fassara ta kalmar Helenanci da ke da alaƙa da lei·tour·giʹa) ga Jehovah. Mai yiwuwa, wannan hidima ta haɗa da yin wa’azi wa jama’a.
Yaya Za Ka Amsa?
• Wace hidima ce mai girma ga jama’a Yesu ya yi?
• Wace hidima ce ga jama’a Kiristoci suke yi?
• Menene tsarkakkiyar hidima ta Kirista, kuma a ina ake yinta?
• Menene dole mu samu idan bautarmu za ta faranta wa Allah rai?
[Hoto a shafi na 8]
Iyaye suna samun farin ciki mai girma a bayarwa
[Hotuna a shafuffuka na 10, 11]
Kiristoci suna hidima ga jama’a yayin da suke taimaka wa wasu da kuma lokacin da suke wa’azin bishara
[Hoto a shafi na 12]
Muna bukatar cikakken sani da fahimi don mu tabbata cewa Allah ya amince da bautarmu