Littafi Mai Tsarki—Ana Sonsa Kuma an Haramta Shi
“Da zan so a fassara littattafai masu tsarki a cikin dukan harsuna,” in ji Desiderius Erasmus manazari da aka ɗaukaka na mutanen Dutch a ƙarni na 16.
SA RAI da Erasmus ya yi shi ne cewa dukan mutane su samu karanta Nassosi kuma su fahimce su. Amma masu adawa da Littafi Mai Tsarki suka yi hamayya da wannan ra’ayin. Hakika, a Turai lokacin, haɗari ne ƙwarai ga duk wanda yake da bukata kaɗan na sanin abin da ke cikin Littafi Mai Tsarki. A Ingila aka kafa wata doka, da ta ba da umurnan cewa “duk wanda ya karanta Nassosi a harshen Turanci za a ci taransa fegi, kayayyaki, da kuma rai . . . kuma bayan haka, idan aka gafarta musu kuma suka ci gaba da taurin kai, ko kuma suka sake komawa, da farko za a rataye su domin cin amanar sarki, kuma a kona su domin kafurta ga Allah.”
A ƙasar Turai, Masu ba da Tsanani na Katolika babu tausayi suka yi farautar ɗariku “da suka ƙi imani na Katolika,” kamar su French Waldenses, aka ware su aka tsananta musu domin halinsu na wa’azi “daga lingila da wasiƙu da kuma wasu ɓangarori na nassosi masu tsarki, . . . tun da yake an haramta wa mutane wa’azi da kuma karatun nassosi masu tsarki.” Maza da mata babu iyaka sun sha azaba mai tsanani wasu sun mutu domin ƙauna da suke yi wa Littafi Mai Tsarki. Suna bakin babban haɗari idan suka maimaita Addu’ar Ubangiji ko kuma Dokoki Goma ko suka koya wa ’ya’yansu.
Irin wannan ibada ga Kalmar Allah ta ci gaba a zukatan mutane da yawa da suka ƙaura su yi mulkin mallaka a kan Amirka ta Arewa. A Amurka ta farko “karatu da addini ba a iya bambance su, wanda ya nuna al’ada da ta nuna fahimtar Littafi Mai Tsarki,” in ji littafin A History of Private Life—Passions of the Renaissance. Hakika, wani huɗuba da aka buga a Boston a shekara ta 1767 ta ce: “Ka natsu wajen karatun nassi mai tsarki. Kowacce safiya da kowanne maraice dole ka karanta sura ɗaya na Littafin Mai Tsarki naka.”
In ji Barna Research Group a Ventura na California, fiye da kashi 90 bisa ɗari na Amurkawa suna da Littafi Mai Tsarki guda uku matsakaici ke nan. Wani nazari na baya bayan nan ya nuna cewa ko da yake ana nan ana daraja Littafi Mai Tsarki sosai a can, “karatunsa, nazari da kuma amfani da abin da aka koya . . . abin da ya riga ya wuce ne.” Wasu suna da sani na sama sama ne kawai na abin da ya ƙunsa. Wani mai rubutu a jarida ya lura: “Tunanin cewa [Littafi Mai Tsarki] har yanzu zai iya shafar matsaloli na yanzu da kuma damuwa, da kyar ya faɗo.”
Rashin Kamewa na Tunanin Duniya
Abin da aka yarda da shi, shi ne cewa za mu iya cin nasara a rayuwa bisa tunani da kuma haɗin kan jama’a. Ana ganin Littafi Mai Tsarki ɗaya ne cikin littattafai na ra’ayin addinai da kuma labaransu, ba littafi na hakikanci da gaskiya ba.
To, ta yaya yawancin mutane suke bi da matsaloli da suke ƙaruwa na batun rayuwa? Suna aiki ne a sarari na ruhaniya, babu ja-gora mai ƙwari na ɗabi’a da kuma na addini. Suna zama kamar jirgin ruwa da ba shi da majuyi, “waɗanda ke jujjuyawa, ta iskar kowace koyarwa, . . . bisa ga wayon mutane da makircinsu.”—Afisawa 4:14, The Twentieth Century New Testament.
Dole ne mu yi tambaya, Littafi Mai Tsarki wani littafi ne kawai na addini? Ko kuma dai da gaske Kalmar Allah ne, da yake ɗauke da sanarwa masu amfani? (2 Timoti 3:16, 17) Littafi Mai Tsarki ya kai mu bincika shi kuwa? Talifi na gaba zai bincika waɗannan tambayoyi.
[Hoto a shafi na 3]
Desiderius Erasmus
[Inda aka Dauko]
Daga littafin nan Deutsche Kulturgeschichte
[Hoto a shafi na 4]
Aka ware Waldenses aka tsananta musu domin wa’azinsu daga Nassosi
[Inda aka Dauko]
Stichting Atlas van Stolk, Rotterdam