Canjin Kamani na “Kiristanci”—Allah Ya Yarda da Shi Kuwa?
ACE ka saka mai zane ya zana hotonka. Lokacin da ya gama, ka yi murna ƙwarai; hoton kamaninka ne sak. Ka yi tunanin ’ya’yanka, jikokinka, da kuma jikokinsu cewa za su kalli hoton nan da alfahari.
Tsararraki daga baya, wani daga cikin zuriyarka ya ji cewa ba ya son rashin gashi a hoton, sai ya sa aka ƙara gashi. Wani kuma ba ya son siffar hancinka, ya sa aka canja. Haka dai wasu “gyara” suka shigo daga tsararraki na baya, a ƙarshe hoton kamaninsa kaɗan ne kawai naka. Idan ka san cewa hakan zai faru, yaya za ka ji? Babu shakka za ka yi ɓacin rai.
Abin baƙin ciki, labarin wannan hoton, da labarin cocin Kirista ɗaya ne. Tarihi ya nuna cewa jim kaɗan bayan mutuwar mazannin Kristi, ainihin kamanin “Kiristanci” ya fara canjawa, kamar yadda Littafi Mai-Tsarki ya annabta.—Matta 13:24-30, 37-43; Ayukan Manzanni 20:30.a
Hakika, daidai ne a yi amfani da mizanan Littafi Mai-Tsarki a aladu da tsararraki dabam dabam. Wani batu ne dabam a canja koyarwan Littafi Mai-Tsarki don su dace da abubuwa da aka yarda da su. Duk da haka, wannan shi ne abin da ya faru. Alal misali, ka lura da canji da aka yi a wasu wurare masu muhimmanci.
Coci ta Rungumi Jiha
Yesu ya koyar da cewa sarautarsa ko kuma Mulkinsa na sama, a lokacin da ya dace, zai halaka dukan sarautar mutane ya yi sarautar duniya duka. (Daniel 2:44; Matta 6:9, 10) Ba zai yi sarauta da tsarin siyasa ta mutane ba. “Mulkina ba na wannan duniya ba ne,” in ji Yesu. (Yohanna 17:16; 18:36) Saboda haka, almajiran Yesu, ko da yake masu bin doka ne, ba sa yin siyasa.
Ko da yake, a zamanin mai mallakar Daular Roma Constantine a ƙarni na huɗu, da yawa da suke da’awar su Kiristoci ne suka zama marasa haƙuri wajen jiran komowan Kristi da kuma kafa Mulkin Allah. A hankali, ra’ayinsu game da siyasa ya canja. “Kafin zamanin Constantine,” in ji littafin nan Europe—A History, “Kiristoci ba su yi ƙoƙarin ɗaukan matsayi [na siyasa] wajen faɗaɗa nufinsu da kuma imaninsu ba. Bayan zamanin Constantine, Kiristanci da mayan ’yan siyasa suka soma tafiya tare.” Kiristanci da aka gyara ya zama sanannen addini “karɓaɓɓe” ko kuma “katolika” na Daular Roma.
Kundin sani Great Ages of Man ya faɗi cewa domin shaƙuwa tsakanin Coci da Jiha, “a ƙarshen shekara ta 385 A.D., shekara 80 kawai bayan tsanantawa mai tsanani wa Kiristoci, Coci kansa ya fara kashe waɗanda ra’ayinsu ya bambanta da na cocin, kuma limamansa suna da iko kusan daidai da na mai mallakar daular.” Ta wannan halin aka soma zamani da a cikinsa takobi ya ɗauki matsayin lallashi wajen rinjayan mutane zuwa Kiristanci, kuma limamai masu son laƙabi da iko suka ɗauki matsayin masu wa’azi da tawali’u na ƙarni na farko. (Matta 23:9, 10; 28:19, 20) Ɗan tarihi H. G. Wells ya rubuta game da “manyan bambance-bambance tsakanin” Kiristoci na ƙarni na huɗu “da kuma koyarwan Yesu Ba’nazare.” Waɗannan “manyan bambance-bambance” ya shafi muhimman koyarwa game da Allah da kuma Kristi.
Sake Yin Gyara ga Allah
Kristi da almajiransa sun koyar da cewa akwai “Allah ɗaya, Uba ne,” wanda sunansa Jehovah da ya bayyana sau 7,000 a littattafan Littafi Mai-Tsarki na dā ya bambanta shi. (1 Korinthiyawa 8:6; Zabura 83:18) Allah ne ya halicci Yesu; shi ne “ɗan fari gaban kowane halitta,” in ji Littafi Mai-Tsarki a Kolossiyawa 1:15. Saboda, an halicce shi ne, Yesu ya faɗa gaskiya cewa: “Uba ya fi ni girma.”—Yohanna 14:28.
A ƙarshen ƙarni na uku, wasu limamai masu rinjaya, da suke ƙaunar koyarwan Dunƙulin-Alloli-Uku na arne mai ussan ilimi na Hellas, Plato, suka fara sake yin gyara ga Allah domin ya dace da yanayin Dunƙulin-Alloli-Uku. A ƙarnuka da suka biyo baya, wannan koyarwan da ba na Nassi ba ya ɗaukaka Yesu ya zama daidai da Jehovah kuma ya mayar da ruhu mai tsarki ko kuma ikon aiki na Allah ya zama wani.
Game da karɓan ra’ayin arna na Dunƙulin-Alloli-Uku, New Catholic Encyclopedia ya ce: “Ƙirƙiro cewa ‘Allah uku ne cikin Ɗaya’ bai kafu sosai ba, hakika ba a karɓe shi cikin rayuwar Kiristoci da kuma da’awar bangaskiyarsa, kafin ƙarshen ƙarni na huɗu. Amma ainihi wannan ƙirƙirowan shi ne farkon da’awar koyarwan Dunƙulin-Alloli-Uku. Tsakanin Iyaye Manzanni, babu wani abu da ya yi kusa da irin wannan hali ko kuma tunani.”
Hakanan, The Encyclopedia Americana ya ce: “Koyarwan Dunƙulin-Alloli-Uku na ƙarni na huɗu bai kamanci daidai koyarwan Kiristoci na farko ba game da yadda Allah yake; akasarin haka kaucewa ne daga koyarwan nan.” The Oxford Companion to the Bible ya kira Dunƙulin-Alloli-Uku ɗaya daga cikin “imani da aka ƙirƙiro daga baya.” Duk da haka, Dunƙulin-Alloli-Uku ba shi ne kaɗai ra’ayin arna da coci ya karɓa ba.
Sake Yin Gyara ga Kurwa
Da yawa sun gaskata cewa mutane suna da kurwa da ba ta mutuwa bayan gangar jiki ta mutu. Amma ka san cewa wannan koyarwar ma ta coci ƙari ne da aka yi daga baya? Yesu ya tabbatar da gaskiyan Littafi Mai-Tsarki cewa matattu “ba su san kome ba,” suna barci ne kamar yadda yake. (Mai-Wa’azi 9:5; Yohanna 11:11-13) Za a sake mai da rai ta hanyar tashin matattu—‘sake tashi’ daga barcin mutuwa. (Yohanna 5:28, 29) Kurwa da ba ta mutuwa, idan tana wanzuwa, ba za ta bukaci tashin matattu ba, tun da idan ba a mutu ba babu zancen mutuwa.
Yesu har ya gwada koyarwan Littafi Mai-Tsarki na tashin matattu ta wurin tayar da mutane da suka mutu. Alal misalin Li’azaru da ya mutu kwanaki huɗu. Lokacin da Yesu ya tashe shi, Li’azaru ya taso daga kabari mutum ne rayayye mai numfashi. Babu wata kurwa da ta yi sanɗa ta fito daga jin daɗi na samaniya ta shigo jikinsa lokacin da Li’azaru ya farka daga mutuwa. Idan haka ya faru, to Yesu bai kyautata masa ba da ya tashe shi daga matattu!—Yohanna 11:39, 43, 44.
To menene tushen ra’ayi na kurwa da ba ta mutuwa? The Westminster Dictionary of Christian Theology ya ce ra’ayin “ya samo tushe ne daga ussan ilimi na Hellenawa ba daga wahayi na littafi mai-tsarki ba.” The Jewish Encyclopedia ya yi bayani: “Imanin cewa kurwa tana ci gaba da wanzuwa bayan mutuwar gangar jiki, batu ne na ussan ilimi ko kuma zato na tauhidi maimakon zalalar bangaskiya, kuma babu wajen da aka koyar da shi cikin Nassosi Masu Tsarki.”
Sau da yawa, ƙarya ɗaya ta kan haifi wata, kuma wannan haka yake da koyarwan kurwa da ba ta mutuwa. Ya buɗe hanya ga ra’ayin arna na azabantarwa a jahannama har abada.b Duk da haka, Littafi Mai-Tsarki ya faɗa sarai cewa “hakkin zunubi mutuwa ne”—ba azaba ta har abada ba. (Romawa 6:23) Saboda haka, da yake kwatanta tashin matattu, King James Version ya ce: “Teku kuma ya bada matattu da suke cikinsa; mutuwa kuma da jahannama suka saki matattu da suke cikinsu.” Hakazalika, Littafi Mai-Tsarki na Douay ya ce “teku. . . da mutuwa da kuma jahannama suka ba da matattunsu.” Hakika, a faɗe shi da sauƙi, waɗanda suke jahannama a mace suke, ‘suna barci,’ kamar yadda Yesu ya ce.—Ru’ya ta Yohanna 20:13.
Ka yarda da gaske cewa koyarwan dawwama cikin jahannama zai jawo mutane kusa da Allah? Da ƙyar. Ga mutane masu gaskiya da kuma ƙauna, mummunan tunani ne! Littafi Mai-Tsarki, ya koyar da cewa “Allah ƙauna ne” kuma mugunta har ga dabbobi ƙyamarsa yake yi.—1 Yohanna 4:8; Misalai 12:10; Irmiya 7:31; Yunana 4:11.
Ɓata “Hoton” a Lokatan Zamani
Ɓata yadda Allah yake da kuma Kiristanci yana ci gaba a yau. Wani shehun malami na addini ba da daɗewa ba ya kwatanta kokawa a cocinsu na Farotasta da cewa a kan “ikon Nassosi ne da kuma tsakanin tsarin dokokin coci da iko da ta bambanta, da ra’ayoyin mutane, tsakanin amincin coci ga ubangijinta Kristi da kuma runguma da sake Kiristanci zuwa halaye irin na zamani. Batu da yake da muhimmanci yanzu shi ne: Waye yake gudanar da batutuwan coci . . . Nassosi Mai-Tsarki ko kuwa sababbin ra’ayin da suka gama gari?”
Abin baƙin ciki, “sababbin ra’ayin da suka gama gari” har yanzu suna yin nasara. Ba asiri ba ne, alal misali, coci da yawa sun canja matsayinsu game da batutuwa dabam dabam don wai a ga suna ci gaba kuma wai su masu buɗaɗɗun zukata ne. Musamman ma a batutuwan ɗabi’a, coci ya zama mai sakaci, kamar yadda aka faɗa a cikin talifi na farko. Duk da haka, Littafi Mai-Tsarki ya ce ba wata tantama fasikanci, zina, luwaɗi duka zunubai ne masu girma a gaban Allah kuma waɗanda suke yin irin waɗannan zunuban “ba za su gāji mulkin Allah ba.”—1 Korinthiyawa 6:9, 10; Matta 5:27-32; Romawa 1:26, 27.
Lokacin da manzo Bulus ya rubuta wannan ayar ta sama, duniyar Romawa da Hellenawa da suka kewaye shi sun cika da kowace irin mugunta. Bulus da ya yi tunani: ‘Hakika, Allah ya ƙona Saduma da Gwamarata har toka domin mummunar lalatar jima’i, amma wannan ai shekara 2,000 ne da ya shige! Wannan bai shafi wannan wayayyen zamani ba.’ Duk da haka, bai nuna yawan hikima ba; ya ƙi ya gurɓata gaskiyar Littafi Mai-Tsarki.—Galatiyawa 5:19-23.
Ka Duba “Hoton” na Ainihi
Da yake magana da shugabannan addinin Yahudawa na zamaninsa, Yesu ya ce bautarsu a ‘banza suke yi domin koyarwa da suke yi dokokin mutane ne.’ (Matta 15:9) Waɗannan shugabannan sun yi abu ɗaya ga Doka da Jehovah ya bayar ta hannun Musa da abin da limaman Kiristendam suka yi, kuma har ila suna yin wannan ga koyarwan Kristi—sun rufe gaskiya ta Allah da al’ada. Amma Yesu ya kwaɓe dukan ƙaryace-ƙaryace domin mutane masu zukatan kirki su amfana. (Markus 7:7-13) Yesu ya faɗi gaskiya, ko mutane sun amince da ita ko a’a. Kalmar Allah koyaushe ita ce makomarsa.—Yohanna 17:17.
Lallai Yesu ya bambanta da yawancin masu da’awar su Kiristoci ne! Hakika, Littafi Mai-Tsarki ya annabta cewa: “Mutane ba za su jure . . . saboda kunnensu na ƙaiƙayi, sai su taro masu koyarwa da za su biya musu muradinsu. Za su toshe kunnensu ga jin gaskiya, su karkata ga jin tatsuniyoyi.” (2 Timothawus 4:3, 4 Littafi Mai Tsarki duk da Afokirifa) Waɗannan “tatsuniyoyi” waɗanda mun bincika kaɗan daga cikinsu, suna halakarwa a ruhaniya, amma kuma gaskiyar Kalmar Allah tana ginawa, kuma tana kai wa ga rai madawwami. Wannan ita ce gaskiyar da Shaidun Jehovah suke ƙarfafa ka ka bincika.—Yohanna 4:24; 8:32; 17:3.
[Hasiya]
a Kamar yadda Yesu ya bayyana a misalinsa na alkama da ciyayi da kuma a cikin misalinsa na ƙuƙuntar ƙofa da mai faɗi (Matta 7:13, 14), mutane kalilan ne za su ci gaba da bin Kiristanci na gaskiya a dukan tsararraki. Duk da haka, da yawa da suke kama da ciyayi za su rufe su, waɗanda za su ɗaukaka kansu da kuma koyarwansu cewa gaskiyan kamanin Kiristanci ne. Wannan shi ne Kiristanci da talifinmu yake nufi.
b “Jahannama” fassara ce ta kalmar Ibrananci Sheol da ta kalmar Hellenanci Hades, waɗanda dukansu suna nufin “kabari.” Saboda haka, lokacin da masu fassaran Turanci na King James Version suka fassara Sheol “jahannama” sau 31, sun kuma fassara shi sau 31 “kabari” sau 3 kuma “rami” wannan ya nuna cewa waɗannan kalmomin ainihi suna nufin abu guda ne.
[Hotuna a shafi na 7]
Ta wa’azinsu ga jama’a, Shaidun Jehovah suna ja-gorar mutane ga Kalmar Allah, Littafi Mai-Tsarki
[Inda Aka Ɗauko Hoto da ke shafi na 4]
Na uku daga hagu, United Nations/Photo daga Saw Lwin