Kalmar nan “Kirista” Ma’anarta Tana Canjawa Ne?
ME YAKE nufi a zama Kirista? Yaya za ka amsa tambayar? Mutane da aka zaɓa babu shiri daga ƙasashe dabam dabam an yi masu wannan tambayar, ga samfurin abin da suka ce:
“Ka bi Yesu kuma ka yi kwaikwayonsa.”
“Ka zama mutumin kirki mai hannu sake.”
“Ka karɓi Kristi Ubangiji ne kuma Mai Ceto.”
“Ka je Coci, ka ƙirga Carbi, kuma ka ci gibi.”
“Ban gaskata cewa sai ka je coci tukuna za ka zama Kirista ba.”
Har ƙamus ma sun bayar da ma’ana da yawa masu wuyan ganewa. Wani, ya bada ma’ana goma a ƙarƙashin kalmar nan “Kirista,” kamawa daga “gaskatawa da ko kuma kasancewa cikin addinin Yesu Kristi” zuwa “mutum mai tarbiyya ko kuma amincecce.” Ba abin mamaki ba ne cewa yana yi wa mutane da yawa wuya su ba da bayanin abin da yake nufi a zama Kirista.
Hanyar ’Yanci
A yau, a tsakanin masu da’awar su Kirista ne—tsakanin waɗanda suke zama tare a kan benci a cikin coci—za a sami ra’ayoyi dabam dabam a kan batutuwa kamar su hurewan Littafi Mai-Tsarki, ra’i na bayyanau, coci suna shiga cikin siyasa, da kuma gaya wa wasu game da bangaskiyarka. A batun ɗabi’a, jigo kamar su zubar da ciki, luwaɗi, da kuma mace da miji suna zama tare babu aure, sau da yawa ya kan zama abin jayayya. Babu shakka hanyar ’yanci ce.
Alal misali, wani mai tsai da shawara a cocin Farotasta, a baya bayan nan ya jefa ƙuri’ar ɗaukaka ’yancin coci ta “zaɓi dattijo da aka san mai luwaɗi ne ya zama mai kula da harkokin cocin,” in ji jaridar Christian Century. Wasu ’yan tauhidi sun ba da ra’ayin cewa bangaskiya ga Yesu ba dole ba ne don a sami ceto. Sun gaskata cewa Yahudawa, Musulmai, da wasu “ƙila za su samu zuwa sama [kamar yadda Kiristoci za su yi],” in ji wani rahoto daga cikin The New York Times.
Ka yi tunani idan za ka iya, mabiyin Marx yana ɗaukaka ’yancin kasuwanci, ɗan dimokuraɗiyya yana ɗaukaka mulkin kama-karya, mai kula da mahalli yana ɗaukaka sare daji. Ka ce: “Ai wannan mutumin ba zai zama mabiyin Marx ko ɗan dimokuraɗiyya ko mai kula da mahalli,” ba—to daidai ka faɗa. Saboda haka, idan ka duba ra’ayoyi dabam dabam da masu da’awar su Kirista suke da shi a yau, za ka ga imani da suke da nisa da juna waɗanda koyaushe suke saɓani da abin da wanda ya Kafa Kiristanci, Yesu Kristi, ya koyar. Menene irin waɗannan ra’ayoyin ya nuna game da irin Kiristancinsu?—1 Korinthiyawa 1:10.
Abin da yake motsa su su canja koyarwan Kiristoci don ya dace da halinsu na zamani yana da dogon tarihi, kamar yadda za mu gani. Yaya Allah da Yesu Kristi suke ji game da waɗannan canji? Cocin da suke goyon bayan koyarwan da ba su da tushe cikin Kristi za su iya kiran kansu Kiristoci ne? Waɗannan tambayoyi za a bincika su a cikin talifi na gaba.