Ka Mai Da Hankali Ga Kalmomin Annabci Na Allah Don Kwanakinmu
“Ya ɗan mutum, sai ka gane; gama ru’uyar ta zamanin ƙarshe ce.”—DANIEL 8:17.
1. Menene Jehovah yake son dukan mutane su sani game da kwanakinmu?
JEHOVAH ba ya riƙe sanin abubuwa da za su faru nan gaba ma kansa kaɗai ba. Maimako, shi Mai Bayyana asirai ne. Hakika, yana son dukanmu mu sani cewa mun yi nisa cikin “zamani na ƙarshe.” Lallai wannan labari ne na musamman ga mutane biliyan shida da suke cikin duniya yanzu!
2. Me ya sa mutane suka damu game da abin da ke zuwa masu a nan gaba?
2 Akwai wani abin mamaki ne cewa wannan duniya ta kai ƙarshenta? Mutum yana iya yin tafiya a duniyar wata, amma a wurare da yawa ba zai iya yin tafiya a tituna na wannan duniya babu tsoro ba. Yana iya cika gida da kayayyakin zamani, amma ba zai iya ɗaure danƙon zumuncin iyalai da suke rabuwa ba. Kuma zai iya kawo ingantaccen ilimi, amma ba zai iya koyar da mutane yadda za su zauna lafiya da junansu ba. Wannan kasawar tana goyon bayan tabbaci na Nassi masu yawa cewa muna rayuwa cikin lokaci na ƙarshe.
3. Yaushe ne aka soma yin amfani da kalmomin nan “zamanin ƙarshe” a duniya?
3 Mala’ika Jibrailu ne ya soma yin amfani da waɗannan kalmomi masu ma’ana—“zamanin ƙarshe”—shekara 2,600 da suka shige. Wani annabin Allah wanda ya tsorata ya ji Jibrailu yana cewa: “Ya ɗan mutum, sai ka gane; gama ru’uyan ta zamanin ƙarshe ce.”—Daniel 8:17.
Wannan Shi ne “Zamanin Ƙarshe”!
4. A waɗanne hanyoyi ne kuma Littafi Mai-Tsarki ya yi nuni ga zamanin ƙarshe?
4 Furcin nan “zamanin ƙarshe” da kuma “sa’a da aka ƙadara ke nan ta ƙarshe” ya auku sau shida cikin littafin Daniel. (Daniel 8:17, 19; 11:35, 40; 12:4, 9) Game da “kwanaki na ƙarshe” suke wanda manzo Bulus ya annabta. (2 Timothawus 3:1-5) Yesu Kristi ya nuna wannan sa’ar cewa ita ce na ‘bayanuwarsa’ Sarki da aka naɗa a sama.—Matta 24:37-39.
5, 6. Su wanene sun ta ‘kaiwa da kawowa’ cikin zamanin ƙarshe, kuma da wane sakamako?
5 Daniel 12:4 ya ce: “Kai, ya Daniel, ka kulle zantattukan, ka rufe littafin da hatimi, har kwanakin ƙarshe; mutane dayawa za su kai da kawo a guje, ilimi kuma za ya ƙaru.” An sa yawancin abin da Daniel ya rubuta ya zama asiri kuma an kulle fahimtarsu daga mutane cikin ƙarnuka. Amma me kuma za a ce game da yau?
6 A cikin wannan zamanin ƙarshe, Kiristoci masu aminci da yawa sun yi ‘kaiwa da kawowa’ cikin shafofin Kalmar Allah, Littafi Mai-Tsarki. Menene Sakamakon haka? Tare da albarkar Jehovah a kan ƙoƙarce-ƙoƙarcensu, sani na gaske ya ƙaru. Alal misali, an albarkaci shafaffu Shaidun Jehovah da hikima, wadda ta taimake su suka fahimci cewa Yesu Kristi ya zama Sarki na samaniya a shekara ta 1914. Daidai da kalmomin manzo da ke rubuce a 2 Bitrus 1:19-21, waɗannan shafaffu da abokansu masu aminci suna ‘saurara ga kalmar annabci’ kuma sun tabbata sarai cewa wannan shi ne zamanin ƙarshe.
7. Waɗanne labarai ne suka sa littafin Daniel ya zama da girma?
7 Littafin Daniel da girma yake a hanyoyi dabam dabam. A cikin shafofinsa, wani sarki ya yi burgan zai kakkashe maza masu hikima domin ba su iya bayyana kuma su fassara mafarkinsa mai wuya ba, amma annabin Allah ya warware matsalar. An jefa samari uku da suka ƙi bauta wa wani gunki mai tsawo a tanderu mai ƙuna, duk da haka sun tsira babu wani taɓo. A lokacin wani biki, ɗarurruwan mutane sun ga hannu da ke rubutu mai wuyan ganewa bisa bangon fada. Wasu miyagun mutane sun jefa wani tsohon mutum da suka ƙulla wa makirci cikin ramin zakuna, amma ya fito babu ko rauni. An ga bisashe huɗu cikin ru’uya, kuma ma’anarsu ta annabci ta kai har cikin zamanin ƙarshe.
8, 9. Ta yaya littafin Daniel zai amfane mu, musamman yanzu, cikin zamanin ƙarshe?
8 A bayyane, littafin Daniel yana ɗauke da mahaɗi biyu da sun bambanta. Ɗaya na labarai ne, ɗaya kuma na annabci. Su biyun za su iya gina bangaskiyarmu. Labaran sun nuna mana cewa Jehovah Allah ya albarkace waɗanda suka riƙe gaskiya gareshi. Sashe na annabci yana gina bangaskiya ta wurin nuna cewa Jehovah ya san tafarkin tarihi na ƙarnuka—har ma na dubban shekaru—tun da daɗewa.
9 Annabce-annabce dabam dabam da Daniel ya rubuta yana magana ne game da Mulkin Allah. Yayin da muke lura da cikan irin waɗannan annabce-annabcen, bangaskiyarmu tana daɗa ƙarfi kuma hakanan ma tabbacin da muke da shi cewa muna zama cikin zamanin ƙarshe. Amma wasu ’yan suka sun tuhume Daniel, suna cewa an rubuta annabce-annabce da ke cikin littafin da ke ɗauke da sunansa ne bayan aukuwan da ake tsammanin wai sun cika su ne. Idan wannan da’awar gaskiya ce, wannan zai tada tambayoyi masu sa tunani game da abin da littafin Daniel ya annabta game da zamanin ƙarshe. Masu-shakka kuma sun tuhume labaran littafin. Saboda haka, bari mu bincika.
A Gaban Shari’a!
10. A wane hali ne littafin Daniel yake gaban shari’a?
10 Ka ji kamar kana cikin fadar shari’a, ana kan yin maka tambayoyi. Lauyan ya nace cewa wanda aka yi ƙararsa yana da laifin ha’inci. To dai, littafin Daniel ya nuna kansa cikakken aiki da annabi Ba’ibra’ine ya rubuta wanda ya rayu cikin ƙarnuka na bakwai da shida K.Z. Amma ’yan suka sun ce wai littafin ha’inci ne. Saboda haka, bari mu soma duba idan sashen labari na littafin ya jitu da lazu na tarihi.
11, 12. Menene ya faru ga tuhumar nan ta cewa Belshazzar wani ne wanda bai wanzu da gaske ba?
11 A ce mu bincika abin da za a iya ce wai shari’ar sarki da ya ɓata. Daniel sura 5 ta nuna cewa Belshazzar yana sarauta cikin Babila lokacin da aka ci birnin a 539 K.Z. ’Yan suka suna jayayyar wannan zance domin babu sunan Belshazzar a wani wuri ban da Littafi Mai-Tsarki. Maimakon haka, ’yan tarihi na dā sun amince cewa Nabonidus ne sarkin Babiloniya na ƙarshe.
12 Amma, cikin shekara ta 1854, an tone wasu rubuce-rubuce bisa dutse cikin kangon birnin Babiloniya ta Ur ta dā, a Iraq ta zamani. Waɗannan rubutu a kan dutsen sun haɗa da wani addu’a wanda Sarki Nabonidus ya ambata “Bel-sar-ussur, babban ɗana.” Ko ’yan sukan kansu sun yarda cewa: Wannan Belshazzar na littafin Daniel ne. Saboda haka sarkin da ya ɓata bai ɓata ba, sai dai ba a sani ba tukuna cikin majiya ta duniya. Wannan ɗaya ne kawai cikin tabbaci da yawa na cewa rubuce-rubucen Daniel suna da gaskiya. Wannan tabbaci ya nuna cewa littafin Daniel sashin Kalmar Allah ce da ta kamata mu mai da hankalinmu sosai yanzu, a cikin zamanin ƙarshe.
13, 14. Wanene Nebuchadnezzar, kuma ga wane allahn ƙarya ne musamman ya ba da kai?
13 An haɗa annabce-annabcen kafa masu ikon duniya da ayyukan wasu sarakunansu cikin littafin Daniel. Za a iya ce da ɗaya cikin waɗannan sarakunan jarumi wanda ya gina daula. Yayin da aka naɗa shi hakimin Babiloniya, shi da rundunarsa suka ragargaje rundunar Fir’auna Necho na Masar a Karchemish. Amma wani saƙo ya sa hakimi mai nasara ya bar janar ɗinsa su tsai da shawarar da suke so. Da ya ji cewa ubansa Nabopolassar, ya mutu, saurayi Nebuchadnezzar ya hau kursiyin a 624 K.Z. A cikin shekara ta 43 na sarautarsa, ya gina daula da ta ƙunshi yankuna da Assuriya suke zama dā, kuma ya faɗaɗa mulkinsa zuwa Suriya da kuma Palasɗinu har zuwa iyakar Masar.
14 Nebuchadnezzar yana sujjadarsa musamman ga Marduk ne, babban allan Babila. Sarkin yana yaba wa Marduk wai shi ne tushen nasarori da ya yi. A cikin Babila, Nebuchadnezzar ya gina kuma adana haikalai na Marduk da kuma allolin Babiloniya da yawa. Mai-yiwuwa ne an keɓe siffar zinariya da wannan sarkin Babila ya kafa a filin Dura, ga Marduk. (Daniel 3:1, 2) Kuma kamar dai Nebuchadnezzar ya dogara sosai bisa duba don ya shirya tafiyar sojojinsa.
15, 16. Menene Nebuchadnezzar ya yi wa Babila, kuma me ya faru lokacin da ya yi fahariya game da girmanta?
15 Da ya gama gina garun Babila da ya yi ninki biyu, wanda ubansa ya soma gininsa, Nebuchadnezzar ya sa ya yi wuya a shiga babban birnin. Don ya gamsar da sarauniyarsa ta Mediya, wadda take sha’awar tuddai da kuma kurmi na ƙasar haihuwarta, an ce Nebuchadnezzar ya yi gonaki da suke rataye—ɗaya cikin abubuwa bakwai na ban mamaki na duniyar dā. Ya sa Babila ta zama birni da take da garu mafi girma a lokacin. Kuma ji yadda ya yi fahariya da wajen bautar ƙarya!
16 Wata rana Nebuchadnezzar ya yi fahariya: “Wannan ba ita ce Babila Babba wadda na gina?” Bisa ga Daniel 4:30-36, “magana tana cikin bakin sarki,” sai ya haukace. Bai dace ya yi sarauta ba, shekara bakwai, yana cin ciyayi, yadda Daniel ya annabta. Sai kuma aka maido masa da mulkinsa. Ka san ma’anar annabci na wannan duka? Za ka iya bayyana yadda cikarsa mai-girma ya kawo mu zuwa zamanin ƙarshe?
Ba da Mahaɗi na Annabci
17. Yaya za ka kwatanta annabci na mafarki da Allah ya yi wa Nebuchadnezzar a shekara ta biyu na sarki mai sarautar duniya?
17 Yanzu bari mu duba wasu mahaɗi na annabci a cikin littafin Daniel. A shekara ta biyu ta sarautar Nebuchadnezzar, sarkin duniya bisa annabcin Littafi Mai-Tsarki daga (606/605 K.Z.), Allah ya sa ya yi wani mafarki mai ban tsoro. Daidai da abin da Daniel sura 2 ta ce, mafarkin ya ƙunshi babban siffa mai kan zinariya, ƙirji da damutsa na azurfa, ciki da kuma cinyoyi na jan ƙarfe, ƙafafu na ƙarfe, da kuma sawaye na ƙarfe haɗe da tabo. Menene kowanne sashen siffar ke wakilta?
18. Menene kan zinariya, ƙirji da kuma damatsan azurfa, da ciki da kuma cinyan jan ƙarfe na siffar mafarki ke wakilta?
18 Annabin Allah ya gaya wa Nebuchadnezzar: “Ya sarki . . . kai ne wannan kai na zinariya.” (Daniel 2:37, 38) Nebuchadnezzar ya shugabanci mulki da ke sarautar Daular Babiloniya. Mediya-Persiya, wanda ƙirjin da kuma damutsan azurfa na siffar ke wakilta ne ya ci shi. Sai kuma ga Daular Hellas, wanda ciki da kuma cinyar jan ƙarfen yake hotonsa. Ta yaya ne mulkin wannan duniyar ya soma?
19, 20. Wanene Iskandari Mai Girma, kuma wane matsayi yake da shi da ya sa Hellas ta zama mai iko da duniya?
19 A cikin ƙarni na huɗu K.Z., wani saurayi ya kasance da muhimmiyar matsayi a cikar annabcin Daniel. An haife shi a shekara ta 356 K.Z., kuma duniya tana kiransa Iskandari Mai Girma. A lokacin da aka kashe ubansa Filibbus, a shekara ta 336 K.Z., Iskandari ɗan shekara 20 ya gaji kursiyi na Makidoniya.
20 A farkon Mayu na 334 K.Z., Iskandari ya soma kamfe na nasararsa. Yana da ƙaramin rundunar sojoji 30,000 da kuma matuƙan karusai 5,000. A kogin Granicus a arewa maso yammacin Asiya Ƙarama (da yanzu ta zama Turkey), Iskandari ya ci nasararsa ta farko a kan ’yan Pasiya a shekara ta 334 K.Z. A shekara ta 326 K.Z., wannan mai nasara ya riga ya ci su kuma ya iso gabashin kogin Indus, da ke Pakistan na zamani. Amma Iskandari ya yi hasarar yaƙinsa na ƙarshe lokacin da yake Babila. A ranar 13 ga Yuni, 323 K.Z., lokacin da yake da shekara 32 da watanni 8 kawai, sai Iskandari ya faɗa cikin hannun babban maƙiyi, mutuwa. (1 Korinthiyawa 15:55) A nasarar da ya ci, Hellas ta riga ta zama mai ikon duniya, yadda yake cikin annabcin Daniel.
21. Ban da Daular Romawa, waɗanne masu iko na duniya ne ƙafafun ƙarfe na siffar mafarkin ke hotonsu?
21 Menene ƙafafu na ƙarfe na babban siffar ke wakilta? To, Roma mai kama da ƙarfe ce ta rugurguje kuma ta ragargaje Daular Hellas. Ba su nuna girma ga Mulkin Allah wanda Yesu Kristi ya yi shelarsa ba, Roma ta kashe shi a kan gungume na azaba a 33 A.Z. A ƙoƙarinta na rushe Kiristanci na gaskiya, Roma ta tsanantawa almajiran Yesu. Amma kuma, ƙafafun ƙarfe na siffar mafarkin Nebuchadnezzar ba Daular Roma kawai take hotonta ba amma kuma girmarta ta siyasa—Masu iko da Duniya na Haɗin Britaniya da Amirka.
22. Ta yaya siffar mafarki yake taimakonmu mu ga cewa mun yi nisa cikin zamani na ƙarshe?
22 Bincike a hankali ya tabbatar da cewa mun yi nisa cikin zamani na ƙarshe, domin mun riga mun kai ƙafafun ƙarfe da tabo na siffar mafarkin. Wasu gwamnatoci na zamani kama suke da ƙarfe ko kuma masu mulkin kama-karya, yayin nan kuma wasu suna kama da tabo. Duk da yadda tabo yake da sauƙin fashewa, wanda da shi aka yi “zuriyar mutane,” wasu masu mulki da suke kama da ƙarfe sun matsu su ba talakawa dama cikin gwamnatocin da suke sarautarsu. (Daniel 2:43; Ayuba 10:9) Babu shakka, sarautar mulkin kama-karya da talakawa ba sa jituwa yadda ƙarfe da tabo suke. Amma ba da daɗewa ba Mulkin Allah zai kawo ƙarshen wannan duniya ta siyasa da take a ragargaje.—Daniel 2:44.
23. Yaya za ka kwatanta mafarki da kuma ru’uya da Daniel ya samu a shekara na farko na sarautar Belshazzar?
23 Sura ta 7 na annabcin Daniel mai ƙarfi ya kawo mu kuma cikin zamani na ƙarshe. Ya ambata wani aukuwa ta shekara na farko na Sarkin Babiloniya Belshazzar. A cikin shekararsa ta 70 Daniel ya yi “mafarki, ya ga ru’uya a cikin kansa yana gadonsa kwance.” Ya tsorata da ya ga ru’uyar! Ya yi ihu, “ga shi”! “Iskoki huɗu na sama suka fasu daga bisa kan babban teku. Manyan bisashe guda huɗu kuma suka taso daga cikin teku, kamarsu dabam dabam.” (Daniel 7:1-8, 15) Lallai kuwa bisashe masu girma! Na farko zaki mai fukafuki ne, na biyun kuma yana kama da karen daji. Sai kuma ga damisa da fukafukai huɗu da kuma kawuna huɗu! Bisan mai yawan ƙarfi yana da babban haƙorin ƙarfe da kuma ƙahoni goma. A tsakanin ƙahoni goman wani “ƙarami” ya taso yana da “idanu, masu-kama da na mutum” da kuma “baki kuma mai-furtadda manyan ruba.” Lallai halittu ne masu ban ƙyama!
24. Bisa ga Daniel 7:9-14, menene Daniel ya gani a sama, kuma menene wannan ru’uya take nuni?
24 Sai kuma ru’uyar Daniel ya juya zuwa sama. (Daniel 7: 9-14) An ga “Mai-Zamanin Dā,” Jehovah Allah, yana zaune bisa kursiyin daraja yana Alƙalanci. ‘Dubban dubbai kuma suna yi masa hidima, zambar goma kuma sau zambar goma suna tsaye a gabansa.’ Aka hukunce bisan da tsanani, Allah ya kwace sarauta daga wurinsu kuma ya halaka bisa na huɗun. Aka ba da sarauta mai daɗewa ga “mai-kama da ɗan mutum” a kan “al’ummai, da dangogi, da harsuna.” Wannan yana nuni ga zamanin ƙarshe da naɗa Ɗan mutum, Yesu Kristi a shekara ta 1914.
25, 26. Waɗanne irin tambayoyi za su iya tasowa bayan mun karanta littafin Daniel, kuma wane littafi zai iya amsa su?
25 Masu karatun littafin Daniel lallai za su yi wasu tambayoyi. Alal misali, menene bisashe huɗu na Daniel sura 7 suke wakilta? Menene fassarar annabcin “bakwai bakwai har saba’in” na Daniel 9:24-27? Me za a ce game da Daniel sura 11 da kuma fāɗa ta annabci tsakanin “sarkin arewa” da kuma “sarkin kudu”? Menene za mu zata daga waɗannan sarakuna a cikin zamanin ƙarshe?
26 Jehovah ya ba da fahimi game da irin al’amuran nan ga bayinsa shafaffu a duniya, “tsarkaka na Maɗaukaki,” yadda aka kira su kenan a Daniel 7:18. Ban da haka ma, “bawan nan mai-aminci, mai-hikima” ya yi tanadi don mu ƙara samun fahimi game da huraren rubuce-rubuce na annabi Daniel. (Matta 24:45) Akwai wannan yanzu a cikin sabon littafi wanda aka fitar mai suna Pay Attention to Daniel’s Prophecy! Wannan littafi mai kyau mai shafi 320 da ke cike da hotuna ya bayana kowanne sashen littafin Daniel. Yana ba da bayyanin kowanne annabci mai gina bangaskiya da kuma kowanne labari da ƙaunataccen annabi Daniel ya rubuta.
Ma’ana ta Gaske don Kwanakinmu
27, 28. (a) Mecece gaskiya game da cikar annabce-annabce a cikin littafin Daniel? (b) A cikin wane lokaci ne muke, kuma me ya kamata mu yi?
27 Yanzu sai ka yi la’akari da wannan darasi na musamman: Sai ko wasu zance kalilan, dukan annabce-annabce da ke cikin littafin Daniel sun cika. Alal misali, mun riga mun ga yanayin wannan duniya yadda sawun siffar mafarki na Daniel sura 2 ta nuna. An kunce itacen da aka ɗaure na Daniel sura 4 a lokacin da aka naɗa Yesu Kristi, Sarki Almasihu a shekara ta 1914. Hakika, yadda aka annabta a Daniel sura 7, Mai-Zamanin Dā ya ba da sarauta ga Ɗan mutum.—Daniel 7:13, 14; Matta 16:27–17:9.
28 Kwanaki 2,300 na Daniel sura 8 da kuma kwanaki 1,290 da 1,335 na sura 12, duk sun wuce—can bayanmu a cikin nisan lokaci. Nazarin Daniel sura 11 ya nuna cewa fāɗa tsakanin “sarkin arewa” da kuma “sarkin kudu” ya kai matuƙa. Duka wannan ya daɗa ga tabbaci na Nassi cewa mun yi nisa cikin zamanin ƙarshe. Sanin inda muke cikin lokacin nan, me za mu ƙudurta aniyar yi? Babu shakka, ya kamata mu ci gaba da saurarawa ga kalmomin annabci na Jehovah Allah.
Yaya Za Ka Amsa?
• Menene Allah yake son dukan mutane su sani game da kwanakinmu?
• Ta yaya ne littafin Daniel zai iya gina bangaskiyarmu?
• Waɗanne fasaloli ne siffar mafarki na Nebuchadnezzar take da shi, kuma menene waɗannan suke ba da alama?
• Menene ya kamata a lura game da cikan annabce-annabce da ke cikin littafin Daniel?