Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w12 7/1 p. 3
  • Dukan Kiristoci Ne Suke Bin Umurnin Kristi?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Dukan Kiristoci Ne Suke Bin Umurnin Kristi?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Makamantan Littattafai
  • Yadda Za Ka San Kiristoci na Gaske
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Ina Yadda Zaka Sami Addini na Gaskiya?
    Menene Allah Yake Bukata a Garemu?
  • Bincike Mafi Muhimmanci da Kake Bukatar Ka Yi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2016
  • Ka Kasance da Tabbaci Cewa Ka Sami Gaskiya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2021
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
w12 7/1 p. 3

Dukan Kiristoci Ne Suke Bin Umurnin Kristi?

KIRISTOCI guda nawa ne suke duniya? Littafin nan Atlas of Global Christianity ya nuna cewa a shekara ta 2010, akwai Kiristoci wajen biliyan 2.3 a faɗin duniya. Wannan littafin ya kuma nuna cewa waɗannan Kiristocin sun kasu ne zuwa ɗarika sama da 41,000, kuma dukansu suna da tasu koyarwa da kuma irin ɗabi’ar da suke bi. Shi ya sa mutane da dama suka rikice ko kuma suka daina bin addini domin akwai ɗariku dabam-dabam masu kiran kansu “Kirista.” Wasu suna mamaki, ‘Shin dukan mutanen da suke da’awar cewa su Kiristoci ne suke bin umurnin Kristi?’

Bari mu duba batun daga wani ɓangare dabam. Matafiyin da zai shiga ƙasarsu daga wata ƙasa yana bukatar ya nuna wa ma’aikacin gwamnati cewa shi ɗan ƙasa ne. Zai yi hakan ne ta wajen nuna katin shaida ko fasfo. Hakazalika, Kirista na gaskiya yana bukatar ya tabbatar da bangaskiyarsa ga Kristi ba da baki kawai ba. Yana bukatar ƙarin shaida. Mece ce shaidar?

An soma amfani da kalmar nan “Kirista” bayan shekara ta 44 A.Z. Ɗan tarihi Luka ya rubuta cewa: “A cikin Antakiya fa aka fara ce da masu-bi Krista.” (Ayyukan Manzanni 11:26) Waɗannan mutanen da aka kira Kiristoci almajiran Kristi ne. Ta yaya mutum yake zama almajirin Yesu Kristi? Littafin nan The New International Dictionary of New Testament Theology ya yi bayani: “Bin Yesu a matsayin almajiri yana nufin cewa mutum zai sadaukar da ransa ba tare da wani sharaɗi ba . . . har iyakacin rayuwar[sa].” Saboda haka, Kirista na gaskiya shi ne mutumin da ke bin koyarwa da umurnin Yesu, sawu da kafa.

Zai yiwu ne a sami irin waɗannan mutanen a tsakanin mutane da yawa da suke da’awar cewa su Kiristoci ne a yau? Mene ne Yesu da kansa ya ce zai zama alamar da zai sa a gane mabiyansa na gaskiya? Muna gayyatarka ka bincika yadda Littafi Mai Tsarki ya amsa waɗannan tambayoyin. A talifofi na gaba, za mu bincika furuci guda biyar da Yesu Kristi ya yi waɗanda za su taimaka mana mu gane mabiyansa na gaskiya. Za mu bincika yadda Kiristoci a ƙarni na farko suka nuna cewa suna da irin waɗannan halayen. Za mu kuma bincika ko su wane ne suke nuna irin waɗannan halayen a cikin mutane masu yawa da suke da’awar cewa su Kiristoci ne a yau.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba