Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w00 2/1 pp. 25-30
  • Yin Murna Cikin Allah Mai Cetonmu

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Yin Murna Cikin Allah Mai Cetonmu
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Habakkuk Ya Yi Addu’a don Jinƙai daga Allah
  • Jehovah Yana Kan Tafiya!
  • An Tabbatar da Ceto ga Mutanen Allah!
  • Ranar Jehovah Tana Zuwa!
  • Ka Dogara ga Jehobah Don Ka Rayu!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2018
  • Nawa Ne Yawan Lokaci Da Ya Rage Ma Miyagu?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • Jehovah Ba Zai Yi Jinkiri Ba
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • Ku Bi Gurbin Annabawa—Habakkuk
    Hidimarmu Ta Mulki—2015
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
w00 2/1 pp. 25-30

Yin Murna Cikin Allah Mai Cetonmu

“Zan yi murna cikin Ubangiji; zan yi murna a cikin Allah mai-cetona.”—HABAKKUK 3:18.

1. Game da menene Daniel ya ga ru’ya kafin faɗuwar Babila a shekara ta 539 K.Z.?

FIYE da shekaru goma kafin faɗuwar Babila a shekara ta 539 K.Z., tsoho annabi Daniel ya ga ru’ya mai ban sha’awa. Ya annabta abubuwa da za su faru a duniya da zai kai har ga yaƙi na ƙarshe tsakanin magabtan Jehovah da Sarki da ya naɗa, Yesu Kristi. Menene Daniel ya yi? Ya ce: “Na suma . . . na yi mamaki da ru’yan.”—Daniel 8:27.

2. Wane faɗā Daniel ya gani cikin ru’ya, kuma yaya ka ke ji game da kusatowarta?

2 Mu kuma fa? Ai lokaci ya ƙare! Menene muke yi yayin da muka gane cewa faɗā da Daniel ya gani cikin ru’yan—yaƙin Allah na Armageddon—ya yi kusa sosai? Menene muke yi yayin da muka gane cewa mugunta da aka nuna cikin annabcin Habakkuk yana ko’ina yadda ba za a iya guje ma hallaka na magabtan Allah ba? Mai-yiwuwa, yadda muke ji ya yi daidai da na Habakkuk kansa, yadda aka kwatanta su cikin sura ta uku na littafin annabcinsa.

Habakkuk Ya Yi Addu’a don Jinƙai daga Allah

3. A madadin su wanene Habakkuk ya yi addu’a, kuma ta yaya kalmominsa za su iya shafan mu?

3 Habakkuk sura ta 3 addu’a ce. Daga aya 1, kalmomin waƙar makoki ne, waƙoƙin baƙinciki ko kuma makoki. Annabin ya yi addu’a kamar dai yana yi ma kansa ne. Amma ainihi, Habakkuk yana magana ne a madadin zaɓaɓɓan al’ummar Allah. A yau, addu’arsa tana da ma’ana mai girma ga mutanen Allah waɗanda suka shagala cikin aikin wa’azi na Mulki. Yayin da muka karanta Habakkuk sura ta 3 tare kuma muka tuna da wannan, kalmominsa za su hana mu abubuwa da yawa amma kuma za su cika mu da farinciki. Addu’ar Habakkuk, ko kuma waƙar makoki, tana ba mu dalili mai ƙarfi na yin murna cikin Jehovah, Allah mai cetonmu.

4. Me ya sa Habakkuk ya tsorata, kuma a wane nuna iko na Allah ne za mu tabbata?

4 Kamar yadda mun lura cikin talifi biyu da suka gabata, yanayin ƙasar Yahuda a kwanakin Habakkuk ba shi da kyau. Amma Allah ba zai yarda yanayin nan ya ci gaba ba. Jehovah zai aikata, kamar yadda ya yi a dā. Babu mamaki da annabin ya damu: “Ya Ubangiji, na ji labarinka, na kuwa ji tsoro: Ya Ubangiji, ka wartsakadda aikinka”! Menene yake nufi? ‘Labari game da Jehovah shine tarihin da aka rubuta na ayyuka masu girma na Allah, kamar waɗanda suka faru a Jan Teku, cikin daji, da kuma a Jericho. Habakkuk ya san da ayyukan nan sosai, kuma sun sa shi jin tsoro domin ya san cewa Jehovah zai sake yin amfani da ikonsa mai-girma akan magabtansa. Yayin da muke ganin muguntar mutane a yau, mu ma mun san cewa Jehovah zai aikata kamar yadda ya yi a lokuttan dā. Shin wannan yana sa mu mu tsorata ne? Hakika kuwa! Duk da haka, muna yin addu’a yadda Habakkuk ya yi: “Ka wartsakadda aikinka a cikin tsakiyar shekaru; ka sanadda shi a cikin tsakiyar shekaru; a cikin fushi ka tuna da jinƙai.” (Habakkuk 3:2) Cikin ayanannen lokaci na Allah, “a cikin tsakiyar shekaru,” bari shi soma aiki da ikonsa mai girma. Kuma a wannan lokacin, bari shi tuna shi nuna jinƙai ga waɗanda suke ƙaunarsa!

Jehovah Yana Kan Tafiya!

5. Yaya ‘Allah ya zo daga Teman,’ kuma menene wannan ya nuna game da Armageddon?

5 Menene zai faru yayin da Jehovah ya amsa addu’armu na neman jinƙai? Mun sami amsa a Habakkuk 3:3, 4. Da farko, annabin ya ce: “Allah ya zo daga Teman, Mai-tsarki kuma daga dutsen Paran.” Can lokacin Musa, Teman da Paran suna kan hanyar Isra’ila a cikin daji ta wajajen Kan’ana. Yayin da al’ummar Isra’ila mai girma ke cikin tafiya, Jehovah kansa kamar yana cikin tafiya ne, kuma babu abin da zai iya dakatar da shi. Jim kaɗan kafin Musa ya mutu, ya ce: “Ubangiji ya zo daga Sinai, Ya taso daga Seir zuwa garesu; daga dutsen Paran ya haskaka masu, daga wurin zambar goma na tsarkaka [na mala’iku] ya taso.” (Kubawar Shari’a 33:2) Yayin da Jehovah zai juya ga magabtansa a Armageddon, hakanan ne ma zai nuna girmansa mai yawa da ba za a iya guje masa ba.

6. Ƙari ga ɗaukakar Allah, menene Kiristoci masu fahimi suke gani?

6 Habakkuk ya kuma faɗa: “Darajatasa [Jehovah] ta rufe sammai, duniya kuwa ta cika da yabonsa. Sheƙinsa yana kama da haske.” Dubi irin wannan kyaun! Gaskiya, mutane ba za su iya ganin Jehovah Allah kuma su rayu ba. (Fitowa 33:20) Amma dai, ga amintattu bayin Allah, idanun zuciyarsu sun yi murna yayin da sun tuna da ɗaukakarsa. (Afisawa 1:18) Kuma Kiristoci masu fahimi suna ganin ƙarin wani abu ga ɗaukakar Jehovah. Habakkuk 3:4 ya kammala da haka: “Ƙalƙali suna fitowa daga hannunsa; ikonsa kuwa a rufe ya ke.” I, mun ga cewa Jehovah a shirye yake ya aika, zai yi amfani da hannun damansa na ƙarfi da iko.

7. Tafiyar da Allah zai yi na nasara zai zama menene ga waɗanda suke masa tawaye?

7 Tafiyar da Allah zai yi na nasara zai zama bala’i ga waɗanda suke masa tawaye. Habakkuk 3:5 ya ce: “A gabansa ga aloba tafe; gawayi masu-cin wuta suna fita daga wajen sawayensa.” Lokacin da Isra’ilawa suka yi kusa da Ƙasar Alkawari a shekara ta 1473 K.Z., da yawa sun yi tawaye, sun yi lalata kuma sun bauta ma gumaka. A sakamakon haka, mutane sama da 20,000 suka mutu daga annoba da Allah ya aiko. (Litafin Lissafi 25:1-9) A nan gaba, lokacin da Jehovah zai yi tafiya zuwa “yaƙin babbar rana ta Allah Mai-iko duka,” waɗanda suke masa tawaye su ma za su sha wahala don zunubansu. Wasu ma za su mutu daga annoba ta zahiri.—Ru’ya ta Yohanna 16:14, 16.

8. Bisa ga Habakkuk 3:6, menene ke akwai ga magabtan Allah?

8 Ka saurara yanzu ga kwatancin annabci na aikatawar Jehovah mai-runduna. A Habakkuk 3:6, mun karanta: “[Jehovah Allah] ya tsaya, ya auna duniya; ya duba, ya kori al’ummai ya warwatsa su; madawaman duwatsu kuma suka warwatsu, tuddai na fil’azal suka sunkuya; tafarkunsa na tun zamanu ne.” Da farko Jehovah “ya tsaya,” kamar janar da yake bincika filin yaƙi. Magabtansa sai rawan jiki suke yi don tsoro. Sun ga yadda abokin gabansu yake kuma sun razana, suna tsalle cikin ruɗewa. Yesu ya annabta lokacin da “dukan kabilan duniya za su yi baƙinciki.” (Matta 24:30) Sun maƙara sosai da za su gane cewa babu wanda zai iya tsayawa a gaban Jehovah. Ƙungiyoyin ’yan Adam—ko ma waɗanda kamar sun kafu sosai, kamar su “madawaman duwatsu” da kuma “tuddai na fil’azal”—za su farfashe. Zai zama kamar ‘tafarkunan [Allah] na tun zamanu,’ kamar yadda ya yi a lokuttan dā.

9, 10. Menene Habakkuk 3:7-11 ya tuna mana?

9 ‘Fushin Jehovah ya yi zafi’ akan abokan gabansa. Amma wane makamai zai yi amfani da su a yaƙinsa mai girma? Ku saurara yayin da annabin yake kwatanta su, yana cewa: “An tsiraitadda bakanka sarai; rantserantse zuwa ga kabilai tabbatacen zance ne. Ka tsaga duniya da koguna. Duwatsu suka gan ka, suka ji tsoro; hadari na ruwaye ya wuce; zurfafa suka furta murya, suka tada hannuwansu sama. Rana da wata suka tsaya kurum a mazauninsu; da ganin hasken kibawunka yayinda su ke tafiya, da sheƙin mashinka mai-walƙiya.”—Habakkuk 3:7-11.

10 A kwanakin Joshua, Jehovah ya sa rana da wata su tsaya cak ta wurin nuna iko na ban mamaki. (Joshua 10:12-14) Annabcin Habakkuk ya tuna mana cewa irin wannan ikon har illa na hannun Jehovah a Armageddon. A shekara ta 1513 K.Z., Jehovah ya nuna ikonsa bisa ruwayen duniya lokacin da ya yi amfani da Jan Teku don hallakar da rundunar Fir’auna. Shekaru 40 daga baya, kogin Urdun da ya cika da ruwa bai hana Isra’ila ta ci nasara a shigewa zuwa Ƙasar Alkawari ba. (Joshua 3:15-17) A kwanakin annabiya Deborah, ruwan sama mai gudu ƙwarai ya wanke karusan Sisera magabtan Isra’ila. (Alƙalawa 5:21) Waɗannan ikon rigyawa, ruwan sama mai gudu ƙwarai, da kuma ruwa mai zurfi har illa yau suna hannun Jehovah a Armageddon. Tsawa da kuma walƙiya ma suna cikin hannunsa, kamar mashi ko kuma kwāri da ke cike da kibiyoyi.

11. Menene zai faru lokacin da Jehovah zai zazzage ƙarfin ikonsa mai girma?

11 A gaskiya, zai zama da ban tsoro lokacin da Jehovah zai zazzage dukan ƙarfin ikonsa mai girma. Kalmomin Habakkuk sun nuna cewa dare zai komo rana, rana kuma za ta yi haske fiye da yadda ta kan iya haskakawa. Ko wannan huraren kwatancin annabci na Armageddon na zahiri ne ko kuma na alama, abin da mun tabbata shine—Jehovah zai yi nasara, kuma babu wani magabci da zai tsira.

An Tabbatar da Ceto ga Mutanen Allah!

12. Menene Allah zai yi ma magabtansa, amma zai ceci su wa?

12 Annabin ya ci gaba da kwatanta ayyukan Jehovah wajen hallaka Magabtansa. A Habakkuk 3:12, mun karanta: “Kā ratsa ƙasan da haushinka, kā dudduke al’ummai da fushi.” Duk da haka, Jehovah ba zai hallaka mutane barkatai kawai ba. Wasu mutane za su tsira. “Kā fita garin ceton mutanenka, domin ceton shafaffenka,” in ji Habakkuk 3:13. I, Jehovah zai ceci amintattu shafaffun bayinsa. A lokacin ne za a gama hallaka Babila Babba, daular duniya ta addinin ƙarya. Amma, a yau, al’ummai suna ƙoƙarin kawar da sujada mai tsarki. Bada daɗewa ba, dakarun Gog na Magog za su faɗā ma bayin Jehovah. (Ezekiel 38:1–39:13; Ru’ya ta Yohanna 17:1-5, 16-18) Wannan faɗāwar za ta yi nasara kuwa? A’a! A lokacin ne Jehovah zai ragargaza magabtansa da fushi, zai tattake su da ƙafa kamar hatsi a wurin bugun hatsi. Amma zai ceci waɗanda suke bauta masa da ruhu da kuma gaskiya.—Yohanna 4:24.

13. Ta yaya Habakkuk 3:13 zai cika?

13 An annabta yadda za a hallaka miyagu gaba ɗaya cikin waɗannan kalmomi: “Cikin gidan miyagu [Jehovah] ka yi ma kan rauni, kana bubbuɗe tushen har zuwa wuya.” (Habakkuk 3:13) Wannan “gidan” shine mugun tsari da ya taso ƙarƙashin tasirin Shaitan Iblis. Za a ragargaza shi. Za a rugurguje “kan,” ko kuma shugabanni magabtan Allah. Za a rushe dukan shirin, har tushensa. Ba zai kasance kuma ba. Dubi kwanciyar rai da wannan zai kawo!

14-16. Bisa ga Habakkuk 3:14, 15, menene zai faru ma mutanen Jehovah da kuma ga magabtansu?

14 A Armageddon, za a rikita waɗanda suke ƙoƙarin su hallaka “shafaffe” na Jehovah. Bisa ga Habakkuk 3:14, 15, annabin ya ce haka game da Allah: “Da nasa sanduna ka sha zarar kan mayaƙansa; suka zo kamar guguwa domin su warwatsa ni; farincikinsu ne su cinye matalauta a ɓoye. Kā taka teku da dawakanka, tattaruwan manyan ruwaye.”

15 Yayin da Habakkuk ya ce “mayaƙa . . . suka zo kamar guguwa domin su warwatsa ni,” annabin yana magana ne a maimakon bayin Jehovah shafaffu. Kamar ɓarayi da ke a ɓoye, wuf al’ummai za su faɗā ma masu bauta ma Jehovah don su hallaka su. Waɗannan magabtan Allah da na mutanensa za su yi ‘farinciki,’ da tabbacin yin nasara. Amintattun Kiristoci za su zama kamar ba su da ƙarfi, kamar “matalauta.” Amma lokacin da magabtan Allah suke kan faɗā masu, Jehovah zai sa su juya da makamansu akan junansu. Za su yi amfani da makamansu, ko kuma “sanduna,” akan mayaƙan nasu.

16 Ba shi kenan ba. Jehovah zai yi amfani da dakaru na ruhu da sun fi na mutane don ya gama hallaka abokan gabansa. Tare da “dawakai” na rundunarsa na samaniya ƙarƙashin Yesu Kristi, zai ci gaba da nasara cikin “teku” da kuma “tattaruwan manyan ruwaye,” watau, tarin mutane magabta. (Ru’ya ta Yohanna 19:11-21) Lokacin ne za a cire miyagu daga duniya. Dubi nuna iko da hukunci mai girma na Allah!

Ranar Jehovah Tana Zuwa!

17. (a) Me ya sa za mu kasance da tabbaci a cikar kalmomin Habakkuk? (b) Yaya za mu zama kamar Habakkuk yayin da muke jiran babbar ranar Jehovah?

17 Za mu iya kasancewa da tabbaci cewa bada daɗewa ba kalmomin Habakkuk za su cika. Ba za su yi jinkiri ba. Yaya ka ke ji game da wannan bayani? Ka tuna cewa Habakkuk ya yi rubutu cikin hurewar Allah ne. Jehovah zai aikata, kuma duniya za ta rikice lokacin da wannan zai faru. Ba mamaki da annabin ya rubuta haka: “Na ji, cikina kuma ya yi rawa, leɓunana suka yi makerketa da jin muryan; ruɓewa ta shigo cikin ƙasussuwana, na yi rawa a matsayina; in huta, ina jiran ranar wahala; sa’anda ta auko ma mutanen da ke kawo masa yaƙi da runduna.” (Habakkuk 3:16) Habakkuk ya damu sosai—hakan daidai ne. Amma bangaskiyarsa ta jijjigu ne? Ko kaɗan! A shirye yake ya jira ranar Jehovah. (2 Bitrus 3:11, 12) Shin ba halinmu ke nan ba ma? Hakika! Muna da cikakkiyar bangaskiya cewa annabcin Habakkuk zai cika. Amma kafin ya cika fa, za mu jira cikin haƙuri.

18. Ko da yake Habakkuk ya san zai sha wahala, wane hali yake da shi?

18 Yaƙi yakan jawo wahala, ko ga waɗanda suka ci nasara ma. Za a iya yin ƙarancin abinci. Za a iya yin hasarar arziki. Yanayin rayuwa zai iya raguwa. Idan wannan ya faru da mu, yaya za mu ji? Habakkuk yana da hali da ya kamata mu yi koyi da shi, don ya ce: “Gama ko da shi ke itacen ɓaure ba za ya yi fure ba, ba kuwa ’ya’ya a cikin kuringar anab ba; wahalar zaitun ta zama banza, gonaki ba su bada abinci ba: ko da za a raba tumaki da wurin zamansu, ba a iske shanu a dangwalinsu ba; duk da haka zan yi murna cikin Ubangiji; zan yi murna a cikin Allah mai-cetona.” (Habakkuk 3:17, 18) Habakkuk ya san zai sha wahala, mai-yiwuwa yunwa. Duk da haka, bai taɓa baƙinciki da Jehovah ba, wanda daga wurinsa ne cetonsa yake.

19. Waɗanne wahala Kiristoci da yawa suke sha, amma menene za mu tabbata idan mun sa Jehovah a farko cikin rayuwarmu?

19 A yau, ko ma kafin Jehovah ya yi yaƙi da miyagu, mutane da yawa suna shan wahala sosai. Yesu ya annabta cewa yaƙe-yaƙe, yunwa, girgizan ƙasa, da kuma cututtuka za su zama wasu cikin ‘alamar bayanuwarsa’ cikin ikon sarauta. (Matta 24:3-14; Luka 21:10, 11) Yan’uwanmu da yawa suna zama cikin ƙasashe inda kalmomin Yesu suke cika sosai, kuma suna shan wahala sosai a sakamakon haka. Wasu Kiristoci za su iya shan irin wahalar nan a nan gaba. Ga yawancinmu fa, zai iya yiwu cewa “itacen ɓaure ba za ya yi fure ba” kafin ƙarshen ya zo. Amma, mun san dalilin da ya sa waɗannan abubuwan ke faruwa, kuma wannan yana ba mu ƙarfi. Ban da haka ma, muna da goyon baya. Yesu ya yi alkawari haka: “Amma ku fara biɗan mulkinsa, da adilcinsa [Allah]; waɗannan abu duka fa za a ƙara maku su.” (Matta 6:33) Wannan bai tabbatar da lafiyayyen rayuwa ba, amma ya tabbatar mana cewa idan mun sa Jehovah farko cikin rayuwarmu, zai lura da mu.—Zabura 37:25.

20. Duk da wahala na ɗan lokaci, menene ya kamata mu ƙuduri aniyar yi?

20 Duk wani wahala na ɗan lokaci da za mu fuskanta, ba za mu yi rashin bangaskiya cikin ikon ceto na Jehovah ba. Yan’uwanmu da yawa cikin Afirka, Gabashin Turai, da kuma wasu wurare suna fuskantar wahala ƙwarai, amma sun ci gaba da ‘yin farinciki cikin Jehovah kansa.’ Bari mu ma, kamar su, kada mu daina yin haka. Ka tuna cewa Jehovah Ubangiji Mai Ikon Mallaka shi ne Tushen “ƙarfi” namu. (Habakkuk 3:19) Ba zai taɓa sa mu nadama ba. Tabbas ne cewa Armageddon zai zo, kuma lallai sabuwar duniya da Allah ya yi alkawarinta za ta biyo Armageddon. (2 Bitrus 3:13) Sai kuma, “duniya za ta cika da sanin darajar Ubangiji, kamar yadda ruwaye sun rufe teku.” (Habakkuk 2:14) Kafin lokacin nan na ban al’ajibi, bari mu bi misali mai kyau na Habakkuk. Bari mu ci gaba da ‘yin farinciki cikin Jehovah kuma mu yi murna cikin Allah mai cetonmu.’

Ka Tuna?

• Ta yaya addu’ar Habakkuk ya shafe mu?

• Me ya sa Jehovah yake kan tafiya?

• Menene annabcin Habakkuk ya ce game da ceto?

• Da wane irin hali ya kamata mu jira babbar ranar Jehovah?

[Hoto a shafi na 29]

Ka san dakaru da Allah zai yi amfani da su a yaƙi da miyagu a Armageddon?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba