Jehovah Ba Zai Yi Jinkiri Ba
“Ko [ru’yar] ta jima, dakanta mata; gama lallai za ta zo, ba za ta yi jinkiri ba.”—HABAKKUK 2:3.
1. Mutanen Jehovah sun nuna sun ƙudura wace niyya ce, kuma menene wannan ya motsa su su yi?
“ZAN tsaya wurin tsarona.” Shawarar da Habakkuk annabin Allah ya tsai da shi kenan. (Habakkuk 2:1) Mutanen Jehovah a wannan ƙarni na 20 sun yi makamancin ƙuduri. Shi ya sa, sun yi ƙwazo wajen amsa kiran nan da aka yi a wani babban taro na musamman a Satumba 1922: “Wannan ita ce babbar rana. Duba, Sarkin yana mulki! Ku ne wakilansa. Saboda haka, ku sanar, ku sanar, ku sanar, da Sarkin da kuma mulkinsa.”
2. Da aka maido su ga yanayin aiki sosai bayan Yaƙin Duniya na I, wace shela ce shafaffu Kiristoci suka yi?
2 Bayan Yaƙin Duniya na I, Jehovah ya maido da ringin shafaffu ga yanayin aiki sosai. Kamar Habakkuk, kowannensu za ya iya cewa: “In tsaya a bisa hasumiya, in duba, in ga abin da za ya fāɗa mani.” Kalmomin Ibrananci na “tsaro” da kuma “tsare” an maimaita su cikin annabce-annabce da yawa.
“Ba Za ta Yi Jinkiri Ba”
3. Me ya sa tilas ne mu yi tsaro?
3 Yayin da Shaidun Jehovah suke yin shelar gargaɗin Allah a yau, tilas ne su kasance a shirye su bi kalmomin ƙarshe na annabci mai girma na Yesu: “Ku yi tsaro fa: gama ba ku san lokacin da ubangijin gida yana zuwa, ko da marece, ko da tsakiyar dare, ko da carar zakara, ko da safe; kada ya iske ku kuna barci da zuwansa ba labari. Abin da ni ke ce maku ina ce ma duka, Ku yi tsaro.” (Markus 13:35-37) Kamar Habakkuk, tilas ne mu yi tsaro cikin jituwa da kalmomin Yesu!
4. Ta yaya yanayinmu ya yi kama da na Habakkuk a misalin shekara ta 628 K.Z.?
4 Mai-yiwuwa Habakkuk ya gama rubutun littafinsa misalin shekara ta 628 K.Z., kafin ma Babila ta zama mai sarautar duniya. Cikin shekaru da yawa, an yi shelar hukuncin Jehovah bisa Urushalima mai ridda. Duk da haka, babu wata alama ta, ko yaushe ne za a zartar da hukunci. Wa zai yarda cewa shekara 21 ne kawai ya rage daga lokacin kuma wa zai yarda cewa Jehovah zai yi amfani da Babila ta zartar da hukuncinsa? Hakanan ma a yau, ba mu san ‘ranar da kuma sa’ar’ da aka shirya a kawo ƙarshen wannan tsari ba, amma Yesu ya yi mana gargaɗi: “Ku fa ku zama da shiri: gama cikin sa’an da ba ku sa tsammani ba Ɗan mutum yana zuwa.”— Matta 24:36, 44.
5. Menene musamman ma yake da ban ƙarfafa game da kalmomin Allah da ke rubuce a Habakkuk 2:2, 3?
5 Da dalili mai kyau, Jehovah ya ba ma Habakkuk aikin nan na ban marmari: “Ka rubuta ru’yan, ta fita a fili cikin alluna, domin mai-karantawa shi yi a guje. Gama ru’yan har yanzu da ayanannen lokacinta, tana kuwa gaggabta zuwa matuƙan, ba kuwa za ta yi ƙarya ba; ko ta jima, dakanta mata; gama lallai za ta zo, ba za ta yi jinkiri ba.” (Habakkuk 2:2, 3) A yau, mugunta da nuna ƙarfi suna daɗa ƙaruwa a dukan duniya, suna nuna cewa muna tsaye a kusa ɓarkewar “rana mai-ban razana ta Ubangiji.” (Joel 2:31) Hakika kuwa, kalmomin Jehovah na tabbaci suna da ban ƙarfafa: “Ba za ta yi jinkiri ba”!
6. Ta yaya ne za mu tsira ma ranar zartar da hukunci da ke zuwa?
6 To fa, ta yaya ne za mu iya tsira ma ranar zartar da hukuncin da ke zuwa? Jehovah ya amsa ta wurin bambanta mai adilci da mara-adilci: “Duba, ransa ya kumbura, ba daidai ya ke ba a cikinsa; amma adili ta wurin bangaskiyatasa za ya rayu.” (Habakkuk 2:4) Sarakuna da kuma mutane masu fahariya da haɗama, sun ɓata tarihi na zamani da jinin miliyoyi marasa-laifi, wannan yana bayyane cikin yaƙe-yaƙen duniya guda biyu da aka yi da kuma cikin zub da jini na ƙabilai. Akasin haka, shafaffu bayin Allah masu son salama sun jimre cikin aminci. Su ne “al’umma mai-adilci, mai-kiyaye gaskiya.” Wannan al’ummar tare da abokan tarayyarta, “waɗansu tumaki,” tana bin gargaɗin nan: “Ku dogara ga Ubangiji har abada: gama cikin Ubangiji Yahweh akwai madawamin dutse.”— Ishaya 26:2-4; Yohanna 10:16.
7. Ta bin Habakkuk 2:4 da Bulus ya yi amfani da shi, menene tilas ne mu yi?
7 Manzo Bulus, da yake rubuta ma Kiristoci Ibraniyawa wasiƙa, ya ɗauko abin da Habakkuk 2:4 ya faɗa, sa’annan ya gaya ma mutanen Jehovah: “Kuna da bukatar haƙuri, domin, bayanda kun aika nufin Allah, ku karɓi alkawarin. Gama da sauran jimawa kaɗan, wanda ke zuwa za shi zo, ba kuwa za shi yi jinkiri ba. Amma adilina da bangaskiya za shi rayu: Idan kuwa ya noƙe, raina ba shi jin daɗinsa ba.” (Ibraniyawa 10:36-38) Kwanakinmu ba lokacin yin sanyin gwiwa ko kuma dulmaya cikin abubuwan duniya ba ne, ta hanyoyin nishaɗi na hauka na duniyar Shaitan. Menene tilas mu yi kafin “sauran jimawa kaɗan” ɗin ya shige? Kamar Bulus, tilas ne mu al’umma mai tsarki na Jehovah mu ‘duba ga abubuwa na gaba, muna biɗan burin’ mu na rai madawwami. (Filibbiyawa 3:13, 14) Kuma kamar Yesu fa, tilas ne mu ‘jimre domin farin zuciya da aka sa a gabanmu.’—Ibraniyawa 12:2.
8. Wanene “mutum” na Habakkuk 2:5, kuma me ya sa ba zai ci nasara ba?
8 Habakkuk 2:5 ya kwatanta ‘mutum mai-fahariya’ wanda, akasi da bayin Jehovah ya kasa cim ma burinsa, ko da shike ya “fāɗaɗa gurinsa kamar kabari.” Wanene wannan mutum wanda “ba shi yiwuwa shi yi ƙoshi”? Da haɗama irin na Babila a lokacin Habakkuk, wannan “mutum,” mai ɓangarori dabam dabam a yau ya ƙunshi masu sarauta—ko na Mulkin Wariya ne, ko na Nazi, ko Kwaminis ne, ko ma dimokuraɗiyya— yana yaƙe-yaƙe don ya faɗaɗa ƙasashensa. Ya kuma cika Sheol, kabari kenan, da rayukan marasa-laifi. Amma wannan “mutum” mai ɓangarori dabam dabam mara-imani na duniyar Shaitan, wanda girman kansa ya fi ƙarfinsa, ya kasa a ƙoƙarinsa na ‘tara ma kansa dukan al’ummai kuma na tara ma kansa dukan mutane.’ Sai dai Jehovah Allah ne kaɗai zai iya haɗa kan dukan mutane, kuma zai cim ma wannan ta wurin Mulki na Almasihu.—Matta 6:9, 10.
Na Farko Cikin Kaito Biyar na Bala’i
9, 10. (a) Menene Jehovah ya ci gaba da shela ta wurin Habakkuk? (b) Game da cin mugun riba, yaya yanayin yake a yau?
9 Ta wurin annabinsa Habakkuk, Jehovah ya ci gaba ya yi shelar kaito biyar, hukunci da tilas ne a yi don shirya duniya ta zama wurin zama ga amintattu masu sujada ga Allah. Irin masu zukatan kirkin nan sun ‘ɗaukaka karin maganar nan’ wanda Jehovah ya gabatar. Mun karanta a Habakkuk 2:6: “Kaiton wanda ya tattara abin da ba nasa ba ne! har yaushe? yana kuwa labta ma kansa kayan jingina!”
10 Anan ana magana ne game da cin mugun riba. A cikin duniya da ta kewaye mu, masu arziki sai daɗa arziki suke yi, matalauta kuma sai daɗa talauci suke yi. Masu sayar da miyagun ƙwayoyi da kuma masu zamba sai shegen arziki suke yi, yayin nan kuma talakawa suna fama da yunwa. An ce wai kashi huɗu na jama’ar duniya suna zama cikin talauci. Yanayin rayuwa da ban tsoro suke cikin ƙasashe da yawa. Waɗanda suke ƙaunar adilci a duniya sun ce: “Har yaushe” ne waɗannan mugunta za su yi ta ƙaruwa! Duk da haka, ƙarshen ya yi kusa! Hakika, wahayin ba zai “yi jinkiri ba.”
11. Menene Habakkuk ya ce game da zub da jinin mutane, kuma me ya sa za mu ce da akwai laifin kisa da yawa a duniyar yau?
11 Annabin ya gaya ma masu mugunta: “Domin kai ka washe al’ummai dayawa, dukan sauran dangogi za su washe ka; sabili da jinin mutane, domin kuma wulakanci wanda aka yi ma ƙasa, da birni da dukan mazauna a ciki.” (Habakkuk 2:8) Dubi irin laifin kisa da muke gani a cikin duniya a yau! Yesu ya faɗa a fili cewa: “Dukan waɗanda suka ɗauki takobi, da takobi za su lalace.” (Matta 26:52) Duk da haka, cikin wannan ƙarni na 20 kaɗai, al’ummai da kuma ƙabilai su ne ke da alhakin kisan mutane fiye da miliyan ɗari. Kaiton waɗanda suke da hannu cikin wannan zub da jinin!
Kaito na Biyu
12. Wane kaito na biyu Habakkuk ya rubuta, kuma yaya za mu iya tabbata cewa ƙazamin riba ba zai kawo kome ba?
12 Kaito na biyu, da aka rubuta a Habakkuk 2: 9-11, ya fāɗa bisa “wanda ya ci mugunyar riba domin gidansa, domin shi sa sheƙassa a sama, domin shi tsira daga hannun mugunta!” Ƙazamin riba ba zai kawo kome ba, kamar yadda mai zabura ya bayyana sarai: “Kada ka ji tsoro lokacinda an wadatasda wani, lokacinda darajar gidansa ta ƙaru: gama sa’anda ya rasu ba za ya tafi da komi ba; a bayansa kuwa darajatasa ba za ta bi shi a ƙasa ba.” (Zabura 49:16, 17) Ƙari ga haka, ya kamata a lura da shawarar hikima na manzo Bulus: “Ka dokace waɗanda ke mawadata cikin wannan zamani na yanzu, kada su yi girman kai, kada su ratayi begensu bisa wadata mara-tsayawa, amma bisa Allah, wanda ke ba mu komi a yalwace mu ji daɗinsu.”—1 Timothawus 6:17.
13. Me ya sa ya kamata mu ci gaba da shelar gargaɗi daga Allah?
13 Dubi yadda yake da muhimmanci a yi shelar saƙon hukunci na Allah a yau! Lokacin da Farisawa suka hana taro ɗaukaka Yesu kamar “Sarki mai-zuwa cikin sunan Ubangiji,” ya ce: “In faɗa maku, da a ce waɗannan za su yi shuru, ko duwatsu su a yi murya.” (Luka 19:38-40) Hakanan, idan mutanen Allah a yau sun kasa fallasa mugunta da ke cikin duniyar nan, ‘Daga cikin katanga dutse za ya tada murya.’ (Habakkuk 2:11) Saboda haka bari mu ci gaba da shelar gargaɗi daga Allah da gabagaɗi!
Kaito na Uku da Zancen Laifin Kisa
14. Wane laifin kisa ne addinan duniya suke da alhakinsa?
14 Kaito na uku da aka yi shelarsa ta wurin Habakkuk ya yi zancen laifin kisa. Habakkuk 2:12 ya ce: “Kaitonsa shi wanda ya gina gari da jini, ya kafa birni da mugunta!” Cikin wannan shirin abubuwa, mugunta da zub da jini abokan juna ne. Lallai kuwa, addinan duniya su ne ke da alhakin yawan zub da jini cikin tarihi. Za mu yi la’akari da Jihadi kaɗai cikinsu, da waɗanda suke kiran kansu Kiristoci suka yi da Musulmai; Zamanun Tsanantawa na Katolik a Spain da kuma Amirka ta Latin; Yaƙin da aka yi a Turai na Shekara Talatin, tsakanin ‘yan Protestant da kuma Katolikawa; kuma mafi muni duka, shine yaƙin duniya guda biyu na wannan ƙarnin namu, duka sun soma ta wurin Kiristendom ne.
15. (a) Menene al’ummai suka ci gaba da yi,tare da goyon baya ko kuma amincewar coci? (b) Majalisar Ɗinkin Duniya za ta kawo ƙarshen makaman yaƙi a wannan duniyar ne?
15 Ɗaya daga cikin fasaloli mafi muni na yaƙin duniya na biyu shine Mummunar Hallaka na Nazi da ya ci miliyoyin Yahudawa da kuma wasu mutane marasa-laifi a Turai. A kwanakin nan ne limaman Roman Katolik a Faransa suka yi ikirari sun kasa hana aika ɗarurruwan dubban mutane zuwa sansanin mutuwa na Nazi. Duk da haka, al’ummai sun ci gaba da yin shiri don zub da jini, tare da goyon bayan coci ko kuma da amincewarsu. Da yake magana game da Cocin Orthodox na Rasha, jaridarTime (bugu na ƙasashe) a kwanan nan ta ce: “Cocin da aka rayar ya kuma kasance da mugun tasiri a wurin da ba a tsammani ba: mayaƙan Rasha. . . . Yin Addu’o’i ga jiragen yaƙi da kuma barikin sojoji sun zama kamar al’ada. A Nuwamba, a Gidajen Zaman Zuhudu na Danilovsky a Moscow, cibiyar hukunci na Manyan Rasha, har cocin sun ɗaukaka matattarin makaman nukiliya na Rasha.” Majalisar Ɗinkin Duniya za ta iya dakatar da sake bayar da miyagun makaman yaƙi a duniyar nan? Da ƙyar! In ji jaridarThe Guardian ta London, a Ingila, wani wanda ya ci Kyautar Nobel Peace ya ce: “Ainihin abin da ba a gane ba shine cewa, ‘yan Hukumar Tsare Lafiya na MƊD guda biyar sune suka fi tanadar da makamai a duniya.”
16. Menene Jehovah zai yi da al’ummai masu shirin yaƙi?
16 Shin Jehovah zai zartar da hukunci bisa al’ummai masu zuga yaƙi ne? Habakkuk 2:13 ya ce: “Ashe, ba nufin Ubangiji mai-runduna ba ne al’ummai su ke wahala domin su sami wuta, danguna kuma suna gajiyadda kansu domin abin wofi?” “Ubangiji mai-runduna”! I, Jehovah yana da rundunar mala’iku na samaniya, da zai yi amfani da su ya wofintar da mutane da kuma al’ummai masu shirin yaƙi!
17. Har yaya sanin Jehovah zai cika duniya bayan ya zartar da hukuncinsa bisa al’ummai masu-zafin rai?
17 Menene zai biyo zartar da hukuncin Jehovah bisa waɗannan al’ummai masu zafin rai? Habakkuk 2:14 ya tanadar da amsar: “Gama duniya za ta cika da sanin darajar Ubangiji, kamar yadda ruwaye sun rufe teku.” Dubi muhimmiyar bege! A Armageddon, za a kunita ikon mallaka na Jehovah har abada. (Ru’ya ta Yohanna 16:16) Ya tabbatar mana cewa zai ‘daraja wurin takawar ƙafafuwansa,’ wannan duniya da muke zama ciki. (Ishaya 60:13) Za a ilimantar da dukan mutane cikin hanyar rayuwa na Allah, saboda sanin darajar ƙudurin Jehovah zai cika duniya kamar ruwa da ke cika teku.
Kaito na Huɗu da na Biyar
18. Wane kaito na huɗu aka yi shelarsa ta wurin Habakkuk, kuma yaya aka nuna shi cikin yanayin ɗabi’a na duniyar yau?
18 An kwatanta kaito na huɗu a Habakkuk 2:15 cikin kalmomin nan: “Kaitonsa shi wanda ke ba maƙwabcinsa sha, kana ƙara naka dafi gareshi, kana kuwa sa shi shi yi maye, domin ka duba tsiraicinsu!” Wannan yana nuna yanayin rashin kunya, da taurin kai na duniyar zamani. Lalatarta wadda har ƙungiyar addinai suka goyo bayanta, ta ƙara lalacewa fiye da dā. Annoba, irinsu AIDS da kuma wasu cututtuka da ake samu ta wurin jima’i, sai daɗa yaɗuwa da sauri suke yi cikin duniya. Maimakon nuna ‘ɗaukakar Jehovah,’ zamanin yau na sai-dai-ni yana ƙara zurfi cikin rashin ɗabi’a da kuma zuwa ga zartar da hukuncin Allah. ‘Maimakon daraja sun cika da kunya,’ wannan duniya mai laifi ta kusan shan fushin Jehovah, wanda ke wakilci nufinsa game da ita. ‘Kunya kuma za ta kasance bisa darajarta.’—Habakkuk 2:16.
19. Buɗewan jawabin kaito na biyar da Habakkuk ya sanar ya nuna menene, kuma me ya sa irin waɗannan kalmomi suke da ma’ana a duniyar yau?
19 Buɗewan jawabin kaito na biyar ya bada gargaɗi sosai game da bautar gumaka. Jehovah ya sa annabin ya furta waɗannan kalmomi masu ƙarfi: “Kaitonsa shi wanda ya ce ma itace, Falka; ya ce ma beben dutse, Tashi! Wannan za shi yi koyarwa? Ga shi, an dalaye shi da zinariya da azurfa, ba kuwa lumfashi ko kaɗan a cikinsa.” (Habakkuk 2:19) Har wa yau, Kiristendom duk da arna suna bauta ma giciyensu, Hoton Maryamu, sifofin mutane, da kuma wasu sifofin dabbobi. Babu wani cikin waɗannan da zai iya ya farka don ya cetar da masu sujadarsa lokacin da Jehovah zai zartar da hukunci. Yawan zinariya da kuma azurfansu sun zama banza in an gwada da ɗaukakar madawwamin Allah, Jehovah , da kuma darajar halittunsa masu rai. Bari mu ɗaukaka sunansa mai daraja har abada!
20. A wane tsarin haikali muke da gatar yin hidima da murna?
20 I, Jehovah, Allahnmu, ya cancanci dukan yabo. Tare da cikakkiyar tsoron shi, bari mu bi wannan gargaɗi mai ƙarfi game da bautar gumaka. Amma mu saurara! Har illa Jehovah yana magana: “Ubangiji yana cikin haikalinsa mai-tsarki; bari dukan duniya ta yi shuru a gabansa.” (Habakkuk 2:20) Babu shakka haikalin Urushalima ne annabin yake maganarsa. Amma kuma, mu a yau mun samu gatar yin sujada cikin shirin haikali mafi daraja, inda aka naɗa Ubangijinmu Yesu Kristi, Babban Firist. Anan, cikin farfajiyar haikalin nan na duniya, muna taruwa, muna yin hidima, kuma muna yin addu’a, muna ba Jehovah girma da ya wajibce sunansa mai daraja. Dubi murna da muke yi a yin sujada daga zuciya ga Ubanmu na samaniya mai ƙauna!
Ka Tuna?
• Yaya ka ke ɗaukan kalmomin Jehovah: “Ba za ta yi jinkiri ba”?
• Menene ma’anar kaito da aka sanar ta wurin Habakkuk a zamanin yau?
• Me ya sa ya kamata mu ci gaba da shelar gargaɗin Jehovah?
• A cikin farfajiya ta wane haikali muke da gatar yin hidima?
[Hotuna a shafi na 21]
Kamar Habakkuk, bayin Allah na zamanin yau sun san cewa Jehovah ba zai yi jinkiri ba
[Hotuna a shafi na 24]
Kana nuna godiya ga gatar bauta ma Jehovah cikin farfajiya na haikalinsa na ruhaniya?
[Inda Aka Ɗauko Hoto da ke shafi na 22]
Hoto daga Sojojin United States