Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w00 2/1 p. 31
  • Taimakon Mutane Iri-Iri a Netherlands

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Taimakon Mutane Iri-Iri a Netherlands
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • Makamantan Littattafai
  • Na Yi Yaƙi da Rashin Adalci da Kuma Mugunta
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Za Ka Iya “Ƙetaro Zuwa Makidoniya”?
    Hidimarmu Ta Mulki—2011
  • Mutane Daga “Kowane Harshe” Sun Ji Bishara
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Kana Magana Da “Harshe Mai-tsarki” Sosai?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
w00 2/1 p. 31

Rahoto Daga Masu-shelar Mulki

Taimakon Mutane Iri-Iri a Netherlands

IBRAHIM mutum ne mai bangaskiya, ba irin ta gama gari ba. “Sa’anda aka kira shi,” in ji manzo Bulus, Ibrahim ya yi biyayya ga Allah “ya kuwa fita, ba ya san inda za shi ba.” Bayan ya ƙaura da dukan iyalinsa, Ibrahim “ya baƙunta cikin ƙasar alkawari” na shekaru ɗari ɗaya na sauran rayuwarsa.—Ibraniyawa 11:8, 9.

Haka ma yau, da yawa cikin Shaidun Jehovah sun karɓi kaluɓalen ƙaura zuwa wata ƙasa domin su yi hidima a wurin da akwai bukata mafi girma. Wasu sun koyi wani yare don su yi wa’azi ma baƙi da suka shigo cikin ƙasarsu. Kamar yadda misalai na biye suka nuna, wannan nagarin hali ya buɗe “ƙofa mai-faɗi mai-yalwar aiki” a Netherlands, inda miliyan ɗaya daga cikin mazauna miliyan 15 daga wasu ƙasashe suka zo.—1 Korinthiyawa 16:9.

◻ Bahram, wanda dā malami ne da ke koyar da faɗān Kung Fu, ya zo ne daga wata ƙasa a Gabas ta Tsakiya. Ya fanshi Littafi Mai-Tsarki da kuma wasu littattafan Watch Tower. Cikin wata ɗaya, Bahram ya fahimci cewa ya sami gaskiya. Aka fara nazari da shi da kuma matarsa, amma da akwai matsala—malaminsu na Littafi Mai-Tsarki ba ya jin yarensu. Suna magana ta bebanci, magana “da hannaye da kuma ƙafafuwa,” kamar yadda suka tuna. Da shigewar lokaci, Bahram da matarsa suka samu ikklisiya inda ake yin yarensu, bayan haka suka sami cin gaba da hanzari. Bahram yanzu Mashaidi ne wanda ya yi baftisma.

◻ Wasu majagaba mata da miji, mutanen Dutch sun doshi wani mutumin Indonesiya wanda yake tsaye a gaban wani babban shago. Ya yi mamaki da farinciki yayin da mata da mijin suka yi masa magana da yarensa. Sun shirya su zo su same shi a gidansa. Sun gano cewa ya zauna a Rasha fiye da shekara 20, lokacin da ya zama likitan lura da lafiyar mata. Yana da’awar bai yarda da wanzuwan Allah ba, amma ya yarda cewa kowane lokacin da ya taimaka a fitar da jariri, sai ya yi ta mamakin, “Yadda kamiltan jikin mutum yake! Mu’ujiza ce ƙwarai!” Ya yarda ya yi nazarin Littafi Mai-Tsarki, bada jimawa ba ya yarda cewa akwai Mahalicci wanda yake kula da ’yan Adam. (1 Bitrus 5:6, 7) Yanzu shi ɗan’uwa ne da ya yi baftisma kuma yana hidima tare da ikklisiya ta yaren mutanen Indonesiya a Amsterdam.

◻ A Rotterdam, ɗaya daga cikin manyan wuraren sauƙan jiragen ruwa ta duniya, wani rukunin majagaba sun yi ƙoƙari wurin yin wa’azi wa ƙabilu dabam dabam da suke sauƙa a wurin kullum. Sakamakon wa’azin wannan rukuni mai ƙwazo na masu wa’azi, ma’aikatan cikin teku, har da kaftin, ma’aikacin jirgin ruwa, da wani ɗan tsaro a dā sun karɓi gaskiya. Yanzu su ma suna taimakawa wurin yaɗa bisharar Mulkin Allah a dukan duniya.—Matta 24:14.

Kamar a sauran ɓangarori na duniya, Shaidun Jehovah a Netherlands sun ƙudura aniyar yin iyakar gwargwadon ƙarfinsu wurin shelar bisharar rai na har abada ga dukan al’ummai, ƙabilu, yare, da kuma mutane.—Ru’ya ta Yohanna 14:6.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba