‘Ku Ci Gaba Da Yin Tsaro’
“Ku yi tsaro fa: gama ba ku sani ba cikin ko wace rana Ubangijinku ke zuwa.”—MATTA 24:42.
1. Yaya bayin Jehovah da suka bauta masa na doguwar lokaci suke ji game da shekaru da yawa da suka yi suna hidimar keɓe kai? Ka bada misali.
BAYI da yawa da suka jima suna bauta wa Jehovah sun koyi gaskiya ne lokacin da suke samari da ’yammata. Kamar mai fatauci wanda ya sami lu’u-lu’u mai tamani na gaske, ya sayar da dukan ƙadararsa don ya saya, waɗannan Ɗaliban Littafi Mai-Tsarki masu kuzari suka ƙi kansu kuma suka keɓe rayukansu ga Jehovah. (Matta 13:45, 46; Markus 8:34) Yaya suke ji game da jira da suka yi na dogon lokaci fiye da yadda suke tsammanin za su ga cikar ƙudurin Allah bisa duniya? Ba su yi da na sani ba! Sun yarda da abin da Ɗan’uwa A. H. Macmillan, wanda bayan hidimar keɓe kai ga Allah na kusan shekara 60, ya ce: “Na ƙuduri aniya fiye da dā in ci gaba a bangaskiyata. Ta ba ni dalilin rayuwa. Har yanzu tana taimako na in fuskanci rayuwa ta nan gaba babu tsoro.”
2. (a) Wane gargaɗi ne Yesu ya ba mabiyansa akan lokaci? (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu bincika a cikin wannan talifin?
2 To kai fa? Ko nawa shekarunka, ka yi la’akari da kalmomin Yesu: “Ku yi tsaro fa: gama ba ku sani ba cikin ko wace rana Ubangijinku ke zuwa.” (Matta 24:42) Wannan furci mai sauƙi ya ƙunshi gaskiya mai zurfi. Ba mu san ko a wace rana ce Ubangiji zai dawo ya yanka hukunci bisa wannan muguwar tsarar ba, kuma bai zama wajibi mu sani ba. Amma ya kamata muna rayuwa a hanyar da in ya dawo, ba za mu yi nadama ba. Game da wannan, wane misalai ne muka samu daga cikin Littafi Mai-Tsarki waɗanda za su taimake mu mu ci gaba da yin tsaro? Yaya Yesu ya bada misalin wannan bukatar? Kuma wane tabbaci ne muke da shi a yau da ya nuna cewa muna rayuwa ne cikin kwanaki na ƙarshe na wannan duniya ta rashin ibada?
Misalai na Kashedi
3. Ta yaya mutane da yawa a yau suka kamanci waɗanda suke kwanakin Nuhu?
3 A hanyoyi da yawa, mutane a yau suna kama da maza da mata da suka rayu a kwanakin Nuhu. A wancan lokacin, duniya ta cika da mugunta kuma dukan tunanin zuciyar mutum “mugunta ce kaɗai kullayaumi.” (Farawa 6:5) Yawancinsu sun shagala da harkokin rayuwa na kullum. Amma kafin ya kawo babbar Ambaliya, Jehovah ya ba mutane damar tuba. Ya ba Nuhu aikin wa’azi, kuma Nuhu ya yi biyayya—ya yi hidima ta “mai-shelan adilci” wataƙila na shekara 40 ko 50 ko ma fiye da haka. (2 Bitrus 2:5) Amma dai, mutanen sun yi kunnen uwar shegu ga saƙon kashedi na Nuhu. Ba su yi tsaro ba. A ƙarshe dai, Nuhu da iyalinsa kaɗai suka tsira daga zartar da hukunci na Jehovah.—Matta 24:37-39.
4. A wane azanci ne za a iya cewa hidimar Nuhu ta yi nasara, kuma me za a iya cewa game da naka aikin wa’azi?
4 Hidimar Nuhu ta yi nasara kuwa? Kada ka kammala don adadi ɗan kaɗan da suka yi na’am. Hakika wa’azin Nuhu ya cim ma burinsa ko da yaya martanin da ya samu. Me ya sa? Domin ya ba mutane zarafi sosai su zaɓi ko za su bauta wa Jehovah ko a’a. Yankin da ka ke wa’azi kuma fa? Ko mutane kaɗan ne kawai suke na’am, kana samun babban nasara. Me ya sa? Domin ta wajen wa’azi, kana sanar da kashedi daga Allah, kuma ta haka kana cika aikin da Yesu ya ba mabiyansa.—Matta 24:14; 28:19, 20.
Yin Kunnen Uwar Shegu ga Annabawan Allah
5. (a) Wane yanayi ne ya cika Yahudiya a zamanin Habakkuk, kuma yaya mutanen suka amsa ga saƙon annabcinsa? (b) Ta yaya mutanen Yahudiya suka nuna hamayya ga annabawan Jehovah?
5 Ƙarnuka bayan Ambaliyar, masarautar Yahudiya ta fuskanci al’amari mai tsanani. Bautar gumaka, rashin adilci, zalunci, har da ƙisa abubuwa ne na kullum. Jehovah ya tada Habakkuk ya yi wa mutanen kashedi cewa idan ba su tuba ba, bala’i zai faɗa masu ta hannun Chaldiyawa, ko kuma Babiloniyawa. (Habakkuk 1:5-7) Amma mutanen suka ƙi su saurara. Wataƙila sun yi tunani cewa, ‘Don me, fiye da shekaru ɗari da suka shige, annabi Ishaya ya sanar da kashedi makamancin haka, amma babu abin da ya faru har wa yau!’ (Ishaya 39:6, 7) Ma’aikatan Yahudiya da yawa ba kawai suna da halin babu ruwana ba, amma suna hamayya da saƙon. A wani lokaci, sun yi ƙoƙari su kashe annabi Irmiya, da sun yi nasara kuwa in ba don Ahikam ya saka hannu ba. Da ya fusata don wani saƙon annabci, Sarki Jehoikim ya sa aka kashe annabi Urijah.—Irmiya 26:21-24.
6. Ta yaya Jehovah ya ƙarfafa Habakkuk?
6 Habakkuk ma ya gabatar da saƙonsa babu tsoro kuma ba a karɓa ba kamar yadda ba a karɓi na Irmiya ba, wanda Allah ya hore shi da annabta hallaka ta shekara 70 bisa Yahudiya. (Irmiya 25:8-11) Saboda haka, za mu iya fahimtar baƙincikin Habakkuk yayin da ya yi kuka: “Ya Ubangiji, har yaushe zan yi kira, kai kuwa ba ka yarda ka ji ba? Ina tada murya gareka saboda zafin mugunta, kai kuwa ka ƙi yin ceto.” (Habakkuk 1:2) Jehovah ya amsa ma Habakkuk da waɗannan kalmomi masu ƙarfafa bangaskiya: “Ru’yan har yanzu da ayanannen lokacinta, tana kuwa gaggabta zuwa matuƙan, ba kuwa za ta yi ƙarya ba; ko ta jima, dakata mata; gama lallai za ta zo, ba za ta yi jinkiri ba.” (Habakkuk 2:3) To Jehovah yana da “ayanannen lokaci” na kawo ƙarshen rashin adilci da zalunci. Idan kamar ana jinkiri, bai kamata Habakkuk ya yi sanyin gwiwa ba, ko kuma ya rage hanzari. Maimakon haka, ya kamata ya ci gaba da “dakata mata,” yana rayuwa kowace rana da azanci na gaggawa. Ranar Jehovah ba za ta yi jinkiri ba!
7. Me ya sa aka faɗi wata hallaka bisa Urushalima a ƙarni na farko A.Z.?
7 Bayan kamar shekaru 20 da Jehovah ya yi ma Habakkuk magana, aka hallaka Urushalima babban birnin Yahudiya. Daga baya aka sake gina ta, abubuwa da yawa da suka baƙanta ma Habakkuk rai aka daina yin su. Amma dai, a ƙarni na farko A.Z., birnin har illa yau an alamta ta don hallaka domin rashin amincin mazauna cikinta. Jehovah ya tausaya wa masu zuciyar kirki ya shirya masu hanyar tsira. A wannan karon, ya yi amfani ne da Yesu Kristi annabi mafi ɗaukaka ya idar da saƙon. A shekara 33 A.Z., Yesu ya gaya wa mabiyansa: “Sa’anda kun ga Urushalima tana kewaye da dāgar yaƙi, sa’annan ku sani ribɗewatta ta kusa. Sa’annan waɗanda ke cikin Yahudiya su gudu zuwa duwatsu.”—Luka 21:20, 21.
8. (a) Me wataƙila ya faru da wasu Kiristoci da shigewar lokaci bayan mutuwar Yesu? (b) Ta yaya kalmomin annabci na Yesu game da Urushalima ya cika?
8 Da shekaru suka shige, wasu Kiristoci a Urushalima ƙila sun yi tunani yaushe ne annabcin nan na Yesu zai cika. Banda haka, ka yi la’akari da sadaukarwa da babu shakka wasu tsakaninsu suka yi. Wataƙila sun ƙi gagarumar hulɗar kasuwanci domin ƙudurinsu su ci gaba da yin tsaro. Da lokaci ya ci gaba da shigewa, sun gaji ne? Ko sun kammala da cewa ɓata lokacinsu kawai suke yi, suna tunani cewa maganar Yesu ga tsara ta nan gaba ce, ba ta su ba? A shekara ta 66 A.Z., annabcin Yesu ya fara cika sa’an da sojojin Roma suka kewaye Urushalima. Waɗanda suka ci gaba da yin tsaro sun fahimci alamar, suka tsere daga birnin, kuma suka tsira daga hallakar Urushalima.
Misalta Bukatar Yin Tsaro
9, 10. (a) Yaya za ka taƙaita misalin da Yesu ya bayar na bayi waɗanda suka jira ubangidansu ya dawo daga wajen aurensa? (b) Me ya sa jiran ubangidansu ƙila ya yi ma bayin wuya? (c) Me ya sa yake da amfani ma bayin su yi haƙuri?
9 Da yake nanata bukatar yin tsaro, Yesu ya kamanta almajiransa da bayin da suke jiran ubangidansu ya dawo daga wurin aurensa. Sun san cewa zai dawo cikin dare—amma a wace sa’a? Lokacin tsaro na farko ne? Na biyu? Ko na uku? Ba su sani ba. Yesu ya ce: “Ko a cikin tsaro na biyu [ubangidan] ya zo, ko cikin na uku, kadan ya iske su haka [suna tsaro], masu-albarka ne waɗannan bayi!” (Luka 12:35-38) Ka yi tunanin yadda waɗannan bayin za su yi tsammani. Kowane motsi, kowane inuwar mutum babu shakka zai ƙara masu tsammani: ‘Ubangidanmu ne?’
10 To yaya idan ubangidan ya dawo lokacin tsaro na biyu, wanda ya kama daga ƙarfe tara har tsakar dare? Dukan bayin, haɗe da waɗanda suka yi aiki tuƙuru tun da safiya, za su kasance a shirye su marabce shi, ko dai wasu za su yi barci ne? To yaya idan ubangidan ya dawo a lokacin tsaro na uku na dare—lokaci da ya kama daga tsakar dare har zuwa kamar ƙarfe uku na asuba? Wasu bayin za su yi sanyin gwiwa ne, har su yi fushi don wai kamar ubangidansu ya yi jinkiri?a Waɗanda aka iske suna yin tsaro lokacin da ubangidan ya dawo ne kawai za su sami albarka. Kalmomin Misalai 13:12 babu shakka zai aika garesu: “Muradin da ba a biya ba ya kan sa zuciya ta yi ciwo: Amma sa’anda abin so ya samu, itacen rai ne.”
11. Ta yaya addu’a za ta taimake mu mu ci gaba da yin tsaro?
11 Lokacin da kamar yana jinkiri, menene zai taimaki mabiyan Yesu su ci gaba da yin tsaro? A cikin lambun Jetsaimane bada jimawa ba kafin a kama shi, Yesu ya gaya wa manzanninsa guda uku: “Ku yi tsaro, ku yi addu’a, kada ku shiga cikin jaraba.” (Matta 26:41) Shekaru bayan haka, Bitrus wanda yana wurin a lokacin, ya bada gargaɗi makamancin haka ga yan’uwansa Kiristoci. Ya rubuta: “Matuƙar dukan abu ta kusa: domin wannan ku yi natsuwa cikin hankalinku, ku yi rai shimfiɗe zuwa ga addu’a.” (1 Bitrus 4:7) A bayyane yake sarai, himmantuwa cikin addu’a ya kamata ya zama sashen rayuwarmu na kullum na Kirista. Hakika, muna bukatar roƙon Jehovah kullum ya taimake mu mu ci gaba da yin tsaro.—Romawa 12:12; 1 Tassalunikawa 5:17.
12. Menene bambanci tsakanin zato da kuma yin tsaro?
12 Ka lura cewa Bitrus ya ce: “Matuƙar dukan abu ta kusa.” Yaya kusanta? Babu wata hanyar da ’yan Adam za su iya su canki daidai rana da kuma sa’ar. (Matta 24:36) Amma akwai bambanci tsakanin yin zato, wanda Littafi Mai-Tsarki ya haramta, da kuma yin tsammanin matuƙa, wanda ya halalta. (Gwada da 2 Timothawus 4:3, 4; Titus 3:9.) Wace hanya ɗaya ce za mu iya amfani da ita wajen tsammanin matuƙa? Ta wajen mai da hankali sosai ga tabbacin cewa matuƙa ta kusa. Saboda haka bari mu sake bincika hanyoyi shida da suka bada tabbaci cewa muna rayuwa ne a kwanaki na ƙarshe na wannan duniya ta marasa ibada.
Tabbaci Shida Masu Gamsarwa
13. Ta yaya annabcin da Bulus ya rubuta a 2 Timothawus sura 3 ya tabbatar maka cewa muna rayuwa cikin “kwanaki na ƙarshe”?
13 Da farko, mun ga cikar annabcin manzo Bulus game da “kwanaki na ƙarshe” sarai. Bulus ya rubuta: “Cikin kwanaki na ƙarshe miyagun zamanu za su zo. Gama mutane za su zama masu-son kansu, masu-son kuɗi, masu-ruba, masu girman kai, masu-zagi, marasa-bin iyaye, marasa-godiya, marasa-tsarki, marasa-ƙauna irin na tabi’a, masu-baƙar zuciya, masu-tsegumi, marasa-kamewa, masu-zafin hali, marasa-son nagarta, masu-cin amana, masu-taurin kai, masu-kumbura, ma-fiya son annishuwa da Allah; suna riƙe da surar ibada, amma sun musunci ikonta: daga wajen waɗannan kuma sai ka bijire. Amma miyagun mutane da masu-hila za su daɗa mugunta gaba gaba, suna ruɗi ana ruɗinsu.” (2 Timothawus 3:1-5, 13) Ba ma ganin wannan annabci yana cika a zamaninmu? Sai dai waɗanda suka ƙi gaskiya ne kawai za su musanci hakan!b
14. Ta yaya kalmomin Ru’ya ta Yohanna 12:9 game da Iblis ya cika a yau, kuma me zai faru da shi bada jimawa ba?
14 Na biyu, muna ganin alamun jefo da Shaitan da kuma aljanunsa daga sama, a cika annabcin Ru’ya ta Yohanna 12:9. A ciki mun karanta: “Aka jefasda babban dragon, tsohon macijin, shi wanda ana ce da shi Iblis da Shaitan, mai-ruɗin dukan duniya; aka jefasda shi a duniya, aka jefasda mala’ikunsa kuma tare da shi.” Wannan ya jawo kaito mai-girma ga duniya. Da gaske, da akwai kaito da yawa ga mutane, musamman ma tun daga shekara ta 1914. Amma annabci da yake cikin Ru’ya ta Yohanna ya ƙara da cewa lokacin da aka jefo da Iblis zuwa duniya, ya sani cewa “sauran zarafinsa kaɗan ne.” (Ru’ya ta Yohanna 12:12) A wannan lokacin, Shaitan ya yi yaƙi da shafaffu mabiyan Kristi. (Ru’ya ta Yohanna 12:17) Babu shakka mun ga alamar farmakinsa a zamaninmu.c Ko da yaya, bada jimawa ba za a rufe Shaitan a rami mara matuƙa saboda “kada shi ƙara ruɗin al’ummai.”—Ru’ya ta Yohanna 20:1-3.
15. Ta yaya Ru’ya ta Yohanna 17:9-11 ya bada tabbacin cewa muna rayuwa a lokacin ƙarshe?
15 Na uku, muna rayuwa ne a lokacin “Sarki” na takwas kuma na ƙarshe da aka ambata a annabcin da aka rubuta a cikin Ru’ya ta Yohanna 17:9-11. A nan manzo Yohanna ya ambaci sarakuna bakwai, waɗanda suka wakilci masu sarautar duniya guda bakwai—Masar, Assuriya, Babila, Mede da Pashiya, Hellas, Roma, da kuma Ingila da Amirka da suke sarauta tare. Ya ga kuma ‘sarki na takwas’ wanda ‘ya taso daga cikin na bakwan.’ Wannan sarki na takwas—na ƙarshe da Yohanna ya gani—yanzu yana wakiltan Majalisar Ɗinkin Duniya. Yohanna ya ce wannan sarki na takwas “yana tafiya kuma zuwa hallaka” bayan wannan babu wani sarki na duniya da aka ambata kuma.d
16. Ta yaya gaskiya ta cikar siffar mafarkin Nebuchadnezzar ta nuna cewa muna rayuwa a kwanaki na ƙarshe?
16 Na huɗu, muna rayuwa ne a lokacin da yake alamta sawun siffa na mafarkin Nebuchadnezzar. Annabi Daniel ya fassara wannan mafarki mai ban mamaki na siffa mai girma mai kamanin mutum. (Daniel 2:36-43) Ɓangarori huɗu na ƙarfe na wannan siffar yana wakiltan masu sarautar duniya dabam dabam, farawa da kan (Daular Babiloniyawa) har zuwa yatsun da kuma sawun (gwamnatocin da suke sarauta a yau). Dukan masu sarautar duniya da aka wakilce su a wannan siffar sun bayyana. Muna rayuwa ne a lokacin da yake alamta sawun siffar. Ba a ambata zuwan wasu masu sarauta kuma ba.e
17. Yaya ayyukanmu na wa’azin Mulki ya bada ƙarin tabbaci cewa muna rayuwa a lokacin ƙarshe?
17 Na biyar, mun ga an cika aikin wa’azin a dukan duniya, wanda Yesu ya ce za a yi kafin ƙarshen wannan tsarin abubuwa ya zo. Yesu ya furta haka: “Wannan bishara kuwa ta mulki za a yi wa’azinta cikin iyakar duniya domin shaida ga dukan al’ummai; sa’annan matuƙa za ta zo.” (Matta 24:14) A yau, wannan annabcin yana kan cika a hanyar da take da girma. A gaskiya, har yanzu akwai yankuna da ba a taɓa ba tukuna, wataƙila a ayanannen lokaci na Jehovah za a buɗe ƙofa mai faɗi da za ta kai ga hidima. (1 Korinthiyawa 16:9) Ko da yake, Littafi Mai-Tsarki bai ce Jehovah zai jira har sai an yi wa kowa wa’azi ba. Maimakon haka, tilas ne a yi wa’azin bisharar yadda za ta gamsar da Jehovah. Sai matuƙa ta zo.—Gwada da Matta 10:23.
18. Menene babu shakka, zai zama gaskiya game da shafaffu lokacin da ƙunci mai-girma ya fara, kuma yaya za a iya tabbatar da wannan?
18 Na shida, adadin almajiran Kristi shafaffu na gaskiya yana raguwa, duk da haka wasunsu babu shakka ƙunci mai-girma zai fara suna duniya. Yawancin ringin sun tsufa, kuma a cikin shekaru da suka shige adadin waɗanda shafaffu ne da gaske ya zama kaɗan. Duk da haka, lokacin da Yesu yake magana game da ƙunci mai-girman, ya ce: “Da ba domin an gajertadda waɗannan kwanaki ba, da ba mai-rai da za ya tsira ba: amma sabili da zaɓaɓu za a gajertadda su.” (Matta 24:21, 22) Babu shakka, wasu “zaɓaɓu” na Kristi za su kasance suna duniya lokacin da ƙunci mai-girman zai fara.f
Menene Yake Zuwa a Nan Gaba?
19, 20. Me ya sa yanzu ya fi dā gaggawa a garemu mu kasance ba barci kuma mu ci gaba da yin tsaro?
19 Menene yake zuwa a nan gaba domin mu? Lokacin farinciki har yanzu yana gaba. Bulus ya yi gargaɗi cewa “ranar Ubangiji tana zuwa misalin ɓarawo da dare.” Da yake nuni ga mutane waɗanda sun bayyana suna fahimtar al’amuran ’yan Adam, ya ce: “Suna cikin faɗin, Kwanciyar rai da lafiya, sai ga hallaka farat ta auko masu.” Saboda haka, Bulus ya aririci masu karatunsa: “Kada fa mu yi barci, kamar sauran mutane, amma mu yi zamanmu ba barci ba maye.” (1 Tassalunikawa 5:2, 3, 6) Da gaske, waɗanda suka dangana ga ƙungiyoyin ’yan Adam su kawo salama da tsaro suna ƙin gaskiya ne. Irin waɗannan mutane suna cikin daɗin barci!
20 Hallakan wannan tsarin abubuwa zai faɗo farat ɗaya ne. Saboda haka, ka ci gaba da tsammanin ranar Jehovah. Allah da kansa ya gaya wa Habakkuk: “Ba za ta yi jinkiri ba”! Babu shakka bai taɓa zama mana da gaggawa ba kamar haka mu ci gaba da yin tsaro.
[Hasiya]
a Ubangidan bai yi sharaɗi da bayinsa ba. Saboda haka, ba zai bada dalilin shiga da fitarsa ba, kuma ba wajib ba ne ya bayyana dalilin jinkiri da suke gani kamar ya yi.
b Don ƙarin bayani akan wannan annabci, ka duba sura 11 na littafin nan Sanin Da ke Bishe Zuwa Rai na Har Abada, Watchtower Bible and Tract Society of New York, Inc., ne suka buga.
c Don ƙarin bayani, duba shafofi 180-186 na littafin nan Revelation—Its Grand Climax At Hand!, Watchtower Bible and Tract Society of New York, Inc., ne suka buga.
d Duba Revelation—Its Grand Climax At Hand!, shafofi 251-254.
e Duba babi na 4 na littafin nan Pay Attention to Daniel’s Prophecy!, Watchtower Bible and Tract Society of New York, Inc., ne suka buga.
f A cikin almara na tumaki da awaki, Ɗan mutum ya zo cikin ɗaukakarsa a lokacin ƙunci mai-girma kuma ya zauna yin shari’a. Ya shar’anta mutane bisa ko sun tallafa ma yan’uwan Kristi shafaffu. Irin wannan shari’a za ta zama babu ma’ana idan a lokacin shari’an dukan yan’uwan Kristi sun bar duniya da daɗewa.—Matta 25:31-46.
Ka Tuna?
• Waɗanne misalai na Nassi za su taimake mu mu ci gaba da yin tsaro?
• Yaya Yesu ya misalta bukatar yin tsaro?
• Waɗanne tabbaci shida ne suka nuna cewa muna rayuwa a kwanaki na ƙarshe?
[Hotuna a shafi na 3]
A. H. Macmillan ya bauta ma Jehovah cikin aminci na kusan shekaru sittin
[Hoto a shafi na 4]
Yesu ya kamanta almajiransa da bayi da suka ci gaba da yin tsaro