“Muradin” Suna Cika Gidan Jehovah
“Zan [Jehovah] raurawadda dukan dangogi; kuma muradin dukan dangogi za ya zo; zan cika wannan gida da ɗaukaka.”—HAGGAI 2:7.
1. A lokacin gaggawa, me ya sa muke tunawa da waɗanda muke ƙauna da farko?
WAƊANNE abubuwan muradi ne suka cika gidanka? Kana da kushin masu sada, na’ura mai ƙwaƙwalwa ta zamani, kana da sabuwar mota a garejinka? Idan ma kana da waɗannan abubuwa duka, ba za ka yarda cewa abubuwa mafi tamani a gidanka mutanen ciki ne ba—iyalinka? Ka yi tunanin warin hayaki ya tashe ka a barci cikin dare. Gidanka yana ci da wuta, kuma mintoci kaɗan ya rage maka ka tsira! Me za ka damu da shi da farko? Kushin ɗinka? Na’ura mai ƙwaƙwalwa da ka ke da ita? Motarka? Maimakon waɗannan ba za ka yi tunanin waɗanda ka ke ƙauna ba? Babu shakka za ka yi, don mutane sun fi kaya tamani.
2. Yaya yawan halittan Jehovah, kuma wane sashensa ne Yesu ya fi ƙauna?
2 Yanzu ka yi tunani game da Jehovah Allah da kuma Ɗansa, Yesu Kristi. Jehovah ne ya “yi sama da ƙasa da teku, da abin da ke cikinsu duka.” (Ayukan Manzanni 4:24) Ta hannun Ɗansa, ‘gwanin aiki,’ Jehovah ya yi dukan wasu abubuwa. (Misalai 8:30, 31; Yohanna 1:3; Kolossiyawa 1:15-17) Hakika Jehovah da Yesu suna ɗaukan dukan abin da suka halitta da tamani. (Gwada da Farawa 1:31.) Amma wane sashe na halitta ka ke tsammanin ya fi masu—abubuwa ko mutane? Lokacin da hikima take alamta Yesu, ya ce: “Daulata tana wurin ’yan Adam,” ko kamar yadda juyin William F. Beck ya juya shi, Yesu ya yi “farinciki ƙwarai da bil Adam.”
3. Wane annabci ne Jehovah ya furta ta wajen Haggai?
3 Babu wata tantama cewa Jehovah yana ɗaukan mutane da tamani. An sami wani tabbaci ga hakan a kalmomin annabci da ya yi a shekara ta 520 K.Z. ta hannun annabinsa Haggai. Jehovah ya sanar: “Zan raurawadda dukan dangogi; kuma muradin dukan dangogi za ya zo; zan cika wannan gida da ɗaukaka. . . . Ɗaukaka ta baya ta wannan gida za ta fi ta farin.”—Haggai 2:7, 9.
4, 5. (a) Me ya sa ba zai zama daidai ba a kammala da cewa “muradi” yana nufin arziki? (b) Yaya za ka bada ma’anar “muradi,” kuma me ya sa?
4 Waɗanne “muradi” ne za su cika gidan Jehovah su kawo daraja babu irinta? Kayayyaki da aka ɓad da kuɗi akansu da kuma abubuwan ƙyali masu sada da ado mai yawa? Zinariya, azurfa, da kuma lu’u lu’u? Waɗannan da ƙyar su zama daidai. Ka tuna da haikali na dā da aka keɓe ƙarnuka biyar da farko, gini ne na biliyoyin daloli!a Babu shakka, Jehovah ba zai yi tsammanin haikali da wannan ƙaramin rukunin Yahudawa da aka komar da su ƙasar haihuwarsu suka gina ya fi haikalin Sulemanu da daraja ta kayayyaki ba!
5 To, menene “muradi” da za su cika gidan Jehovah? Hakika, za su zama mutane ne. Ban da haka ma, abin da yake sa zuciyar Jehovah take murna ba azurfa ba ce, ba kuma zinariya ba amma mutane ne waɗanda suke bauta masa cikin ƙauna. (Misalai 27:11; 1 Korinthiyawa 10:26) I, Jehovah yana ƙaunar dukan maza da mata da yara waɗanda suke yi masa sujada da yake gamsar da shi. (Yohanna 4:23, 24) Waɗannan “muradi” ne, kuma sun fi tamani wurin Jehovah fiye da dukan ƙyali da ta yi ma haikalin Sulemanu ado.
6. Wane amfani ne haikalin Allah na dā ya yi?
6 Duk da hamayya mai tsanani, an gama gina haikalin a 515 K.Z. Har sai lokacin hadayar Yesu, haikalin na Urushalima shine cibiyar sujada mai tsarki ga “muradi” da yawa da ya ƙunshi Yahudawa na jiki da kuma ’Yan Al’umma da suke addinin Yahudawa. Amma haikalin yana wakiltan abu ne mai girma, kamar yadda za mu gani.
Cika ta Ƙarni na Farko
7. (a) Menene haikalin Allah na Urushalima ta dā yake alamtawa? (b) Ka kwatanta aikin babban firist a Ranar Gafartawa.
7 Haikali da yake Urushalima alamu ne na tsari mai girma na sujada. Haikali ne na ruhaniya na Allah, wanda Jehovah ya kafa a shekara ta 29 A.Z. da Yesu shine Babban Firist. (Ibraniyawa 5:4-10; 9:11, 12) Ka duba kamani tsakanin ayyukan babban firist na Isra’ila da kuma ayyukan Yesu. Kowace shekara a Ranar Gafartawa, babban firist yakan je gaban bagadi da yake farfajiyar haikalin ya miƙa bijimi don zunuban firistoci. Daga baya, zai shiga cikin haikalin da jinin bijimin, zai wuce ta tsakanin ƙofofi da sun raba farfajiyar daga Mai-Tsarki sai kuma ta tsakanin labule da ya raba Mai-Tsarki daga Mafi-Tsarki. Yayin da ya shiga cikin Mafi-Tsarki, babban firist zai yarɓa jinin a gaban sunduƙi na alkawari. Sai ya sake yin haka, ya miƙa bunsuru don zunuban ƙabilu 12 na Isra’ila da ba firistoci ba. (Leviticus 16:5-15) Ta yaya wannan yake da alaƙa da haikalin ruhaniya na Allah?
8. (a) Ta wace hanya ce aka miƙa Yesu farawa daga 29 A.Z.? (b) Wace dangantaka ce ta musamman Yesu ya more da Jehovah lokacin hidimarsa a duniya?
8 Watau, an miƙa Yesu kan bagadin nufin Allah lokacin da aka yi masa baftisma kuma aka shafa shi da ruhu mai-tsarki na Allah a shekara ta 29 A.Z. (Luka 3:21, 22) Hakika, wannan aukuwa ta alamta farkon rayuwar sadaukarwa na Yesu wanda ya kai shekaru uku da rabi. (Ibraniyawa 10:5-10) A wannan lokacin, Yesu ya more dangantaka daga ruhu da Allah. Wannan dangantaka ta musamman na Yesu da Ubansa na samaniya ’yan Adam ba za su iya fahimtar ta ba sosai. Kamar dai ƙyalle ya rufe masu idanunsu na fahimi, kamar yadda danga ta tare waɗanda suke cikin haikali Mai-Tsarki daga farfajiyar alfarwa.—Fitowa 40:28.
9. Me ya sa Yesu ba zai iya shiga sama ba lokacin da yake mutum, kuma yaya aka magance wannan yanayi?
9 Ko da yake shi Ɗan Allah ne shafaffe daga ruhu, Yesu bai kai ga samun rayuwa a sama ba. Me ya sa? Domin nama da jini ba za su gaji Mulkin sama ba. (1 Korinthiyawa 15:44, 50) Tun da jiki na nama ne katanga, labule da ya raba Mai-Tsarki da Mafi-Tsarki na haikalin Jehovah na dā ya bada alamarsa sosai. (Ibraniyawa 10:20) Amma kwanaki uku bayan mutuwarsa, Allah ya tashi Yesu cikin ruhu. (1 Bitrus 3:18) Saboda haka ya shiga cikin Mafi-Tsarki na haikalin ruhaniya na Allah—sama kanta. Bulus ya rubuta daidai abin da ya faru: “Kristi ba ya shiga cikin wani wuri mai-tsarki [babu shakka yana nufin Mafi-Tsarki] wanda aka yi da hannuwa ba, mai-kama da na gaskiya ga zancen fasali; amma cikin sama kanta, shi bayana a gaban fuskar Allah sabili da mu yanzu.”—Ibraniyawa 9:24.
10. Menene Yesu ya yi da komawarsa sama?
10 A sama, Yesu ya ‘yarɓa jinin’ hadayarsa ta wurin miƙa tamani na fansa na jinin ransa ga Jehovah. Duk da haka, Yesu ya yi fiye da haka. Jim kaɗan kafin mutuwarsa, ya gaya wa mabiyansa: “Zan tafi garin in shirya maku wuri. Kadan na tafi na shirya maku wuri kuma, sai in sake dawowa, in karɓe ku wurin kaina; domin wurin da ni ke, ku zauna kuma.” (Yohanna 14:2, 3) Ta wurin samun shiga Mafi-Tsarki, ko sama, Yesu ya buɗe hanya ma wasu su biyo shi. (Ibraniyawa 6:19, 20) Waɗannan mutane, da adadinsu ya kai 144,000, za su yi hidiman mataimakan firist a tsarin haikalin ruhaniya na Allah. (Ru’ya ta Yohanna 7:4; 14:1; 20:6) Kamar dai yadda babban firist na Isra’ila yake ɗaukan jinin bijimi da farko ya shiga cikin Mafi-Tsarki ya nemi gafara ga zunuban firist, an yi amfani da tamani na jinin da Yesu ya zubar da farko ga waɗannan mataimaka firistoci 144,000.b
“Muradi” na Zamanin Yau
11. Saboda su wa babban firist na Isra’ila yake miƙa bunsuru, kuma menene wannan yake alamtawa?
11 Kamar dai tara shafaffu ya kare a shekara ta 1935.c Amma Jehovah bai gama daraja gidansa ba tukuna. A’a, “muradin” har yanzu za su shigo cikinsa. Ka tuna cewa babban firist a Isra’ila yana miƙa dabbobi biyu ne—bijimi don zunuban firistoci da kuma bunsuru don zunuban ƙabilun da ba firistoci ba. Tun da firistocin suna alamta shafaffu ne waɗanda za su zauna tare da Yesu a Mulkin sama, su wanene ƙabilun da ba firistoci ba suke alamtawa? An sami amsar a kalmomin Yesu da aka rubuta a Yohanna 10:16: “Ina da waɗansu tumaki kuma, waɗanda ba na wannan garke ba ne: su kuma dole zan kawo, za su kuma ji muryata: ya zama garke ɗaya, makiyayi ɗaya.” Saboda haka, jininsa da Yesu ya zubar ya amfani rukuni biyu na mutane—na farko, Kiristoci waɗanda begensu su yi sarauta tare da Yesu a sama kuma na biyu, waɗanda suke sauraran rayuwa har abada a aljanna a duniya. Babu shakka, wannan rukuni na biyu ne yake alamta “muradi” na annabcin Haggai.—Mikah 4:1, 2; 1 Yohanna 2:1, 2.
12. Ta yaya ake jawo “muradi” da yawa zuwa gidan Allah a yau?
12 Waɗannan “muradin” har yanzu suna cika gidan Jehovah. A shekarun baya bayan nan, a Gabashin Turai, ɓangarorin Afirka, da wasu ƙasashe an ɗaga takunkumi da aka saka masu, ya bar bisharar kafaffen Mulkin Allah ta bunƙasa a yankunan da har yanzu ba a taɓa su ba tukuna. Yayin da muradin suka shigo cikin tsarin haikalin Allah, sai su ma su yi ƙoƙari su almajirantar da wasu, a yin biyayya ga umurnin Yesu. (Matta 28:19, 20) Yayin da suke yin haka, suna gamuwa da mutane da yawa, matasa da tsofaffi, waɗanda da alamar za su iya zama “muradi” waɗanda za su daraja gidan Jehovah. Ka yi la’akari da misalai kaɗan na yadda wannan yake faruwa.
13. Ta yaya ’yar yarinya a Bolivia ta nuna himmarta ta yaɗa saƙon Mulki?
13 A Bolivia, wata yarinya ’yar shekara biyar da iyaye da suka yi renonta Shaidu ne ta tambaye malamarta ta ba ta hutu na mako ɗaya daga makaranta lokacin ziyarar mai-kula mai-ziyara. Me ya sa? Tana so ta yi hidima duk cikin mako na musamman na hidima. Wannan ya ba iyayenta mamaki, amma sun yi farinciki cewa tana da hali nagari. Wannan ’yar yarinyar yanzu tana tafiyar da nazarin Littafi Mai-Tsarki na gida guda biyar, kuma wasu cikin waɗannan ɗaliban suna zuwa taron Kirista. Har ta kawo malaminta na makaranta zuwa Majami’ar Mulki. Wataƙila a nan gaba, wasu ɗalibanta za su nuna su “muradi” ne da zai daraja gidan Jehovah.
14. A Korea, yaya naciyar wata yar’uwa ga wani wanda kamar ba shi da marmari ya sami albarka?
14 Da take jira a tashan jirgin ƙasa, wata Kirista ’yar Korea ta yi ma wani ɗalibi magana da yake sauraron kaɗe-kaɗe a rediyonsa. “Kana da addini?” ta tambaye shi. “Babu ruwana da addini,” ɗalibin ya amsa. Yar’uwar ba ta yi sanyin gwiwa ba. “Da aka jima kaɗan,” sai ta ci gaba, “mutum zai so ya zaɓi addini. Amma idan ba shi da sani game da addini, yana iya zaɓan mara kyau.” Furcin ɗalibin ya canja, sai ya fara sauraranta baki a buɗe. Ta ba shi littafin nan Is There a Creator Who Cares About You? ta kuma ce wannan littafin zai taimake shi sosai idan lokacin ya kai da zai zaɓi addini. Ya karɓa littafin. Mako na gaba, ya fara nazarin Littafi Mai-Tsarki da Shaidun Jehovah, kuma yanzu yana zuwa dukan taron ikklisiya.
15. Ta yaya wata ƙaramar yarinya a Japan ta fara nazarin Littafi Mai-Tsarki, kuma yaya ƙoƙarinta ya sami albarka?
15 A Japan, Megumi ’yar shekara 12 ta ga makarantarta fage ne mai amfani na yin wa’azi da koyarwa. Ta fara nazarin Littafi Mai-Tsarki da yawa. Ta yaya Megumi ta yi haka? Tun da tana karatun Littafi Mai-Tsarki ko kuma tana shiri don taro a lokacin cin abincin rana, ’yan ajinta sau da yawa suna tambayarta me take yi. Wasu suka tambaye Megumi dalilin da ya sa ba ta yin wasu ayyukan makaranta. Megumi ta amsa tambayoyinsu ta kuma gaya masu cewa Allah yana da suna. Wannan sau da yawa yana jawo hankalin masu sauraranta. Sai ita kuma ta ce za ta yi nazarin Littafi Mai-Tsarki da su. Megumi yanzu tana tafiyar da nazarori guda 20—18 cikinsu da ’yan ajinta.
16. Ta yaya wani ɗan’uwa a Kamaru ya iya fara nazarin Littafi Mai-Tsarki da wasu a rukunin ’yan ba’a?
16 A Kamaru, wasu maza takwas da suke aiki a wani wurin gini, suka kira wani ɗan’uwa da yake ba masu wucewa littattafan Littafi Mai-Tsarki. Don su yi ma ɗan’uwan ba’a suka tambaye shi dalilin da ya sa bai gaskata da Dunƙulin-Alloli-Uku ba, wutar jahannama, ko kuma rashin mutuwar kurwa. Ɗan’uwan ya yi amfani da Littafi Mai-Tsarki, ya amsa tambayoyinsu. Sakamakon haka, uku cikin mutane suka yarda a yi nazarin Littafi Mai-Tsarki da su. Ɗaya cikinsu, Daniel, ya fara zuwa taruwa har ma ya hallaka dukan abubuwansa da ke da alaƙa da sihiri. (Ru’ya ta Yohanna 21:8) Bai kai shekara ba, ya yi baftisma.
17. Ta yaya wasu yan’uwa maza a El Salvador suka yi amfani da dabara wajen yi ma wani mutum wanda da farko ba ya so ya ji saƙon Mulki?
17 A El Salvador, wani mutum sai ya ɗaure mafaɗacin karensa a ƙofar gidan duk lokacin da ya ga Shaidun Jehovah suna kusa. Mutumin zai jira lokacin da Shaidun suka shige, sai ya mai da karen cikin gida. Yan’uwan ba su taɓa samu sun yi ma mutumin magana ba. Wata rana suka gwada wata dabara. Da sanin cewa mutumin zai ji abin da suke faɗa, suka shawarta su yi ma karen wa’azi. Suka isa gidan suka gaida karen, suka ce sun yi farinciki da zarafi da suka samu su yi masa magana. Suka yi magana game da lokaci da za a yi aljanna a duniya, lokacin da babu wanda zai yi fushi—I, lokacin da dabbobi ma za su zama masu salama. Sai suka ce wa karen sai an jima suka fara tafiya. Ga mamakinsu sai mutumin ya fito daga gidan ya roƙi gafara don rashin ba Shaidun zarafi su yi magana da shi. Ya karɓi jaridu, kuma aka fara nazarin Littafi Mai-Tsarki da shi. Wannan mutumin yanzu ɗan’uwanmu ne—ɗaya cikin “muradin”!
“Kada Ku Ji Tsoro”
18. Waɗanne kalubale ne Kiristoci da yawa suke fuskanta, amma yaya Jehovah yake ganin bayinsa?
18 Ka na sa hannu cikin muhimmin aikin wa’azi da kuma na almajirantarwa? Idan haka ne, kana da gata na gaske. Babu shakka, ta wannan aikin ne ake jawo “muradin” zuwa gidan Jehovah. (Yohanna 6:44) A gaskiya, wani lokaci za ka ɗan gaji ko kuma ka yi sanyin gwiwa. Wasu lokutta, wasu—har a tsakanin bayin Jehovah masu aminci ma—sun yi kokawa da jin ba su da amfani. Sai ka yi ƙarfin zuciya! Jehovah yana ganin kowane bawansa da sha’awa, kuma yana damuwa da cetonka.—2 Bitrus 3:9.
19. Wace ƙarfafa ce Jehovah ya tanadar ta wajen Haggai, kuma ta yaya waɗannan kalmomi za su zama mana abin ƙarfafa?
19 Lokacin da ma ka yi sanyin gwiwa, ko saboda hamayya ko wasu yanayi da ba su da daɗi, kalmomin Jehovah ga Yahudawa da aka dawo da su ƙasar haihuwarsu za su zama abin ƙarfafa. A Haggai 2:4-6, mun karanta: “Duk da haka yanzu, ya Zerubbabel, ka yi ƙarfi, in ji Ubangiji; ka yi ƙarfi, ya Joshua, ɗan Jehozadak, babban firist; ku yi ƙarfi, dukanku mutanen ƙasa, in ji Ubangiji, ku yi aiki; gama ina tare da ku, in ji Ubangiji mai-runduna. Ku tuna da magana wadda na yi alkawari da ku sa’anda kuka fito daga Masar, ruhuna kuma yana zaune a wurinku; kada ku ji tsoro. Gama hakanan Ubangiji mai-runduna ya ce: Sauran so ɗaya, bayan an jima kaɗan, sai in raurawadda sammai, da duniya, da teku, da sandararriyar ƙasa.” Ka lura cewa Jehovah ba kawai ya gargaɗe mu mu yi ƙarfi ba amma ya yi tanadin abin da zai ba mu ƙarfi. Ta yaya? Ka lura da kalmomin tabbacin nan: “Ina tare da ku.” Lallai yana ƙarfafa bangaskiyarmu, sani cewa kowane irin abu da muka fuskanta, Jehovah yana tare da mu!—Romawa 8:31.
20. A wace hanya ce daraja da ba ta da iyaka take cika gidan Jehovah a yanzu?
20 Babu shakka Jehovah ya nuna cewa yana tare da mutanensa. Hakika, kamar yadda ya faɗa ne ta wajen annabi Haggai: “Ɗaukaka ta baya ta wannan gida za ta fi ta farin . . . A cikin wurin nan zan bada kwanciyar rai.” (Haggai 2:9) A gaskiya, daraja mafi girma a yau za a same ta ne a haikalin Jehovah na ruhaniya. Da Gaske, mutane dubbai ɗarurruwa suke taruwa ga sujada ta gaskiya kowace shekara. Waɗannan ana ciyar da su sosai a ruhaniya, kuma a cikin wannan duniya da babu kwanciyar rai, suna moran salama wadda ta sabuwar duniya ta Allah ce kawai za ta fi ta.—Ishaya 9:6, 7; Luka 12:42.
21. Me ya kamata ya zama ƙudurinmu?
21 Hukuncin Jehovah bisa al’ummai a Armageddon ya yi kusa. (Ru’ya ta Yohanna 16:14, 16) Saboda haka bari mu yi amfani da lokaci da ya rage mu taimaka mu ceci rayuka da yawa. Bari mu yi ƙarfi kuma mu dogara sosai ga Jehovah. Mu ƙudura aniyar mu ci gaba da bauta masa a cikin haikalinsa na ruhaniya mai-girma, mu cika ta da “muradin” da yawa har sai Jehovah ya ce aikinmu ya ƙare.
[Hasiya]
a Kyauta da aka bayar don ginin haikalin Sulemanu za ta kusa yin daidai da dala biliyan 40 a kuɗin yanzu. Dukan abin da ba a yi amfani da shi wurin ginin ba, an zuba cikin asusun haikalin.—1 Sarakuna 7:51.
b Yesu ba shi da zunubai da zai nema gafara, kamar na babban firist na Isra’ila. Amma dai, abokansa firistoci suna da zunubai domin an saye su daga tsakanin mutane masu zunubi.—Ru’ya ta Yohanna 5:9, 10.
c Duba Hasumiyar Tsaro, 1 ga Maris, 1998, shafofi 13-18.
Ka Tuna?
• Menene ya fi tamani ga Jehovah fiye da abubuwan duniya?
• Jinin Yesu da ya zubar ya amfani wane rukuni ne na mutane?
• Su wanene “muradi” da za su cika gidan Jehovah da daraja?
• Wane tabbaci ne muke da shi cewa annabcin Haggai yana cika a yau?
[Hotuna da ke shafi na 10]
Ka san muhimmancin alamta haikalin Jehovah na dā?
Labule
Mai-Tsarki
Bagadi
Mafi-Tsarki
Harabar Ƙofa
Farfajiya
[Hoto a shafi na 11]
Babban firist yana miƙa bijimi don zunuban firistoci, bunsuru kuma don zunuban ƙabilu da ba firistoci ba na Isra’ila
[Hoto a shafi na 12]
Wa’azin Mulki na dukan duniya yana jawo jama’a da yawa zuwa gidan Jehovah