TARIHI
Yadda Jehobah Ya Taimaka Mini in Kyautata Halina
BA ZAN taɓa manta da lokaci na farko da na shiga inda ake buga littattafai a Bethel ba, wato Bethel da ke Brooklyn, a jihar New York na Amurka. Da zarar na shiga inda ake buga littattafan, na yi mamaki don yadda injunan buga littattafan suke ƙara da kuma yadda suke jujjuyawa. Ƙura daga littattafan da ake bugawa sun cika koꞌina, ga kuma warin mān fetur.
Na lura da abubuwa da yawa, amma abin da ya fi burge ni shi ne mutanen da suke aiki a wurin. Na ga matasa maza da mata suna yin irin aikin da mutane da yawa ba za su so su yi ba. Saboda aikin nan da suke yi, ba a yawan ganin su ko kuma a yaba musu. Amma suna yin aikin da farin ciki da kuma gamsuwa. Misalinsu ya koya mini yadda zan bauta ma Allah da sauƙin kai.
Jehobah ya yi shekaru da yawa yana taimaka mini in kyautata halina. Amma bari in fara da gaya muku yadda na nemi gaskiya saꞌad da nake bin addinin Buddha.
NA YI ƘOƘARIN SANIN ALLAH NA GASKIYA SAꞌAD DA NAKE ƘARAMI
An haife ni a birnin Chicago da ke jihar Illinois a Amurka. Mu yara guda huɗu ne, kuma ni ne ɗan fari. Iyayena sun ƙaura daga Jafan zuwa Chicago domin sun yi tsammanin cewa yin rayuwa zai fi sauƙi a can. Sun so yaransu su je makaranta mafi inganci don su yi nasara a rayuwa.
Iyayena mabiyan addinin Buddha ne sosai. Mahaifiyata ta yi girma a gidan da akwai haikalin Buddha. Mahaifinta da kuma ꞌyanꞌuwanta maza biyu sun taɓa yin hidima a matsayin shugabanni a addinin Buddha. Saꞌad da nake girma, iyalina ba sa wasa da bin addinin. A duk lokacin da na dawo daga makaranta, abin da nake fara yi shi ne, ƙona turare mai ƙamshi, da kuma ba wa gunkin Buddha shinkafa da ruwa. A kowace ranar Lahadi, mukan je haikalin Buddha mu bauta ma gunki da ke kamar wanda muke da shi a gida, ko da yake gunkin nan ya fi na gidanmu girma kuma an shafe shi da zinariya.
Na tuna wani lokaci da na zuba wa gunkinmu ido saꞌad da nake shekara bakwai. Sai na tambayi kaina cewa, ‘Mene ne zai faru da ni bayan na mutu?’ A addinin Buddha, an koya mana cewa idan mutum ya mutu, zai je wani wuri da ruhohin matattu suke zama. Hakan ya sa na gano cewa ni ma wata rana zan mutu. Zan yi rayuwa a matsayin ruhu, amma ba zan sake jin daɗin rayuwa a matsayin mutum kuma ba. Wannan ya sa na yi baƙin ciki sosai, kuma na ji kamar ba ni da bege.
Saꞌad da nake wajen shekara 15, na soma jin cewa ayyukan bauta da nake yi wa Buddha ba su da amfani. Na gano cewa akwai abin da nake bukata a rayuwata. (Mat. 5:3) A cikin zuciyata, na san cewa akwai Allah mai rai wanda kuma shi ne mafi iko duka. Na so in san shi, kuma na yi tunani cewa Littafi Mai Tsarki zai taimaka mini in san shi. Sai na sayi juyin King James a wani bikin addinin Buddha. Abin mamaki ne cewa a irin wannan wurin ne na sayi Littafi Mai Tsarki.
Ni da Wilson Bashou, wanda ya koya mini gaskiya
Saꞌad da nake shekara 17, akwai lokacin da nake tafiya da karena, sai wani ɗanꞌuwa mai suna Wilson Bashou ya tambaye ni cewa: “Ka san alkawarin da Allah ya yi mana game da nan gaba?” Tambayar ta sa muka ɗau dogon lokaci muna tattaunawa game da Littafi Mai Tsarki. WIlson ya karanta Ruꞌuya ta Yohanna 17:1 sai ya tambaye ni cewa, “Mene ne ‘ruwa mai yawa’ da karuwar take zaune a kai yake nufi?” Ni kuma ban sani ba. Ya nuna mini aya ta 15 da ta nuna cewa mutane ne yake nufi. Na yi mamaki sosai da sanin cewa Shaidun Jehobah suna yin amfani da dukan Littafi Mai Tsarki don su iya bayyana wasu wurare a littafi Mai Tsarki da suke da wuyar fahimta. Bayan mun gama tattaunawar, sai ya ba ni littafi nan The Truth That Leads to Eternal Life. Ɗan ƙaramin littafin nan da ya ba ni ne ya canja rayuwata gabaki ɗaya.
Bayan kwana goma, sai na halarci taron Shaidun Jehobah a karo na farko a Majami’ar Mulki. Ba zan taɓa manta da yadda suka marabce ni hannu bibbiyu ba. Tun daga lokacin na ci-gaba da halartan taro. Jim kaɗan bayan haka, Wilson ya soma nazarin Littafi Mai Tsarki da ni. Na ji daɗin koyan abubuwa daga Littafi Mai Tsarki sosai, har akwai lokacin da muka yi awa takwas muna nazari.
Iyayena sun damu sosai don nazarin Littafi Mai Tsarki da nake yi. Amma da na ci-gaba da yin nazarin, na ƙara kasance da tabbaci cewa wannan ita ce hanyar gaskiya. Na yi baftisma a shekara ta 1983.
NA BAR MAKARANTAR JAMIꞌA DON IN YI HIDIMAR MAJAGABA
A lokacin da na yi baftisma, ina karatu don in zama likita a wata sananniyar makarantar jamiꞌa. Iyayena sun sadaukar da abubuwa da yawa don su iya kai ni makarantar. Da a ce na so, da na ci-gaba da karatun, amma na daina domin ina son in bauta wa Jehobah da dukan zuciyata ta wurin yin hidima ta cikakken lokaci.
Mahaifina ya riga ya gaya mini cewa, “Idan ka bar makarantar jamiꞌa, zan kore ka daga gidana!” Hakan ya sa na yi baƙin ciki, kuma ban san abin da zan yi ba. Ina ƙaunar iyayena kuma ba na so in yi abin da zai sa su baƙin ciki. Don haka, kullum a makaranta nakan fita da daddare in yi adduꞌa ga Jehobah ina cewa, “Ya Jehobah, ka taimaka mini in yanke shawarar da ta dace.” Da na yanke shawarar barin makaranta, mahaifina ya kore ni daga gida. Sai na kira Wilson na gaya masa abin da ya faru. Ya gaya mini cewa in zo gidansa. Na kwashi dukan kayana, sai na shiga mota zuwa gidansa. Na tuna cewa hankalina ya kwanta nan take, domin na san cewa na yanke shawarar da ta dace.
Na ji kamar tsuntsun da aka sake daga akurkinsa, wato na sami damar mai da hankali ga bauta wa Jehobah. A shekara ta 1984 na soma hidimar majagaba.
A lokacin da nake yin hidimar majagaba, Jehobah ya taimaka mini in koyi halaye masu kyau kamar haƙuri. Alal misali, akwai wata rana da na ji kamar kada in fita waꞌazi domin babu wanda ya fita waꞌazi a ranar. Duk da haka, na je waꞌazin. Bayan na yi awa biyu ina waꞌazi, sai na ce bari in kwankwasa ƙofa ta ƙarshe. Na riga na gaji da yin waꞌazi ni kaɗai, kuma kamar za a yi ruwan sama. Sai na yi tunani, ‘In koma gida ne?’ Ana nan, sai na hangi wani mutumin Filifin yana tsaye a can gaba. Sai na ce wa kaina. ‘Mutumin nan ba zai saurare ni ba.’ Amma na yi kuskure da yin tunanin nan, na soma nazari da mutumin, kuma daga baya ya soma bauta wa Jehobah da aminci.
NA KOYI DARUSSA MASU MUHIMMANCI A BETHEL DA KE BROOKLYN
Bayan na yi shekaru biyu a gidan Wilson, an gayyace ni hidima a Bethel da ke Brooklyn a 1985. Kamar yadda na ambata ɗazu, an ce in yi aiki a sashen buga littattafai. Wata rana da nake aiki a kan wani injin, sai na yi kuskure. Hakan ya jawo hasarar darurruwan bangon littattafai. ꞌYanꞌuwan sun gaya mini cewa in je in gaya wa ɗanꞌuwan da ke kula sashen abin da ya faru. Na gaya masa dalilan da suka sa na yi kuskuren, amma akwai abu ɗaya da ban yi ba. Cikin hankali ɗanꞌuwan ya tunasar da ni cewa, “Ba da haƙuri yana da kyau.” A lokacin ne na koyi cewa idan na yi laifi, kada in yi musu, kuma in ce, “Ka yi haƙuri.”
A sashen buga littattafai da ke Brooklyn
Misalin waɗanda suka daɗe suna hidima a Bethel ya koya mini yadda zan ƙara yi wa ꞌyanꞌuwa hidima. Akwai wata rana da muke teburi a wurin cin abinci tare da wani ɗanꞌuwa mai suna Milton Henschel, wanda shi memba Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu ne. A ranar, wurin ya cika da mutane da yawa, kuma ꞌyanꞌuwan da suke raba abinci suna iya ƙoƙarinsu don su ba wa kowa abinci. Mu, wato ni da wasu ꞌyanꞌuwa matasa da ke teburin muka soma gunaguni don muna ganin cewa masu raba abincin ba sa sauri. Ɗanꞌuwa Henschel bai ce kome ba, kawai ya tashi ya je ya sami masu raba abincin ya soma aiki da su wajen raba abinci. Aikin nan da ɗanꞌuwa Henschel ya yi ya nuna sauƙin kai, kuma ya tuna mini lokacin da Yesu ya wanke ƙafafun almajiransa. Ba zan taɓa manta da darasin ba.—Yoh. 13:3-5.
“KA KOYI YAREN JAFAN!”
Ni tare da Michiko Oda da magidanta
A shekara ta 1987 da na je ƙasar Jafan, na ji daɗin irin ƙwazo da kuma sauƙin kai da ꞌyanꞌuwa da ke wurin suke da su. Na so in taimaka musu a hidimar da suke yi, amma ban iya yaren Jafan ba. Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Michiko Oda da ke Bethel ta kalle ni a fuska ta ce mini, “Ka koyi yaren Jafan!” Kuma abin da na yi ke nan. Ban yi tunanin cewa abin da ta gaya mini zai canja rayuwata ba.
Bayan wasu ꞌyan watanni, sai na ƙaura zuwa wata ikilisiyar Jafan da ke birnin New York. Koyan yaren Jafan ya ba ni dama da yawa na bauta wa Jehobah. Shekara ta 1989 ne karo na farko da na halarci taron yanki a yaren Jafan a Los Angeles, California. Wata ꞌyarꞌuwa majagaba mai suna Miwako Onami da take ɗaya daga cikin waɗanda suka yi wasan kwaikwayo ta ɗauke hankalina.
Ni da Miwako mun yi aure a shekara ta a 1992, kuma mun sami gatan yin hidima tare a Bethel da ke Brooklyn. Miwako mace ce mai alheri da kuma hankali sosai, a kullum tana a shirye ta taimaka wa mutane. Misalinta ya koya mini yadda zan ƙara bi da mutane cikin alheri. Tana sa ni farin ciki kullum, babu shakka ita kyauta ce daga wurin Jehobah.
A ranar bikin aurenmu
BETHEL DA KE JAFAN DA KUMA HIDIMAR MAJAGABA NA MUSAMMAN
Da shigewar lokaci, iyayen Miwako da suke zama a Jafan sun soma rashin lafiya mai tsanani. Don haka, an bar mu mu je reshen ofishinmu na Jafan da ke kusa da iyayenta don mu iya kula da su. Mun ƙaura zuwa wurin a 1999.
Iyalin Bethel na Jafan sun marabce mu sosai, kuma ba da jimawa ba muka saba da wurin. Na ci-gaba da koyan halaye masu kyau daga wurin ꞌyanꞌuwa a Jafan, kamar bayarwa da kuma karɓan baƙi. Saꞌad da suke aiki, sukan yi shi da dukan zuciyarsu da kuma natsuwa. Kuma suna aiki cikin haɗin kai da juna. Ta yaya? A alꞌadar Jafan, mutane sun fi yin aiki tare don su cim ma wani abu maimakon mutum ya yi ƙoƙarin cim ma abin shi kaɗai. Misalinsu ya koya min yadda zan yi aiki tare da mutane cikin sauƙin kai, ya kuma taimaka mini in ga yadda aikin da nake yi yana taimaka wajen cim ma nufin Jehobah.
Duk da haka, da yake alꞌadarmu ba ɗaya ba ne, akwai lokutan da ya yi mini wuya in fahimci dalilin da ya sa ꞌyanꞌuwa a Jafan suka ɗauki wasu matakai. Na koyi yin haƙuri kuma kada in yi saurin fushi idan ban fahimci wani abu ba. Da shigewar lokaci, na canja yadda nake tunani, kuma na fahimci cewa Jehobah zai albarkaci kowace shawara da muka yanke muddin mun bi ja-gorancin da ya ba mu ta wurin ƙungiyarsa. Alhali ma, Jehobah ne yake sa aikin da muka yi ya yi nasara.
Nakan kwatanta yadda Bethel ya kyautata halina da yadda aka kyautata halin Musa. Jehobah ya taimaka wa Musa ya kasance da tawaliꞌu saꞌad da ya yi shekaru 40 a matsayin makiyayi. Kamar Musa, ni ma na yi makaranta sosai. Ilimin ya sa na zama mai girman kai kuma ina dogara da kaina. Bethel ya koya min in kasance da sauƙin kai kuma in dogara ga Jehobah. Kamar yadda Jehobah ya yi haƙuri saꞌad da yake kyautata halin Musa, ni ma ya yi haƙuri da ni a cikin shekaru da suka wuce.
Aiki a Bethel da ke Jafan
Mun yi ta kula da iyayen Miwako har na tsawon shekaru 24 kafin su mutu. A lokacin, mun yi ta kai da kawowa wajen kula da su. Yanayin mahaifiyar Miwako ya daɗa muni har ya kai lokacin da ta gagara yin tafiya. Ya yi mata wuya sosai ta halarci taro ko kuma ta fita waꞌazi. Makonni kafin ta mutu, ta soma yin amfani da keken guragu. Duk da matsalolin nan, ƙaunarta ga Jehobah ba ta yi sanyi ba. Tana farin ciki a duk lokacin da take gaya ma wasu game da Allah. Yadda Mahaifiyar Miwako ta ci-gaba da bauta wa Jehobah da gamsuwa da kuma farin ciki duk da yanayin da take ciki, abu ne da nake so in koya.
Waꞌazi da matata a Okinawa
A 2024, mun fuskanci wani babban canji. Bayan mun yi shekaru 30 muna hidima a Bethel, sai aka ce mu koma yin hidimar majagaba na musamman. A yanzu, muna yin hidimar a tsibirin Okinawa, kuma muna yin waꞌazi ga iyalan da suke zama kusa da sansanin soja da ke wurin. Abubuwan da aka koya mana a Bethel sun sa canjin bai yi mana wuya ba. Mun yi amfani da lokacinmu a hanyar da ta dace don mu iya mai da hankali ga yin waꞌazi da kuma wasu ayyukan ibada. Jehobah ya albarkace mu da ɗalibai waɗanda suka zama kamar iyali a gare mu. Mun ci-gaba da koya fiye da dā cewa yana da muhimmanci mu ƙaunaci mutane. Ni da matata Miwako muna godiya kullum don wannan gatan da Jehobah ya ba mu.
ZAN BAR JEHOBAH YA CI-GABA DA KYAUTATA HALINA
Ko da yake iyalina sun daina tsananta mini, ba su soma bauta wa Jehobah tukuna ba. Yesu ya yi alkawari cewa duk waɗanda suka bar iyalinsu kuma suka zama mabiyansa, za su sami fiye da sau ɗari, wato za su sami waɗanda suke bauta wa Jehobah da za su zama kamar iyalinsu. (Mar. 10:29, 30) Hakan ya faru da ni. Ba zan iya ƙirga yawan iyalai a duk faɗin duniya da suka nuna mini ƙauna ba, kuma suka ɗauke ni kamar ɗan iyalinsu.
Har wa yau, ina da littafin Truth da Wilson ya ba ni. A duk lokacin da na kalli littafin, sai in tuna da yadda Jehobah jawo ni wurinsa. (1 Tar. 28:9) Na ƙudiri niyyar barin Jehobah ya ci-gaba da kyautata halina, kuma in taimaka ma wasu su koyi gaskiyar da take kai ga rai na har abada.