TARIHI
Jehobah Ya Taimaka Mini Sosai
Ni da amaryata Evelyn ce muka sauko daga jirgi a garin Hornepayne da ke arewacin Ontario a ƙasar Kanada. Mun isa garin da sanyin safiya. Wani ɗan’uwa daga garin ne ya marabce mu kuma ya kai mu gidansa, inda ni da matarsa da ɗansa muka ƙarya. Bayan haka, sai muka fita wa’azi gida gida muna bin kan ƙanƙara. A wannan ranar ne na yi jawabina na farko a matsayin mai kula da da’ira. Mu biyar ne kawai a taron.
A GASKIYA, ƙanƙantar waɗanda suka halarci wannan taron a shekara ta 1957 bai dame ni ba, domin ina jin kunya sosai. A lokacin da nake matashi ma, nakan ɓuya a duk lokacin da iyalinmu ta yi baƙi, ko da ma na waye su.
Hakika, za ka yi mamakin sanin cewa saboda ire-iren hidimar da na yi a ƙungiyar Jehobah, na shaƙu da mutane dabam-dabam, wato da abokai da kuma baƙi. Ba zan iya buga ƙirji da duk wani abin da na cim ma a hidimata ba domin na yi ta fama da kunya da kuma tsoro. Maimakon haka, na ga tabbacin wannan alkawarin da Allah ya yi cewa: ‘Zan ƙarfafa ka: in taimake ka, i, in riƙe ka da hannun dama na adalcina.’ (Isha. 41:10) Wata muhimmiyar hanya da Jehobah ya taimaka mini ita ce goyon bayan da ’yan’uwa Kiristoci suka yi mini. Bari in ba ka wannan labarin. Zan soma da lokacin da nake ƙarami.
TA YI AMFANI DA LITTAFI MAI TSARKI DA WANI ƘARAMIN LITTAFI
A wajen shekara ta 1944, wata mata mai suna Elsie Huntingford ta ƙwanƙwasa ƙofarmu a lardin Ontorio. Mahaifiya ta ce ta je ta buɗe ƙofar yayin da ni da mahaifina muke zaune a ciki. Shi ma mai jin kunya ne sosai. Mahaifina ya zata cewa ’Yar’uwa Huntingford ta zo tallan kaya ne, kuma yana ganin cewa mahaifiyata za ta sayi abin da ba ma bukata. Da ya jira ya ji shuru, sai ya je bakin ƙofar kuma ya gaya mata cewa ba ma so. Sai ’yar’uwar ta tambaye shi cewa: “Kana nufin ba ku so ku yi nazarin Littafi Mai Tsarki?” Shi kuma ya amsa da cewa: “Haba, muna so mana.”
Hakika, ’yar’uwa Huntingford ta zo a daidai lokacin da muke bukatarta. Kafin wannan lokacin iyayena mabiya cocin da ake kira United Church of Canada ne. Amma sun daina zuwa cocin. Me ya sa? Domin limamin cocin yakan manna jerin sunayen waɗanda suka ba da gudummawa a farfajiyar cocin, kuma ana jera sunayen bisa ga yawan kuɗin da mutum ya biya ne. Tun da yake iyayena ba su da arziki, sunayensu sukan kasance a ƙarshe kuma limaman cocin suna matsa musu su daɗa kuɗin da suke bayarwa. Wani limamin cocin ya ce ba ya koyar da gaskiya domin ba ya so ya rasa aikinsa. Saboda haka, mun bar cocin amma har ila mun nemi hanyar koyo game da Allah.
An hana Shaidun Jehobah yin wa’azi a Kanada, saboda haka, ’yar’uwa Huntingford tana yin amfani da Littafi Mai Tsarki kaɗai da kuma wani ƙaramin littafin da ta yi rubutu a ciki don ta yi nazari da iyalinmu. Sa’ad da ta ga cewa ba za mu kai ƙararta wajen hukuma ba, sai ta soma ba mu littattafan da ke bayyana Littafi Mai Tsarki. Bayan kowane nazari, mukan ɓoye waɗannan littattafan da kyau.a
Duk da hamayya da kuma matsalolin da ’Yar’uwa Huntingford ta fuskanta, ta ci gaba da yin wa’azi da ƙwazo. Hakan ya burge ni kuma ya sa ni ma na soma bauta wa Jehobah. Shekara ɗaya bayan baftismar iyayena, ni ma na yi baftisma a ranar 27 ga Fabrairu na shekara ta 1949, a cikin wani komin dabbobi da aka ƙera da ƙarfe. Ina da shekara 17 a lokacin. Bayan haka, na ƙudura cewa zan soma hidima ta cikakken lokaci.
JEHOBAH YA TAIMAKA MINI IN KASANCE DA GABA GAƊI
Na yi jinkirin soma hidimar majagaba nan da nan. Na ɗan yi aiki a banki da kuma wani ofishi don ina ganin cewa ina bukatar yin ajiya don in tallafawa wa kaina yayin da nake hidimar majagaba. Amma da yake ba ni da basira, nakan kashe kuɗin nan da nan. Wani ɗan’uwa mai suna Ted Sargent ya ƙarfafa ni in kasance da gaba gaɗi kuma in dogara ga Jehobah. (1 Laba. 28:10) Hakan ya sa na soma hidimar majagaba a watan Nuwamba 1951. Ina da dalla 40 ne kawai a lokacin da wani tsohon keke da kuma jaka. Amma Jehobah ya biya bukatuna a kullum. Ina farin ciki sosai da yadda Ɗan’uwa Ted ya ƙarfafa ni in yi hidimar majagaba! Hakan ya sa na sami albarka sosai.
A wata yammar watan Agusta na shekara ta 1952, an kira ni a waya daga Toronto, babban birnin ƙasar Kanada. Ofishin reshen Shaidun Jehobah ne suka gayyace ni don in soma hidima a Bethel daga watan Satumba. Ko da yake ni mai jin kunya ne kuma ban taɓa zuwa ofishin ba, na yi farin ciki sosai domin abubuwan da wasu majagaba suka gaya mini game da Bethel sun burge ni sosai. Da na iso, na saki jiki nan da nan.
“KA NUWA WA ’YAN’UWA CEWA KANA ƘAUNARSU”
Shekaru biyu bayan na isa Bethel, na ɗauki matsayin Ɗan’uwa Bill Yacos na bawan ikilisiya, wanda yanzu ake kira mai tsara ayyukan rukunin dattawa a wata ikilisiya da ke birnin Toronto. Da yake shekaruna 23 ne kawai, sai na ji kamar wani ba-ƙauye. Amma Ɗan’uwa Yacos ya ƙaunace ni kuma ya nuna mini yadda zan yi wannan hidimar. Babu shakka, Jehobah ya taimaka mini sosai.
Yacos ɗan’uwa ne mai jiki da kuma fara’a. Yana ƙaunar ’yan’uwa kuma ’yan’uwan ma suna ƙaunarsa. Yakan ziyarce su a kai a kai, ba ya jira sai sun shiga matsala. Bill Yacos ya ƙarfafa ni in bi misalinsa kuma in riƙa fita wa’azi da ’yan’uwa maza da mata dabam-dabam. Ya ce: “Ka ga Kenneth, ka nuna wa ’yan’uwa cewa kana ƙaunarsu. Hakan zai sa ba za su damu da kasawarka ba.”
MATATA TA RIƘE AMANA
Jehobah ya taimaka mini a wata muhimmiyar hanya tun daga watan Janairu 1957. A wannan watan ne na auri Evelyn, wadda ta sauke karatu a Makarantar Gilead, aji na 14. Kafin mu yi aure, tana hidima a lardin Quebec da ake yaren Faransa. A wannan lokacin cocin Katolika ta mallaki wannan lardin. Saboda haka, hidimar Evelyn bai kasance mata da sauƙi ba, amma ba ta daina ba kuma ta kasance da aminci ga Jehobah.
Matata ta kuma riƙe amana. (Afis. 5:31) Hakika, akwai abin da ya faru bayan aurenmu da ya sa matata ta nuna cewa tana da riƙon amana. Mun shirya mu je hutu a birnin Florida da ke Amirka bayan aurenmu. Amma washegari, an kira ni daga ofishin reshe cewa in halarci wani taro na mako ɗaya a Bethel da ke Kanada. Wannan taron ya dagula shirin da muka yi na zuwa hutu bayan aurenmu, amma ni da matata mun ƙudura mu yi nufin Jehobah. A wannan makon, ta yi wa’azi a yankin da ke kusa da ofishin reshe. Ko da yake yankin ba ya kamar yankinta na dā, wato Quebec, amma ta dāge da yin wa’azi.
A ƙarshen makon, sai ga wani abin mamaki kuma, an ce in soma hidimar mai kula da da’ira a arewacin Ontario. Ban daɗe da aure ba, ga shi shekaruna 25 ne kawai kuma ba ni da ƙwarewa. Duk da haka, na kama hanya da gaba gaɗi cewa Jehobah zai taimake ni. A cikin sanyin Kanada, muka shiga jirgi mai tafiyar dare tare da wasu ƙwararrun masu kula masu ziyara da suke komawa yankunan hidimarsu. Sun ƙarfafa mu sosai! Ɗaya daga cikinsu ya nace cewa in yi amfani da ɗakin da ya yi haya a cikin jirgin don kada mu yi zama kawai duk dare. Washegari, wato kwana 15 bayan aurenmu, sai ga mu a wani ƙaramin rukuni da ke Hornepayne, kamar yadda na ambata ɗazun.
Tsugune ba ta kare wa ni da matata ba tukun. Yayin da muke hidimar masu kula da gunduma a ƙarshen shekara ta 1960, an gayyace ni zuwa aji na 36 na Makarantar Gilead, wanda zai ɗauki wata goma kuma za a soma a watan Fabrairu, 1961 a Brooklyn, Amirka. Na yi farin ciki sosai, amma kuma na damu cewa zan bar matata a gida. Kamar sauran matan ’yan’uwa da aka gayyata zuwa makarantar, an ce ta rubuta wasiƙa cewa ta yarda mu rabu da juna na tsawon watanni goma. Ko da yake Evelyn ta yi kuka, amma ta amince in je makarantar kuma ta yi murna cewa za a koyar da ni sosai a Gilead.
Yayin da nake makaranta, matata ta yi hidima a ofishin reshe na Kanada. Ta zauna a ɗaki ɗaya da ’yar’uwa Margaret Lovell, wadda take da begen zuwa sama. Hakika, hakan gata ne babba ga matata. A gaskiya, mun yi kewar juna sosai. Amma da taimakon Jehobah, mun ji daɗin hidimarmu. Yadda matata ta yarda mu rabu da juna na ɗan lokaci don Jehobah ya yi amfani da mu a ƙungiyarsa ya ratsa zuciyata sosai.
Bayan na yi wata uku a Gilead, sai Ɗan’uwa Nathan Knorr da ke kula da aikinmu a faɗin duniya a lokacin ya ba ni wani babban gata. Ya ce ko zan so in bar Makarantar Gilead kuma in koma Kanada don in koyar da ɗaliban Makarantar Hidima ta Mulki a ofishin reshen. Ɗan’uwa Knorr ya gaya mini cewa ba lallai sai na karɓi wannan gatan ba. Ya ce idan ina so, zan iya sauke karatuna kuma wataƙila a tura ni wa’azi a ƙasashen waje. Amma idan na amince in tafi Kanada, mai yiwuwa ba za a sake gayyata na zuwa Makarantar Gilead ba, kuma wataƙila a ce in koma ikilisiyarmu a Kanada. Sai ya ce ni da matata mu yi shawara.
Da yake na san ra’ayin matata game kowace irin hidima a ƙungiyar Allah, sai na gaya wa Ɗan’uwa Nathan Knorr cewa, “Duk abin da ƙungiyar Jehobah ta ce mu yi, za mu yi shi da farin ciki.” Ra’ayinmu shi ne, ya kamata mu je duk inda ƙungiyar Jehobah ta ce mu je.
Saboda haka, na bar Brooklyn a watan Afrilu, 1961 zuwa Kanada don in koyar da ɗaliban Makarantar Hidima ta Mulki. Bayan makarantar, muka soma hidimar Bethel. Amma daga baya, sai na sami gayyata zuwa Makarantar Gilead, aji na 40 da za a soma a shekara ta 1965. Hakan yana nufin cewa matata za ta sake rubuta wata wasiƙar da za ta nuna cewa ta amince mu rabu na ɗan lokaci. Amma bayan ’yan makonni, sai ga wani abin mamaki! Ita ma ta sami wasiƙar gayyata zuwa makarantar tare da ni.
Da muka isa Makarantar Gilead, Ɗan’uwa Nathan Knorr ya gaya mana cewa za a tura ɗaliban da suke ajin koyon Faransanci a Afirka, don su yi hidima. Amma da muka sauke karatu, an ce mu koma hidima a Kanada. An naɗa ni a matsayin mai kula da ofishin reshe, (wato mai tsara ayyukan Kwamitin da Ke Kula da Ofishin Reshe a yanzu). Da yake shekaruna 34 ne kawai, sai na gaya wa Ɗan’uwa Nathan Knorr cewa, “Ni ƙaramin yaro ne fa.” Amma ya ƙarfafa ni. Kafin in tsai da duk wata muhimmiyar shawara, nakan tuntuɓi ’yan’uwa da suka yi kwana-biyu a Bethel kuma suka ƙware sosai.
BETHEL WURIN KOYO NE DA KUMA KOYARWA
Hidimar Bethel ta ba ni zarafin koyan abubuwa da yawa daga wurin mutane. Ina daraja sauran ’yan mambobin Kwamitin da Ke Kula da Ofishin Reshen sosai. Na koyi abubuwa da yawa daga ’yan’uwa maza da mata, manya da ƙanana da yawa da suke hidima a nan Bethel da kuma a ikilisiyoyi dabam-dabam da muka yi hidima.
Hidimar Bethel ta sa na sami damar koyar da wasu da kuma ƙarfafa su. Manzo Bulus ya gaya wa Timoti cewa: “Ka lizima kai a cikin al’amuran da ka koyo.” Sai ya kuma ce: “Abubuwan da ka ji daga gareni kuwa a gaban shaidu da yawa, sai ka danƙa ma mutane masu-aminci, waɗanda za su iya su koya ma waɗansu kuma.” (2 Tim. 2:2; 3:14) A wasu lokuta, ’yan’uwana Kiristoci sukan tambaye ni darussan da na koya a cikin waɗannan shekaru 57 da na yi hidima a Bethel. Ina ce musu, “Ka amince da duk aikin da ƙungiyar Jehobah ta ba ka, kuma ka yi shi nan da nan, sa’an nan ka dogara ga Jehobah don ya taimaka maka.”
A lokacin da na zo Bethel, ni matashi ne da bai ƙware ba, kuma ina jin kunya. Amma cikin shekarun nan, Jehobah ya ‘riƙe hannun damana.’ Ƙari ga haka, alheri da kuma taimakon da ’yan’uwa masu bi suka yi mini, ya zama kamar Jehobah ne yake tabbatar mini cewa: “Kada ka ji tsoro, ni taimake ka.”—Isha. 41:13.
a A ranar 22 ga Mayu 1945, gwamnatin ƙasar Kanada ta ba da ’yancin yin wa’azi a ƙasar.