Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w12 2/15 pp. 31-32
  • ‘Ya Sa Ana Ta Kallo Na’

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • ‘Ya Sa Ana Ta Kallo Na’
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
w12 2/15 pp. 31-32

Daga Tarihinmu

‘Ya Sa Ana Ta Kallo Na’

Mutane suna ta kallon Charlotte White mai wa’azi na cikakken lokaci sa’ad da ta isa birnin Louisville, Kentucky da ke Amirka, tana tura akwati mai taya.

A SHEKARA ta 1908 ’Yar’uwa White ta jawo hankalin mutane ta wajen yin amfani da sabon akwati mai taya da ake kiran “Dawn Mobile” na ɗaukan littattafai. Ta ce, “Mutane sun yi magana game da shi, kuma akwatin ya sa ana ta kallo na.”

Ɗaliban Littafi Mai Tsarki, yadda ake kiran Shaidun Jehobah a lokacin sun ga ya dace su gaya wa mutane game da gaskiya mai tamani da suka koya ta wajen yin nazarin Nassosi sosai. Mutane da yawa a lokacin sun koya game da Littafi Mai Tsarki ta wajen jerin littattafai masu jigo Millennial Dawn (wanda daga baya ake kiran su Studies in the Scriptures). Waɗannan Kiristoci da suke a shirye kuma suna da ƙarfin yin hakan sun yi tafiya mai nisa sosai, suna zuwa garuruwa da ƙauyuka suna rarraba waɗannan littattafan ga waɗanda suke ɗokin su karanta su.

A shekara ta 1908, ’Yar’uwa White da wasu masu shelar Mulki da ƙwazo sun rarraba wannan littafi mai kundi shida da aka rufe bangon da zane. Kuma farashin wannan littafin kusan dala biyu ne. Maimakon su ba mai-gidan littattafan nan da nan, suna karɓan odar yawan littattafan da mutane suke so sai kuma su dawo daga baya, musamman ranar da ake biyan albashi don su ba da littattafan kuma su karɓi ɗan kuɗi don buga littattafan kawai. Wani mai hamayya ya nemi laifi don mutane suna ba da ɗan gudummawar kuɗi sa’ad da suka karɓi littattafan.

Malinda Keefer ta tuna karɓan odar littattafai ɗari biyu zuwa ɗari uku a mako. Son littattafan da ake yi ya kawo matsala. Littafi na shida yana da shafuffuka 740! Marubutan sun ce, “Nauyin littattafai hamsin laba arba’in ne,” hakan ya sa rarraba su “yake da wuya ainun,” musamman ga ’yan’uwa mata.

Don a taimaki mutane su rarraba littattafan, Ɗan’uwa James Cole ya saka wa akwatin ɗaukan kaya tayoyi guda biyu. Wannan sabuwar fasaha ta sa suka daina ɗaukan katan mai cike da littattafai. Kuma ɗan’uwan da ya ƙera wannan akwati mai taya ya ce: “Yanzu, na daina ɗaukan littattafai masu nauyi a kafaɗa ta.” Ya fito da wannan sabuwar fasaha ga waɗanda suka hallara a taron gundumar da aka yi a shekara ta 1908, a birnin Cincinnati, a garin Ohio. Da yake ainihi muna ɗaukan littattafan Millennial Dawn a cikin wannan akwatin, sai muka rubuta Dawn-Mobile a jikin akwatin. Bayan ɗan lokaci, muka saba yin tafiya da akwati mai cike da littattafai. Za a iya daɗa ko kuma rage tsawon akwatin, kuma za a iya jan akwatin a hanyar da motoci suke bi. Bayan an kammala wa’azi, ana iya naɗe tayar akwatin kuma a komar da akwatin gida a kafa ko kuma da mota.

’Yan’uwa mata da suke hidima ta cikakken lokaci suna samun wannan akwatin kyauta. Amma ainihin kuɗin wannan akwatin dala biyu da rabi ne. ’Yar’uwa Keefer, da aka nuna a wannan hoton ta san yadda ake amfani da wannan akwatin sosai har tana iya tura wannan akwatin da hannu ɗaya kuma ta riƙe wasu littattafai da ɗayan hannun. Don ta kai wa mutanen da suke wani garin da ake haka ƙwal, a Pennsylvania, a ƙasar Amirka littattafan, tana ƙetare gada sau uku ko huɗu.

A shekara ta 1980 zuwa 1989, wani matuƙin jirgin sama ya ƙera akwati mai tayoyi da muke yawan gani a yau a tashar jirgin sama da kuma wurare da yawa. Amma shekara ɗari da suka shige, ɗaliban Littafi Mai Tsarki masu ƙwazo suna farin ciki don mutane suna kallonsu sa’ad da suke tura akwati mai taya yayin da suke koya wa mutane gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki.

[Bayanin da ke shafi na 32]

’Yar’uwa Keefer tana ƙetare gada sau uku ko huɗu a rana don ta rarraba littattafai

[Bayanin da ke shafi na 32]

Wannan akwatin ya sa ɗaukan littafin nan Millennial Dawn ya yi sauƙi

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba