Za a Iya Yin Farin Ciki a Iyalin da ba Kowa Ba Ne Yake Bauta wa Jehobah
“Ina kin sani, ko za ki ceci mijinki? . . . ina ka sani, ko za ka ceci matarka?”—1 KOR. 7:16.
SHIN ZA KA IYA BA DA AMSOSHIN?
․․․․․
Mene ne waɗanda suke bauta wa Jehobah za su yi don a kasance da salama a cikin iyalin da ba kowa ba ne yake bauta wa Jehobah?
․․․․․
Ta yaya Kirista zai taimaka wa danginsa da ba sa bauta wa Jehobah su soma yin hakan?
․․․․․
Mene ne za mu iya yi don mu taimaka wa waɗanda suke da dangin da ba sa bauta wa Jehobah?
1. Idan mutum ya soma bauta wa Jehobah, yaya hakan zai shafi iyalinsa?
A WANI lokaci da Yesu ya tura manzanninsa wa’azi, ya ce: “A cikin tafiyarku kuma ku yi wa’azi, ku ce, Mulkin sama ya kusa.” (Mat. 10:1, 7) Wannan bishara za ta kawo salama da farin ciki ga waɗanda suka karɓa saƙon da farin ciki. Amma, Yesu ya gargaɗi manzanninsa cewa mutane da yawa za su yi musu hamayya don aikinsu na wa’azi. (Mat. 10:16-23) Hamayya da ta fi sa mutum baƙin ciki ita ce sa’ad da waɗanda suke cikin iyali suka ƙi saƙon Mulki.—Karanta Matta 10:34-36.
2. Me ya sa zai yiwu mu yi farin ciki ko idan waɗanda suke cikin iyalinmu ba sa bauta wa Jehobah?
2 Shin hakan yana nufin cewa ba za mu yi farin ciki ba idan waɗanda suke cikin iyalinmu ba sa bauta wa Jehobah? A’a! Ko da yake ana tsananta wa wasu Kiristoci sosai, amma ba dukansu ba ne ake wa hakan ba. Kuma wataƙila, hamayya ta iyali ba za ta kasance na dindindin ba. Hakan ya dangana ga yadda masu bauta wa Jehobah suke aikatawa ga hamayyar ko kuma rashin son saƙonmu. Bugu da ƙari, Jehobah yana taimaka wa waɗanda suke da aminci a gare shi, yana sa su yi farin ciki a cikin yanayi mai wuya. Kiristoci za su fi farin ciki idan suka (1) yi ƙoƙari su kasance da salama a cikin iyali da kuma (2) yi ƙoƙari su taimaka wa waɗanda suke cikin iyalinsu su soma bauta wa Jehobah.
KA KASANCE DA SALAMA A CIKIN IYALI
3. Me ya sa Kirista zai yi aiki tuƙuru don a kasance da salama a cikin iyalinsa?
3 Mutane a cikin iyali suna iya soma bauta wa Jehobah idan akwai salama. (Karanta Yaƙub 3:18.) Idan dukan waɗanda suke cikin iyalin ba su soma bauta wa Jehobah ba tukuna, dole ne Kirista ya yi aiki tuƙuru don a kasance da salama a cikin iyali. Ta yaya zai iya yin hakan?
4. Ta yaya Kiristoci za su kasance da kwanciyar hankali?
4 Dole ne Kiristoci su kasance da kwanciyar hankali. Don a yi hakan, muna bukatar mu yi addu’a don “salama kuwa ta Allah.” (Filib. 4:6, 7) Ana yin farin ciki da kasancewa da salama ta wajen koyo game da Jehobah da kuma yin rayuwa da ta jitu da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki. (Isha. 54:13) Muna bukatar mu halarci tarurrukan ikilisiya kuma mu kasance da ƙwazo a yin wa’azi idan muna son mu samu salama kuma mu yi farin ciki. Waɗanda suke cikin iyali da ba kowa ba ne yake bauta wa Jehobah suna iya yin waɗannan abubuwa masu muhimmanci. Alal misali, ka yi la’akari da wata ’yar’uwa mai suna Enza,a wadda mijinta yake tsananta mata sosai. Tana aikin wa’azi bayan ta yi aikace-aikacen gida. Enza ta ce: “Jehobah ya albarkace ni sosai da sakamako mai kyau a kowane lokacin da na yi ƙoƙari na yi wa mutane wa’azin bishara.” Irin wannan albarka tana sa a kasance da salama da wadar zuci da kuma farin ciki.
5. Wane ƙalubale ne waɗanda suke bauta wa Jehobah suke fuskanta daga danginsu da ba sa bauta wa Jehobah, kuma a ina ne za su samu taimako?
5 Muna bukatar mu yi iya ƙoƙarinmu don mu kasance da salama da waɗanda suke cikin iyalinmu da ba sa bin imaninmu. Hakan yana iya kasance da wuya domin a wasu lokatai suna iya son mu yi abubuwa da sun saɓa wa ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki. Wasu da suke cikin iyalinmu da ba sa bauta wa Jehobah suna iya yin fushi sa’ad da muke bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki da aminci, amma yin hakan yana sa a kasance da salama. Hakika, muna yin iya ƙoƙarinmu don mu ba da haɗin kai ga iyalin idan wani abu bai saɓa wa ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki ba, ta hakan za mu guji yin jayayya. (Karanta Misalai 16:7.) Sa’ad da muke fuskantar ƙalubale, yana da muhimmanci mu nemi gargaɗi na Nassi daga littattafan da bawan nan mai-aminci, mai-hikima ya wallafa da kuma daga dattawa.—Mis. 11:14.
6, 7. (a) Me ya sa wasu suke hamayya da waɗanda suke cikin iyali da suka soma nazari da Shaidun Jehobah? (b) Ta yaya ya kamata ɗalibin Littafi Mai Tsarki ko kuma Mashaidi ya aikata ga hamayya ta iyali?
6 Za mu kasance da salama a cikin iyali idan muka dogara ga Jehobah kuma muka yi ƙoƙari mu fahimci yadda iyalinmu take ji. (Mis. 3:13; 16:20) Sababbin ɗaliban Littafi Mai Tsarki ma suna iya gwada wannan. Wasu magidanta ko kuma mata da ba sa bauta wa Jehobah ba za su yi hamayya da mazansu ko matansu ba idan suna nazarin Littafi Mai Tsarki. Suna iya faɗan cewa hakan zai amfane iyalinsu. Amma, wasu suna iya yin hamayya sosai. Esther wadda Mashaidiya ce yanzu ta ce ta yi “fushi sosai” sa’ad da mijinta ya soma nazari da Shaidun Jehobah. Ta ce, “Na jefar da littattafansa ko kuma na ƙone su.” Howard, wanda da farko ya tsananta wa matarsa sa’ad da ta soma nazarin Littafi Mai Tsarki ya ce: “Magidanta da yawa suna jin tsoro cewa an ruɗi matansu su shiga wata ɗarika na addini. Tun da yake mijin yana ganin cewa matarsa tana cikin haɗari, yana iya magana da kuma aikata da fushi.”
7 Ya kamata mu taimaka wa ɗalibai na Littafi Mai Tsarki da mazansu ko matansu suke hamayya su gane cewa ba sa bukatar su daina nazarinsu na Littafi Mai Tsarki. Shi ko ita tana iya kyautata yanayin ta wajen kasancewa da sauƙin hali da kuma daraja mijinta ko matarsa. (1 Bit. 3:15) Howard ya ce, “Na gode wa Allah cewa matata ta kasance da sauƙin hali kuma ba ta yi saurin fushi ba!” Matarsa ta bayyana: “Howard ya ce na daina nazarin Littafi Mai Tsarki. Ya ce ana ruɗi na. Maimako na yi musu, na ce wataƙila gaskiya ne, amma da gaske ban ga yadda ake ruɗi na ba. Sai na gaya masa ya karanta littafin da nake nazarinsa. Ya yi hakan kuma ya amince da abin da littafin ya ce. Hakan ya shafe shi sosai.” Yana da kyau a tuna cewa mutane suna iya kaɗaitawa ko kuma su yi tunani cewa aurensu yana cikin haɗari sa’ad da abokin aurensu ya bar su ya tafi tarurruka ko kuma wa’azi. Amma nuna ƙauna da kuma ƙin yin baƙar magana ga mijin ko matar zai sa kada su damu.
KA TAIMAKE SU SU SAN GASKIYA
8. Wace shawara ce manzo Bulus ya ba Kiristoci da suke da abokan aure da ba sa bauta wa Jehobah?
8 Manzo Bulus ya ba Kiristoci shawara kada su bar abokin aurensu domin ba mai bauta wa Jehobah ba ne.b (Karanta 1 Korintiyawa 7:12-16.) Tuna cewa wata rana abokin aure yana iya zama Mashaidi zai iya taimaka wa mai bauta wa Jehobah ya ci gaba da farin ciki. Amma yana da kyau ya mai da hankali ga yadda yake ƙoƙarin taimaka wa abokiyar aurensa ta fahimci gaskiya kamar yadda labarai na gaba suka nuna.
9. Bai kamata Kirista ya yi mene ne ba sa’ad da yake gabatar da gaskiyar da ke Littafi Mai Tsarki ga iyalinsa da ba sa bauta wa Jehobah?
9 Wani mai suna Jason ya yi farin ciki sosai sa’ad da ya koyi gaskiyar da ke Littafi Mai Tsarki. Ya ce, “Ina son na gaya wa kowa!” Sa’ad da ɗalibin Littafi Mai Tsarki ya fahimci cewa abin da ya koya a cikin Littafi Mai Tsarki gaskiya ne, yakan yi farin ciki sosai da har zai riƙa maganarsa kusan a kowane lokaci. Yana iya sa rai cewa waɗanda suke cikin iyalinsa za su soma bauta wa Jehobah nan da nan, amma suna iya ƙin yin hakan. Yaya matar Jason ta aikata ga farin cikin da yake yi? Ta ce, “Na ji kamar kada ya taɓa daina magana game da gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki.” Wata mata da ta soma bauta wa Jehobah bayan shekara 18 da mijinta ya soma, ta ce, “Ina bukatar na koyi gaskiya a hankali.” Idan kana nazari da wanda matarsa ba ta son ta bauta wa Jehobah, zai dace ka nuna wa ɗalibin yadda zai bayyana wa matarsa gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki a hanyar da ba za ta yi fushi ba. Musa ya ce: ‘Koyarwata kuma ta ɗiga kamar ruwan sama, zancena ya yi tururi kamar raɓa; kamar yayyafi bisa yabanya.’ (K. Sha 32:2) Gajeren kalami game da gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki da aka faɗa yadda ya dace da kuma a lokacin da ya dace sau da yawa ya fi yawan maganganu kyau.
10-12. (a) Wane gargaɗi ne manzo Bitrus ya ba Kiristoci da abokan aurensu ba sa bauta wa Jehobah? (b) Ta yaya wata ɗalibar Littafi Mai Tsarki ta koya ta bi shawarar da ke 1 Bitrus 3:1, 2?
10 Manzo Bitrus ya gargaɗi mata Kiristoci da mazansu ba sa bauta wa Jehobah. Ya ce: “Ku yi zaman biyayya ga mazaje naku; domin ko da akwai waɗansu da ba su yin biyayya da magana, su rinjayu ban da magana saboda halayen matansu; suna lura da halayenku masu-tsabta tare da tsoro.” (1 Bit. 3:1, 2) Ta wajen zama mai tawali’u da kuma daraja mijinta, mata za ta iya shawo kansa ya soma bauta ta gaskiya ko idan yana tsananta mata. Haka nan ma, ya kamata miji mai bauta wa Jehobah ya aikata yadda Allah yake so kuma ya zama shugaban iyali mai ƙauna, ko idan matarsa tana yi masa hamayya.—1 Bit. 3:7-9.
11 Kiristoci da yawa a yau sun amfana ta wajen bin shawarar Bitrus. Ka yi la’akari da misalin wata mai suna Selma. Mijinta, Steve, bai yi farin ciki ba sa’ad da ta soma nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehobah. Ya ce, “Na yi fushi da kishi kuma na ji tsoro.” Selma ta ce: “Kafin ma na soma bauta wa Jehobah, zama da shi ba shi da sauƙi. Shi mai zafin rai ne. Kuma wannan matsalar ta daɗa muni sa’ad da na soma nazarin Littafi Mai Tsarki.” Mene ne ya taimaka mata?
12 Selma ta tuna da darasin da ta koya daga Mashaidiya da ta yi nazari da ita. Ta ce: Akwai wata rana da ba na so a yi nazarin Littafi Mai Tsarki da ni. A daren da ya gabata, mijina Steve, ya mare ni yayin da muke yin gardama, na yi baƙin ciki kuma na tausaya wa kaina. Sa’ad da na gaya wa ’yar’uwar abin da ya faru da yadda nake ji, sai ta ce na karanta 1 Korintiyawa 13:4-7. Yayin da na yi hakan, sai na soma tunani, ‘Mijina Steve, bai taɓa ƙauna ta haka ba.’ Amma, ’yar’uwar ta sa na yi tunani dabam ta wajen tambaya ta, ‘A cikin waɗannan ayyukan ƙauna, guda nawa ne ki ke wa mijinki?’ Na amsa cewa, ‘Ban taɓa yin kowanne ba, gama yana da wuya a zauna da shi.’ ’Yar’uwar ta ce a hankali, ‘Selma, wane ne yake ƙoƙari ya zama Kirista a nan? Ke ko Mijinki?’ Da yake na fahimci cewa ina bukatar na daidaita ra’ayi na, sai na yi addu’a ga Jehobah ya taimake ni na ƙaunaci Steve. Abubuwa suka soma gyaruwa a hankali.” Steve ya soma bauta wa Jehobah bayan shekara 17.
YADDA WASU ZA SU IYA TAIMAKA
13, 14. Ta yaya wasu za su taimaka wa waɗanda ba dukansu ba ne suke bauta wa Jehobah a cikin iyali?
13 Kamar yadda yayyafi ke jika ƙasa da kuma taimaka wa shuke-shuke su yi girma, mutane da yawa a cikin ikilisiya za su iya taimaka wa waɗanda suke cikin iyali da ba kowa ba ne ke bauta wa Jehobah su yi farin ciki. Elvina da ke Brazil ta ce, “Ƙaunar da ’yan’uwana ke nuna mini ce ta taimaka mini na yi tsayin daka a bauta ta ga Jehobah.”
14 Mutumin da ba ya bauta wa Jehobah zai iya canja ra’ayinsa idan ’yan’uwa da ke cikin ikilisiya suka nuna masa alheri da kuma ƙauna. Wani miji a Nijeriya wanda ya soma bauta wa Jehobah shekara 13 bayan matarsa, ya ce: “Sa’ad da nake tafiya da wani Mashaidi, motarsa ta lalace a hanya. Sai ya nemi ’yan’uwa Shaidu a wani ƙauye da ke kusa, sai suka ba mu wurin kwanciya daddare nan. Sun kula da mu kamar mun san su tun muna yara. Nan da nan, na shaida ƙauna ta Kirista da matata take maganarsa.” A ƙasar Ingila, wata mata da ta soma bauta wa Jehobah shekara 18 bayan mijinta ta tuna: “Ina sake jiki duk sa’ad da Shaidun Jehobah suka gayyace ni da mijina zuwa gidansu.”c Wani mutum daga Ingila da ya zama Mashaidi daga baya ya ce: “’Yan’uwa suna ziyararmu ko kuma su gayyace mu zuwa gidajensu, kuma na lura cewa suna da halin kula da mutane. Na lura da hakan musamman sa’ad da nake asibiti kuma mutane da yawa sun zo sun ziyarce ni.” Shin za ka nuna cewa ka damu da iyalan da ba dukansu ba ne suke bauta wa Jehobah ba?
15, 16. Mene ne zai taimaka wa wanda ke bauta wa Jehobah ya yi farin ciki ko da wasu a cikin iyalinsa sun ƙi su bauta wa Jehobah?
15 Hakika, ko da mun yi abin da ya dace kuma mun yi wa’azi cikin shekaru da yawa, ba kowa ba ne zai bauta wa Jehobah. Har ila, wasu ba za su so saƙon ba ko kuma za su ci gaba da yin hamayya sosai. (Mat. 10:35-37) Amma, sa’ad da Kiristoci suka nuna halaye masu kyau, hakan zai kawo sakamako mai kyau. Wani magidanci da ba ya bauta wa Jehobah a dā ya ce: “Sa’ad da mace ko miji da ke bauta wa Jehobah ta soma nuna waɗannan halaye masu kyau, ba za ka iya sanin abin da wanda ba ya bauta wa Jehobah yake tunani ba. Saboda haka, kada ki fid da rai cewa abokin aurenki da ba ya bauta wa Jehobah ba zai taɓa yin hakan ba.”
16 Har ila waɗanda iyalansu ba sa bauta wa Jehobah za su iya yin farin ciki. Ko da yake mijinta bai amince da saƙon Mulki bayan shekara 21 da ta yi ƙoƙari sosai ba, wata ’yar’uwa ta ce: “Na ci gaba da farin ciki ta wajen yin ƙoƙari na faranta wa Jehobah rai da kasancewa da aminci a gare shi da kuma ƙarfafa dangantakata da Jehobah. Shagalawa a ayyukanmu ga Jehobah, wato, yin nazari na kaina da halartan tarurruka da wa’azi da kuma taimakon mutane a cikin ikilisiya sun taimaka mini na kusaci Jehobah da kuma kasance da aminci a gare shi.”—Mis. 4:23.
KADA KA KARAYA
17, 18. Ta yaya Kirista zai kasance da bege a cikin iyalin da ba kowa ba ne yake bauta wa Jehobah?
17 Idan kai Kirista ne mai aminci kuma kana zama a cikin iyalin da ake bin addini dabam dabam, kada ka karaya. Ka tuna cewa “Ubangiji ba za ya yarda jama’atasa ba sabili da sunansa mai-girma.” (1 Sam. 12:22) Yana tare da kai muddin ka kusace shi. (Karanta 2 Labarbaru 15:2.) Saboda haka, “ka faranta zuciyarka cikin Ubangiji.” Hakika, “ka danƙa wa Ubangiji tafarkinka; ka dogara gareshi.” (Zab. 37:4, 5) Ka “lizima cikin addu’a,” kuma ka kasance da tabbaci cewa Ubanmu na samaniya zai taimaka maka ka jimre da matsaloli iri-iri.—Rom. 12:12.
18 Ka yi addu’a ga Jehobah don ya ba ka ruhunsa mai tsarki da zai taimaka maka ka kasance da salama a cikin iyali. (Ibran. 12:14) Hakika, zai yiwu ka sa salama ta kasance, kuma hakan daga baya za ta motsa zuciyar waɗanda ba sa bauta wa Jehobah a cikin iyalinka su soma yin hakan. Za ka yi farin ciki kuma ka kasance da kwanciyar rai yayin da kake ‘yin dukan abubuwa domin a girmama Allah.’ (1 Kor. 10:31) Ka kasance da tabbaci cewa ’yan’uwanka Kiristoci za su ƙaunace ka kuma su tallafa maka!
[Hasiya]
a An canja sunayen.
b Gargaɗin Bulus bai hana Kiristoci su rabu da abokan aurensu a yanayi mai tsanani ba. Wannan shawara ce mai muhimmanci da mutum zai tsai da wa kansa. Ka duba littafin nan “Ku Tsare Kanku Cikin Ƙaunar Allah,” shafuffuka na 220-221.
c Nassosi ba su hana cin abinci tare da waɗanda ba sa bauta wa Jehobah.—1 Kor. 10:27.
[Hoto a shafi na 28]
Ka nemi lokacin da ya dace don ka bayyana wa matarka imaninka
[Hoto a shafi na 29]
Ka nuna wa waɗanda ba sa bauta wa Jehobah cewa kana ƙaunar su