Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w11 2/15 pp. 6-10
  • Ruhu Mai Tsarki Ya Yi Aiki Wajen Halitta!

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ruhu Mai Tsarki Ya Yi Aiki Wajen Halitta!
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Mu’ujizar Halitta
  • Ikon Allah Marar Iyaka
  • Ruhu Mai Tsarki da kuma Duniya
  • Ruhu Mai Tsarki da kuma Halittu Masu Rai
  • Kammala Halitta a Duniya
  • Sanin Matsayin Ruhu Mai Tsarki
  • Ruhu Mai Tsarki da Imaninmu ga Allah
  • Me Ya Sa Ruhun Allah Zai Yi Mana Ja-gora?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Ikon Halitta—‘Mahaliccin Sama da Kasa’
    Ka Kusaci Jehobah
  • Yadda Ruhun Allah Ya Yi Ja-gora A Ƙarni Na Farko Da Kuma A yau
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Ka Yi Tafiya Bisa Ga Ruhu Kuma Ka Yi Rayuwar Da Ta Jitu Da Keɓe Kanka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
w11 2/15 pp. 6-10

Ruhu Mai Tsarki Ya Yi Aiki Wajen Halitta!

“Da maganar Ubangiji aka yi sammai; rundunansu duka kuma da lumfashin bakinsa.”—ZAB. 33:6.

1, 2. (a) Ta yaya ilimin mutane game da sammai da duniya ya ƙaru da shigewar lokaci? (b) Wacce tambaya ce take bukatar amsa?

FIYE da shekaru ɗari da suka shige, masana da yawa sun gaskata cewa sararin samaniya yana ɗauke da damin tauraro guda, wato, Kwalkwaɗa. Sun rage girman sararin samaniya sosai! A yanzu ana koyar cewa sararin samaniya yana ɗauke da damin taurari fiye da biliyan ɗari, wasu suna ɗauke da biliyoyin taurari. Yayin da ake yin amfani da madubi mai kawo nesa kusa masu ƙarfi sosai a duniya, hakan nan ma adadin taurari da ake ganowa suna daɗa yawa.

2 Kamar yadda ilimin kimiyya yake da iyaka a shekara ta 1905, hakan nan ma ilimi game da duniya yake. A gaske, mutane da suke rayuwa a ƙarnin da ya wuce suna da ilimi fiye da kakaninsu. A yau, mutane suna da ilimi sosai game da hanyoyin da duniya take kiyaye rayuwa fiye da zamanin dā. Kuma babu shakka za mu koya ƙarin abubuwa game da duniya da kuma sammai a shekaru masu zuwa. Kuma ya dace a yi tambaya, Ta yaya dukan waɗannan suka soma? Za mu iya samun amsar wannan tambayar domin Mahalicci ya bayyana ta cikin Nassosi Masu Tsarki.

Mu’ujizar Halitta

3, 4. Ta yaya Allah ya halicci sararin samaniya, kuma ta yaya ayyukansa suke ɗaukaka shi?

3 An bayyana yadda sararin samaniya ya soma a kalaman fari na Littafi Mai Tsarki: “A cikin farko Allah ya halitta sama da ƙasa.” (Far. 1:1) Ta ruhunsa mai tsarki, Jehobah ya halicci kayan aikin da zai yi amfani da shi wajen yin sammai da duniya da dukan abin da ke sararin samaniya. Maƙeri ɗan Adam yana amfani da hannayensa da kayan aiki don ya ƙera abubuwa, amma Allah yana aika da ruhunsa mai tsarki don cim ma ayyukansa masu girma.

4 A alamance Nassosi sun yi ƙaulin ruhu mai tsarki kamar “yatsan” Allah. (Luk 11:20; Mat. 12:28) Kuma “aikin hannuwansa,” wato, abin da Jehobah ya halicci ta ruhunsa mai tsarki, suna yabonsa. “Sammai suna bayyanawar ɗaukakar Allah,” in ji Dauda marubucin wannan zaburar, “sararin sama kuma yana nuna aikin hannuwansa.” (Zab. 19:1) Hakika, halitta tana bayyana ikon ruhu mai tsarki na Allah. (Rom. 1:20) Ta yaya yake yin hakan?

Ikon Allah Marar Iyaka

5. Ka kwatanta ƙarfin ruhu mai tsarki na Jehobah a halitta.

5 Sararin samaniya da ya fi gaban a faɗe shi ya nuna cewa ikon Jehobah da kuma ƙarfinsa ba su da iyaka. (Karanta Ishaya 40:26.) Ranarmu, wadda tauraruwa ce, awon zafinta ya kai miliyan 27. A kowace daƙiƙa, rana tana fid da zafi da ya yi daidai da fashewar ɗarurruwan miliyoyin bom na nukiliya. Babu shakka, an halicci rana da kuma biliyoyin taurari da kuzari mai yawa. Jehobah yana da kuzarin da ake bukata da kuma iko sosai.

6, 7. (a)Me ya sa za mu iya ce Allah ya yi amfani da ruhunsa mai tsarki a hanyar da ta dace? (b) Mene ne ya nuna cewa sararin samaniya bai kasance farat ɗaya ba?

6 Muna kewaye da abubuwa da suka nuna mana cewa Allah ya yi amfani da ruhunsa mai tsarki a hanyar da ta dace. Alal misali: A ce kana da akwati da ke ɗauke da ƙwallaye masu kala iri-iri. Ka girgiza akwatin don ka harhaɗa ƙwallayen sosai. Sai ka zubar da su a ƙasa a lokaci ɗaya. Shin za ka sa rai cewa ƙwallayen za su ware kansu bisa kallarsu, wato, shuɗi dabam, ruwan ɗorawa dabam, da sauran su? Hakika ba zai kasance haka ba!

7 Duk da haka, idan muka kalli sama da madubin da ke kawo nesa kusa, me muke gani? Za mu ga damin taurari, taurari, da duniyar taurari, dukansu suna tafiya daidai wa daida. Hakan ba zai iya kasancewa farat ɗaya ba ko kuma kamar hatsari. Don hakan wajibi ne mu yi tambaya, Wane kuzari ne aka yi amfani da shi don a halicci sararin samaniya mai tsari sosai? Kimiyya da fasaha ba za su iya faɗa ainihin yadda sararin samaniya ya kasance ba. Amma dai, Littafi Mai Tsarki ya faɗa cewa ruhu mai tsarki na Allah ne, wato, iko mafi ƙarfi a sararin samaniya. Marubucin wannan zabura ya rera waƙa: “Da maganar Ubangiji aka yi sammai; rundunansu duka kuma da lumfashin bakinsa.” (Zab. 33:6) Kuma idanunmu za su iya ganin kaɗan cikin waɗannan ‘rundunar’ taurari yayin da muka kalli sama da daddare!

Ruhu Mai Tsarki da kuma Duniya

8. Yaya yawan iliminmu game da ayyukan Jehobah yake?

8 Abubuwan da za a koya a nan gaba ya fi abin da muka sani yanzu yawa. Iliminmu game da abin da Allah ya halitta yana da ƙanƙanta sosai, kamar yadda Ayuba ya kammala: “Ga shi, waɗannan gefen al’amuran ikonsa ne kawai, ƙanƙanuwar raɗar labarinsa kuwa mu ke ji.” (Ayu. 26:14) Ƙarnuka da yawa bayan hakan, Sarki Sulemanu wanda masani ne a halittar Jehobah ya ce: “[Allah] ya sa kowane abu ya yi jamali a lokacinsa: ya kuma sa madawaman zamanai a cikin zuciyarsu, yadda mutum ba za ya bincike aikin Allah ba da ya yi tun farko, har ƙarshe kuma.”—M. Wa. 3:11; 8:17.

9, 10. Wane iko ne Allah ya yi amfani da shi sa’ad da ya halicci duniya, kuma waɗanne abubuwa ne suka faru a ranar halitta na ɗaya zuwa uku?

9 Amma dai, Jehobah ya bayyana abubuwa da yawa game da ayyukansa. Alal misali, Nassosi sun sanar da mu cewa ruhun Allah ya kasance a duniya shekaru aru aru da suka shige. (Karanta Farawa 1:2.) A lokacin, babu busashiyar ƙasa, babu haske, kuma babu iska da za a iya shaƙa a duniya.

10 Littafi Mai Tsarki ya ci gaba da bayyana abin da Allah ya yi sa’ad da yake halitta. Waɗannan ba sa’o’i ashirin da huɗu ba ne amma lokaci mai ɗauke da aukuwa ne. A ranar halitta ta farko, Jehobah ya sa haske ta bayyana a duniya. Za a kammala wannan aikin halitta sa’ad da rana da wata suka bayyana a duniya. (Far. 1:3, 14) A rana ta biyu, aka soma kafa sarari. (Far. 1:6) Saboda haka, duniya a lokacin ta kasance tana da ruwa da haske, da kuma iska amma babu busasshiyar ƙasa. A ranar halitta ta uku, Jehobah ya yi amfani da ruhunsa mai tsarki wajen halittar busasshiyar ƙasa, wataƙila ya yi amfani da ikokin da suke duniya wajen halittar nahiya. (Far. 1:9) Za a halicci abubuwa masu ban al’ajabi a kwanakin halitta ta uku da na gaba.

Ruhu Mai Tsarki da kuma Halittu Masu Rai

11. Mene ne wuyar fahimtar halittu, daidaitansu da kuma kyaunsu suka nuna?

11 Ruhun Allah ya kuma halicci abubuwa masu rai da aka tsara sosai. A ranakun halitta na uku zuwa na shida, Allah ya halicci abubuwa masu rai iri-iri masu yawan gaske ta wajen ruhunsa mai tsarki. (Far. 1:11, 20-25) Saboda haka, abubuwa masu rai suna da wuyar fahimta, sun yi kama da juna kuma suna da tsabar kyau.

12. (a) Wane aiki ne DNA yake yi? (b) Me ya kamata mu koya daga aikin da DNA yake yi?

12 Ka yi la’akari da DNA, (matattarin sanin asalin halitta), wanda ke sa halittu na zamani ɗaya su samu irin halaye na wani zamani. Dukan halittu masu rai a duniya, haɗe da ƙananan halittu, ciyayi, giwaye, babban jinsin kifi, wato, blue whales, da ’yan Adam suna hayayyafa ta wurin yin amfani da matattarin sanin asalin halitta. Ko da yake halittu suna da bambanci sosai, matattarin sanin asalin halitta da ke sarrafa halayensu ba sa canjawa kuma hakan ya sa halittu da yawa ba sa canjawa cikin shekaru da yawa. Bisa ga ƙudurin Jehobah Allah, halittu iri iri da suke duniya suna cika matsayinsu. (Zab. 139:16) Wannan tsari mai kyau ya ba da tabbaci cewa halitta aikin “yatsan” Allah ne, ko kuma na ruhu mai tsarki.

Kammala Halitta a Duniya

13. Ta yaya Allah ya halicci mutum?

13 Bayan shekaru aru-aru, Allah ya riga ya halicci abubuwa masu rai da marasa rai, kuma duniya ba ‘siffa, da wofi’ ba ce kuma. Duk da haka, Jehobah bai gama yin amfani da ruhunsa don halitta ba. Yana dab da yin amfani da shi wajen halittar abu mafi girma a duniya. Kusan ƙarshen rana ta shida na halitta, Allah ya halicci mutum. Ta yaya ne Jehobah ya yi hakan? Ta yin amfani da ruhunsa mai tsarki da kuma abubuwan da suke duniya.—Far. 2:7.

14. A wace muhimmiyar hanya ce ’yan Adam suka bambanta da dabbobi?

14 Farawa 1:27 ya ce: “Allah fa ya halicce mutum cikin kamaninsa, cikin kamanin Allah ya halicce shi; na miji da ta mace ya halicce su.” Da yake ya halicce mu cikin kamaninsa yana nufin cewa Jehobah ya yi mu da ingancin yin ƙauna da yin zaɓi da kuma ƙulla dangantaka da Mahaliccinmu. Domin hakan, ƙwaƙwalwarmu ta bambanta sosai da na dabbobi. Hakika, Jehobah ya ƙera ƙwaƙwalwar ’yan Adam don mu iya ci gaba da koyon abubuwa game da shi da kuma ayyukansa da farin ciki har abada.

15. Mene ne aka shirya wa Adamu da Hauwa’u?

15 A farkon ’yan Adam, Allah ya ba Adamu da matarsa, Hauwa’u, duniya da dukan abubuwa masu al’ajabi don su bincika da kuma more su. (Far. 1:28) Jehobah ya tanadar da abinci mai yawa da kuma aljanna da za su zauna. Suna da zarafin yin rayuwa har abada kuma su zama ƙaunatattun iyayen biliyoyin kamiltattun ’ya’yansu. Duk da haka, abubuwa ba su kasance haka ba.

Sanin Matsayin Ruhu Mai Tsarki

16. Wane bege ne muke da shi duk da tawayen da mutane na fari suka yi?

16 Maimakon su yi biyayya ga Mahaliccinsu cikin farin ciki, Adamu da Hauwa’u sun yi tawaye. Dukan ’yan Adam ajizai da suka haifa sun sha wahala a sakamakon tawayensu. Amma Littafi Mai Tsarki ya bayyana yadda Allah zai kawar da dukan ɓarnar da zunubin iyayenmu na farko ya jawo. Nassosi sun kuma nuna cewa Jehobah zai cika ainihin ƙudurinsa. Duniya za ta zama aljanna mai cike da mutane masu farin ciki da koshin lafiya da aka albarkace su da rai na har abada. (Far. 3:15) Don kasancewa da imani ga wannan ingancin mai ban ƙarfafa, muna bukatar taimakon ruhu mai tsarki na Allah.

17. Wane irin tunani ne ya kamata mu guje wa?

17 Ya kamata mu roƙi Jehobah don ya ba mu ruhu mai tsarki. (Luk 11:13) Yin hakan zai taimaka mana mu ƙarfafa tabbacinmu cewa Allah ne ya halicci komi. A yau, ra’ayin cewa babu Allah da kuma ra’ayin bayyanau suna daɗa yaɗuwa kuma waɗannan ra’ayoyin ba gaskiya ba ne. Bai kamata mu ƙyale waɗannan ra’ayoyi marasa kyau su ruɗar da mu ba. Wajibi ne dukan Kiristoci su shirya kansu don su yi tsayayya da irin wannan farmaki da kuma matsi na tsara da ke haɗe da shi.—Karanta Kolosiyawa 2:8.

18. Sa’ad da muke yin la’akari da tushen sararin samaniya da kuma ’yan Adam, me ya sa ba zai dace ba mu ce babu Mahalicci mai hikima?

18 Yin bincike a kan gaskiya cewa akwai Mahalicci zai ƙarfafa imaninmu ga Littafi Mai Tsarki da kuma Allah da kansa. Mutane da yawa suna jin cewa bai kamata a gaskata koyarwa game da sararin samaniya da ba za a iya bayyana da kimiyya ba. Idan muna son mu yi amfani da wannan ra’ayin wajen bayyana abubuwa, dukan ra’ayinmu ba zai kasance gaskiya ba. Bugu da ƙari, za mu ƙi tabbacin cewa halittu marasa “iyaka” waɗanda aka tsara su da kyau sun wanzu. (Ayu. 9:10; Zab. 104:25) A matsayin Kiristoci, muna da tabbaci cewa an yi amfani da ruhu mai tsarki don a halicci abubuwa a ƙarƙashin ja-gorancin Jehobah mai hikima.

Ruhu Mai Tsarki da Imaninmu ga Allah

19. Mene ne ya tabbatar maka cewa Allah ya wanzu kuma ruhunsa na aiki?

19 Ba ma bukatar sanin kome game da halitta don mu yi imani ga Allah kuma mu ƙaunace da kuma girmama shi. Kamar yadda yake da yin abota da ’yan Adam, yin imani ga Jehobah ya fi samun tabbaci kawai. Kamar yadda dangantaka tsakanin abokai yake daɗa ƙarfi yayin da suke fahimtar juna sosai, imaninmu ga Allah zai daɗu yayin da muka koya abubuwa da yawa game da shi. Hakika, muna da tabbaci cewa ya wanzu sa’ad da ya amsa addu’o’inmu kuma mun san sakamako mai kyau na bin ƙa’idodinsa a rayuwarmu. Muna kusantar Jehobah sosai yayin da muka ga ƙarin tabbaci da suka nuna cewa yana mana ja-gora, yana kāre mu, yana albarkace ƙoƙarce-ƙoƙarcenmu a hidimarsa kuma yana tanadar da bukatunmu. Dukan waɗannan suna tabbatar mana cewa Allah ya wanzu kuma ruhunsa mai tsarki na aiki.

20. (a) Me ya sa Allah ya halicci sararin samaniya da kuma mutum? (b) Mene ne zai faru idan mun ci gaba da bin ja-gorancin ruhu mai tsarki na Allah?

20 Littafi Mai Tsarki misali ne mai kyau na yadda Jehobah yake amfani da ikonsa, domin waɗanda suka rubuta shi ‘sun yi magana daga wurin Allah, ruhu mai-tsarki kuma yana motsa su.’ (2 Bit. 1:21) Yin nazarin Nassosi sosai zai iya gina imaninmu ga Allah a matsayin wanda ya halicci komi. (R. Yoh. 4:11) Jehobah ya zama Mahalicci domin halinsa na musamman wato, ƙauna. (1 Yoh. 4:8) Bari mu yi iya ƙoƙarinmu don mu taimaka wa mutane su koya game da Ubanmu da kuma Abokinmu mai ƙauna na samaniya. A yanayinmu, idan mun ci gaba da ƙyale ruhun Allah ya yi mana ja-gora, za mu samu gatar koyo game da shi har abada. (Gal. 5:16, 25) Bari kowannenmu ya ci gaba da koyo game da Jehobah da kuma ayyukansa masu ban al’ajabi kuma a rayuwarmu mu nuna irin ƙaunar da yake da ita sa’ad da ya yi amfani da ruhunsa mai tsarki wajen halittar sammai, da duniya da kuma ’yan Adam.

Za Ka Iya Bayyanawa?

• Mene ne wanzuwar sammai da duniya suke koya mana game da yadda Allah yake amfani da ruhu mai tsarki?

• Wanne zarafi muke da shi don an halicce mu cikin kamanin Allah?

• Me ya sa ya kamata mu bincika cewa an halicci abubuwa?

• A waɗanne hanyoyi ne za mu iya kyautata dangantakarmu da Jehobah?

[Hoton da ke shafi na 7]

Mene ne tsarin da ke sararin samaniya yake koya mana game da halitta?

[Inda Aka Ɗauko]

Taurari: Anglo-Australian Observatory/David Malin Images

[Hotuna da ke shari na 8]

Yaya dukan waɗannan halittu suke da DNA?

[Hoton da ke shafi na 10]

Kana a shirye don ka kāre imaninka?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba