Kwalliya Ce da Ke Biyan Kuɗin Sabulu!
BAUTA TA IYALI da nazarin Littafi Mai Tsarki suna da muhimmanci idan za a yi renon yara cikin ‘horon Ubangiji da gargaɗinsa.’ (Afis. 6:4) Idan kana da yara, ka san cewa yara suna saurin gajiya. Ta yaya za ka hana su yin gajiya? Ka yi la’akari da abin da wasu iyaye suka yi.
“Sa’ad da yaran suke ƙanana,” in ji George, a jihar Kalifoniya da ke Amirka, “Ni da matata mun yi ƙoƙari mu sa nazarin Littafi Mai Tsarki na iyali ya kasance da ban sha’awa. Wani lokaci dukanmu muna ado kamar waɗanda aka ambata a cikin Littafi Mai Tsarki kuma mu aikata labarin yayin da muke karanta su daga littafin nan Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki. Har mun yi takubba da sanduna da kwanduna, da kuma makamancinsu. Mun yi wasannin Littafi Mai Tsarki da ake kira ‘ka faɗa ko wane ne ni’ mun kuma yi wasan Littafi Mai Tsarki da tambayoyi dabam dabam masu wuya. Sa’annan kuma muna bincike a kan darussa dabam dabam, kamar gina jirgin Nuhu ko kuma taswirar lokacin da abubuwan da aka faɗa cikin Littafi Mai Tsarki suka faru. Wani lokaci muna zana mutane da aka ambata su cikin Littafi Mai Tsarki ko kuma aka ba da labaransu. A yanzu, muna shirin zana makamai na ruhaniya da aka kwatanta a cikin Afisawa 6:11-17, kuma kowannenmu zai bayyana abin da kowane makami yake wakilta. Waɗannan ayyuka sun taimaka mana mu more nazarinmu na iyali.”
Debi, wata uwa a jihar Michigan da ke Amirka, ta faɗa: “Yana wa ni da maigidana wuya mu sa ’yarmu ta natsu sa’ad da take ’yar shekara uku. Wata rana, sa’ad da nake karanta labarin Ishaku da Rifkatu da babbar murya daga littafin nan Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki, na ɗauko ’yan tsana guda biyu kuma na soma yin amfani da su don na kwatanta labarin, ina faɗan abubuwan da wataƙila Ishaku da Rifkatu sun faɗa. Yanzu ta mai da hankali sosai ga dukan abin da aka faɗa! Watanni bayan hakan, aka yi amfani da waɗannan ’yan tsana biyu don kwatanta mutane dabam dabam da aka ambata a cikin Littafi Mai Tsarki. Bayan mun karanta wani labari, ’yarmu za ta nemi kayan wasa a gida ko kuma wasu abubuwa da za a iya yin amfani da su don a gwada labarin. Yana kama da neman dukiya! Akwatin takalma da jar igiya sun zama gidan Rahab mai jar igiya. ’Yar tsana na maciji mai inci biyar da aka nannaɗe a jikin ƙwayar tsintsiya ya dace sosai da macijin tagulla da ke Littafin Lissafi 21:4-9. Mun ajiye waɗannan abubuwa a cikin babban jaka. Abin farin ciki, ’yarmu sau da yawa tana zama a cikin falo kuma ta riƙa bincika ‘jakarta da ke ɗauke da kayayyaki na labarin Littafi Mai Tsarki.’ Abin farin ciki ne ganin yadda take kwatanta waɗannan labaran a nata hanyar!”
Renon yara ba shi da sauƙi. Iyaye suna bukatar su koya wa yaransu su yi sha’awar bauta wa Jehobah. Ya kamata su yi haka a kowace rana da kuma hanyoyi da yawa. Amma bauta ta iyali da kuma nazarin Littafi Mai Tsarki kowane mako sashe ne mai muhimmanci da ke taimaka wa iyaye su cim ma wannan. Babu shakka, kwalliya ce da ke biyan kuɗin sabulu!