Abin da Yesu Ya Koyar Game da Allah
“Ainihin wanda ya san Uba shi ne Ɗa. Amma Ɗan yana so ya gaya wa wasu game da Uba, domin su ma su san shi.”—LUKA 10:22, CONTEMPORARY ENGLISH VERSION.
SA’AD da yake sama, Ɗan Allah makaɗaici ya yi shekaru aru-aru yana dangantaka na kud da kud da Ubansa. (Kolosiyawa 1:15) Da haka, Ɗan ya san tunanin Ubansa, yadda yake ji, da kuma hanyoyinsa. Daga baya sa’ad da wannan Ɗa ya zo duniya a matsayin mutumin nan Yesu, yana ɗokin koyar da gaskiya game da Ubansa. Za mu iya koyan abubuwa masu yawa game da Allah ta wajen sauraron abin da wannan Ɗa zai faɗa.
Sunan Allah Hurarren sunan nan, Jehobah, shi ne mafi muhimmanci ga Yesu. Wannan ƙaunataccen Ɗa yana son wasu su san sunan Ubansa kuma su yi amfani da shi. Sunan Yesu yana nufin “Jehobah Ne Ceto.” A darensa na ƙarshe kafin ya mutu, Yesu ya ce a addu’a ga Jehobah: “Na kuma sanar . . . da sunanka.” (Yohanna 17:26) Ba abin mamaki ba ne ba cewa Yesu ya yi amfani da sunan Allah kuma ya sanar da shi ga wasu. Idan ba haka ba, ta yaya waɗanda suka saurari Yesu za su fahimci gaskiya game da Jehobah ba tare da sun san sunansa da kuma ma’anarta ba?a
Ƙauna mai girma ta Allah A cikin addu’a ga Allah, Yesu ya taɓa cewa: “Ya Uba, . . . ka ƙaunace ni tun ba a kafa duniya ba.” (Yohanna 17:24) Domin ya shaida ƙaunar Allah a sama, sa’ad da yake duniya Yesu ya bayyana fasaloli da yawa masu kyau na wannan ƙaunar.
Yesu ya nuna cewa ƙaunar Jehobah tana da faɗi sosai. Yesu ya ce: “Allah ya yi ƙaunar duniya har ya bada Ɗansa, haifaffe shi kaɗai, domin dukan wanda yana bada gaskiya gare shi kada ya lalace, amma ya sami rai na har abada.” (Yohanna 3:16) Kalmar Helenanci da aka fassara “duniya” ba ta nufin duniyar da muke ciki. Kamar yadda aka yi amfani da ita a nan, tana nufin dukan ’yan Adam. Ƙaunar da Allah yake yi wa ’yan Adam tana da girma sosai wadda hakan ya sa ya ba da Ɗansa wanda ya fi ƙauna domin mutane masu aminci su sami ceto daga zunubi da mutuwa kuma su sami begen rai na har abada. Babu yadda za mu iya gwada faɗi ko zurfin irin wannan ƙauna mai girma.—Romawa 8:38, 39.
Yesu ya ƙara tabbatar da gaskiyar nan mai ƙarfafawa: Jehobah yana matuƙar ƙaunar kowanne cikin masu bauta masa. Yesu ya koyar da cewa Jehobah yana kama ne da makiyayi wanda a wurinsa kowanne cikin dabbobinsa ya fita dabam kuma yana da tamani. (Matta 18:12-14) Yesu ya ce babu gwarar da za ta faɗi ba tare da sanin Jehobah ba. Yesu ya daɗa: “Gasussuwan kanku dukansu an ƙididdige su.” (Matta 10:29-31) Idan Jehobah zai iya lura cewa gwara guda ba ta cikin sheƙa, zai fi mai da hankali da kuma kula ga kowanne mutumin da ke bauta masa, ko ba haka ba? Idan Jehobah ya riga ya ƙirga kowane gashin da ke kanmu kuma ya san su, to, akwai wani bayani game da rayuwarmu, wato, bukatunmu, abubuwan da muke fama da su, da waɗanda ke damun mu da ba zai iya sani ba?
Uba na samaniya Kamar yadda muka gani a talifin da ya gabata, Yesu kaɗai ne Ɗa makaɗaici na Allah. Shi ya sa ba abin mamaki ba ne ba da a yawancin lokaci wannan ƙaunataccen Ɗa yake gaya wa mutane kuma ya kira Jehobah, “Uba.” Hakika, a cikin rubutacciyar kalmomin Yesu na farko, waɗanda ya furta a haikali sa’ad da yake ɗan shekara sha biyu, ya kira Jehobah “Ubana.” (Luka 2:49) Kalmar nan “Uba” ta bayyana wajen sau 190 a cikin Linjiloli. A wurare dabam-dabam Yesu ya kira Jehobah “Ubanku,” “Ubanmu,” da kuma “Ubana.” (Matta 5:16; 6:9; 7:21) Ta wajen yin amfani da wannan sunan ba tsoro, Yesu ya nuna cewa mutane ajizai kuma masu zunubi za su iya yin dangantaka mai daɗi kuma mai aminci da Jehobah.
Mai rahama kuma mai son gafartawa Yesu ya san cewa mutane ajizai suna bukatan rahamar Jehobah sosai. A cikin almararsa ta ɗa mubazzari, Yesu ya kwatanta Jehobah da uba mai tausayi kuma mai gafartawa wanda ya buɗe hannuwansa biyu don ya marabci ɗansa da ya tuba. (Luka 15:11-32) Kalmomin Yesu sun ba mu tabbaci cewa Jehobah yana son mutum mai zunubi da zai canja zuciyarsa wanda hakan zai sa Ya nuna gafara. Jehobah yana ɗokin gafarta wa mai zunubi da ya tuba. Yesu ya yi bayani: “Ina ce muku, Hakanan kuma za a yi murna cikin sama bisa mai-zunubi guda ɗaya wanda ya tuba, ta fi ta bisa mutum casa’in da tara masu-adalci waɗanda ba su da bukatar tuba ba.” (Luka 15:7) Wanene ba zai so ya kusaci irin wannan Allah mai rahama ba?
Mai jin addu’o’i Sa’ad da yake sama kafin ya zo duniya, Yesu ya gani da kansa cewa Jehobah Shi ne “Mai-jin addu’a” kuma Yana son jin addu’o’in amintattu masu bauta masa. (Zabura 65:2) Shi ya sa, a lokacin hidimarsa, Yesu ya koya wa masu sauraronsa yadda za su yi addu’a da kuma abin da za su yi addu’a a kansa. Ya gargaɗe su cewa “kada ku yi ta maimaitawa ta banza.” Ya aririce masu sauraronsa su yi addu’a don a yi nufin Allah “cikin duniya, kamar yadda a ke yinsa cikin sama.” Muna kuma iya yin addu’a don samun abin biyan bukata a kowace rana, domin a gafarta mana zunubanmu, da kuma guje wa gwaji. (Matta 6:5-13) Yesu ya koyar da cewa Jehobah Yana amsa addu’o’in bayinsa kamar uba, yana amsa roƙon da suka yi da gaske cikin bangaskiya.—Matthew 7:7-11.
Babu shakka, Yesu ya koyar da gaskiya game da Jehobah da kuma kowane irin Allah ne shi. Amma akwai wani abu kuma game da Jehobah da Yesu yake ɗokin koyarwa, wato, hanyar da Jehobah ya kawo canje-canje a cikin dukan duniya don cika manufarsa ga wannan duniyar da kuma mutanen da ke cikinta. Hakika, wannan sashen na saƙon Yesu shi ne jigon wa’azinsa.
[Hasiya]
a Sunan nan Jehobah ya bayyana wajen sau 7,000 a cikin rubutu na ainihi na Littafi Mai Tsarki. Ma’anar da ke tattare da wannan sunan shi ne “Zan kasance abin da Na ga dama.” (Fitowa 3:14, New World) Allah zai iya zama abin da ya ga cewa ya dace domin ya cim ma nufinsa. Wannan sunan tabbaci ne cewa a kowane lokaci Allah ba zai taɓa yin ƙarya ba kuma duk wani abin da ya yi alkawari zai cika.