Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w10 4/1 p. 5
  • Abin da Yesu Ya Koyar Game da Kansa

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Abin da Yesu Ya Koyar Game da Kansa
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Makamantan Littattafai
  • Wanene Yesu Kristi?
    Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
  • Wane ne Yesu Kristi?
    Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?
  • Amsoshin Tambayoyinmu Game da Yesu Kristi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Wane ne Yesu?
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
w10 4/1 p. 5

Abin da Yesu Ya Koyar Game da Kansa

“Yesu bai taɓa yin shakka ba ko kaɗan game da ko wanene shi, daga inda ya fito, dalilin da ya sa ya shiga duniyarmu, da kuma abin da zai shaida a gaba.”—MAWALLAFI HERBERT LOCKYER.

KAFIN mu amince kuma mu ba da gaskiya ga abubuwan da Yesu ya koyar, muna bukatan mu san wasu abubuwa game da shi. Wanene Yesu? Daga ina ya fito? Mecece manufarsa a rayuwa? A cikin Linjiloli, wato, Matta, Markus, Luka, da Yohanna, za mu iya jin amsoshin waɗannan tambayoyin daga bakin Yesu a alamance.

Ya rayu kafin a haife shi a duniya Yesu ya taɓa cewa: “Tun ba a haifi Ibrahim ba, Ni ne.” (Yohanna 8:58) Ibrahim ya rayu wajen shekaru 2,000 kafin a haifi Yesu. Duk da haka, Yesu ya rayu kafin wannan uban iyali mai aminci ya rayu. Amma a ina ne Yesu ya rayu? Ya bayyana: “Na sabko daga sama.”—Yohanna 6:38.

Ɗan Allah Jehobah yana da ’ya’ya mala’iku masu yawa. Amma, Yesu ya fita dabam daga cikinsu. Ya kira kansa “Ɗa haifaffe kaɗai na Allah.” (Yohanna 3:18) Wannan furcin yana nufin cewa Yesu ne ainihin wanda Allah ya halitta da kansa. Ta hanyar Ɗa makaɗaici ne Allah Ya halicci sauran dukan abubuwa.—Kolosiyawa 1:16.

“Ɗan mutum” Yesu ya yi amfani da wannan furcin fiye da duk sauran sa’ad da yake nuni ga kansa. (Matta 8:20) Ta haka, ya nuna cewa shi ba mala’ika ba ne da ya rikiɗa zuwa mutum ko fasalin ruhu ba. Maimakon haka, shi cikakken ɗan Adam ne. Ta hanyar ruhunsa mai tsarki, Allah ya tura ran Ɗansa daga sama zuwa duniya, kuma ya sa wata budurwa mai suna Maryamu ta ɗauki cikinsa. A sakamakon haka, an haifi Yesu a matsayin kamiltacce, ɗan Adam marar zunubi.—Matta 1:18; Luka 1:35; Yohanna 8:46.

Almasihun da aka yi alkawarinsa “Na sani Almasihu yana zuwa,” in ji wata mata Basamariya ga Yesu. Sai ya amsa ya ce: “Ni wanda na ke zance da ke, ni ne shi.” (Yohanna 4:25, 26) Kalmar nan “Almasihu,” kamar kalmar nan “Kristi,” tana nufin “Shafaffe.” Allah ne ya shafa, ko kuma ya naɗa Yesu, don ya cika wani matsayi na musamman game da cikar alkawuran Allah.

Ainihin dalilin zuwansa Yesu ya taɓa cewa: “Dole in kai Bishara ta mulkin Allah ga sauran birane kuma: gama saboda wannan aka aiko ni.” (Luka 4:43) Ko da yake ya yi abubuwa da yawa masu kyau ga mabukata, yin wa’azi game da Mulkin Allah ne ainihin abin da ya mai da wa hankali a rayuwarsa. A nan gaba, za mu tattauna abin da koyar game da wannan Mulkin.

Babu shakka, Yesu ba mutum ba ne ba kawai.a Kamar yadda za mu gani, rayuwar da ya yi a sama ta ba da ƙarin ma’ana ga kalmomin da ya furta a duniya. Shi ya ba bai kamata mu yi mamaki ba cewa ya yi wa’azin saƙon da zai shafi rayukan miliyoyin mutane a dukan duniya.

[Hasiya]

a Don ƙarin bayani game da Yesu da kuma matsayinsa a manufar Allah, duba babi na 4 a cikin littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Shaidun Jehobah ne suka wallafa shi.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba