Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w10 2/15 pp. 19-21
  • Ka Ƙi Dabarun Shaiɗan

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Ƙi Dabarun Shaiɗan
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • “Tushensu Cikin Turɓaya Ne”
  • Mutum “Mai-Haɗiyan Mugunta”
  • “Ka Taɓa Ƙashinsa da Namansa”
  • Ka “Ɗauki Kwalkwali na Ceto”
  • Ka Kāre Kanka daga Karyace-Karyacen Shaidan
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2017
  • Ayuba Ya Ɗaukaka Sunan Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Rayuwa a Hanyar da Take Faranta wa Allah Rai
    Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
  • “Ba Zan Daina Tsare Mutuncina Ba!”
    Ka Yi Koyi da Bangaskiyarsu
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
w10 2/15 pp. 19-21

Ka Ƙi Dabarun Shaiɗan

‘KADA a yaudare ku. Allahnku ba zai cece ku ba. Ku miƙa kanku ko kuma ku sha wahala!’ Wannan ne saƙon da Rabshakeh, wakilin Sarkin Sennakerib na Assuriya, ya idar ga mazauna Urushalima. Rundunar sarkin sun kai wa ƙasar Yahuda hari. An tsara kalaman wakilin ne don a yi wa gaba gaɗin mutanen Urushalima zagon ƙasa kuma a tsoratar da su don su miƙa kansu.—2 Sar. 18:28-35.

An san Assuriyawa da mugunta da kuma zalunci. Suna sa magabtansu su ji tsoro ta wajen sanar da su dalla-dalla yadda suke cin zalin waɗanda suka kama bauta. In ji ɗan tarihi Philip Taylor, suna amfani ne “da hanyar ban tsoro tare da yaɗa ƙarya, wadda wata salo ce ta saka mutanen da suka kame a ƙarƙashin ikonsu da kuma tsorata waɗanda za su iya zama abokan gābansu, ta wajen yin amfani da furofaganda su cusa musu tunanin yadda suke azabtar da mutane, don hakan ya shafi tunaninsu.” Furofaganda mugun makami ne. Yana “ɓata tunani,” in ji Taylor.

Kiristoci na gaskiya suna kokawa ‘ba da nama da jini ba amma da rundunai masu-ruhaniya na mugunta,’ wato, halittu na ruhu da suka yi tawaye ga Allah. (Afis. 6:12) Shaiɗan Iblis ne magabcinmu na musamman. Shi ma yana amfani da tsoro da yaɗa ƙarya.

Shaiɗan ya yi da’awar cewa zai iya karya amincin kowannenmu. A zamanin Ayuba uban iyali, ya gaya wa Jehobah Allah: “Dukan abin da mutum ya ke da shi, ya bayar a bakin ransa.” Wato, idan aka matsa wa mutum sosai, ba da daɗewa ba zai karya amincinsa ga Allah. (Ayu. 2:4) Gaskiya ne Shaiɗan ya faɗa? Dukanmu muna da iyakar yadda za mu iya jimrewa, idan ya wuce hakan za mu yasar da ƙa’idodinmu domin mu kasance da rai? Shaiɗan yana so mu gaskata hakan. Saboda haka, yana amfani da mugun furofaganda don ya cusa wannan ra’ayin a zuciyarmu. Bari mu bincika wasu cikin dabarunsa na yin hakan kuma mu yi la’akari da yadda za mu yi tsayayya da shi.

“Tushensu Cikin Turɓaya Ne”

Shaiɗan ya yi amfani da Eliphaz, ɗaya daga cikin abokan Ayuba guda uku da suka ziyarce shi, ya ce ’yan Adam ba su da ƙarfin yin tsayayya da farmakin Shaiɗan. Da yake nuni ga ’yan Adam a matsayin waɗanda ke “zaune a cikin gidajen ƙasa,” ya gaya wa Ayuba: “Waɗanda tushensu cikin turɓaya ne, waɗanda a ke mākewa sai ka ce assu. Tsakanin safiya da yamma a kan parpashe su: su kan lalace har abada, ba mai-kulawa.”—Ayu. 4:19, 20.

A wani waje cikin Nassosi, an kamanta mu da “tukwane na ƙasa” da ba su da ƙarfi da aka yi da yumɓu. (2 Kor. 4:7) Mu kumamai ne domin mun gaji zunubi da ajizanci. (Rom. 5:12) Idan aka ƙyale mu, za mu faɗa farmakin Shaiɗan. Amma a matsayin Kiristoci, muna da taimako. Duk da kumamancinmu, muna da tamani a idanun Allah. (Isha. 43:4) Bugu da ƙari, Jehobah yana ba da ruhu mai tsarki ga waɗanda suke roƙonsa. (Luk 11:13) Ruhunsa zai iya ba mu “mafificin girman iko” da zai taimaka mana mu jimre da duk wata wahala da Shaiɗan zai kawo mana. (2 Kor. 4:7; Filib. 4:13) Idan muka yi tsayayya da Iblis, ‘cikin bangaskiya,’ Allah zai sa mu yi tsayin daka kuma ya ƙarfafa mu. (1 Bit. 5:8-10) Saboda haka, ba ma bukatan mu ji tsoron Shaiɗan Iblis.

Mutum “Mai-Haɗiyan Mugunta”

“Mi ne mutum da za shi zama mai-tsabta, haifaffe na mace kuma da za shi zama mai-adalci?” in ji Eliphaz. Sai ya amsa cewa: “Ga shi! Ko tsarkakansa ba ya amince da su ba; I, har sammai marasa-tsabta ne a wurinsa. Balle fa wanda ya ke mai-ban ƙyama, ruɓaɓe ne kuma, mai-haɗiyan mugunta kamar ruwa!” (Ayu. 15:14-16) Eliphaz yana gaya wa Ayuba cewa babu ɗan Adam da Jehobah yake ɗauka mai adalci. Iblis ma yana amfani da irin wannan mugun tunanin. Yana son mu riƙa damuwa game da kuskurenmu na dā, mu riƙa ɗaura wa kanmu laifi ainun, kuma mu yi tunanin cewa mun riga mun yi nisa ba za mu ji kira ba. Yana son mu yi tunani cewa Jehobah yana bukatan abin da ya fi ƙarfinmu kuma yana son mu raina juyayinsa, gafararsa da kuma taimakonsa.

Hakika, dukanmu mun “yi zunubi, [mun] kasa kuma ga darajar Allah.” Babu ɗan Adam ajizi da zai iya cika cikakken mizanan Jehobah. (Rom. 3:23; 7:21-23) Amma, hakan ba ya nufin cewa ba mu da amfani a gare shi. Jehobah ya san cewa “tsohon macijin nan, shi wanda ana ce da shi Iblis da Shaitan” ne yake amfani da yanayinmu na zunubi. (R. Yoh. 12:9, 10) Allah yana yin la’akari cewa “mu turɓaya ne,” kuma ba ya ‘tsauta mana kullum.’—Zab. 103:8, 9, 14.

Idan muka daina bin mugun tafarki kuma muka kusaci Jehobah da zuciyar da ta tuba, zai “yi gafara a yalwace.” (Isha. 55:7; Zab. 51:17) Ko da yake zunubanmu “sun yi baƙi kamar mulufi, za su yi fari kamar kankara,” in ji Littafi Mai Tsarki. (Isha. 1:18) Saboda haka, bari mu ƙuduri aniya mu ci gaba da yin nufin Allah.

A yanayinmu na zunubi, ba za mu taɓa kasancewa da adalci a gaban Allah ba. Adamu da Hauwa’u sun yi rashin zama kamiltattu da kuma begen rai na har abada ba kawai ga kansu ba amma ga dukanmu. (Rom. 6:23) Amma, domin ƙaunarsa ga ’yan Adam, Jehobah ya yi tanadin gafarta zunubanmu idan mun ba da gaskiya ga hadayar fansa na Ɗansa, Yesu Kristi. (Mat. 20:28; Yoh. 3:16) Wannan nuni ne mai ban al’ajabi na “alherin Allah”! (Tit. 2:11) Za a iya gafarta mana zunubanmu! To, me zai sa mu ƙyale Shaiɗan ya sa mu yi tunanin cewa ba za a iya gafarta mana ba?

“Ka Taɓa Ƙashinsa da Namansa”

Shaiɗan ya yi da’awar cewa Ayuba zai daina kasancewa da bangaskiya idan ya yi rashin lafiya. Da yake ƙalubalantar Jehobah, Iblis ya ce: “Miƙa hannunka yanzu kaɗai, ka taɓa ƙashinsa da namansa, sai shi la’anta ka a fuskarka.” (Ayu. 2:5) Babu shakka, abokin gaban Allah zai yi farin ciki idan zai iya sa mu ji cewa ba mu da amfani domin kumamancinmu.

Amma, Jehobah ba zai yasar da mu ba sa’ad da muka kasa yin dukan abubuwan da muke yi a dā a hidimarsa. Idan an kai wa abokinmu farmaki kuma an ji masa rauni kuma fa? Za mu rage darajar da muke nuna masa ne domin ba zai iya yin abin da yake yi mana ba a dā? Ko kaɗan! Za mu ƙaunace shi har ila kuma mu kula da shi, musamman idan ya ji raunin ne domin yana ƙoƙarin ya biya bukatarmu. Ya kamata mu sa rai cewa Jehobah zai yi hakan! “Allah ba marar-adalci ba ne da za shi manta da aikinku da ƙauna wadda kuka nuna ga sunansa,” in ji Littafi Mai Tsarki.—Ibran. 6:10.

Nassosi sun yi maganar “wata gwauruwa kuma matalauciya” wadda wataƙila ta tallafa wa bautar Allah shekaru da yawa. Sa’ad da Yesu ya ga tana “zuba anini biyu” a cikin ma’aji na haikali, ya yi mata kallon cewa ita da gudummawarta ba su da amfani ne? Akasin haka, ya yaba mata don yin dukan abin da yanayinta ya ƙyale ta ta yi don ta tallafa wa bauta ta gaskiya.—Luk 21:1-4.

Idan muka kasance da aminci, muna da tabbaci cewa dangantakarmu da Jehobah za ta kasance daram, komi yawan ɓarnar da ajizanci ya yi mana ta wajen tsufa ko kuma rashin lafiya. Allah ba zai taɓa yasar da masu aminci ba domin wahala ta rage abin da za su iya yi wajen bauta masa.—Zab. 71:9, 17, 18.

Ka “Ɗauki Kwalkwali na Ceto”

Ta yaya za mu kāre kanmu daga furofaganda na Shaiɗan? Manzo Bulus ya rubuta: “Ku ƙarfafa cikin Ubangiji, cikin ƙarfin ikonsa kuma. Ku yafa dukan makamai na Allah, domin ku sami ikon da za ku yi tsayayya da dabarun Shaiɗan.” Wani makami na ruhaniya shi ne “kwalkwali na ceto.” (Eph. 6:10, 11, 17) Game da furofaganda na Shaiɗan, ya kamata mu tabbata cewa mun karɓi wannan kwalkwalin kuma mu saka shi. Kwalkwali na soja yana kāre kansa. ‘Kwalkwalinmu na ceto’ wato, tabbacin da muke da shi game da cikar alkawuran da Allah ya yi na sabuwar duniyarsa mai ɗaukaka zai kāre zuciyarmu daga ƙaryace-ƙaryacen Shaiɗan. (1 Tas. 5:8) Muna bukatan mu sa wannan begen ya zama da gaske kuma ya kasance mai ƙarfi ta wajen yin nazarin Nassosi.

Ayuba ya jimre mugun farmaki da ƙiyayya daga Shaiɗan. Ayuba yana da bangaskiya sosai a tashin matattu da har barazanar mutuwa ba ta sa shi sanyin gwiwa ba. Maimakon haka, ya gaya wa Jehobah: “Za ka yi kira, ni ma in amsa maka: Za ka yi marmarin aikin hannuwanka.” (Ayu. 14:15) Ko da Ayuba zai mutu domin kasancewa da aminci, yana da tabbaci cewa ƙaunar Allah ga bayinsa masu aminci za ta motsa shi ya ta da su daga matattu.

Bari mu kasance da irin wannan tabbaci ga Allah na gaskiya. Jehobah zai iya kawar da duk wani abin da Shaiɗan da mabiyansa za su haddasa mana. Ka tuna cewa Bulus ya ba mu tabbaci: “Allah mai-aminci ne, da ba za ya bari a yi maku jaraba wadda ta fi ƙarfinku ba; amma tare da jaraba za ya yi maku hanyar tsira, da za ku iya jimrewa.”—1 Kor. 10:13.

[Hoton da ke shafi na 20]

Jehobah yana daraja hidimarka na aminci

[Hoton da ke shafi na 21]

Ka karɓi kwalkwali na ceto kuma ka saka shi

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba