Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w10 2/15 pp. 14-18
  • “Ruhu Da Amarya Suna Cewa, Zo!”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “Ruhu Da Amarya Suna Cewa, Zo!”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Gayyata ga Kowa
  • “Amarya” Ta Ce, “Zo!”
  • “Mai Ji Kuma, Bari Ya Ce, Zo”
  • “Ruhu” Ya Ce, “Zo!”
  • Sun Ci Gaba da “Cewa, Zo!”
  • Ka Ci Gaba da Cewa, “Zo!”
  • Ka Yi Tafiya Bisa Ga Ruhu Kuma Ka Yi Rayuwar Da Ta Jitu Da Keɓe Kanka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Ka Yi Murna Saboda Auren Ɗan Ragon!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Gayyata ga Kowa
    Hidimarmu Ta Mulki—2015
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
w10 2/15 pp. 14-18

“Ruhu Da Amarya Suna Cewa, Zo!”

“Ruhu da amarya suna cewa, Zo. . . . Mai jin ƙishi kuma, bari ya zo: wanda ya ke so, bari ya ɗiba ruwa na rai kyauta.”—R. YOH. 22:17.

1, 2. Wane matsayi ne ya kamata al’amura na Mulki ya ɗauka a rayuwarmu, kuma me ya sa?

WANE matsayi ne ya kamata al’amura na Mulki su ɗauka a rayuwarmu? Yesu ya aririci mabiyansa su ‘fara biɗan mulkin,’ ya tabbatar da su cewa idan sun yi hakan, Allah zai ba su abin da suke bukata. (Mat. 6:25-33) Ya kwatanta Mulkin Allah da lu’u lu’u mai tamani da mai fatauci ya gani kuma “ya sayarda dukan abin da ya ke da shi, ya saye shi.” (Mat. 13:45, 46) Ya kamata aikin wa’azin Mulki da almajirantarwa su fi kasancewa da muhimmanci a gare mu, ko ba haka ba?

2 Kamar yadda muka gani a talifofi biyu da suka gabata, sa’ad da muka yi magana da ƙarfin zuciya kuma muka yi amfani da Kalmar Allah daidai a hidima, muna nuna cewa ruhun Allah yana yi mana ja-gora. Wannan ruhun yana da muhimmanci wajen sa mu yi aikin wa’azin Mulki a kai a kai. Bari mu ga hakan.

Gayyata ga Kowa

3. Wane irin ruwa aka gayyaci dukan ’yan Adam su “zo” su sha?

3 An gayyaci dukan ’yan Adam ta hanyar ruhu mai tsarki. (Karanta Ru’ya ta Yohanna 22:17.) Gayyatar ita ce mutum ya “zo” ya gamsar da ƙishirwa da yake ji da wani irin ruwa na musamman. Ba ruwan da muka saba sha ba ne da ya ƙunshi haidirjin kashi biyu da kuma iskar sheƙa kashi ɗaya. Ko da yake ruwa na zahiri yana da muhimmanci don kiyaye rai a duniya, Yesu yana nuni ne ga wani irin ruwa dabam sa’ad da ya gaya wa wata Basamariya a bakin rijiya cewa: “Amma dukan wanda zai sha daga cikin ruwan da ni zan ba shi, ba zai ji ƙishi har abada ba; amma ruwan da zan ba shi zai zama rijiyar ruwa a cikinsa, yana ɓulɓula zuwa rai na har abada.” (Yoh. 4:14) Ruwa mai ban al’ajabi da aka gayyaci ’yan Adam su sha yana ba da rai madawwami.

4. Me ya sa bukatan ruwa na rai ya taso, menene wannan ruwan yake wakilta?

4 Bukatan irin wannan ruwa na rai ya taso sa’ad da mutum na farko Adamu ya haɗa kai da matarsa Hauwa’u wajen yin rashin biyayya ga Jehobah Allah, wanda ya halicce su. (Far. 2:16, 17; 3:1-6) An kori ma’aurata na farko daga gidansu na lambu domin “kada [Adamu] ya miƙa hannunsa, ya ɗauka kuma daga itace na rai, ya ci, ya yi rai har abada.” (Far. 3:22) Da yake shi ne kakanmu, Adamu ya jawo mutuwa ga dukan ’yan Adam. (Rom. 5:12) Ruwa na rai yana wakiltar dukan tanadin da Allah ya yi don ya fanshi ’yan Adam masu biyayya daga zunubi da mutuwa da kuma ba su kamiltaccen rai na har abada a Aljanna ta duniya. Waɗannan tanadodi sun yiwu ne ta wurin hadayar fansa na Yesu Kristi.—Mat. 20:28; Yoh. 3:16; 1 Yoh. 4:9, 10.

5. Wanene ya yi gayyatar a zo a “ɗiba ruwa na rai kyauta”? Ka ba da bayani.

5 Wanene tushen wannan gayyatar na a zo a “ɗiba ruwa na rai kyauta”? Sa’ad da dukan ’yan Adam suka sami cikakkun tanadodi na rai ta hanyar Yesu a lokacin Sarautar Kristi na Shekara Dubu, an kira tanadodin “kogin ruwa na rai, mai-sheƙi kamar kiristal.” An ga wannan kogin yana “fitowa daga cikin kursiyin Allah da na Ɗan rago.” (R. Yoh. 22:1) Saboda haka, Jehobah Mai ba da Rai shi ne Tushen ruwan nan mai ba da rai. (Zab. 36:9) Shi ne ya yi tanadin wannan ruwa ta wurin “Ɗan rago,” Yesu Kristi. (Yoh. 1:29) Wannan kogi na alama shi ne hanyar da Jehobah zai yi amfani da ita ya kawar da dukan wahalar da Adamu ya jawo wa ’yan Adam domin rashin biyayyarsa. Hakika, Jehobah Allah shi ne Tushen wannan gayyata a “zo.”

6. A wane lokaci ne “kogin ruwa na rai” ya soma gudana?

6 Ko da yake “ruwa na rai” zai gudana a hanya mai girma a lokacin Sarautar Shekara Dubu na Kristi, ya riga ya soma gudana a “ranar Ubangiji,” wanda ya soma sa’ad da aka naɗa ‘Ragon’ a sama a shekara ta 1914. (R. Yoh. 1:10) Saboda haka, an yi wasu tanadodi don rai bayan hakan. Waɗannan tanadodin sun shafi Kalmar Allah, Littafi Mai Tsarki, gama an kira saƙon da ke cikinsa “ruwa.” (Afis. 5:26) An yi wa dukan mutane wannan gayyatar ta ‘ɗiban ruwa na rai’ ta wajen saurara da kuma yin na’am ga bisharar Mulki. Amma su wanene ke yin ainihin gayyatar a ranar Ubangiji?

“Amarya” Ta Ce, “Zo!”

7. Su waye ne a “ranar Ubangiji” suka fara miƙa gayyatar, “Zo,” kuma ga wanene?

7 Waɗanda suke cikin rukunin amarya, wato, shafaffun Kiristoci, sune suka soma miƙa gayyatar a “zo.” Ga wanene? Amaryar ba ta gaya wa kanta “Zo” ba! Tana faɗin kalmominta ne ga waɗanda suke da begen samun rai madawwami a duniya bayan “yaƙin babbar rana ta Allah Mai-iko duka.”—Karanta Ru’ya ta Yohanna 16:14, 16.

8. Menene ya nuna cewa shafaffu Kiristoci sun soma miƙa gayyatar Jehobah tun shekara ta 1918?

8 Mabiyan Kristi, shafaffu na ruhu sun soma wannan gayyatar tun shekara ta 1918. A wannan shekara, jawabi ga jama’a mai jigo “Millions Now Living May Never Die” (“Miliyoyi da Suke Rayuwa Yanzu Ƙila Ba Za Su Taɓa Mutuwa Ba”) ya ba da bege cewa mutane da yawa za su samu rai a cikin aljanna ta duniya bayan yaƙin Armageddon. Jawabi da aka ba da a taron gunduma na Ɗaliban Littafi Mai Tsarki da aka yi a Cedar Point, Ohio, a Amirka a shekara ta 1922 ya aririci masu sauraro su ‘yi shelar Sarkin da mulkinsa.’ Wannan roƙon ya taimaki rukunin amarya da suka rage su gayyaci ƙarin mutane. A shekara ta 1929, fitowar Hasumiyar Tsaro na 15 ga Maris ya ƙunshi talifi mai jigo “Gracious Invitation,” (Gayyata na Alheri) kuma Ru’ya ta Yohanna 22:17 ne ayar jigon. A taƙaice, talifin ya ce: “Rukunin shafaffu masu aminci da suka rage sun bi [Maɗaukaki Duka] a wannan gayyata na alheri kuma sun ce, ‘Zo.’ Za a sanar da wannan saƙon ne ga waɗanda suke son adalci da gaskiya. Dole ne a yi hakan yanzu.” Har yau, rukunin amarya sun ci gaba da miƙa wannan gayyata.

“Mai Ji Kuma, Bari Ya Ce, Zo”

9, 10. Yaya aka gayyaci waɗanda suke jin gayyatar su ce, “Zo”?

9 Waɗanda suka samu gayyatar “zo” kuma fa? An gayyace su su ma su ce “zo.” Alal misali, Hasumiyar Tsaro na 1 ga Agusta, ta shekara ta 1932, ta ce a shafi na 232: “Bari shafaffu su ƙarfafa dukan waɗanda za su iya, su saka hannu a shelar bisharar mulkin. Ba sa bukatan su zama shafaffu na Ubangiji kafin su yi shelar saƙon Ubangiji. Abin ban ƙarfafa ne sosai ga Shaidun Jehobah su san cewa suna da izini su ɗibi ruwa na rai su ba rukunin mutane da za a iya tsirar da su a Armageddon kuma su sami rai madawwami a duniya.”

10 Sa’ad da take nuni ga hakkin waɗanda suka ji kuma su ce, “Zo!” Hasumiyar Tsaro na 15 ga Agusta, shekara ta 1934, shafi na 249 ta ce: “Dole ne waɗanda suke cikin rukunin Jonadab su tafi tare da waɗanda suke cikin rukuni na alama na Jehu, wato, shafaffu kuma su sanar da saƙon mulkin, ko da yake su ba shafaffun shaidun Jehobah ba.” A shekara ta 1935, an bayyana sarai waɗanda suka zama “taro mai-girma” da aka ambata a Ru’ya ta Yohanna 7:9-17. Hakan ya sa aka ƙara ba da ƙwazo a aikin miƙa gayyatar Allah. Tun lokacin, adadin taro mai girma na masu bauta na gaskiya da ke ƙaruwa, wato, fiye da mutane miliyan bakwai sun yi na’am ga wannan gayyata. Bayan sun ji wannan saƙon, sun keɓe kansu ga Allah, sun yi baftisma na ruwa, kuma sun bi rukunin amarya wajen gayyatar wasu su ‘zo su ɗiba ruwa na rai kyauta.’

“Ruhu” Ya Ce, “Zo!”

11. A ƙarni na farko A.Z., yaya ruhu mai tsarki ya ba da taimako a aikin wa’azi?

11 Sa’da da yake wa’azi a majami’a a Nazarat, Yesu ya buɗe naɗaɗɗen littafin annabi Ishaya kuma ya karanta: “Ruhun Ubangiji yana bisa na, gama ya shafe ni da zan yi shelar bishara ga talakawa: Ya aike ni domin in yi wa ɗaurarru shela ta saki, da mayarwar gani ga makafi, in kwance waɗanda an ƙulle su, in yi shelar shekara ayananniya ta Ubangiji.” Sai Yesu ya yi amfani da waɗannan kalaman ga kansa yana cewa: “Yau an cika wannan nassi a cikin kunnuwanku.” (Luk 4:17-21) Kafin ya koma sama, Yesu ya gaya wa almajiransa: “Za ku karɓi iko lokacin da ruhu mai-tsarki ya zo bisanku; za ku zama shaiduna . . . har kuma iyakan duniya.” (A. M. 1:8) A ƙarni na farko, ruhu mai tsarki ya cika matsayi mai muhimmanci game da aikin wa’azi.

12. Yaya ruhun Allah yake taimako wajen miƙa gayyata a zamaninmu?

12 Yaya ruhu mai tsarki na Allah yake aiki wajen gayyatar mutane a zamaninmu? Jehobah ne Tushen ruhu mai tsarki. Yana amfani da ruhu don ya buɗe zukatan rukunin amarya su fahimci Kalmarsa, Littafi Mai Tsarki. Ruhun yana motsa su su miƙa wannan gayyata kuma su bayyana gaskiyar Nassi ga waɗanda suke da begen rayuwa har abada a Aljanna a duniya. Waɗanda suka amshi gayyatar, suka zama almajiran Yesu Kristi, kuma suka miƙa gayyatar har ila ga wasu kuma fa? Su ma ruhun ya taimaka musu. Da yake an yi musu baftisma ‘cikin sunan ruhu mai tsarki,’ sun ba da haɗin kai ga ruhu mai tsarki kuma sun dogara ga taimakonsa. (Mat. 28:19) Ka yi tunanin saƙon da shafaffu da taro mai girma da suke ƙaruwa suke wa’azinsa. Yana fitowa ne daga Littafi Mai Tsarki, littafin da aka rubuta a ƙarƙashin ja-gorancin ruhun Allah. Da haka, ana miƙa gayyatar ta hanyar ruhu mai tsarki. Wannan ruhun ne yake yi mana ja-gora. Yaya ya kamata hakan ya shafi yawan lokaci da muke ba da wa a aikin gayyatar mutane?

Sun Ci Gaba da “Cewa, Zo!”

13. Menene furcin nan “ruhu da amarya sun ci gaba da cewa: ‘Zo’” take nufi?

13 Ba wai “ruhu da amarya” suna cewa, “Zo” kawai ba ne! Aikatau na yare na asali da aka yi amfani da shi a nan yana nufin ci gaba da aiki. Ta wajen yin la’akari da hakan, shi ya sa fassarar New World Translation ta ce: “Ruhun da amarya sun ci gaba da cewa: ‘Zo!’” Hakan ya nuna cewa za a ci gaba da isar da gayyatar Allah. Waɗanda suka ji kuma suka karɓi gayyatar kuma fa? Su ma sun ce, “Zo!” An ce taro mai girma na masu bauta ta gaskiya ‘suna bauta dare da rana a cikin haikalin Jehobah.’ (R. Yoh. 7:9, 15) Ta yaya suke bauta ‘dare da rana’? (Karanta Luka 2:36, 37; A. M. 20:31; 2 Tasalonikawa 3:8.) Misalan annabiya tsohuwa, Hannatu, da manzo Bulus sun nuna cewa ‘bauta dare da rana’ tana nufin yi a kai a kai da kuma kasancewa da ƙwazo sosai a hidima.

14, 15. Ta yaya Daniyel ya nuna muhimmancin bauta a kai a kai?

14 Annabi Daniyel ya nuna muhimmancin yin bauta a kai a kai. (Karanta Daniyel 6:4-10, 16.) Bai canja tsarinsa na ruhaniya ba, wato, halinsa na yin addu’a ga Allah “so uku kowace rana . . . kamar yadda ya kan yi a dā” ko na wata ɗaya, ko da hakan ya sa an jefa shi cikin ramin zakuna. Abin da ya yi ya nuna wa masu kallo cewa babu abin da ya fi bauta wa Jehobah a kai a kai muhimmanci!—Mat. 5:16.

15 Bayan da Daniyel ya yi kwana ɗaya a ramin zakuna, sarki da kansa ya je wajen kuma ya ta da murya da kuka yana cewa: “Ya Daniyel, bawan Allah mai-rai, ko Allah naka, wanda ka ke bauta masa kullum, ya iya ya cece ka daga bakin zakuna?” Daniyel ya amsa nan da nan: “Ya sarki, ranka shi daɗe. Allahna ya aiko mala’ikansa, ya rufe bakin zakuna, ba su kuwa ji mani ciwo ba; da shi ke a gabansa aka iske rashin laifi a gareni: a gabanka kuma, ya sarki, ban yi wani laifi ba.” Jehobah ya albarkaci Daniyel domin yana bauta masa “kullum.”—Dan. 6:19-22.

16. Waɗanne tambayoyi ne ya kamata misalin Daniyel ya motsa mu mu yi wa kanmu game da yadda muke fita hidima?

16 Daniyel yana shirye ya mutu maimakon ya daina bin tsarinsa na ruhaniya. Mu kuma fa? Waɗanne sadaukarwa ne muke yi ko kuma muke a shirye mu yi domin mu yi shelar bisharar Mulkin Allah a kullum? Bai kamata mu ƙyale wata guda ya wuce ba tare da yi wa mutane magana game da Jehobah ba! Idan zai yiwu, ya kamata mu yi ƙoƙari mu fita hidima a kowane mako, ko ba haka ba? Ko da muna rashin lafiya mai tsanani kuma za mu iya yin wa’azi na minti 15 kawai a wata, ya kamata mu ba da rahoton wannan aikin. Me ya sa? Domin, tare da ruhu da amarya, muna son mu ci gaba da cewa, “Zo!” Hakika, ya kamata mu yi iyakar ƙoƙarinmu don mu ci gaba da kasancewa a cikin masu shelar Mulki a kai a kai.

17. Wane zarafi ne na miƙa gayyatar Jehobah ya kamata mu yi amfani da shi?

17 Ya kamata mu nemi miƙa gayyatar Jehobah a kowane zarafi, ba kawai a lokatan da muka keɓe don wa’azin fage ba. Gata ne mu gayyaci masu ƙishi su ‘zo su ɗibi ruwa na rai kyauta’ a wasu lokatai, kamar lokacin da muke sayayya, ko tafiya, ko hutu, ko aiki, ko kuma zuwa makaranta! Ko da hukumomi sun hana aikin wa’azi, za mu ci gaba da yin wa’azi da basira, wataƙila ba za mu riƙa zuwa kowace ƙofa a unguwarmu ba ko kuma mu ƙara hidimar da muke yi sa’ad da muka samu zarafi.

Ka Ci Gaba da Cewa, “Zo!”

18, 19. Yaya za ka nuna cewa kana daraja gatan zama abokin aiki na Allah?

18 Fiye da shekaru casa’in yanzu, ruhu da amarya suna cewa, “Zo!” ga duk mutumin da yake ƙishirwa na rai. Ka ji gayyatarsu mai ban sha’awa kuwa? Idan haka ne, ana ariritar ka ka miƙa wannan gayyata ga wasu.

19 Ba mu san tsawon lokacin da za a ci gaba da miƙa wannan gayyata ta ƙauna daga Jehobah ba, amma amsawar da muke ba da wa cewa, “Zo!” za ta sa mu zama abokan aiki na Allah. (1 Kor. 3:6, 9) Wannan gata ne! Bari mu nuna cewa muna daraja wannan gatan kuma mu riƙa “miƙa hadaya ta yabo ga Allah kullayaumi” ta wajen yin wa’azi a kai a kai. (Ibran. 13:15) Tare da rukunin amarya, bari mu da muke da begen zama a duniya mu ci gaba da cewa, “Zo!” Fatanmu shi ne mutane da yawa su “ɗibi ruwa na rai kyauta”!

Menene Ka Koya?

• Wanene aka miƙa wa gayyatar su “zo”?

• Me ya sa za a ce Jehobah ne tushen gayyatar a “zo”?

• Yaya ruhu mai tsarki yake ba da taimako wajen miƙa gayyatar a “zo”?

• Me ya sa za mu yi ƙoƙari mu riƙa fita hidima a kai a kai?

[Taswira/Hotuna da ke shafi na 16]

(Don ganin cikakken rubutun, ka duba littafin)

Ka Ci Gaba da Cewa, “Zo!”

1914

Masu shela 5,100

1918

Mutane da yawa za su samu rai a cikin Aljanna a duniya

1922

“Ku sanar, ku sanar, ku sanar da Sarkin da kuma mulkinsa”

1929

Shafaffu masu aminci da suka rage sun ce, “Zo!”

1932

An miƙa gayyatar “Zo” ga wasu ba shafaffu kaɗai ba

1934

An gayyaci rukunin Jonadab su yi wa’azi

1935

An gano “taro mai-girma”

2009

Masu shela 7,313,173

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba