Wadata da Ake Samu Daga Wurin Allah
IDAN ka riƙe amincin ka ga Allah, zai albarkace ka da wadata ne? Mai yiwuwa, amma wataƙila ba da irin wadatar da kake tunani ba. Ka yi la’akari da Maryamu, mahaifiyar Yesu. Mala’ika Jibra’ilu ya bayyana mata kuma ya ce ita “mai-samun alheri” ce daga Allah kuma za ta haifi Ɗan Allah. (Luka 1:28, 30-32) Duk da haka, ba ta da wadata. Sa’ad da Maryamu ta ba da hadaya bayan ta haifi Yesu, ta ba da “kurciya biyu, ko yan tantabarai biyu,” wadda ita ce hadayar da matalauta suke yi wa Jehobah.—Luka 2:24; Levitikus 12:8.
Domin Maryamu talaka ce, hakan na nufi ne cewa ba ta da albarkar Allah? Akasin haka, sa’ad da ta je wurin Alisabatu, danginta, “Alisabatu ta cika da Ruhu Mai-tsarki; ta tāda murya da ƙarfi, ta ce, Mai-albarka ki ke [Maryamu] cikin mata, abin haihuwa na cikinki kuma mai-albarka ne.” (Luka 1:41, 42) Maryamu ta samu gata na zama mahaifiyar ƙaunatacen Ɗan Allah a duniya.
Yesu ma ba mawadaci ba ne. An haife shi ne a cikin talauci kuma ya kasance matalauci a dukan rayuwarsa a duniya. Ya taɓa gaya wa wani mutumin da yake so ya zama mabiyinsa cewa: “Yanyawa suna da ramummukansu, tsuntsayen sama kuma suna da sheƙunansu, amma Ɗan mutum ba shi da wurin da za ya sa kansa.” (Luka 9:57, 58) Duk da haka, abin da Yesu Kristi ya yi na zuwa duniya ya sa ya yiwu almajiransa su samu wadata mai yawa. Manzo Bulus ya rubuta: “Ya zama da talauci, domin ta wurin talaucinsa ku zama mawadata.” (2 Korintiyawa 8:9) Wace irin wadata ce Yesu ya ba almajiransa? Wace irin wadata ce mu ma muke da ita a yau?
Wace Irin Wadata?
A yawancin lokaci, wadatar dukiya ta kan zama ƙalubale ga imani, tun da mutumin da ke da wadata zai iya dogara ga dukiyarsa maimakon ga Allah. Yesu ya ce: “Da ƙyar kamar me masu-dukiya za su shiga cikin mulkin Allah!” (Markus 10:23) Babu shakka, wadatar da Yesu ya ba almajiransa ba ta dukiya ba ce.
Hakika, yawancin Kiristoci na ƙarni na farko matalauta ne. Sa’ad da wani mutumin da aka haife shi gurgu ya roƙi a ba shi kuɗi, Bitrus ya ce masa: “Azurfa da zinariya ba ni da su; amma abin da ni ke da shi, shi na ke ba ka. Cikin sunan Yesu Kristi Ba-nazarat, ka miƙe tsaye ka yi tafiya.”—Ayyukan Manzanni 3:6.
Kalaman almajiri Yaƙub ya nuna cewa waɗanda suke ikilisiyar Kirista a lokacin matalauta ne. Ya rubuta: “Ku ji, ’yan’uwana ƙaunatattu; ko Allah bai zaɓi fakirai ga wajen duniya su zama mawadata cikin bangaskiya ba, da magadan mulki wanda ya alkawarta ga waɗanda su ke ƙaunarsa?” (Yaƙub 2:5) Bugu da ƙari, manzo Bulus ma ya faɗi cewa ba yawancin ‘masu-hikima ga zancen jiki ba’ ko “masu iko” ko “masu-daraja” aka ƙira su kasance cikin ikilisiyar Kirista ba.—1 Korintiyawa 1:26.
Idan wadatar da Yesu ya ba almajiransa ba ta dukiya ba ce, wace irin wadata ce ya ba su? A wasiƙar da ya aika wa ikilisiyar Smirna, Yesu ya ce: “Na san ƙuncinka da talaucinka amma mawadaci ne kai.” (Ru’ya ta Yohanna 2:8, 9) Ko da yake Kiristocin da ke Smirna talakawa ne, suna da wadatar da ta fi azurfa da zinariya tamani. Mawadata ne su domin imani da nagartarsu ga Allah. Imani abu ne mai tamani domin ba ‘duka ke da shi ba.’ (2 Tasalunikawa 3:2) Hakika waɗanda ba su da imani talakawa ne a wurin Allah.—Ru’ya ta Yohanna 3:17, 18.
Wadatar da Ake Samu Don Imani
A waɗanne hanyoyi ne wadata take da tamani? Waɗanda suke da imani ga Allah suna amfana daga “wadatar alherinsa da haƙurinsa da tsawon jimrewarsa.” (Romawa 2:4) Suna kuma more “yafewar laifofin[su]” bisa ga imaninsu ga hadayar fansa ta Yesu. (Afisawa 1:7) Bugu da ƙari, suna da hikimar da “maganar Kristi” ke kawo wa waɗanda ke da imani. (Kolosiyawa 3:16) Sa’ad da suke yi wa Allah addu’a da imani, “salama kuwa ta Allah, wadda ta fi gaban ganewa duka” tana tsare zukatansu da tunaninsu, kuma tana kawo musu gamsuwa da farin ciki.—Filibiyawa 4:7.
Ƙari ga dukan waɗannan albarkar, waɗanda suka yi imani ga Allah ta hanyar Ɗansa, Yesu Kristi, suna da gata na musamman na samun rai har abada. Waɗannan kalaman Yesu Kristi sanannu ne: ‘Allah ya yi ƙaunar duniya har ya bada Ɗansa, haifaffe shi kaɗai, domin dukan wanda yana bada gaskiya gareshi kada ya lalace, amma ya sami rai na har abada.’ (Yohanna 3:16) Ana ƙarfafa wannan gatan sa’ad da mutum ya samu cikakken sani na Uba da kuma Ɗa, domin Yesu ya ce: “Rai na har abada ke nan, su san ka, Allah makaɗaici mai-gaskiya, da shi kuma wanda ka aiko, Yesu Kristi.”—Yohanna 17:3.
Ko da yake albarkar da Allah ke bayarwa ta ruhaniya ce, yakan kuma ba da albarka ta motsin rai da kuma ta zahiri. Ga misalin Dalídio da ke ƙasar Brazil. Kafin ya samu cikakken sani game da nufin Allah, yana mugun shan giya. Hakan ya ɓata dangantakarsa da iyalinsa sosai. Ƙari ga hakan, kuɗinsa ba sa zama. Sai ya soma nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehobah kuma ya canja halayensa.
Sabon ilimin da Dalídio ya samu ya sa ya yi watsi da halayensa marar kyau. Ya samu ci gaba na ruhaniya sosai har ma ya ce, “A dā nakan je gidajen giya dabam-dabam; amma yanzu ina zuwa gida-gida.” Yanzu ya zama mai hidima na cikakken lokaci na Kalmar Allah. Canjin da ya yi ya sa ya kyautata lafiyar jikinsa kuma yana samun kuɗi. Dalídio ya ce, “Kuɗin da nake shan giya da shi a dā, ina amfani da shi ne a yanzu na taimaka wa mabukata ko kuwa na sayi abubuwan da nake bukata.” Kuma ya yi abokai nagari masu yawa ta wajen yin tarayya da mutane masu ruhaniya. A yanzu Dalídio yana more kwanciyar rai da gamsuwa fiye da kowacce abu da ya taɓa samu kafin ya san Allah.
Wani misali na labarin wanda rayuwarsa ta kyautata domin ya yi imani da Jehobah, shi ne na Renato. Idan ka ga fuskarsa mai cike da murmushi a yau, ba za ka taɓa yarda cewa ya samu babbar matsala a rayuwarsa ba. Sa’ad da yake ɗan jariri, uwarsa ta jefar da shi. Ta bar shi a cikin jaka a ƙarƙashin benci, jikinsa cike da raunuka kuma ba a yanke cibiyarsa ba. Mata biyu da suke tafiya sun ga jakar a ƙarƙashin bencin yana motsi. Da farko sun yi tsammanin cewa wani ne ya bar ’yar kyanwa a ciki. Sa’ad da suka gano cewa jariri ne, sai suka kai shi asibiti da ke kusa da sauri don a ba shi magani.
Ɗaya daga ciki matan Mashaidiyar Jehobah ce, kuma ta gaya wa Rita wata Mashaidiya game da jaririn. Rita ta rasa jarirai da yawa sa’ad da take son ta haife su, kuma tana da ’ya guda kawai. Tana bala’in son samun ɗa, sai ta yanke shawarar ɗaukan riƙon Renato.
Rita ta gaya wa Renato tun yana ɗan yaro cewa ba ita ce uwarsa ba. Amma ta kula da shi cikin ƙauna kuma ta yi ƙoƙarin koya masa ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki. Sa’ad da ya yi girma, sai ya soma son abin da ke cikin Littafi Mai Tsarki. Godiyarsa ga yadda aka cece shi ta kuma daɗu. Idanunsa suna cika da hawaye a duk lokacin da ya karanta kalaman mai zabura Dauda: “Gama ubana da uwata sun yashe ni. Amma Ubangiji za ya ɗauke ni.”—Zabura 27:10.
Don nuna godiya ga dukan abin da Jehobah ya yi masa, Renato ya yi baftisma a shekara ta 2002 kuma ya soma hidima ta cikakken lokaci a shekara ta gaba. Har ila bai san ainihin ubansa da uwarsa ba kuma wataƙila ba zai taɓa sani ba. Amma dai, Renato yana ji cewa baiwa mafi muhimmanci da ya taɓa samu ita ce sani da kuma yin imani ga Jehobah a matsayin Ubansa mai ƙauna kuma mai kula.
Wataƙila kana ɗokin samun dangantaka na kud da kud da kuma na ƙauna da Allah, wadda za ta kyautata rayuwarka sosai. Zarafin samun irin wannan dangantakar da Jehobah Allah da kuma Ɗansa, Yesu Kristi, a buɗe yake ga kowa, talaka ko mawadaci. Wataƙila ba zai kawo wadata ta dukiya ba amma zai kai ga samun kwanciyar hankali da gamsuwa wadda dukan kuɗaden da ke duniyar nan ba za su iya saye ba. Kalaman da ke Misalai 10:22 gaskiya ne: “Albarkar Ubangiji ta kan kawo wadata, ba ya kan haɗa ta da baƙinciki ba.”
Jehobah yana ƙaunar mutanen da suka zo gare shi sosai: “Da ma ka yi sauraro ga dokokina! da hakanan ne da salamarka ta yi kamar kogi, adalcinka kuma kamar raƙuman teku.” (Ishaya 48:18) Kuma ya yi alkawari cewa waɗanda suka zo gare shi da muradi mai kyau za su samu albarka sosai: “Ladar tawali’u da tsoron Ubangiji Dukiya ne, da girma, da rai.”—Misalai 22:4.
[Bayanin da ke shafi na 5]
Ko da ba su da wadatar dukiya, Iyalin Yesu a duniya sun samu albarkar Allah
[Hotunan da ke shafi na 6]
Imani ga Allah yana kawo salama, gamsuwa da farin ciki