Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w09 10/1 p. 8
  • Talauci Alamar Rashin Amincewar Allah Ce?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Talauci Alamar Rashin Amincewar Allah Ce?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Makamantan Littattafai
  • Duk ‘Inda Za Ki Tafi, Nan Za Ni’
    Ka Yi Koyi Da Bangaskiyarsu
  • Ruth da Naomi
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
  • Darussa Daga Littafin Rut
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Taimaka Wa Gwauraye Mata Cikin Gwadawarsu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
w09 10/1 p. 8

Talauci Alamar Rashin Amincewar Allah Ce?

ALLAH ya gaya wa Isra’ilawa na dā: ‘Kada ku iske matalauci a cikinku.’ Hakan ya faru ne domin a dokar da ya ba su, ya yi musu tanadi na kula da matalauta da kuma yafe bashi. (Kubawar Shari’a 15:1-4, 7-10) Saboda haka, bai kamata matalauta su wanzu a cikin al’ummar Isra’ila ba, domin Jehobah ya yi alkawari zai albarkace su. Amma fa, samun wannan albarkar ya dangana ne a kan yin biyayya ga Doka, wanda Isra’ilawa suka ƙi yi.

Amma hakan baya nufin cewa, marasa wadata ba su da amincewar Allah ba, ko kuma waɗanda suke da wadata sun samu albarkar Allah. Yawancin amintattun bayin Jehobah matalauta ne. Annabi Amos makiyayi ne kuma ɗan ƙwadago. (Amos 1:1; 7:14) A zamanin annabi Iliya, sa’ad da aka yi yunwa a ƙasar Isra’ila, Iliya ya dogara ne ga kyautar da wata gwauruwa ta yi masa, wacce ta mu’ujiza garin ta da man ta basu ƙare ba a lokacin yunwar. Iliya da gwauruwar ba su zama mawadata ba; amma Jehobah ya yi musu tanadin ainihin abubuwan da suke bukata.—1 Sarakuna 17:8-16.

Aukuwan da ba a yi tsammani ba za su iya sa mutum ya zama matalauci babu zato. Haɗari da ciwo za su iya naƙasa mutum ya hana shi aiki na ɗan lokaci ko na dindindin. Kuma mutuwa za ta iya sa mutane su zama marayu ko gwauraye. Irin waɗannan yanayin ba alamu ba ne na rashin amincewar Allah. Labarin Naomi da Ruth misali ne mai kyau na kular da Jehobah yake yi wa mabukata. Ko da yake mutuwar maigidan Naomi da na Ruth ta mai da su matalauta, Jehobah Allah ya albarkace su kuma ya yi musu tanadi don ya kula da bukatunsu.—Ruth 1:1-6; 2:2-12; 4:13-17.

Babu shakka, talauci ba alamar rashin amincewar Allah ba ne. Waɗanda suke da aminci ga Jehobah za su iya samun ƙarfafa da kalaman Sarki Dauda: “Dā yaro na ke, yanzu kuwa na tsufa: amma ban taɓa gani an yas da mai-adalci ba, Ko kuwa zuriyarsa suna roƙon abincinsu.”—Zabura 37:25.

[Hotunan da ke shafi na 8]

Ko da yake matalauta ne su, Allah ya albarkace Naomi da Ruth kuma ya kula da su

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba