Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w09 10/1 p. 3
  • Allah Ya Yi Maka Alkawarin Kuɗi Ne?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Allah Ya Yi Maka Alkawarin Kuɗi Ne?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Makamantan Littattafai
  • Allah Ya Gwada Bangaskiyar Ibrahim
    Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
  • Jehobah Ya Kira Shi “Aminina”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2016
  • An Gwada Bangaskiyarsa
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
  • Ibrahim da Saratu Sun Yi Biyayya ga Allah
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
w09 10/1 p. 3

Allah Ya Yi Maka Alkawarin Kuɗi Ne?

‘Allah yana son ka yi arziki, ka samu motoci da yawa, sana’a mai kawo kuɗi . . . Ka yi imani da shi kawai, ka buɗe aljihun ka ka ba shi dukan kuɗin da za ka iya ba da wa.’

IRIN wannan sakon ne wasu addinai suke yaɗawa a ƙasar Brazil, in ji wata jaridar da aka buga a ƙasar. Saƙo ne da yawanci suke ɗauka da muhimmanci. Game da wani ƙirge da aka yi a ƙasar Amirka na mutanen da ke da’awar cewa su Kiristoci ne, jaridar nan mai suna Time ta ce: “Kashi sittin da ɗaya sun gaskata cewa Allah yana son mutane su yi arziki. Kuma kashi talatin da ɗaya . . . sun yarda cewa idan ka ba Allah kuɗinka, Allah zai albarkace ka da ƙarin kuɗi.”

Irin waɗannan ra’ayoyin, waɗanda a yawancin lokaci ana kiransu ilimin arziki, suna yaɗuwa sosai musamman a ƙasashen Latin-Amirka, kamar su Brazil, kuma mutane suna yin jerin gwano zuwa Cocin da aka faɗi cewa Allah zai ba da arziki. Amma da gaske ne cewa Allah ya yi wa waɗanda suke bauta masa alkawarin samun kuɗi? Dukan bayin Jehobah na zamanin dā ne suke da arziki?

Hakika, a cikin Nassosin Ibrananci, muna yawan karanta cewa waɗanda Allah ya yi wa albarka suna da arziki. Alal misali, a Kubawar Shari’a 8:18, mun karanta: “Amma za ka tuna da Ubangiji Allahnka, gama shi ne ya ke ba ka iko ka sami arziki.” Hakan ya tabbatar wa Isra’ilawa cewa idan sun yi biyayya ga Allah, zai sa su zama al’umma mai arziki.

Amma mutane ɗaɗɗaya fa? Mutumin nan Ayuba yana da wadata sosai, kuma bayan Shaiɗan ya talautar da shi, Jehobah ya sake maida masa wadatarsa “sau biyu.” (Ayuba 1:3; 42:10) Ibrahim ma mai wadata ne. Farawa 13:2 ta ce shi kuwa “yana da arziki dayawa na bisashe, da azurfa, da zinariya.” Sa’ad da sojojin ƙasashe huɗu na Gabas suka tsare Lutu ɗan’uwan Ibrahim, Ibrahim ya ‘fita da nasa mazaje, forarrun mutane, haifaffun gidansa, mutum ɗari uku da goma sha takwas.’ (Farawa 14:14) Tare da ‘horarrun’ mutane ɗari uku da sha takwas da suke riƙe da makamai, babu shakka iyalin Ibrahim suna da yawa sosai. Tun da yake yana ciyar da irin wannan iyali mai yawa, hakan ya nuna cewa shi mai wadata ne sosai, mai garke da yawa.

Hakika, yawancin bayin Jehobah na zamanin dā, Ibrahim, Ishaƙu, Yakubu, Dauda, Sulemanu da sauransu mawadata ne. Amma hakkan yana nufi ne cewa Allah zai sa dukan waɗanda suke bauta masu su yi arziki? A wani ɓangaren kuma, idan wani ba shi da wadata, hakan ya nuna ne cewa shi ko ita bai da albarkar Allah ne? Talifi na gaba zai tattauna waɗannan tambayoyin.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba