TARIHI
Na Yi Kusan Shekaru 70 Ina Bauta wa Jehobah a Cuba
AN HAIFE ni a 1947 a wani tsibiri mai kyau a Cuba. Tsibirin yana wurin da Tekun Karibiyan da Tekun Atilantika suka haɗu. Bayan ni, iyayenmu sun haifi mata biyu. Mu da iyayenmu mun yi zama a wani ƙauye a Esmeralda.
A lokacin, muna zaman lafiya tare da danginmu da yawa a wurin. Muna da isasshen abinci kuma muna farin ciki.
Saꞌad da na kai wajen shekara biyar, wani ɗanꞌuwa mai suna Walton Jones ya soma nazarin Littafi Mai Tsarki da iyayenmu. Ɗanꞌuwan yana da ƙwazo sosai kuma yana yin tafiya na wajen awa goma zuwa ƙauyenmu. A duk lokacin da ya zo, danginmu da yawa sukan taru a gidan kakanmu don ya yi nazari da su. Iyayenmu, da ƙannen mahaifinmu wato Pedro da Ela sun ji daɗin abin da suke koya, kuma jim kaɗan bayan hakan suka yi baftisma. A yanzu, Ela ta kusan shekaru 100, kuma har ila tana hidimar majagaba a Cuba.
A lokacin, gwamnati ba ta hana Shaidun Jehobah yin waꞌazi a Cuba ba. Mutanen Cuba sun san Shaidun Jehobah sosai don muna yin waꞌazi gida-gida, kuma a kowane lokaci muna da littattafai da yawa da za mu ba su. Ban da haka, mun sha tafiya sosai da ƙafa! A duk lokacin da na tuna yadda muka bauta wa Jehobah a lokacin, ina farin ciki sosai. Amma bayan wasu lokuta, mun fuskanci matsaloli.—2 Tim. 4:2.
MATSALOLI SUN TASO A CUBA
Saꞌad da na kai wajen shekara biyar, mahaifinmu da ƙanensa Pedro sun halarci wani babban taronmu da aka yi a wani wuri a tsibirin. Abin baƙin cikin shi ne, sanadiyyar gurɓataccen ruwan da suka sha a wurin su biyun sun kamu da cutar typhoid. Da suka dawo gida, cutar ta sa gashin kawunmu sun zube gabaki ɗaya, sai dai bai mutu ba. Amma cutar ta kashe mahaifinmu. A lokacin, shekarunsa 32 ne kawai.
Bayan da mahaifinmu ya rasu, sai mahaifiyarmu ta yanke shawara cewa za mu je mu zauna tare da yayanta a wani ƙauye mai suna Lombillo. Hakan yana nufin cewa za mu bar danginmu, har da kakanninmu da muke ƙauna sosai. Duk da haka, mun ci-gaba da bauta wa Jehobah.
Na yi baftisma a wani tafki da ke kusa da Lombillo a ranar 26 ga Agusta 1957 saꞌad da nake shekara goma. Kusan shekaru biyu bayan hakan a shekara ta 1959, an yi juyin mulki kuma abubuwa suka canja wa Shaidun Jehobah a Cuba.
Gwamnatin da ta ƙwace mulkin ta mai da hankali a kan samun sojoji masu yawa. Wannan ya sa rayuwa ta yi wa Shaidun Jehobah wuya sosai, domin a duk inda suke ba sa shiga aikin soja, kuma ba sa saka hannu a harkokin siyasa. Hakan ya sa ba ma iya yin waꞌazi ko yin taro kamar yadda muka saba. Ana nan, sai gwamnatin ta hana mu yin ayyukan ibada, kuma an ƙulle darurruwan ꞌyanꞌuwanmu a kurkuku. An gana ma wasunsu azaba kuma ba sa samun isasshen abinci.
Duk da matsalolin nan, mun ci-gaba da yin taronmu. (Ibran. 10:25) Mun kuma gudanar da manyan taronmu a gonaki da kuma wasu wurare a duk faɗin ƙasar. Na tuna wani lokacin da muka yi babban taronmu a wurin da wani ɗanꞌuwa yake kiwon tumaki. Ba mu sami damar share wurin kafin taron ba. Saboda da haka, mun yi taron tare da tumakinsa.—Mik. 2:12.
Ba za mu taɓa manta da ꞌyanꞌuwan da suka taimaka mana mu ci-gaba da samun abubuwan da suka ƙarfafa bangaskiyarmu ba. Alal misali, wasu ꞌyanꞌuwa sukan ɗauki jawaban da za a yi a babban taro a cikin kaset kuma su tura wa sauran ꞌyanꞌuwa a Cuba. A wasu lokuta, ꞌyanꞌuwa biyu ne kawai suke ɗaukan dukan jawaban taron. Da yake ꞌyanꞌuwan suna yin hakan a ɓoye, a wasu lokuta mukan ji carar zakara da wasu irin ƙara masu ban dariya. Idan babu wutar lantarki a wurin da za a yi babban taron, wani ɗanꞌuwa zai riƙa tuƙa keken da aka haɗa da wani abin da ke ba da wutar lantarki. Ta hakan mukan sami wutar kunna jawaban da aka ɗauka. Ko da yake ba mu da ꞌyancin yin ayyukan ibada, kuma ba ma samun littattafai da yawa kamar sauran ꞌyanꞌuwanmu a wasu ƙasashe, ba mu rasa abubuwan da za su taimaka mana mu kusaci Jehobah ba, kuma mun ji daɗin bauta wa Jehobah tare.—Neh. 8:10.
NI DA MATATA MUN ZAMA MAJAGABA DA KUMA IYAYE
Da na kai shekara 18 na soma hidimar majagaba na kullum a wani gari a Florida. Wajen shekara ɗaya bayan haka, na soma hidimar majagaba na musamman a birnin Camagüey, a Cuba. A wurin ne na haɗu da Emilia, wata kyakkyawar ꞌyarꞌuwa daga Santiago de Cuba. Sai muka soma fita zance, kuma a cikin shekara ɗaya muka yi aure.
(Hagu) Makarantar Hidima ta Mulki da aka yi a Camagüey, Cuba, a 1966
(Dama) Ranar bikin aurenmu a 1967
Na soma aiki a wani kamfanin gwamnati da ake yin suga. Ni da Emilia ba mu iya ci-gaba da yin hidimar majagaba na kullum ba, amma mun yi iya ƙoƙarinmu a bautarmu ga Jehobah. Ina aiki kullum daga ƙarfe uku na safe zuwa ƙarfe goma sha ɗaya na safe. A gaskiya, a lokacin ba na jin daɗin tashiwa da sassafe, amma tsarin aikin yana ba ni damar yin waꞌazi kullum da kuma halartan dukan taro tare da matata Emilia.
A shekara ta 1969 mun haifi ɗan farinmu mai suna Gustavo, sai ꞌyanꞌuwan da suke ja-goranci sun ce in soma hidimar mai kula da daꞌira. A lokacin a Cuba, akwai masu kula da daꞌira da yawa da suke da yara. Ta haka muka soma ayyuka da yawa, kuma mun yi farin ciki sosai. Mun ji daɗin yi wa ꞌyanꞌuwanmu hidima, kuma mun san cewa albarka ce daga gun Jehobah. Ana nan, muka haifi Obed, da Abner da kuma ꞌyarmu Mahely.
Idan na tuna lokacin da muke hidimar kula da daꞌira, ina farin ciki don yadda Jehobah ya albarkace mutanensa a Cuba. Ƙari ga haka, Jehobah ya taimaka mana mu koya wa yaranmu su ƙaunace shi. Bari in gaya muku yadda rayuwarmu ta kasance a lokacin da muke hidimar kula da daꞌira.
NI MAI KULA DA DAꞌIRA NE A LOKACIN DA AKA HANA AYYUKAN IBADARMU A CUBA
Bayan da aka hana ayyukan ibadarmu, ya yi wa ꞌyanꞌuwanmu wuya sosai su halarci taro da kuma fita waꞌazi. An rufe Majamiꞌun Mulkinmu. An kori ꞌyanꞌuwanmu da suke waꞌazi a ƙasar waje da ke Cuba. An ƙulle ꞌyanꞌuwa maza matasa da yawa a kurkuku, aka kuma rufe reshen ofishinmu da ke Havana.
Hidimar mai kula da daꞌira daga 1990-1999
Da yake an hana ayyukan ibadarmu, a ƙarshen mako ne kawai muke ziyartar ikilisiyoyi. Don haka, mukan ɗau makonni biyu muna ziyartar kowace ikilisiya. Da keke ne muke tafiya zuwa ikilisiyoyi, kuma ba ma ɗaukan kaya da yawa don kada ꞌyan sanda ko wasu su gane abin da muke yi. Idan za mu ziyarci wata ikilisiya, ba za a sanar wa jamaꞌa game da zuwan mu ba. Mukan sa a ga kamar danginmu ne muke ziyarta. Yin hakan yana sa mu shaƙu da ꞌyanꞌuwan sosai har wasu lokuta muna kusan manta cewa hidimar kula da daꞌira ne muke yi. (Mar. 10:29, 30) Duk da haka, ya zama dole mu yi hattara, domin sau da yawa ꞌyan sanda sukan tare mu su yi mana tambayoyi, kuma da a ce sun gano abin da muke yi, da za su kama ꞌyanꞌuwan da muke zama a gidansu.—Rom. 16:4.
A wannan lokacin, mun haɗu da ꞌyanꞌuwa da yawa da suka nuna mana karimci duk da cewa su ma kaɗan ne suke da shi. A wasu wurare akwai sauro da yawa fiye da mutanen garin, amma ꞌyanꞌuwan sukan ba mu iya gidan sauron da suke da shi don mu iya yin barci da kyau. Wasu kuma suna so mu zauna a gidansu, duk da cewa ba su da isasshen abincin da za su ba mu. Don haka, a wasu lokuta mukan raba abincinmu da waɗanda muke zama da su.
Zai yi wuya mu riƙa ziyartar ikilisiyoyi da dukan yaranmu. Don haka, mukan je da ɗaya ne kawai, sai mu bar sauran yaran a gida tare da mahaifiyata da kuma ƙanwata. A gaskiya yin tafiya da ɗan jaririnmu ya taimake mu sosai. Akwai lokacin da ꞌyan sanda suka tare mu don su yi bincike, amma ba su ga kome ba, domin mun ɓoye littattafanmu a jakar da muke ajiye ƙunzugun yara (diaper) da suka yi datti, kuma ba su duba wurin ba.
Na ji daɗin irin ƙoƙarin da Emilia ta yi don ta kula da yaranmu, da kuma yadda ta goyi bayana a lokacin da muke hidima ta cikakken lokaci. Na yi ƙoƙari don kada aikin kamfani da nake yi a lokacin ya shafi hidimar kula da daꞌira da aka ba ni. Bari in gaya muku yadda na yi hakan. A wasu lokuta, nakan ƙara awoyin da nake aiki so ɗaya ko sau biyu a mako. Hakan zai sa in sami lokaci a ƙarshen mako. Amma daga baya, yanayin aikina ya canja. Na zama mai yin ja-goranci a wurin aiki kuma an bukace ni in dinga aiki kwana bakwai a mako. Ban ƙi sabon tsarin aikin ba. Amma na zo na ga cewa idan na ba wa waɗanda suke aiki a ƙarƙashina isasshen aikin yi a ƙarshen mako, za su samu isasshen aikin yi har in je in dawo.
KASANCEWA DA FARIN CIKI A LOKACIN CANJI
Babban taro na farko da muka yi bayan an cire takunkumin da aka sa a aikinmu a 1994
Wata rana a shekara ta 1994, ꞌyanꞌuwan da suke ja-goranci a Cuba sun kira dukan masu kula da daꞌira guda 80 da ke ƙasar zuwa wani taro na musamman da aka yi a Havana. Mun yi farin ciki sosai cewa a ƙarshe mun iya haɗuwa da juna bayan shekaru da yawa! Abu na farko da aka tattauna a taron shi ne wasu canje-canjen da aka yi a ƙungiyarmu. Saꞌan nan aka yi wata sanarwa da ta tayar mana da hankali. ꞌYanꞌuwan sun gaya mana cewa suna shirin ba wa hukumomi sunayenmu! Me ya sa za su yi hakan?
ꞌYanꞌuwan sun gaya mana cewa hukumomin sun ce suna so a ba su sunayen dukan masu kula da daꞌira. Sun kuma bayyana mana cewa sun haɗu da hukumomin sau da yawa don inganta dagantaka da ke tsakanin hukumomin da Shaidun Jehobah. Sai dukanmu muka yarda cewa za mu ba da sunayenmu. Hakan ya inganta dagantaka da ke tsakanin mu da hukumomin.
Da shigewar lokaci, mun soma halartar taro da kuma yin waꞌazi kamar yadda muke yi a dā, duk da cewa gwamnati ba ta yi rajista ɗinmu a matsayin addini ba. Daga baya mun gano cewa hukumomin sun riga sun san sunayen wasu masu kula da daꞌirar, suna so ne kawai su tabbata cewa sunayen haka suke.
A Satumba 1994, gwamnati ta ba mu izinin sake soma aiki a reshen ofishinmu. Da taimakon Jehobah, mun sami damar sake koma ofishinmu da aka rufe na shekaru 20.
A 1996, wani ɗanꞌuwa daga Bethel ya kira ni da matata ya ce ana so mu soma hidima a Bethel. Hakan ya ba ni mamaki sosai. Daga baya sai na tuna musu cewa muna da yara biyu da muke bukatar mu kula da su. Duk da haka, ꞌyanꞌuwan sun ce suna son mu zo mu yi hidima a Bethel. Mun amince, kuma muka soma shirya yadda mu da yaranmu za mu ƙaura zuwa Havana.
(Hagu) Matata Emilia a Sashen Ɗinka Kaya a reshen ofishinmu da ke Cuba
(Dama) Lokacin da ake taron keɓe Majamiꞌar Babban Taro a 2012
Gaskiyar ita ce, da farko ban ji daɗin yin hidima a Bethel ba. Na yi shekaru da yawa ina hidimar mai kula da daꞌira kuma na ji daɗin aikin ba kaɗan ba. Yin aiki a ofishi bai yi mini sauƙi ba. Amma ꞌyanꞌuwa a Bethel musamman matata sun taimaka mini in canja raꞌayina. Da shigewar lokaci, na soma jin daɗin aikin, kuma yanzu ina farin cikin yin hidima a Bethel.
(Hagu) Ranar sauke karatu na Makarantar Littafi Mai Tsarki don Kiristoci Maꞌaurata, a 2013
(Dama) Kwamitin da Ke Kula da Reshen Ofishin Shaidun Jehobah a Cuba, a 2013
Ni da matata da ꞌyarmu da mijinta a wani taron daꞌira
A yanzu ni da matata Emilia mun tsufa, amma muna farin ciki sosai a duk lokacin da muka tuna da ꞌyanꞌuwa da muka haɗu da su kuma muka yi hidima tare. Muna kuma matuƙar farin ciki yayin da muke ganin yaranmu da kuma jikokinmu suna bauta wa Jehobah. Muna ji kamar yadda manzo Yohanna ya ji saꞌad da ya tsufa. Ya ce: “Ba abin da ya fi sa ni farin ciki fiye da in ji cewa ꞌyaꞌyana suna bin gaskiya.”—3 Yoh. 4.
Ni da matata mun yi kusan shekaru 30 muna hidima a Bethel. Duk da cewa mun tsufa kuma muna fama da rashin lafiya, muna iya ƙoƙarinmu wajan yin ayyukan da aka ba mu. Mun yi fama da matsaloli yayin da muke hidima, amma muna farin ciki cewa mun yi kusan shekaru 70 a tsibirin Cuba muna bauta wa Jehobah Allah mai farin ciki!—1 Tim. 1:11; Zab. 97:1.