Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w26 Yuni pp. 20-25
  • Ka Riƙa Mai da Hankali a Taro

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Riƙa Mai da Hankali a Taro
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2026
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • JEHOBAH NE YAKE KOYAR DA MU A TARO
  • ME YA SA MUKE BUKATAR MU MAI DA HANKALI SOSAI A TARO?
  • YADDA ZA MU TAIMAKA MA WASU SU MAI DA HANKALI A TARO
  • ABUBUWAN DA ZA SU TAIMAKA MANA MU RIƘA MAI DA HANKALI A TARO
  • KA CI-GABA DA SAURARON JEHOBAH
  • Ku Yi Saurin Taimaka ma Waɗanda Suke da Zuciyar Kirki
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Ka Inganta Yadda Kake Koyarwa a Waꞌazi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2026
  • Ka Nemi Amsoshin Waɗannan Tambayoyin
    Tsarin Ayyuka na Taron Daꞌira na Mai Kula da Daꞌira na 2026
  • Ku Tsai da Shawarwari da Za Su Nuna Kun Dogara Ga Jehobah
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2023
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2026
w26 Yuni pp. 20-25

31 GA AGUSTA–6 GA SATUMBA, 2026

WAƘA TA 89 Mu Ji, Mu Yi Biyayya Don Mu Sami Albarka

Ka Riƙa Mai da Hankali a Taro

“Ku mai da hankali ga yadda kuke ji.”—LUK. 8:18.

ABIN DA ZA MU KOYA

Za mu ga dalilin da ya sa zai dace mu dinga mai da hankali a taro da kuma yadda za mu iya yin hakan.

1-2. (a) Mene ne Jehobah yake yi wa bayinsa a yau? (Zabura 23:​1, 2, 5) (b) Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

A YAU, Jehobah yana tanada mana abubuwan da za su taimaka mana mu fahimci abin da ke Littafi Mai Tsarki. Don haka, muna ji kamar yadda Dauda ya ji saꞌad da ya ce: “Yahweh shi ne makiyayina, ba zan rasa kome ba.”—Karanta Zabura 23:​1, 2, 5.

2 Hanya ɗaya da Jehobah yake taimaka mana mu fahimci abin da ke Littafi Mai Tsarki ita ce ta wurin taronmu. A taronmu, ana yawan maimaita abubuwan da muka sani. Amma ko da mun “kafu sosai cikin gaskiya,” muna bukatar irin tunasarwar nan. (2 Bit. 1:12) Shin yana yi maka wuya ka mai da hankali a taro idan abin da ake tattaunawa abu ne da ka saba ji? Idan haka ne, wannan talifin zai taimaka maka. A talifin nan, za mu ga dalilin da ya sa yake da muhimmanci mu mai da hankali sosai idan muka halarci taro. Za mu kuma ga yadda ꞌyanꞌuwa da suke ba da jawabai za su iya sa ya yi wa ꞌyanꞌuwa sauƙi su riƙa mai da hankali a taro. A ƙarshe, za mu ga wasu abubuwan da za mu iya yi da za su taimaka mana mu inganta yadda muke mai da hankali a taro. Da farko, bari mu ga ainihin wanda yake koyar da mu saꞌad da muka halarci taro.

JEHOBAH NE YAKE KOYAR DA MU A TARO

3. Ta yaya Jehobah yake koyar da mu, kuma ta yaya bayinsa suke amfani da Littafi Mai Tsarki wajen koyarwa?

3 Jehobah yana amfani da Littafi Mai Tsarki wajen koyar da mu. (2 Tim. 3:​16, 17) Yesu ya san da hakan, shi ya sa saꞌad da yake duniya ya yi amfani da Littafi Mai Tsarki wajen koyar da mutane, har masu sauraron sa suka yi mamaki suka ce: “Yaya aka yi mutumin nan yake da ilimin Nassosi haka, duk da cewa bai yi karatu a makarantu ba?” (Yoh. 7:15) Mutane masu zuciyar kirki sun yi farin ciki sosai da suka ji yadda Yesu yake bayyana Kalmar Allah. Kristoci a ƙarni na farko kamar su manzo Bulus da Afollos sun bi misalin Yesu wajen yin amfani da Kalmar Allah don su taimaka wa mutane su fahimci abin da Jehobah yake so su yi. (A. M. 17:​2, 3; 18:​24, 28) A matsayinmu na Shaidun Jehobah, mun san cewa abin da ke talifofinmu, da shirye-shiryen Tashar JW, da awutlayin jawabai, da kuma bidiyoyinmu daga Littafi Mai Tsarki ne. Mutane da yawa da suka halarci taronmu a lokaci na farko suna jin daɗin yadda muke amfani da Littafi Mai Tsarki. Waɗanda suke koyarwa a taro suna amfani da Littafi Mai Tsarki. Ba kawai karanta ayoyi suke yi ba, amma suna taimaka wa kowa ya fahimci kuma ya bi abin da ke ciki.—Luk. 24:32.

4. Kafin mu iya bin abin da mutum yake gaya mana, mene ne muke bukatar mu yi?

4 Kafin mu iya bin abin da mutum yake gaya mana, wajibi ne mu saurari abin da yake cewa. Haka ma, don mu iya yin biyayya ga abubuwan da Jehobah yake koya mana, wajibi ne mu kasa kunne da kyau saꞌad da muke taro. Idan muka saurara da kyau kuma muka bi abubuwan da muka koya, Jehobah zai albarkace mu.—K. Mag. 27:11.

ME YA SA MUKE BUKATAR MU MAI DA HANKALI SOSAI A TARO?

5. Me za mu yi idan muna ƙaunar Jehobah? (Yohanna 4:​23, 24; 1 Yohanna 5:3)

5 Muna kasa kunne a taro domin muna ƙaunar Jehobah. (Mat. 22:37) Yayin da muke ƙara koya game da Jehobah, hakan yana sa mu ƙara ƙaunar sa sosai. Ƙaunar ce take sa mu saurari abin da yake koya mana daga Littafi Mai Tsarki, mu yi masa biyayya kuma mu bauta masa yadda yake so.—Karanta Yohanna 4:​23, 24; 1 Yohanna 5:3.

6. Mene ne Jehobah yake koya mana a taro?

6 Muna kasa kunne a taro domin muna ƙaunar mutane. (Mat. 22:39) A taronmu, Jehobah yana koya mana yadda za mu iya taimaka wa ꞌyanꞌuwanmu da kuma waɗanda ba mu sani ba. Alal misali, ƙasidar nan Ƙaunar Mutane Za Ta Sa Ka Almajirtar da Su tana taimaka mana mu kasance da halayen da za su taimaka mana a waꞌazi. Yana yi maka wuya ka soma tattaunawa da mutane a waꞌazi? Idan haka ne, ka mai da hankali sosai yayin da ꞌyanꞌuwa maza da mata suke gudanar da ayyukansu a sashen Ka Yi Waꞌazi da Ƙwazo a taron tsakiyar mako.

7. Me ya sa yake da muhimmanci mu riƙa bin abubuwan da Jehobah yake koya mana?

7 Muna kasa kunne a taro domin muna so mu ji daɗin rayuwa yanzu da kuma har abada. Kamar yadda Jehobah ya gaya wa bayinsa a dā, idan muna so mu ji daɗin rayuwa yanzu da kuma har abada, dole ne mu yi masa biyayya. (M. Sha. 32:​44-47) Idan muka kasa kunne a taro, za mu sami ƙarfafar da muke bukata don mu iya jimre matsalolinmu har zuwa lokacin da Mulkin Allah zai zo. (Rom. 8:25) Da yake muna rayuwa a kwanakin ƙarshe, muna bukatar mu riƙa bin abubuwan da Jehobah yake koya mana kuma mu ci-gaba da bauta masa da ƙwazo.—Mat. 24:​42-44; R. Yar. 1:3.

YADDA ZA MU TAIMAKA MA WASU SU MAI DA HANKALI A TARO

8. Me ya sa ꞌyanꞌuwan da suke ba da jawabai a taro suke bukatar su ci-gaba da inganta yadda suke koyarwa?

8 ꞌYanꞌuwa maza da suke ba da jawabai, musamman waɗanda suke ba da jawabi ga jamaꞌa, suna bukata su riƙa inganta yadda suke koyarwa. Idan ɗanꞌuwa ya shirya jawabinsa da kyau, hakan zai iya sa sabbi su yanke shawarar bauta wa Jehobah, kuma zai taimaka wa ꞌyanꞌuwa su ci-gaba da bauta wa Jehobah. Idan an ba ka wani aiki a taro, ka tuna cewa abin da ka faɗa zai iya amfanar ꞌyanꞌuwa sosai. Saboda haka, idan an ba ka wani aiki a taro, ka yi tunani a kan shawarwarin da ke gaba. Shawarwarin za su taimaka wa dukan masu aiki a taro, musamman masu ba da jawabi ga jamaꞌa.—2 Tim. 4:2; Tit. 1:9.

9. Me za ka iya yi don ya yi wa masu sauraro sauƙi su fahimce ka saꞌad da kake ba da jawabi?

9 Ka sa batutuwan da kake so ka tattauna su fita dalla-dalla. Saꞌad da kake ba da jawabi, babu shakka kana so ya yi wa masu sauraron ka sauƙi su fahimce ka. Amma idan ka shirya batutuwa da yawa da kake so ka tattauna, hakan zai sa ya yi wa masu sauraro wuya su fahimce ka. Me zai taimaka maka? Ga wasu shawarwari: (1) Ka fara da ambata batutuwan da kake so ka tattauna. (2) Ka bayyana batutuwan ɗaya bayan ɗaya. Zai dace ka ɗan dakata bayan ka kammala wani batu, saꞌan nan ka ambata batu na gaba kafin ka ci-gaba. (3) Ka kammala jawabin da taƙaita batutuwan da ka tattauna.

10. Me ya sa zai dace ka so batutuwan da kake so ka tattauna sosai?

10 Ka so batutuwan da kake so ka tattauna sosai. Idan kana son batutuwan da kake tattaunawa, za ka riƙa magana da kuzari. (K. Mag. 2:​4, 5; A. M. 4:20) Don ka so batutuwan da za ka tattauna, wajibi ne ka yi tunani mai zurfi a kan batutuwan da kuma nassosin da ke jawabin. Wani ɗanꞌuwa daga Amurka da ya tsufa ya ce ba zai taɓa manta da wani jawabin da ya ji a lokacin da yake matashi ba. Ɗanꞌuwan ya kuma ce: “Har wa yau, ina tuna da yadda mai jawabin ya ƙarfafa mu mu riƙa yin tunani mai zurfi saꞌad da muke karanta Kalmar Allah. Ya bayyana dalla-dalla yadda za mu yi hakan, kuma na ga cewa batun yana da muhimmanci a gare shi. Jawabin ya canja yadda nake tunani gabaki ɗaya. Ya taimaka mini in kusaci Jehobah kuma in riƙa amfana sosai saꞌad da nake karanta Littafi Mai Tsarki.”

11. Saꞌad da kake ba da jawabi, me ya sa zai dace ka ba masu sauraronka shawarwarin da suka dace da bukatunsu? (1 Timoti 4:​13-16)

11 Ka yi tunani a kan abin da masu sauraronka suke bukata, kuma ka ba da shawarwarin da suka dace da bukatunsu. Maimakon ka yi bayani a dunƙule, ka yi amfani da Littafi Mai Tsarki wajen ƙarfafa masu sauraronka, kuma ka taimaka musu su ga yadda za su bi shawarwarin a rayuwarsu. Alal misali, manzo Bulus ya ba wa Timoti wasu shawarwari da za su taimaka masa ya ci-gaba da bauta wa Jehobah yayin da yake iya ƙoƙarinsa wajen taimaka wa ꞌyanꞌuwa a Afisa. (Karanta 1 Timoti 4:​13-16.) Ka yi tunani a kan abin da masu sauraronka suke bukata, kuma ka taimaka musu su ga yadda za su iya yin amfani da shawarwari daga jawabinka a rayuwarsu.

12. Me ya sa zai fi kyau ka yi magana a sake idan kana ba da jawabi?

12 Ka maimaita jawabinka da babbar murya sau da yawa saꞌad da kake shiri don ka iya yin magana a sake. Maimakon ka rubuta kuma ka je ka karanta jawabin, ka yi ƙoƙari ka riƙa yin magana a sake. Hakan zai sa ya yi wa masu sauraronka sauƙi su saurare ka, kuma su fahimci abin da kake faɗa. Ƙasidar nan mai jigo Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa ta ce: “Ka yi magana a sake yadda zai nuna cewa kana son batun da kake tattaunawa kuma ka damu da masu sauraronka.” Idan muna magana a sake kuma daga zuciyarmu, hakan zai sa masu sauraro su mai da hankali ga jawabin, kuma su aikata abin da suka koya.

13. Saꞌad da kake shirya jawabi, me ya sa zai dace ka nemi shawara daga wurin ɗanꞌuwan da ya ƙware a yin jawabi? (Ka kuma duba hoton.)

13 Ka nemi shawara daga wurin ɗanꞌuwan da ya ƙware a yin jawabi. Alal misali, za ka iya nuna wa ɗanꞌuwan da ya ƙware yadda ka shirya jawabinka, kuma ka yi amfani da shawarwarin da ya ba ka don jawabinka ya yi daɗi. Ƙari ga haka, ka gaya masa cewa za ka so ya ji jawabin da kake so ka bayar kuma ya gaya maka wuraren da kake bukatar ka yi gyara. (K. Mag. 1:5) A wasu lokuta, ba ma iya sanin wuraren da muke bukatar mu yi gyara. Don haka, ɗanꞌuwan zai iya taimaka maka ka san yadda za ka ba da jawabinka a hanyar da zai yi wa ꞌyanꞌuwa sauƙin fahimta, kuma su bi darussan da suka koya. Dukanmu muna bukatar mu inganta yadda muke koyarwa don mu iya taimaka wa mutane su fahimci abubuwa masu kyau da ke cikin Littafi Mai Tsarki kuma su yi amfani da shi.a

Wani ɗanꞌuwa yana yin jawabinsa a gaban wani ɗanꞌuwan da ya ƙware a Majamiꞌar Mulki kafin ya je ya ba da jawabin a taro. Ɗanꞌuwan da ya ƙwaren yana rubuta wasu abubuwa.

Ka nemi shawara daga wurin ɗanꞌuwan da ya ƙware a yin jawabi (Ka duba sakin layi na 13)


ABUBUWAN DA ZA SU TAIMAKA MANA MU RIƘA MAI DA HANKALI A TARO

14. Me ya sa zai dace mu kasance da irin raꞌayin marubucin Zabura sura 119? (Zabura 119:​24, 111, 167)

14 Za mu mai da hankali sosai a taro idan muka tuna cewa abubuwan da Jehobah yake tuna mana wato ƙaꞌidodinsa suna da muhimmanci sosai. Muna bukatar tunasarwar da Jehobah yake ba mu don mu iya jimre matsalolin “kwanakin ƙarshe” da muke ciki. (2 Tim. 3:1) Don haka, idan muna ganin kamar abin da ake tattauna wa a taro abu ne da muka ji sau da yawa, zai dace mu kasance da irin raꞌayin da marubucin Zabura sura 119 ya kasance da shi game da ƙaꞌidodin Allah.—Karanta Zabura 119:​24, 111, 167.

15. Me zai taimaka mana mu ci-gaba da ɗaukan abubuwan da ake koya mana a taro da muhimmanci?

15 Yana da muhimmanci mu ci-gaba da tuna cewa abubuwan da ake koya mana a taronmu daga wurin Jehobah ne. Za mu iya koyan darasi daga abin da ya faru da Israꞌilawa a daji lokacin da Jehobah ya ba su manna. (Fit. 16:​15, 31) Da farko sun ji daɗin mannar da Jehobah ya ba su domin yana da daɗi kuma yunwa bai kashe su ba. Amma da shigewar lokaci, wasu daga cikinsu sun gaji da cin mannar kowace rana. (L. Ƙid. 21:5) Darasin shi ne, wasu abubuwan da muke ji a taro abubuwa ne da muka saba ji. Amma bai kamata mu soma rena irin abubuwan nan ba. Zai dace mu riƙa tuna cewa abubuwan da muke koya a taronmu daga wurin Jehobah ne. Mu kuma tuna cewa ƙungiyar Jehobah tana mai da hankali sosai wajen shirya abubuwan da ake tattaunawa a taro. Abubuwan da muke koya za su taimaka mana mu yanke shawarwari masu kyau kuma mu yi rayuwa har abada.—K. Mag. 3:​13, 16-18; Yoh. 17:3.

16. Waɗanne abubuwa ne suka taimaka ma wasu da suka daɗe suna bauta wa Jehobah su ci-gaba da mai da hankali sosai a taro? (Ka kuma duba akwatin nan “Abubuwan da Za Su Taimaka Maka Ka Riƙa Mai da Hankali a Taro.”)

16 Za mu iya mai da hankali sosai a taro idan muka bi shawarwarin da ke gaba. Ga wasu abubuwan da suka taimaka ma waɗanda suka daɗe suna bauta wa Jehobah su ci-gaba da mai da hankali sosai a taro. Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Ashley da ta yi shekaru 30 tana bauta wa Jehobah ta ce: “Shirya taro yana taimaka mini in mai da hankali idan na halarci taro. Idan ban yi haka ba, yin kalami yana yi mini wuya kuma hankalina ba ya zama wuri ɗaya.” Wani ɗanꞌuwa mai suna József da ya yi shekaru 52 yana bauta wa Jehobah ya ce: “Ina jin daɗi sosai idan ana tattauna wani batun da na saba ji a taro. Nakan koyi sabbin abubuwa game da batun saꞌad da wasu ꞌyanꞌuwa dabam suka yi kalami ko jawabi a kan batun.” Ya kuma ƙara da cewa: “Idan ɗanꞌuwa da bai iya jawabi sosai ba yana ba da jawabi, nakan mai da hankali a kan abin da yake koyarwa daga Littafi Mai Tsarki maimakon a kan yadda yake koyarwar.”

Abubuwan da Za Su Taimaka Maka Ka Riƙa Mai da Hankali a Taro

Ga abin da wasu ꞌyanꞌuwa da suka daɗe suna bauta wa Jehobah suka ce game da abin da yake taimaka musu su mai da hankali a taro:

  • Suefawn da ta yi baftisma a shekara ta 1986, ta ce: “Zama a gaba zai taimaka wa mutum ya mai da hankali ga mai jawabin da kuma bidiyoyin da ake nunawa.”

  • David da ya yi baftisma a shekara ta 1983, ya ce: “Sau da yawa nakan roƙi Jehobah ya taimaka mini in mai da hankali a taro. Nakan tuna wa kaina cewa halartan taro, da mai da hankali, da kuma yin kalami, hanyoyi ne da nake bauta wa Jehobah.”

  • Nicolas da ya yi baftisma a shekara ta 1982, ya ce: “Nakan yi ƙoƙari in gode wa waɗanda suka yi aiki a taro don wani misali, ko bayani, ko kuma wani kwatanci da suka yi da na ji daɗinsa.”

  • Augustin da ya yi baftisma a shekara ta 1988, ya ce: “Nakan tuna wa kaina cewa idan bawan nan mai aminci da hikima ya sa a maimaita wani batu a taro, abu ne da muke bukata.”

17. Waɗanne abubuwa ne kuma za ka iya yi don ka mai da hankali sosai a taro? (Ka kuma duba hoton.)

17 Ga wasu abubuwa kuma da za su iya taimaka maka ka mai da hankali sosai a taro. (1) Kada ka ci abinci da yawa kafin taro don kada ka soma jin barci. (2) Ka zo da wuri kuma ka sami wurin zama kafin a soma taron. (3) Ka seta wayarka yadda ba za ta dame ka ba. (4) Ka ɗan yi tunani a kan abin da mai jawabin zai yi magana a kai. (5) Ka riƙa kallon mai jawabin. (6) Ka rubuta ko ka zana darussa masu muhimmancin da ka koya. (7) Ka mai da hankali a kan nassosin da ake karantawa kuma ka yi ƙoƙari ka san alaƙar da ke tsakaninsu. (8) Ka tambayi kanka, ‘Ta yaya zan yi amfani da darussan da na koya a taron wajen taimaka wa wani a ikilisiya ko kuma a waꞌazi?’ (9) Kafin ka halarci taron daꞌira da taron yanki, ka bincika tsarin ayyukan, da jigon kowace rana, da jawaban da za a yi da kuma nassosinsu. (10) Ka zauna shuru kuma ka saurari sauti da bidiyon da ake sakawa kafin a soma taron. Hakan zai nuna cewa kana nan a shirye don Jehobah ya koyar da kai.

Wani ɗanꞌuwa yana tura wa abokinsa saƙo ta waya saꞌad da ake gudanar da nazarin “Hasumiyar Tsaro.”

Kada ka yarda wayarka ko naꞌurarka ta ɗauke hankalinka a taro (Ka duba sakin layi na 17)


KA CI-GABA DA SAURARON JEHOBAH

18. Me ya sa yake da muhimmanci mu ci-gaba da mai da hankali sosai a taro?

18 Zai dace mu ci-gaba da mai da hankali sosai a taro, domin yin hakan zai nuna cewa muna so Jehobah ya ‘bi da mu a hanyar adalci.’ (Zab. 23:3; 31:3) Muna bukatar ja-gorancin Jehobah don mu ci-gaba da yin abubuwan da suka dace. Saboda haka, bari mu ci-gaba da kasa kunne a taro kuma mu yi amfani da abubuwan da muka koya. (Luk. 8:18) Dukan waɗanda suke yin hakan za su yi farin ciki yanzu, kuma za su yi rayuwa har abada a nan gaba.—Zab. 119:​2, 14.

MECE CE AMSARKA?

  • Me ya sa yake da muhimmanci mu riƙa mai da hankali sosai a taro?

  • Waɗanne abubuwa ne ꞌyanꞌuwan da suke ba da jawabi a taro za su yi don ya yi wa ꞌyanꞌuwa sauƙi su riƙa mai da hankali a taro?

  • Waɗanne abubuwa ne za su taimaka mana mu riƙa mai da hankali a taro?

WAƘA TA 87 Ku Zo Mu Sami Ƙarfafa!

a Don samun ƙarin bayanai a kan yadda za ka inganta yadda kake koyarwa, ka duba ƙasidar nan Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba