Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w26 Yuni p. 31
  • Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2026
  • Makamantan Littattafai
  • ‘Misali’ da Ke da Ma’ana a Gare Mu
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2019
  • Ka Ba da Gaskiya Sosai ga Mulkin
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Za Ku Zama “Mulki na Firistoci”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2026
w26 Yuni p. 31

AMSOSHIN TAMBAYOYIN MASU KARATU

Waɗanne yarjejeniya biyu ne Bulus yake magana a kai a Galatiyawa 4:24?

Bayan da manzo Bulus ya yi magana game da dangantakar da ke tsakanin Ibrahim da Saratu da kuma Hajaratu (Hagar), sai ya ce: “Wannan misali ne, matan nan biyu sun kwatanta yarjejeniya biyu.” (Gal. 4:​22-24) A dā, mun bayyana cewa yarjejeniya biyun nan su ne alkawari bisa doka da sabon alkawari. Amma, da muka sake bincika ayoyin nan, mun gano cewa suna nufin wani abu dabam. Da alama Bulus yana magana game da alkawari da aka yi wa Ibrahim ne, ba game da sabon alkawari ba. Ga wasu dalilai da suka sa muka faɗi hakan.a

Bulus ya kwatanta baiwar nan, wato Hajaratu da Babban Tudun Sinai. (Gal. 4:25) Hakan ya nuna cewa Hajaratu tana nufin Alkawari bisa doka da aka yi a tudun Sinai a 1513 K.H.Y. (Fit. 19:​5, 6) Dukan Yahudawa ajizai ne, kuma babu yadda za su yi biyayya ga dokar ba tare da yin kuskure ba. Saboda haka, alkawarin zai taimaka musu su riƙa tuna cewa su bayi ne ga zunubi. Ƙari ga haka, alkawarin zai taimaka wa alꞌummar Israꞌila su san Almasihu idan ya zo, domin shi kaɗai ne zai iya bin dokar ba tare da yin kuskure ba. Saꞌad da Almasihu ya ba da kamiltaccen ransa a matsayin fansa, ya ꞌyantar da ꞌyanꞌadam ajizai daga zunubi da kuma mutuwa. (Gal. 3:​19, 24, 25) Bayan da Yesu ya cika nufin Allah sai aka kawo ƙarshen dokar.—Rom. 10:4.

Bulus ya kwatanta Hajaratu da Saratu “mace mai ꞌyanci” da ta haifi ɗa ta wurin alkawarin da Allah ya yi. (Gal. 4:23) Alkawarin nan shi ne Alkawarin da Jehobah ya yi wa Ibrahim. (Gal. 3:29; 4:​28, 30) A Farawa 22:​18, Jehobah ya yi magana game da alkawari da kuma yarjejeniyar nan, ya ce: “Ta wurin zuriyarka, dukan kabilun duniya za su roƙa wa kansu albarka, saboda ka yi biyayya ga abin da na ce maka ka yi.”

Alkawarin nan da aka yi wa Ibrahim ya sa mun ƙara gane alkawarin da Jehobah ya yi a Lambun Adnin. (Far. 3:15) Ya nuna cewa zuriyar da aka annabta zai zama wani daga zuriyar Ibrahim. Bulus ya ambata cewa, ‘zuriyar’ nan ta ƙunshi Yesu Kristi da kuma waɗanda suke na “Almasihu Yesu,” wato mutane 144,000 da za su yi sarauta tare da Yesu a Mulkinsa. (Gal. 3:​16, 29; R. Yar. 14:​1-3) Jehobah zai saka wa waɗanda suka gaskata kuma suka yi biyayya ga Yesu don alkawarin da Jehobah ya yi wa Ibrahim.

Me ya sa Bulus ya yi amfani da ‘misalin’ nan? Bulus ya nuna cewa, idan Yahudawa a zamaninsa sun nace cewa sai sun bi Dokar Musa, za su ci-gaba da zama bayi kamar Hajaratu. Amma, idan suka gaskata da zuriyar Ibrahim wato Yesu Kristi, za su sami ꞌyanci kamar Saratu. Za a ꞌyantar da su daga zunubi da kuma mutuwa. (Yoh. 8:​32-34) Amma idan suka ƙi ba da gaskiya ga Yesu, hakan zai nuna cewa ba su fahimci ainihin dalilin da ya sa aka ba da Dokar ba, wato ta kai su ga Kristi.

Da yawa daga cikin Kristoci da ke Galatiya da Bulus ya rubuta wa wasiƙa ba Yahudawa ba ne, kuma ba su taɓa kasancewa a ƙarƙashin Dokar Musa ba. Wasu daga cikin Kristocin sun nace cewa sai Kristocin da ba Yahudawa ba sun bi Dokar, har da dokar yin kaciya. Bulus ya bayyana cewa, zai zama wauta idan suka soma bin Dokar Musa domin son riga sun sami ꞌyanci bayan da suka ba da gaskiya ga Yesu Kristi.—Gal. 5:​1, 10-14.

a Wannan ƙarin haske ne a kan abin da aka rubuta a Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Maris, 2006, shafi na 10-12 na Turanci.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba