24-30 GA AGUSTA, 2026
WAƘA TA 65 Mu Riƙa Samun Ci Gaba!
Rukunin Waꞌazi Na Taimaka Mana a Hanyoyi da Yawa
“Zan gode wa Yahweh da dukan zuciyata, a cikin taron jamaꞌa masu gaskiya a zuci.”—ZAB. 111:1.
ABIN DA ZA MU KOYA
Za mu ga dalilin da ya sa ya dace kowannenmu ya kasance a cikin rukunin waꞌazi.
1-2. Yaya kake ji game da shirin da aka yi na yin waꞌazi rukuni-rukuni?
SHIN ka tuna da ranar da aka gaya maka cewa ka zama mai shela? Babu shakka, ka yi farin ciki sosai a ranar domin ka zama ɗaya daga cikin waɗanda suke ɗaukaka sunan Jehobah. (Zab. 148:1, 2, 12, 13) Ban da haka, mai yiwuwa a ranar an gaya maka cewa ka zama ɗaya daga cikin ƙaramin rukuni da ake kira rukunin waꞌazi da ya ƙunshi ꞌyanꞌuwa maza da mata kaɗan a ikilisiya. Yesu ya umurci dukan bayinsa su yi shelar labari mai daɗi na Mulkin “a dukan duniya,” kuma kasancewa a cikin rukunin waꞌazi yana taimaka mana mu yi hakan.—Mat. 24:14.
2 Yaya kake ji game da shirin da aka yi na yin waꞌazi rukuni-rukuni? Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Wendya ta ce: “Rukunin waꞌazinmu ya taimaka mini a hanyoyi dabam-dabam. Alal misali, na koyi sabbin hanyoyin yin waꞌazi da koyarwa, an taimaka mini in yi abubuwan da za su sa in ƙara kusantar Jehobah, kuma na ƙulla abota da ꞌyanꞌuwa masu aminci.” Wani ɗanꞌuwa mai suna Rich ya ce: “Yin hidima a matsayin mai kula da rukunin waꞌazi abu ne mai muhimmanci sosai a gare ne. Yayin da wasu masu shela suke taimaka wa ɗalibi ya yi baftisma, mai kula da rukunin waꞌazi yana da damar taimaka wa ɗalibin ya ci-gaba da ƙarfafa dangantakarsa da Jehobah, kuma ya zama Kristan da ya manyanta.” Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Dinah ta ce: “Kasancewa a rukunin waꞌazi yana da kyau sosai! Ina ɗaukan kowa a rukunin kamar ꞌyan iyalina.”
3. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?
3 A wannan talifin, za mu soma da tattauna game da aikin da mai kula da rukunin waꞌazi da mataimakinsa suke yi, da kuma yadda suke taimaka wa ꞌyanꞌuwa da ke rukuninsu. Saꞌan nan, za mu tattauna yadda mu ma za mu taimaka wa ꞌyanꞌuwan da ke rukuninmu. A ƙarshe, za mu ga yadda dukanmu za mu amfana daga wannan shirin da aka yi.
MAI KULA DA RUKUNIN WAꞌAZI DA MATAIMAKINSA
4. (a) Waɗanne ayyuka ne mai kula da rukunin waꞌazi yake yi? (b) Ta yaya mai kula da rukunin waꞌazi yake kula da ꞌyanꞌuwan da ke rukuninsa? (Ka kuma duba akwatin nan “Shawarwari ga Mai Kula da Rukunin Waꞌazi.”)
4 Mai kula da rukunin waꞌazi dattijob ne da dattawa suka zaɓa ya riƙa taimaka wa ꞌyanꞌuwa da ke rukuninsa su kusaci Jehobah kuma su inganta yadda suke yin waꞌazi da koyarwa. Ta yaya yake yin hakan? Da farko, yana nuna cewa ya damu sosai da ꞌyanꞌuwan da ke rukuninsa. (K. Mag. 27:23) Yana iya ƙoƙarinsa don ya san ꞌyanꞌuwan da kyau, kuma yana tattaunawa da su a kai a kai don ya san yadda suke. Yin hakan yana sa ya iya taimaka musu su kusaci Jehobah, da nuna musu cewa yana ƙaunar su idan suna cikin damuwa, da kuma tanada musu abubuwan da suke bukata. (K. Mag. 12:25; Isha. 32:2; Yak. 2:15-17) Na biyu, yana taimaka wa kowane mai shela a rukuninsa ya riƙa yin waꞌazi. Yana iya ƙoƙarinsa wajen yin waꞌazi da rukunin kowane mako. Yana kuma yin waꞌazi tare da kowane mai shela da ke rukuninsa don ya ƙarfafa, da kuma taimaka wa mai shelar ya inganta yadda yake yin waꞌazi da koyarwa. Idan kuma bai samu fita waꞌazi ba, yana tabbata cewa ɗanꞌuwan da ke taimaka masa ko wani ɗanꞌuwa dabam zai kula da rukunin. Na uku, yana taimaka wa ꞌyanꞌuwa maza da suka yi baftisma su cancanci samun ƙarin ayyuka a ikilisiya. (1 Tim. 3:1) Yana yaba musu don ƙoƙarin da suke yi, yana ba su shawara daga Littafi Mai Tsarki, kuma yana koyar da su don su iya zama bayi masu hidima da dattawa a nan gaba. Mai kula da rukunin waꞌazi yana ayyuka masu muhimmanci sosai. Saboda haka, idan dattawa suna so su zaɓi ɗanꞌuwan da zai zama mai kula da rukunin waꞌazi, suna zaɓan dattijon da zai iya yin aikin da kyau.
5. Waɗanne abubuwa ne za su iya sa ya yi wa mai kula da rukunin waꞌazi wuya ya kula da rukuninsa?
5 Akwai abubuwa da yawa da za su iya sa ya yi wa mai kula da rukunin waꞌazi wuya ya kula da rukuninsa. Alal misali, wani dattijo mai kula da rukunin waꞌazi mai suna Jörg daga ƙasar Jamus yana da wasu ayyuka da yake yi a ikilisiya kamar yadda dattawa da yawa suke yi. Ɗanꞌuwan ya ce: “Yin hidimar mai kula da rukunin waꞌazi tare da yin wasu ayyuka a ikilisiya bai da sauƙi. Don haka, ba na iya cim ma burina na kiran dukan ꞌyanꞌuwan da ke rukunina.” Wani dattijo mai shekaru 70 daga ƙasar Yuganda mai suna Abel ya ce: “Dattawa da bayi masu hidima da ke ikilisiyarmu ba su da yawa. Don haka, ꞌyanꞌuwan da suke kowane rukunin waꞌazi suna da yawa. Ba na iya yin waꞌazi da kuma ƙarfafa ꞌyanꞌuwan yadda ya kamata.” Wani dattijo daga Suriname mai suna Obed ya ce: “Ina son koyar da ꞌyanꞌuwa sosai. Amma hakan bai da sauƙi, yana ɗaukan lokaci kuma ba a ganin amfaninsa nan da nan. Saboda haka, ba na samun lokacin koyar da wasu domin wasu ayyukan da naka yi.” To, mene ne zai taimaka wa dattawa da suke cikin irin yanayoyin nan?
6. Ta yaya mai kula da rukunin waꞌazi zai yi aikinsa da kyau idan ꞌyanꞌuwan da ke rukunin waꞌazin ba su da yawa?
6 Idan zai yiwu, kada ꞌyanꞌuwan da ke kowane rukunin waꞌazi su yi yawa. Hakan zai ba wa mai kula da rukunin damar sanin ꞌyanꞌuwan da ke rukunin da kyau, kuma ya taimaka musu su kusaci Jehobah. Idan dattawa da ke ikilisiya ba su da yawa kuma fa? Zai yi wa mai kula da rukunin waꞌazi wuya ya riƙa kula da ꞌyanꞌuwan da ke rukunin idan ꞌyanꞌuwan suna da yawa. Saboda haka, idan babu dattawa da yawa, dattawa za su iya zaɓan bawa mai hidima ya kula da wani rukunin waꞌazi. Yin hakan zai ba wa mai kula da rukunin waꞌazi damar yin aikinsa mafi muhimmanci, wato taimaka wa ꞌyanꞌuwan da ke rukuninsa su kasance da aminci ga Jehobah da kuma jimre matsaloli.
7. Idan dattawa ba su da yawa a ikilisiya, mene ne mai kula da rukunin waꞌazi yake bukatar ya yi don ya tabbata cewa an kula da ꞌyanꞌuwan da ke rukuninsa? (1 Bitrus 5:2) (Ka kuma duba hoton.)
7 Idan kai mai kula da rukunin waꞌazi ne a ikilisiyar da babu dattawa da yawa, ka mai da hankali sosai wajen koya wa ɗanꞌuwan da ke taimaka maka yadda shi ma zai iya kula da ꞌyanꞌuwan da ke rukunin. (Karanta 1 Bitrus 5:2.) Ka ba wa ɗanꞌuwan da ke taimaka maka wasu ayyuka. Alal misali, a wasu lokuta, ka gaya masa ya gudanar da taron fita waꞌazi, kuma ya shirya yadda ꞌyanꞌuwa a rukunin za su yi waꞌazi. Yana da muhimmanci kuma ku tattauna yadda za ku taimaka wa ꞌyanꞌuwa a rukunin su kusaci Jehobah, kuma su inganta yadda suke yin waꞌazi. Ka riƙa zuwa ziyarar ƙarfafa da ɗanꞌuwan da ke taimaka maka. Kafin ku kai ziyarar, ku tattauna yadda ku biyun za ku ƙarfafa wanda za ku je wurinsa. Bayan kun gama, ka yaba masa kuma ka gaya masa wuraren da zai iya yin gyara idan da bukata. Idan ka koyar da ɗanꞌuwan da ke taimaka maka da kyau, hakan zai sa ya cancanci zama mai kula da rukunin waꞌazi a nan gaba. (2 Tim. 2:2) Za ka kuma iya gaya wa ꞌyanꞌuwan da suka manyanta a rukunin su taimaka wajen koyar da wasu. Majagaba da wasu ꞌyanꞌuwan da suka ƙware wajen yin waꞌazi za su iya taimaka wa sabbi da waɗanda ba su ƙware a yin waꞌazi ba. Za su iya koya musu yadda za su iya soma tattaunawa, da komawa ziyara, da kuma yin nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane. Yanzu, bari mu tattauna abubuwa uku da dukanmu za mu iya yi don mu taimaka wa rukunin waꞌazinmu.
Dattijo zai iya koyar da bawa mai hidima da ke rukuninsa ta wurin gaya masa ya gudanar da taron fita waꞌazi (Ka duba sakin layi na 7)
YADDA ZA KA IYA TAIMAKA WA RUKUNIN WAꞌAZINKU
8. Ta yaya za ka iya taimaka wa rukunin waꞌazinku? (Romawa 1:12)
8 Ka yi waꞌazi da rukuninku. Idan kana waꞌazi da ꞌyanꞌuwan da ke rukuninku, hakan zai sa ku samu damar “ƙarfafa juna.” (Karanta Romawa 1:12.) Yin waꞌazi tare da ꞌyanꞌuwa zai taimaka maka ka rage jin tsoro kuma ka samu kāriya saꞌad da kake yin waꞌazi. Idan aikinka ya sa ba ka iya yin waꞌazi tare da rukuninku, za ka iya roƙa a canja tsarin aikinka a wurin aiki. Mai yiwuwa za a canja. (Neh. 2:4-6) Idan ba ka iya fita waꞌazi tare da rukuninku don rashin lafiya ko tsufa, ka tattauna da mai kula da rukunin waꞌazinku. Mai yiwuwa zai iya shirya yadda za ka shiga taron fita waꞌazi ta naꞌura, da kuma yadda za ka yi waꞌazi ta wajen rubuta wasiƙu ko kuma ta waya. Idan kai matashi ne mai ƙoshin lafiya amma yana yi maka wuya ka fita waꞌazi babu fashi, za ka iya shirya yin waꞌazi tare da wani a rukuninku kowane mako. Zai dace ka yi tunani a kan abin da ya fi muhimmanci a rayuwarka da kuma yadda za ka yi amfani da lokacinka da kyau. (Rom. 12:11; Kol. 4:5) Idan ka yi iya ƙoƙarinka wajen yin waꞌazi tare da rukuninku, kowa a rukunin zai amfana. Ka roƙi Jehobah ya taimaka maka domin shi ne yake sa mu yi niyyar yin abu, kuma shi ne yake ba mu ƙarfin yin sa.—Filib. 2:13.
9. Ta yaya za mu taimaka wajen sa rukunin waꞌazinmu ya zama kamar iyali? (Romawa 12:13)
9 Ka zama mai bayarwa da kuma karɓan baƙi hannu bibbiyu. Za mu iya sa ꞌyanꞌuwan da ke rukuninmu su san cewa muna ƙaunar su idan mu masu “karɓan baƙi hannu bibbiyu” ne. (Karanta Romawa 12:13.) Alal misali, za mu iya yarda a dinga yin taron fita waꞌazi a gidanmu. A wasu ikilisiyoyi, a duk lokacin da wani ɗanꞌuwa daga wata ikilisiya ya zo ya ba da jawabi, akan shirya rukunin waꞌazi guda ɗaya da za su yi liyafa tare da mai jawabin. A wasu lokuta, ko da ɗanꞌuwan ba zai iya zuwa liyafar ba, ꞌyanꞌuwan sukan haɗu su yi liyafar kuma su ƙarfafa juna bayan taron. Wata ꞌyarꞌuwa majagaba na musamman mai suna Sarah ta ce: “Ina yawan damuwa idan mutane za su zo gidana. Don haka, nakan mai da hankali wajen ƙara sanin ꞌyanꞌuwan maimakon shirya abubuwa da yawa.” Idan muka taimaka wajen sa rukunin waꞌazinmu ya zama tamkar iyali, hakan zai sa mu kusaci Jehobah da kuma juna.—Neh. 8:10; A. M. 20:35.
10. Me za mu iya yi don mu inganta yadda muke waꞌazi da koyarwa? (Karin Magana 1:5; 27:17) (Ka kuma duba hoton.)
10 Ka yi ƙoƙari ka inganta yadda kake waꞌazi da koyarwa. Idan muka inganta yadda muke waꞌazi da koyarwa, za mu riƙa son yin waꞌazi kuma za mu daɗa jin daɗin yin waꞌazi da rukuninmu. Shin za ka so ka inganta yadda kake waꞌazi da kuma koyarwa? Ka nemi taimakon wani a rukuninku. (Karanta Karin Magana 1:5; 27:17.) Ka gaya wa mai kula da rukunin waꞌazinku abin da kake so ka cim ma. Zai yi iya ƙoƙarinsa wajen taimaka maka. Za ka kuma iya neman taimakon waɗanda suka ƙware wajen yin waꞌazi da koyarwa. Abin da wata ꞌyarꞌuwa mai suna Heather ta yi ke nan. Duk da cewa ita mai kunya ce sosai, ta ce: “Na gaya ma wata majagaba ta taimaka mini a batun komawa ziyara. ꞌYarꞌuwar tana da kirki, kuma ta yi waꞌazi tare da ni a kai a kai. Ta ma taimaka mini in soma nazari da wata. Ina farin ciki sosai cewa na nemi taimako daga wurinta. A yanzu, ina jin daɗin yin waꞌazi.” Babu shakka, akwai abubuwa da yawa da za mu iya yi don mu taimaka wa rukunin waꞌazinmu.
Idan ꞌyanꞌuwa da ke rukunin waꞌazi ba su da yawa, hakan zai taimaka mana mu ƙara sanin juna kuma mu sami zarafin yin waꞌazi da dukansu (Ka duba sakin layi na 10)
YADDA ZA KA AMAFANA DAGA RUKUNIN WAꞌAZINKU
11-12. Ta yaya rukunin waꞌazinmu zai taimaka mana mu ƙara kusantar Jehobah? Ka ba da misali.
11 Rukunin waꞌazinmu yana taimaka mana mu ci-gaba da kusantar Jehobah. Ga wasu hanyoyi da dukanmu muke amfana daga rukunin waꞌazinmu. Alal misali, Jehobah yana amfani da rukunin waꞌazi wajen kula da kuma ƙarfafa gwauraye, da marayu, da kuma tsofaffi domin yana ƙaunar su sosai. (1 Tas. 2:8; Yak. 1:27) Ana koya mana yadda za mu inganta yadda muke waꞌazi da koyarwa. Ana kuma koya wa ꞌyanꞌuwa maza da suka yi baftisma abubuwan da suke bukatar su yi don su cancanci samun ƙarin ayyuka a ikilisiya.—1 Tim. 3:10.
12 ꞌYarꞌuwa Wendy da aka ambata ɗazu ta amfana sosai daga rukunin waꞌazinsu. ꞌYarꞌuwa Wendy ta ce: “Da yake mahaifina ba ya so mu bauta wa Jehobah, a yawancin lokuta mahaifiyata ba ta iya fita waꞌazi da rukunin waꞌazinmu a ƙarshen mako, amma ina iya fita. Wata ꞌyarꞌuwa majagaba da ta tsufa ta taimaka mini sosai, kuma muna yawan fita waꞌazi tare. Ta sa na inganta yadda nake yin waꞌazi da kuma abubuwa a ikilisiya. Akwai wasu shawarwari daga Littafi Mai Tsarki da mai kula da rukunin waꞌazinmu ya ba ni da suke taimaka mini har wa yau.”
13. Ta yaya rukunin waꞌazinmu zai taimaka mana mu sami abokan da suke ƙaunar mu da kuma taimaka mana? (Ka kuma duba hoton.)
13 Rukunin waꞌazinmu yana taimaka mana mu samu abokan da suke ƙaunar mu da kuma taimaka mana. Yayin da muke waꞌazi da ꞌyanꞌuwan da suke rukunin waꞌazinmu, hakan yakan sa mu kusaci juna sosai. (Filib. 1:27) Da yake ꞌyanꞌuwan da suke kowane rukunin waꞌazi ba su da yawa, hakan yana sa ya yi wa waɗanda suke kunya sauƙi su sami abokai. (2 Kor. 6:13) ꞌYanꞌuwan da suke rukunin waꞌazinmu suna taimaka mana saꞌad da muke rashin lafiya, ko cikin damuwa, ko kuma saꞌad da wani namu ya mutu. (1 Tas. 5:14) Babu shakka, za mu bukaci taimakon irin abokan nan yayin da ƙunci mai girma yake ƙara gabatowa. (Mat. 24:21) Zai yi mana sauƙi mu jimre matsalolinmu domin mun san cewa ꞌyanꞌuwanmu suna ƙaunar mu, kuma za su taimaka mana.—K. Mag. 17:17.
ꞌYanꞌuwa mata biyu da rukunin waꞌazinsu ɗaya ne suna waꞌazi tare (Ka duba sakin layi na 13)
14. Ta yaya za mu amfana daga rukunin waꞌazinmu saꞌad da balaꞌi ya auku?
14 Rukunin waꞌazinmu yana taimaka mana saꞌad da balaꞌi ya auku. Muna samun taimako daga rukunin waꞌazinmu idan wani balaꞌi ya auku, ko wata cuta ta ɓarke, ko ana tsananta mana, ko muna bukatar jinyar gaggawa, ko kuma an samu taɓarɓarewar tattalin arziki. Alal misali, idan balaꞌi ya auku, masu kula da rukunin waꞌazi za su tuntuɓi kowane iyali da ke rukuninsu don su san abin da suke bukata, kamar su magani, da abinci, da ruwan sha, da wurin zama da kuma riguna. Babu shakka, za mu amfana sosai daga rukunin waꞌazinmu idan balaꞌi ya auku!
15. Mene ne dukan bayin Jehobah suke so?
15 Masu bauta wa Jehobah suna da yawa sosai a sama da kuma duniya. Akwai malaꞌiku masu aminci da yawa a sama. A duniya kuma, akwai mutane fiye da miliyan tara da suke bauta wa Jehobah, kuma a kullum suna daɗa ƙaruwa. (Zak. 8:23; R. Yar. 5:11) Dukan bayin Jehobah a sama da kuma duniya suna so mutane da yawa su ji labari mai daɗi na Mulkin Allah! (R. Yar. 14:6, 7) Saboda haka, bari dukanmu mu ci-gaba da goyon bayan rukunin waꞌazinmu. Yin hakan zai sa mu amfana sosai kuma zai taimaka mana mu yabi Jehobah da dukan zuciyarmu.—Zab. 111:1.
WAƘA TA 61 Bayin Jehobah, Kar Mu Gaji!
a An canja wasu sunayen.
b Idan da bukata, bawa mai hidiman da ya ƙware zai iya kula da rukunin waꞌazi har sai an sami dattijo. Ana kiran bawa mai hidima da aka ce ya kula da rukunin waꞌazi bawa mai kula da rukuni. Yana taimaka wa dattawa ne kuma su ne suke gaya masa abubuwan da yake bukatar ya yi.