17-23 GA AGUSTA, 2026
WAƘA TA 90 Mu Riƙa Ƙarfafa Juna
Yadda Za Mu Ci-gaba da Ƙarfafa Dangantakarmu da ꞌYanꞌuwanmu
“Ku ɗauki hali na jin tausayin juna, kuna yin alheri, kuna nuna tawaliꞌu da sauƙin kai da jimrewa.”—KOL. 3:12.
ABIN DA ZA MU KOYA
Za mu ga yadda za mu shawo kan matsalolin da za su iya ɓata dangantakarmu da ꞌyanꞌuwa a ikilisiya.
1. A ina ne za mu iya samun abokan kirki?
“A DUNIYAR nan in ba abokai, rayuwa ba sauƙi. Jehobah ya san dukanmu na son abokan kirki.” Shin, kun tuna da kalmomin nan daga waƙar jw mai jigo, “Abokan Kwarai”? Abin alfahari ne cewa, za mu iya samun abokan kirki a ƙungiyar Jehobah! (Zab. 119:63) Mu iyali ne masu ƙaunar juna, kuma muna bauta ma Jehobah tare.
2. Yaya ya kamata abokantakarmu ta kasance da ꞌyanꞌuwa a ikilisiya?
2 Bai kamata a ce mun san ꞌyanꞌuwa a ikilisiya sama-sama kawai ba, a maimakon haka, zai dace mu ƙulla abokantaka ta kud da kud da su. Muna yin ibada tare kuma muna ƙaunar Jehobah da Yesu, ƙaunar ce take sa mu kasance da haɗin kai. (Yoh. 13:35) Amma ba a iya zama abokai na kud da kud haka kawai. Wajibi ne mu yi iya ƙoƙarinmu don mu iya yin hakan. Da yake dukanmu ajizai ne, a wasu lokuta, matsaloli za su iya sa ya yi mana wuya mu kasance da dangantaka ta kud da kud da ꞌyanꞌuwanmu.
3. Me ya sa a wani lokaci yana da wuya mu ci-gaba da yin abota da ꞌyanꞌuwa?
3 Gaskiyar ita ce, akwai waɗanda muka fi kusa da su fiye da wasu. Me ya sa? Wataƙila abubuwan da muke so, da yadda muke yin abubuwa ko kuma tunaninmu iri ɗaya ne. Amma akwai wasu a ikilisiya da zai iya yi mana wuya mu zama abokansu. A wasu lokuta zai iya yi mana wuya mu kusace su don saɓanin raꞌayi. Mai yiwuwa yadda muke yin abubuwa ko tunani ya bambanta, hakan zai iya sa ba za mu ji daɗin tarayya ba. Kuma idan ꞌyanꞌuwanmu suna fama da rashin lafiya ko wani abu yana damun su a zuciya, hakan zai iya sa ya yi mana wuya mu kusace su. A wannan talifin, za mu tattauna yadda misalin Yesu zai taimaka mana mu ci-gaba da ƙulla dangantaka ta kud da kud da ꞌyanꞌuwa, musamman a lokacin da yin hakan yake da wuya. Amma bari mu ga yadda yin koyi da Jehobah zai taimaka mana mu ci-gaba da yin abota da ꞌyanꞌuwanmu.
YIN KOYI DA JEHOBAH ZAI TAIMAKA MANA MU CI-GABA DA YIN ABOTA DA ꞌYANꞌUWANMU
4. Me zai iya sa abokantakarmu ta yi ƙarfi?
4 Idan muna mai da hankali ga halaye masu kyau na ꞌyanꞌuwanmu, hakan zai sa dangantakarmu ta yi ƙarfi. Wani abin da zai iya sa mu riƙa tunawa da halayensu masu kyau shi ne, kasancewa tare da su. Manzo Bulus ya yi marmarin kasancewa tare da ꞌyanꞌuwa, shi ya sa ya rubuta wa Tasalonikawa cewa: “Muna ta ƙoƙari mu gan ku fuska da fuska.” (1 Tas. 2:17) ꞌYanꞌuwa da yawa suna ganin yin tarayya fuska da fuska ne zai iya sa abokantakarsu ta yi ƙarfi. Muna samun damar yin hakan idan muka fita waꞌazi, ko muka halarci taro na ikilisiya, ko na daꞌira, ko kuma na yanki. Amma idan mun sami saɓani da wani a ikilisiya, ba yin tarayya ne kawai zai sa mu sasanta ba.
5. Mene ne zai taimaka mana mu iya shawo kan matsalar da za ta iya ɓata dangantakarmu da ꞌyanꞌuwa? Ka ba da misali. (Kolosiyawa 3:12)
5 Yin koyi da Jehobah zai taimaka mana mu iya shawo kan matsalar da za ta iya ɓata dangantakarmu da ꞌyanꞌuwa. (Karanta Kolosiyawa 3:12.) Idan mun kasance da halaye kamar, sauƙin kai, da haƙuri, da tausayi da kuma yi wa mutane alheri, zai yi mana sauƙi mu warware matsalolin da za su iya sa dangantakarmu da ꞌyanꞌuwa ta yi tsami. Alal misali, kamar yadda injin mota yake bukatar baƙin mai don ya ci-gaba da yin aiki da kyau, haka mu ma muke bukatar halaye masu kyau don mu ci-gaba da ƙarfafa dangantakarmu da ꞌyanꞌuwa. Yanzu, bari mu tattauna abubuwa uku da za su iya sa ya yi mana wuya mu ƙulla abota da ꞌyanꞌuwa a ikilisiya. Kuma za mu ga yadda yin koyi da halayen Yesu kamar, sauƙi kai, da haƙuri, da alheri da kuma tausayi za su taimaka mana mu ci-gaba da zama abokan kirki.
IDAN RAꞌAYINKU YA BAMBANTA
6. Me ya sa zai yi wuya a ci-gaba da zama abokai idan aka sami saɓanin raꞌayi?
6 Me ya sa hakan zai iya zama matsala? Idan mutane biyu suka samu saɓanin raꞌayi, kowannensu zai riƙa gani kamar raꞌayinsa ne daidai. Alal misali, ꞌyanꞌuwa maza biyu za su iya kasancewa da raꞌayi dabam-dabam game da yadda za a riƙa yin waꞌazi a yankinsu. Kowannensu zai iya ɗauka cewa raꞌayinsa ne daidai. Irin yanayin nan zai iya jawo matsala, har ya sa ya yi musu wuya su ci-gaba da zama abokai. Girman kai zai iya sa su ƙi amincewa da juna, kuma idan sun ƙi sasantawa, hakan zai iya sa su soma baƙin ciki. Da shigewar lokaci, za su soma guje wa juna har su daina zama abokai don abin da bai kai ya kawo ba.
7. Ta yaya Yesu ya nuna wa almajiransa cewa suna bukatar sauƙin kai don su iya warware matsaloli tsakaninsu?
7 Ka zama mai sauƙin kai kamar Yesu. Yesu ya koya wa almajiransa cewa suna bukatar su zama masu sauƙin kai don su iya warware matsaloli tsakaninsu. Almajiran sun daɗe suna gardama a kan ko waye ne babba a cikinsu. Yesu ya yi ƙoƙarin taimaka musu ta wajen bayyana musu cewa, suna bukatar su zama kamar bayi, maimakon su ga kamar sun fi wasu. (Mat. 20:25-28) Babu shakka, yana ƙoƙarin koya musu yadda za su zama masu sauƙin kai ne. Har ma a dare na ƙarshe kafin ya mutu, Yesu ya nuna musu misali ta wurin wanke ƙafafunsu, aikin da bayi ne suke yi. (Yoh. 13:3-5, 12-16) Ta yin haka, ya nuna musu yadda za su ci-gaba da zama abokai. Idan suna ganin cewa wasu sun fi su, hakan zai sa su amince da raꞌayin mutane ko da ya yi dabam da nasu. Zai yi musu sauƙi su ci-gaba da zama abokai ko da raꞌayinsu ba ɗaya ba ne.
8. Ta yaya sauƙin kai zai taimaka mana mu ci-gaba da zama abokai idan muka sami saɓani? (Kolosiyawa 3:13) (Ka kuma duba hotunan.)
8 Me za ka yi don ku ci-gaba da zama abokai? Sauƙin kai zai sa ba za mu damu da ƙananan laifuffukan da aka yi mana ba, kuma zai taimaka mana mu riƙa gafarta wa mutane. (Karanta Kolosiyawa 3:13.) Ƙari ga haka, sauƙin kai zai sa ba za mu yi fushi ba idan muka sami saɓanin raꞌayi da wasu, kuma hakan zai sa mu ci-gaba da zama abokai. (Zab. 4:4) Ko da mun riga mun gaya wa juna wasu maganganun da ba su dace ba, mu tuna cewa dukanmu mukan yi da na sani don wasu abubuwan da muka faɗa. (M. Wa. 7:21, 22) Zai dace ka tambayi kanka cewa, ‘Shin, zumuncin da ke tsakaninmu ne ya fi muhimmanci a gare ni ko raꞌayina?’ Ko da raꞌayinku ya bambanta, za ka iya amincewa da raꞌayin wasu, kuma idan ba ka sake tā da batun ba, za ka sami kwanciyar hankali.
Sauƙin kai zai sa ba za mu damu da ƙananan laifuffukan da aka yi mana ba, kuma zai taimaka mana mu riƙa gafarta wa mutane (Ka duba sakin layi na 8)a
9. Ta yaya sauƙin kai zai taimaka mana mu warware matsalar da ta ƙi ci ta ƙi cinyewa? (Karin Magana 17:9)
9 Sauƙin kai zai kuma taimaka muku ku warware matsalar da ta ƙi ci ta ƙi cinyewa. Ba zai dace mu yi gardama don mu nuna cewa raꞌayinmu ne daidai ba. (Karanta Karin Magana 17:9; 1 Kor. 6:7) Zai yi kyau kada ku manta cewa abin da ya fi muhimmanci shi ne, ku ci-gaba da zama abokai na kud da kud. ꞌYanꞌuwa da yawa da suka kasance da irin raꞌayin nan kuma suka tattauna batun, sun yi nasara wajen sasanta matsalar da ke tsakaninsu. (Zab. 34:14) Za ka iya gaya wa wanda kake so ka sasanta da shi cewa: ‘Abokina na lura cewa ba ma maꞌamala yadda muke yi a dā, zai dace mu tattauna don mu ci-gaba da abotarmu.’ Ka kasance a shirye cewa za ka amince da duk wani laifin da mutumin ya ce ka yi, kuma ka ba shi haƙuri. Idan mutumin ne ya yi maka laifi, kuma ya ba ka haƙuri, ka yafe masa. (Luk. 17:3, 4) Ka tuna cewa, niyyarka shi ne ku sasanta, kuma ku ci-gaba da zama abokai, maimakon a san waye ne mai gaskiya.—K. Mag. 18:24.
IDAN YADDA MUKE YIN ABUBUWA DA KUMA TUNANI YA BAMBANTA
10. Mene ne zai iya sa ya yi mana wuya mu ci-gaba da zama abokai da ꞌyanꞌuwa?
10 Me ya sa hakan zai iya zama matsala? Zai iya yi mana wuya mu ci-gaba da zama abokai da ꞌyanꞌuwan da tunaninmu da yadda muke yin abubuwa ya bambanta. Wasu na da halayen da ba ma so. Wasu da an taɓa wulaƙanta su a dā, ko kuma sun yi girma a alꞌadar da mutane ba sa faɗan yadda suke ji, za su dinga yin abubuwa wani iri. Ban da haka ma, mai yiwuwa muna son mu riƙa yin tarayya da mutane, wasu kuma ba sa so, wataƙila don suna jin kunya.
11. Ta yaya Yesu ya ci-gaba da zama abokin waɗanda tunaninsu ya yi dabam da nashi?
11 Ka zama mai haƙuri kamar Yesu. Yesu ya ci-gaba da zama abokin waɗanda tunaninsu da yadda suke yin abubuwa ya yi dabam da nashi. Alal misali, manzo Yaƙub da Yohanna sun nuna cewa suna son matsayi saꞌad da suka gaya wa Yesu cewa, suna so su zauna a hannun dama da kuma hagunsa a Mulkin sama. (Mar. 10:35-37) Amma Yesu bai nuna irin halin nan ba, ya nuna sauƙi kai ta wajen barin matsayinsa a sama kuma ya zo duniya. (Filib. 2:5-8) Halin da suka nuna ya bambanta sosai da na Yesu. Duk da haka, Yesu ya kasance da haƙuri saꞌad da yake tare da su.
12. Me ya taimaka wa Yesu ya iya yin haƙuri da abokansa?
12 Yesu ya san cewa ba kullum ne almajiransa za su kasance da halin da ya kamata ba. Ya san cewa almajiransa da yawa sun damu da samun matsayi kamar yadda Yaƙub da Yohanna suka yi. (Mar. 9:34) Yesu ya fahimci abin da ya sa suke tunani haka, domin alꞌadarsu ɗaya ne kuma sun yi girma a wuri ɗaya. A lokacin, shugabannin addinai suna sa mutane su ga kamar yin suna da samun matsayi yana da muhimmanci sosai. Duk da haka, Yesu ya yi haƙuri da su, kuma ya ba su lokaci don su iya canja irin halaye da kuma tunanin nan da ba su dace ba.—Mar. 10:42-45.
13. Ta yaya kasancewa da haƙuri zai taimaka mana mu ci-gaba da zama abokai? (Afisawa 4:2)
13 Me za ka yi don ku ci-gaba da zama abokai? Ka ci-gaba da kasancewa da haƙuri da ꞌyanꞌuwa a ikilisiya ko da suna da wasu halayen da ba ka so. (K. Mag. 14:29) Kowannenmu na da halinsa dabam. Wasu halayen ba laifi ba ne, amma da shi muka taso. Babu shakka, muna jin daɗi idan ꞌyanꞌuwa suna haƙuri da mu. (Karanta Afisawa 4:2.) Don haka, zai dace mu ma mu riƙa haƙuri da mutane idan suna yin wani abin da ba ma so. Alal misali, yana iya yi wa mai kunya wuya ya yi cuɗanya da mutane. Amma yana da sauƙi wanda ba ya jin kunya ya soma cuɗanya da mutane da kuma hira da su. Saboda haka, muna bukatar mu yi haƙuri da su. A gaskiya, ba kowa ba ne zai iya zama abokinmu na kud da kud, amma za mu iya zama da dangantaka mai kyau da ꞌyanꞌuwa a ikilisiya.
14. Mene ne kasancewa da haƙuri zai taimaka mana mu riƙa yi?
14 Kasancewa da haƙuri zai taimaka mana mu riƙa mai da hankali a kan halaye masu kyau na ꞌyanꞌuwanmu. Yin hakan zai sa ba za mu bar yadda halayenmu ya bambanta da nasu ya hana mu zama abokai ba. Alal misali, duk da cewa Yaƙub da Yohanna sun nuna son kai saꞌad da suka nemi wa kansu matsayi, halinsu ya nuna cewa sun yi imani da Mulkin Allah. Yesu ya lura cewa suna da bangaskiya, kuma ya ji daɗin hakan. Idan mu ma mun mai da hankali a kan halaye masu kyau da ꞌyanꞌuwanmu suke da su, za mu nuna cewa muna yin koyi da Yesu da kuma Ubansa, Jehobah.
15. A ina ne za mu sami taimako don mu ci-gaba da zama abokai da ꞌyanꞌuwan waɗanda halayensu ya bambanta da namu?
15 Abu mafi muhimmanci da za mu iya yi shi ne, mu roƙi Jehobah ya taimaka mana mu ci-gaba da zama abokai da ꞌyanꞌuwa waɗanda halayensu ya bambanta da namu. Ka yi tunanin irin yanayin da zai iya ɓata maka rai, sai ka yi adduꞌa tun kafin wani abu ya faru. Ka tuna cewa, Jehobah Mahaliccinmu ya san cewa kowannenmu na da halinsa dabam. Don haka, a duk lokacin da muke yin adduꞌa, bari mu kasance da tabbaci cewa Jehobah ya san abin da muke bukata da zai taimaka mana mu ci-gaba da jimrewa. Ƙari ga haka, a duk lokacin da yake maka wuya ka jimre, ka roƙi Jehobah ya ba ka ruhunsa don ya taimaka maka ka san yadda za ka bi da yanayin.—Luk. 11:13; Gal. 5:22, 23.
IDAN ꞌYANꞌUWA SUNA SHAN WAHALA
16. Me zai iya faruwa idan ꞌyanꞌuwa suna shan wahala?
16 Me ya sa hakan zai iya zama matsala? Idan ꞌyanꞌuwa suna shan wahala ko kuma suna baƙin ciki, hakan zai iya sa su faɗa ko su yi abin da zai iya ɓata mana rai. Alal misali, za su iya daina yin magana da mu, ko abu kaɗan ya dinga ɓata musu rai, ko kuma su yi wani abin da zai iya sa mu yi mamaki. (Ayu. 6:2, 3) A wasu lokuta, ꞌyanꞌuwa sukan yi fama da wata matsala da ba mu sani ba, don haka, zai dace mu san cewa hakan zai iya sa su faɗa ko su yi abin da bai kamata ba.
17. Mene ne ka koya daga yadda Yesu ya warkar da makaho mai suna Bartimawus?
17 Ka zama mai alheri da tausayi kamar Yesu. Yesu ya nuna alheri da kuma tausayi ga waɗanda suke fama da wahala, har da ma waɗanda bai taɓa haɗuwa da su ba. Alal misali, ka yi laꞌakari da yadda Yesu ya warkar da wani makaho mai suna Bartimawus. Saꞌad da Bartimawus ya ji cewa Yesu yana wurin, ya soma ihu don ya jawo hankalin Yesu. Wasu a cikin jamaꞌar suka gaya masa cewa ya yi shuru. Amma bai saurare su ba, ya ci-gaba da yin ihu domin yana son Yesu ya warkar da shi. Wataƙila yadda Bartimawus ya yi ta yin ihu ya sa wasu a cikin jamaꞌar fushi. Amma Yesu ya tausaya masa sosai. (Mat. 20:34; Mar. 10:46-52) Ya nuna masa alheri ta wajen yi masa magana a hankali. Yesu ya lura cewa yana da bangaskiya, kuma ya ji daɗin hakan. Sai Yesu ya warkar da shi.
18. Ta yaya za ka bi da abokanka da suke shan wahala? (1 Tasalonikawa 5:14)
18 Me za ka yi don ku ci-gaba da zama abokai? Ka zama mai alheri da kuma tausayi. Halayen nan za su taimaka maka ka riƙa ƙarfafa ꞌyanꞌuwa da suke shan wahala. (Karanta 1 Tasalonikawa 5:14.) Ka tuna cewa aboki na ƙwarai yana a shirye ya taimaka, musamman a lokacin wahala. (K. Mag. 17:17) Irin wannan abokin yana tausayawa, kuma yana yin iya ƙoƙarinsa don ya taimaka. Ƙari ga haka, yana kuma ƙarfafa da kuma yin abubuwan da za su sa wanda yake shan wahala ya ji sauƙi.
19. Ta yaya za mu iya nuna alheri da kuma tausayi? (Ka kuma duba hotunan.)
19 A waɗanne hanyoyi ne za mu iya nuna alheri da kuma tausayi? Gaskiyar ita ce, ba mu da ikon magance dukan matsalolin da suke damun ꞌyanꞌuwa a ikilisiya, amma za mu iya yin iya ƙoƙarinmu don mu fahimci yadda suke ji. (Mat. 7:12; 1 Bit. 3:8) Ta yaya za mu yi hakan? Saꞌad da wani yana gaya mana abin da yake damun sa, zai dace mu saurare shi da kyau. Idan zai yiwu, ka faɗi abin da zai ƙarfafa shi. (K. Mag. 12:25) Kada mu ɗauka cewa mun fahimci kome da kome game da yanayin da yake ciki. (K. Mag. 18:13) Mu kasance da haƙuri, kuma kada mu ga kamar dole ne ya riƙa yin abubuwa ba kuskure.—Afis. 4:32.
Abokan ƙwarai sukan ƙarfafa juna ta wajen nuna wa juna alheri da kuma tausayi (Ka duba sakin layi na 19)
20. Wane irin aboki ne kake so ka zama?
20 Muna jin daɗin abokantakar da ke tsakaninmu da ꞌyanꞌuwa a ikilisiya. Amma da yake dukanmu ajizai ne, a wasu lokuta abubuwa marasa kyau da suka faru da mu za su iya sa mu faɗi ko mu yi abin da zai iya ɓata ma wani rai. Don haka, za mu ji daɗi idan ꞌyanꞌuwa suka kasance da sauƙin kai, suka ci-gaba da nuna mana alheri da tausayi, kuma suka yi haƙuri da mu a matsayin abokansu na kud da kud. Bari dukanmu mu yi ƙoƙari mu kasance da irin halayen nan don mu zama abokan kirki.
WAƘA TA 124 Mu Kasance da Aminci
a BAYANI A KAN HOTO: Wani ɗanꞌuwa da ya manyanta da wani ɗanꞌuwa da bai kai shi shekaru ba, suna da raꞌayi dabam-dabam game da yadda za a riƙa yin waꞌazi a yankinsu. Daga baya suna jin daɗin yin waꞌazi tare.