3-9 GA AGUSTA, 2026
WAƘA TA 113 Salamar da Muke Morewa
Kada Ka Shariꞌanta Mutane don Shawarar da Suka Yanke
“Kada ku shariꞌanta [mutum] idan raꞌayinsa ya yi dabam da naku.”—ROM. 14:1.
ABIN DA ZA MU KOYA
Za mu ga yadda za mu nuna cewa muna daraja shawarwarin da ꞌyanꞌuwanmu suka yanke ko da raꞌayinsu ya yi dabam da namu.
1-2. Me ya sa shawarwarin da muke yankewa a wasu lokuta suke bambanta da na wasu ꞌyanꞌuwa?
SHIN wani ya taɓa shariꞌanta ka don wata shawarar da ka yanke? Ka taɓa shariꞌanta wani don wata shawarar da ya yanke? Babu shakka, yawancinmu an taɓa shariꞌanta mu, kuma mu ma mun taɓa shariꞌanta wasu.
2 Gaskiyar ita ce a wasu lokuta, shawarwarin da muka yanke za su iya bambanta da na wasu ꞌyanꞌuwa. Me ya sa? Domin yadda muke tunani ya bambanta. Alꞌadarmu, da inda muka yi girma, da kuma abubuwan da suka faru a rayuwarmu suna shafan yadda muke tunani. Ko da yake yadda muke tunani da raꞌayoyinmu sun bambanta, bai kamata mu bar hakan ya shafi dangantaka da ke tsakaninmu da ꞌyanꞌuwa a ikilisiya ba.—Afis. 4:3.
3. Me zai iya sa mu shariꞌanta wani ɗanꞌuwa ko wata ꞌyarꞌuwa don shawarar da ta yanke?
3 Idan wata shawarar da wani ɗanꞌuwa ko wata ꞌyarꞌuwa ta yanke ba ta gamshe mu ba, za mu iya yin iya ƙoƙarinmu mu sa mutumin ya canja raꞌayinsa. Ko kuma mu soma gaya wa mutane cewa muna ganin shawarar da mutumin ya yanke ba ta dace ba. Mai yiwuwa, dalilin da ya sa muka yi hakan ba don mu cutar da mutumin ba ne. Muna ƙaunar ꞌyanꞌuwanmu, kuma muna yi musu fatan alheri. (K. Mag. 17:17) Saboda haka, ba ma son su yanke shawarar da za ta sa su yi da na sani, ko kuma wadda za ta ɓata dangantakarsu da Jehobah.
4-5. Me ya kamata mu yi idan wani ɗanꞌuwa ko wata ꞌyarꞌuwa ta yanke wata shawara da ba mu gamsu da shi ba?
4 Shin, zai dace mu tattauna da wani ɗanꞌuwa ko wata ꞌyarꞌuwa idan muna ganin shawarar da ta yanke bai dace ba? A wasu lokuta yin hakan zai dace, a wasu lokuta kuma ba zai dace ba. Alal misali, idan mun ga wani yana so ya yanke shawarar da ba ta jitu da abin da ke Littafi Mai Tsarki ba, zai dace mu taimaka wa mutumin ya gane raꞌayin Jehobah game da batun. Yin hakan zai nuna cewa muna ƙaunar sa. (K. Mag. 27:5, 6) Amma me za mu yi idan wani ɗanꞌuwa ko wata ꞌyarꞌuwa ta yanke shawarar da bai gamshe mu ba amma bai saɓa wa dokar Allah ba? Amsar na cikin ayar da aka ɗauko jigon wannan talifin. Ayar ta ce, “kada ku shariꞌanta [mutum] idan raꞌayinsa ya yi dabam da naku.”—Rom. 14:1.
5 Duk da haka, a wasu lokuta zai iya yi mana wuya mu daraja shawarar da wasu suka yanke. A wannan talifin, za mu tattauna dalilin da ya sa muke bukata mu riƙa daraja shawarwarin da wasu suka yanke, da kuma yadda za mu yi hakan. Amma kafin nan, bari mu ga wasu yanayoyin da za su iya sa mu soma shariꞌanta ꞌyanꞌuwanmu maza da mata don shawarar da suka yanke.
ABUBUWAN DA ZA SU IYA SA MU SHARIꞌANTA MUTANE
6-7. A waɗanne yanayoyi ne za mu iya ganin kamar shawarar da wasu suka yanke bai dace ba?
6 Kamar yadda aka ambata ɗazu, wurin da muka yi girma, ko abubuwan da suka faru a rayuwarmu za su iya sa mu kasance da wani irin raꞌayi game da wani batu. Za mu iya ganin kamar mutane da yawa suna da irin raꞌayinmu. Amma a wasu lokuta hakan ba gaskiya ba ne. Bari mu yi laꞌakari da wasu yanayoyi. Yanayi na 1: Wani ɗanꞌuwa ya yi fushi sosai saꞌad da ya ga wasu ꞌyanꞌuwa suna shan giya. Yana ganin abin da suke yi ba daidai ba ne, domin a lokacin da yake ƙarami kafin ya zama Mashaidi, mahaifinsa yana buguwa da giya. Sai ya je ya gaya wa ꞌyanꞌuwan cewa abin da suke yi bai dace ba. Yanayi na 2: Wata ꞌyarꞌuwa da ta warke daga wani rashin lafiya mai tsanani tana ƙoƙari ta sa wata ꞌyarꞌuwa da take irin rashin lafiyar ta yi irin jinyar da ta yi. Tana ganin yin hakan zai taimaka mata sosai. Sai ta yi ƙoƙarin sa ꞌyarꞌuwar ta riƙa cin wasu irin abinci da shan wasu irin magungunan asibiti ko kuma na gargajiya. Yanayi na 3: Wani ɗanꞌuwa ya yi fushi sosai saꞌad da ya ji cewa wani ɗanꞌuwa ya halarci janaꞌiza a coci. Ɗanꞌuwan yana ganin hakan bai dace ba, domin a dā shi memban wani coci ne kuma ba ya son wani abu ya sake haɗa shi da wani coci.a
7 Yanayi na 4: Wani ɗanꞌuwa yana ganin bai dace ꞌyanꞌuwa maza su riƙa barin gemu ba, kuma bai dace mata su sa wando zuwa taro ko waꞌazi ba. Yana da irin wannan raꞌayin domin a lokacin da yake tasowa, yawancin mutane suna ganin yin hakan bai dace ba. Duk da cewa ɗanꞌuwan ya san wasu canje-canje da ƙungiyarmu ta yi kwanan nan game da waɗannan batutuwan, ya ci-gaba da gaya wa ꞌyanꞌuwa cewa bai kamata maza su bar gemu ba, kuma bai kamata mata su sa wando zuwa ayyukan ibada ba. Yanayi na 5: Saꞌad da wani dattijo ya ji cewa wani matashi a ikilisiyarsu yana son ya je ya samu ƙarin ilimi, sai ya yi ƙoƙarin ya sa matashin da iyayensa su canja raꞌayinsu. Yana yin hakan ne domin ya san wani ɗanꞌuwa da ya je samun ƙarin ilimi kuma ya daina bauta wa Jehobah.
8. (a) Wane yanayi ne zai iya sa iyaye su soma shariꞌanta wasu iyaye? (b) Mene ne zai iya faruwa idan muka soma tunanin da bai dace ba game da shawarwarin da ꞌyanꞌuwa a ikilisiya suke yankewa?
8 Bari mu yi laꞌakari da wani yanayi da iyaye za su iya samun kansu a ciki. Yanayi na 6: A ce a matsayinku na iyaye kun yi iya ƙoƙarinku wajen taimaka wa yaranku su ƙaunaci Jehobah kuma su riƙa yin abubuwan da za su faranta masa rai. (Afis. 6:4) Sai kuka ga kamar wasu iyaye suna ba wa yaransu damar yin wasu abubuwa. Alal misali, suna barin yaransu su yi dare a waje, su riƙa buga wasu wasannin bidiyo da ba na faɗa ba, ko kuma sun saya wa yaransu waya tun suna nan ƙanana. Mai yiwuwa, hakan ya sa yaranku sun soma ganin kamar kuna taƙura musu, kuma suka soma gwada yadda kuke bi da su da yadda iyayen nan suke bi da yaransu. Irin yanayin nan zai iya sa ku soma ganin cewa abin da iyayen nan suke yi bai dace ba. Gaskiyar ita ce, idan wasu suka yanke wata shawara da ta yi dabam da raꞌayinmu, hakan zai iya sa mu yi fushi kuma mu soma shariꞌanta su. Alal misali, za mu iya gani kamar yadda mutum yake kashe kuɗinsa, ko yawan tafiye-tafiyen da yake yi don shaƙatawa, ko kuma irin nishaɗin da yake yi ba su dace ba. Amma ko da mene ne raꞌayinmu, ya kamata mu tuna cewa, abin da ya fi muhimmanci shi ne samun zaman lafiya a ikilisiya, ba raꞌayinmu ba.
9. Mene ne dukanmu muke so mu yi, kuma wane abu ne ya kamata mu guje wa? (Ka kuma duba hoton.)
9 A matsayinmu na Kristoci, za mu iya yanke shawarwarin da suka bambanta da na wasu ꞌyanꞌuwa. Hakan ba ya nufin cewa namu ne daidai, ko kuma nasu ne daidai ba. (Rom. 14:5) Ko da yake Littafi Mai Tsarki ya ce, “bari tunaninku ya zama ɗaya” idan ya zo ga batun bin ƙaꞌidodin Jehobah, hakan ba ya nufin cewa tunanin mu zai zo ɗaya a kome da kome ba. (2 Kor. 13:11) Za mu iya kwatanta hakan da shawarwarin da muke yanke wa idan muna so mu je wani wuri. A yawancin lokuta, akan samu hanyoyi dabam-dabam da za su iya kai mu inda muke so mu je. Mukan zaɓi hanyar da muka fi so da kuma hanyar da ta dace da yanayinmu. Haka ma, ko da yake shawarwarin da muka yanke za su iya yin dabam da na sauran ꞌyanꞌuwa, burinmu shi ne mu yanke shawarar da za ta sa Jehobah farin ciki. Saboda haka, ba zai dace mu shariꞌanta mutane a kan shawarwarin da suka yanke ba.—Mat. 7:1; 1 Tas. 4:11.
Idan muna so mu je wani wuri mukan zaɓi hanyar da muka fi so. Haka ma, bayin Jehobah suna iya yanke shawarwarin da suka bambanta da na juna (Ka duba sakin layi na 9)
DALILIN DA YA SA ZA MU DARAJA SHAWARWARIN DA WASU SUKA YANKE
10. Bisa ga Yakub 4:12, wane iko ne ba mu da shi, kuma me ya sa?
10 Littafi Mai Tsarki ya ba mu dalilai da yawa da za su sa mu riƙa daraja shawarwarin da wasu suka yanke. Ga wasu daga cikinsu. Ba mu da ikon gaya wa mutane abin da za su yi a kan abin da Littafi Mai Tsarki bai ba da wata doka kai tsaye ba. (Karanta Yakub 4:12.) Jehobah ne kaɗai ya cancanta kuma yana da ikon gaya mana abubuwan da ya kamata mu yi. Dukanmu za mu tsaya a gaban kujerar shariꞌa na Allah wanda zai yi mana shariꞌa. (Rom. 14:10) Saboda haka, ba mu da ikon shariꞌanta wasu idan suka yanke shawarar da ta yi dabam da namu.b
11. Me za mu yi da zai sa a ci-gaba da samun zaman lafiya da haɗin kai a ikilisiya? (Ka kuma duba hoton.)
11 Jehobah yana son bayinsa su zama da haɗin kai, ba wai su zama iri ɗaya ba. Abubuwan da Jehobah ya halitta sun nuna cewa, yana son abubuwa su kasance dabam-dabam, ba iri ɗaya ba! Alal misali, idan ka tsinka ganyaye biyu daga bishiya ɗaya za ka ga cewa sun bambanta. Ban da haka ma, a cikin fiye da mutane biliyan takwas da ke rayuwa a duniya, babu mutane biyu da kamaninsu da tunaninsu iri ɗaya ne. Jehobah ya halicce mu yadda za mu yi dabam da sauran mutane. Amma yana so mu kasance da haɗin kai. Saboda haka, idan wasu suna yin wani abu dabam da yadda muke yi, kada mu yi fushi da su. Abin da ya fi muhimmanci shi ne a samu zaman lafiya da haɗin kai a ikilisiya, ba sa wasu su bi raꞌayinmu ba.—Rom. 14:19.
Jehobah ya halicce mu dabam-dabam, amma yana so mu kasance da haɗin kai (Ka duba sakin layi na 11)
YADDA ZA MU NUNA CEWA MUNA DARAJA SHAWARWARIN DA WASU SUKA YANKE
12-13. Me ya kamata mu tuna idan muna ganin kamar wani yana so ya yi abin da Littafi Mai Tsarki ya haramta? (Galatiyawa 6:1; ka kuma duba akwatin nan “Idan Kana Ganin Shawarar da Wani Ya Yanke Ba Daidai Ba.”)
12 Saꞌad da wasu suka yanke shawara a kan abin da Littafi Mai Tsarki bai ba da wata doka kai tsaye ba. Zai dace kowannenmu ya tambayi kansa, ‘Shin mutumin yana ƙoƙarin yin abin da Littafi Mai Tsarki ya haramta ne, ko kuma yadda yake yin abin ne bai gamshe ni ba?’ Idan mutumin yana yin wani abu ne da Littafi Mai Tsarki ya haramta, zai dace ka tambayi kanka, ‘Ni ne ya kamata in yi masa magana game da wannan batun, ko kuma wani kamar dattijo ne ya kamata ya yi masa magana?’ Idan kana ganin za ka iya yi wa mutumin magana game da batun, ka yi hakan cikin sauƙin kai. (Karanta Galatiyawa 6:1.) Amma a yawancin lokuta, zai iya yiwuwa ba laifi ne mutumin yake yi ba. Yana yin abinsa ne a hanyar da ta yi dabam da yadda muka saba yi. Idan haka ne, zai dace mu tuna cewa, mutumin yana da ꞌyancin yanke wa kansa shawarwari. Kada mu shariꞌanta shi, ko mu soma yin maganganun da ba su dace ba game da shawarar da ya yanke.—Rom. 14:2-4.
13 Bari mu yi laꞌakari da wani misali: A ce kai da abokinka kun je sayan abinci, za ka tilasta masa ya ci irin abincin da ka saya? Aꞌa. Za ka bar shi ya ci wanda yake so. Ko da ba ka son irin abincin da yake so, ba zai dame ka ba don shi ne zai ci kayansa. Haka ma, za mu nuna cewa muna daraja mutane ta wajen ba su dama su zaɓi abin da suke so, ba tare da tilasta musu su bi raꞌayinmu ba.
14. Idan kana so ka yanke wata shawara, me za ka yi don ꞌyanꞌuwa su ci-gaba da kasancewa da haɗin kai? (1 Korintiyawa 8:12, 13)
14 Saꞌad da kake so ka yanke shawara a kan abin da Littafi Mai Tsarki bai ba da wata doka kai tsaye ba. Za ka iya sa ꞌyanꞌuwa su ci-gaba da zama da haɗin kai idan ka yi iya ƙoƙarinka wajen guje wa duk wani abin da zai sa su ji wani iri. (Karanta 1 Korintiyawa 8:12, 13.) A wasu lokuta, za ka iya sanin cewa shawarar da kake so ka yanke ba laifi ba ne. Amma shin zai dace ka yanke shawarar idan ka san cewa shawarar za ta iya sa wasu su ji wani iri ko ta ɓata musu rai?c (1 Kor. 10:23, 24) Maimakon ka ci-gaba da yin abin da ka fi so a irin wannan yanayin, zai dace ka yi tunani a kan yadda wasu za su ji. (Rom. 15:1) Ko da yake an ambata cewa, muna bukatar mu daraja shawarwarin da mutane suka yanke, kuma su ma suna bukatar su yi hakan. Amma wajibi ne mu riƙa tuna da abin da ke Romawa 12:18, da ta ce: “Ku yi iya ƙoƙarinku in zai yiwu, ku yi abin da zai sa ku yi zaman salama da kowa.” Saboda haka, muna bukatar mu yi duk abin da za mu iya yi don mu zauna lafiya da mutane, kuma mu guje wa duk wani abin da zai ɓata musu rai.
15. Ta yaya dattawa za su taimaka a ci-gaba da kasancewa da haɗin kai a ikilisiya? (1 Korintiyawa 4:6)
15 Dattawa suna daraja shawarwarin da ꞌyanꞌuwa suka yanke. Idan dattawa ba su kafa dokoki a kan abubuwan da ꞌyanꞌuwa suna da ikon zaɓan abin da za su yi, kuma ba su yi “fiye da abubuwan da aka rubuta” a Littafi Mai Tsarki ba, hakan zai sa a ci-gaba da zama da haɗin kai a ikilisiya. (Karanta 1 Korintiyawa 4:6.) Dattawa kuma suna bukatar su riƙa faɗan abubuwan da suka jitu da abin da aka rubuta a littattafanmu. Ƙari ga haka, idan wani ɗanꞌuwa ko ꞌyarꞌuwa ta nemi shawara daga wurin dattawa, zai dace su yi iya ƙoƙarinsu don kada su faɗa raꞌayinsu. A maimakon haka, su yi amfani da abin da ke Kalmar Allah.—Isha. 48:17, 18.
16. Ta yaya kowane dattijo zai nuna cewa yana daraja shawarar da dattawa suka yanke?
16 Kowane dattijo yana bukatar ya daraja shawarar da sauran dattawa suka yanke. Bayan dattawa sun yi adduꞌa, kuma suka bincika abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa, sukan yanke shawara tare. Kowane dattijo yana bukatar ya daraja kuma ya goyi bayan shawarar da aka yanke ko da hakan ya yi dabam da abin da yake so. (Afis. 5:17) Ƙari ga haka, kowane dattijo yana bukatar ya bi umurnin da ke Littafi Mai Tsarki da kuma littattafanmu ba tare da sa umurnin ya jitu da raꞌayinsa ba. Alal misali, ba zai dace dattijo ya ɗauki layi ɗaya daga wani littafinmu don ya nuna cewa abin da yake faɗa daidai ne ba tare da bincika sauran bayanan da aka bayar a littafin ba.
17. Ta yaya za mu amfana idan muna daraja zaɓin da ꞌyanꞌuwa a ikilisiya suka yi?
17 Kamar yadda muka tattauna a wannan talifin, dukanmu mun bambanta da juna. Kowannenmu yana da raꞌayinsa da kuma abin da yake so. Hakan ba laifi ba ne! Da yake mun fito daga wurare dabam-dabam kuma muna da halaye dabam-dabam, hakan yana sa muna marmarin kasancewa da juna. Saboda haka, kada mu bar bambanci ya kawo saɓani tsakaninmu. A maimakon haka, mu riƙa daraja shawarwarin da wasu suka yanke. Idan muka yi iya ƙoƙarinmu wajen yin hakan, za mu yi farin ciki, kuma za a samu zaman lafiya da haɗin kai a ikilisiya.—Zab. 133:1; Mat. 5:9.
WAƘA TA 89 Mu Ji, Mu Yi Biyayya Don Mu Sami Albarka
a Kafin Krista ya yanke shawarar zuwa janaꞌiza ko bikin aure a wani wurin ibada, ya kamata ya yi tunani a kan wasu abubuwa. Ka duba akwatin da ke sakin layi na 17 na talifin nan “Yadda Za Mu Taimaka wa Danginmu da Ba Sa Bauta wa Jehobah” a Hasumiyar Tsaro ta Fabrairu, 2026.
b A wasu lokuta, dattawa suna bukatar su yi wa wanda ya yi zunubi mai tsanani shariꞌa. Amma ya kamata su tuna cewa Jehobah yana son su yi hakan bisa ga abin da ke cikin Kalmarsa, ba bisa ga raꞌayinsu ba.—Ka duba 2 Tarihi 19:6.
c Don samun wasu misalai, ka duba darasi na 35 batu na 5 na littafin nan Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada!