Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w26 Mayu p. 32
  • Ka Sa Bautar Jehobah Farko Kamar Yadda Manayen Ya Yi

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Sa Bautar Jehobah Farko Kamar Yadda Manayen Ya Yi
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2026
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Ci gaba da Yin Kwazo a Wannan Kwanaki na Karshe
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2018
  • Ka Tsai da Shawara Mai Kyau Game da Samun Ƙarin Ilimi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2026
  • Ta Yaya ‘Za Ka Sa Hanyarka ta Yi Nasara’?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Iyaye, Wace Irin Rayuwa Ce Kuke Son Yaranku Su Yi A Nan Gaba?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2026
w26 Mayu p. 32

LABARIN WANI DAGA LITTAFI MAI TSARKI

Ka Sa Bautar Jehobah Farko Kamar Yadda Manayen Ya Yi

Manayen yana ɗaya daga cikin waɗanda suka yi ja-goranci a ikilisiyar Antakiya a ƙarni na farko. Manayen ya yi “karatu tare da Hirudus mai mulkin yanki.” (A. M. 13:1) Saboda haka, Manayen ya yi karatu sosai, kuma mai yiwuwa ya yi girma a iyalin da suke da arziki.

Duk da haka, Manayen ya zama Krista kuma ya taimaka a ikilisiya. Bai yi amfani da karatunsa don ya amfani kansa ba. A maimakon haka, ya yi aiki tuƙuru don ya taimaka a ikilisiya.

Labarin Manayen ya nuna mana cewa, bauta wa Jehobah ne ya fi muhimmanci fiye da neman suna da kayan duniya. Kamar Manayen, mu ma zai dace mu sa ayyukan ibada farko a rayuwarmu fiye da neman suna da kuma kayan duniya. (Mat. 6:33) Ƙari ga haka, ko da muna ganin cewa yin karatu yana da kyau, zai dace mu zaɓi “abin da ya fi kyau,” kuma kada mu bar neman abin duniya ya shafi bautarmu ga Jehobah.—Filib. 1:​9, 10.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba