27 GA YULI–2 GA AGUSTA, 2026
WAƘA TA 56 Ka Riƙe Gaskiya
Ka Kusaci Jehobah Saꞌad da Kake Samun Ƙarin Ilimi
“Duk inda ci-gaban da muka samu ya kai, bari mu ci-gaba da bin wannan hanyar rayuwa.”—FILIB. 3:16.
ABIN DA ZA MU KOYA
Za mu ga ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki guda huɗu da za su taimaka wa mutum idan ya yanke shawara cewa zai samu ƙarin ilimi.
1-2. (a) Idan ka yanke shawarar samun ƙarin ilimi, mene ne kake bukatar ka ci-gaba da yi? (b) Mene ne ake nufi da “ci-gaba da bin wannan hanyar rayuwa”? (Filibiyawa 3:16)
WASU Shaidun Jehobah sun yanke shawarar samun ƙarin ilimi bayan sun gama makarantar sakandare. Suna ganin kamar idan sun nemi ƙarin ilimi, hakan zai sa su sami aikin da zai ba su isasshen kuɗin biyan bukatunsu, kuma su iya bauta wa Jehobah. Saboda haka, idan ka riga ka yanke shawarar samun ƙarin ilimi, mene ne zai taimaka maka ka ci-gaba da kusantar Jehobah? (Yak. 4:8a) Babu shakka, a lokacin da kake makarantar sakandare, ka fuskanci wasu matsalolin da suka sa ya yi maka wuya ka riƙe amincinka ga Jehobah. Don haka, zai dace ka “ci-gaba da bin wannan hanyar rayuwa” wato ka ci-gaba da riƙe amincinka ga Jehobah, kamar yadda ka yi a lokacin da kake makaranta sakandare.—Karanta Filibiyawa 3:16.
2 Furucin Girkanci da aka fassara zuwa “ci-gaba da bin wannan hanyar rayuwa” yana sa mutane su yi tunanin sojojin da suke macin ba tare da tsayawa ko juyawa ba. Idan ka riga ka yanke shawarar samun ƙarin ilimi, kana bukatar ka yi kamar sojojin nan, wato ka ci-gaba da tafiya tare da ꞌyanꞌuwa a ikilisiya ba gudu ba ja da baya ta wajen yin ayyukan ibada. A talifin nan, za mu tattauna ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki guda huɗu da za su taimaka maka. Babu shakka, ka riga ka san waɗannan ƙaꞌidodin. Sun taɓa taimaka maka ka yanke shawarwari masu su kyau a rayuwarka, kuma za su ci-gaba da taimaka maka yayin da kake samun ƙarin ilimin, da kuma bayan ka gama.
KA CI-GABA DA SA ƘWAZO A AYYUKAN IBADA
3. Saꞌad da ka soma samun ƙarin ilimi, wace matsala ce za ka iya fuskanta?
3 Matsalar. Saꞌad da ka soma samun ƙarin ilimi, za ka ga cewa abubuwan da kake yi kowace rana sun ƙaru sosai. Babu shakka za ka so ka yi nasara a karatun da kake yi. Amma hakan zai iya sa ka sa ayyukan makaranta a kan gaba fiye da na ibada. Wataƙila har ka rage zuwa taro, da waꞌazi, da karatun Littafi Mai Tsarki, da kuma yin adduꞌa.—R. Yar. 2:4.
4. Mene ne ake nufi da “yin ayyuka da yawa a hidimar Ubangiji”? (1 Korintiyawa 15:58)
4 Karanta 1 Korintiyawa 15:58. Kamar yadda mai tuƙa keke yake bukatar ya ci-gaba da tuƙawa idan yana son keken ya ci-gaba da tafiya, haka ma kake bukatar ka ci-gaba da sa ƙwazo a ayyukan ibada idan kana so ka daɗa kusantar Jehobah. Littafi Mai Tsarki ya ce mu riƙa “yin ayyuka da yawa a hidimar Ubangiji.” ‘Da yawa’ da aka ambata a ayar nan, ba ya nufin yawan lokacin da muke ɗaukawa wajen yin ayyukan ibada kawai. Amma yana da kyau mu san dalilin da ya sa muke yin su, kuma mu yi su domin su ne abu mafi muhimmanci a gare mu. Ka tuna cewa bauta wa Jehobah ne ya fi muhimmanci a rayuwa ba ƙarin ilimi ba. (Mat. 22:37) Wata matashiya mai suna Samantha ta ce: “Kafin in fara samun ƙarin ilimi, na yanke shawara cewa idan ayyukan makaranta za su shafi ayyukan ibadata, zan bar makarantar.”
5. Me zai taimaka maka ka ci-gaba da sa ƙwazo a hidimarka ga Jehobah?
5 Abin da za ka iya yi kafin ka soma samun ƙarin ilimi. Ka tabbata cewa kana sa ibadarka farko a rayuwa. Ka tambayi kanka cewa: ‘Mene ne zan yi don in riƙa shirya da kuma halartar taro, da fita waꞌazi, da kuma karanta Littafi Mai Tsarki?’ (Yosh. 1:8; Mat. 28:19, 20; Ibran. 10:25) Za ka kuma iya tambayar kanka cewa: A lokacin da nake makaranta a dā, mene ne na yi don in iya yin abubuwan nan? Idan kana ganin akwai abin da ya kamata ka yi da ba ka yi ba, mene ne za ka iya yi yanzu don ka yi abin da ya dace? Ka ƙudura niyyar ƙara ƙwazo a hidimarka ga Jehobah. Ka yi iya ƙoƙarinka a makaranta, amma kar ka bar karatun ya shafi ibadarka.a—Mat. 6:24.
6. Waɗanne tambayoyi ne za ka iya yi ma kanka don ka san ko kana sa hidimar Jehobah farko a rayuwa? (Ka kuma duba hoton.)
6 Yayin da kake makarantar, zai dace ka riƙa bincika kanka, ko da sau ɗaya ne a wata. Ka tambayi kanka cewa: ‘Shin, ina sa ayyukan ibada a kan gaba a rayuwata? Ko ina yawan fasa taro ko zuwa latti? Ina yawan tunani game da ayyukan makaranta saꞌad da ake taro? Na fi son halartar taro ta naꞌura ne kawai maimakon in je Majamiꞌar Mulki?’ Za ka kuma iya tambayar kanka cewa: ‘Shin, yadda nake adduꞌa da kuma karatun Littafi Mai Tsarki ya ragu? Ina fita waꞌazi ne kawai don ꞌyanꞌuwa su ga cewa na fita waꞌazi, kuma ina yin hakan cikin hanzari?’ Idan ka ga cewa kana yin ko ɗaya daga cikin abubuwan nan, wajibi ne ka yi canje-canje. Kada ka bar ayyukan makaranta su hana ka sa hidimar Jehobah farko a rayuwa.
Kada ka bar samun ƙarin ilimi ya hana ka sa ayyukan ibada farko a rayuwa (Ka duba sakin layi na 6)
KADA KA BARI A SA KA YI SHAKKAR KOYARWAR LITTAFI MAI TSARKI
7. Ta yaya samun ƙarin ilimi zai iya shafan yadda muke tunani?
7 Matsalar. Irin abin da kake karantawa a makaranta, zai sa a wasu lokuta a koyar da kai abubuwan da ba su jitu da Littafi Mai Tsarki ba. Irin koyarwar nan ne Littafi Mai Tsarki ya kira “ilimin duniyar nan da kuma ilimin ruɗu na banza.” Alal misali, za a iya koya maka cewa babu Allah ko kuma ba halittar mutane aka yi ba. (Kol. 2:8) Ƙari ga haka, wasu malamai za su iya gaya maka cewa kana bukatar ka dogara ga iyawarka don ka yi nasara a rayuwa. Wani ɗanꞌuwa ya ce: “Ba kawai sabbin abubuwa game da aikin da za mu yi ake koya mana ba, amma har da yadda za mu riƙa yin tunani, kuma hakan ya yi dabam da raꞌayin Jehobah. Alal misali, an gaya mana cewa, don mu yi farin ciki a rayuwa, dole ne mu dogara ga iyawarmu. Hakan ya sa na soma tunani cewa ba na bukatar taimakon Jehobah don in yi farin ciki a rayuwa. Wannan ya sa ya ƙara min wuya in dogara ga Jehobah.”
8. Me ya sa yake da muhimmanci ka riƙa yin “kome cikin hankali”? (Karin Magana 5:1, 2)
8 Karanta Karin Magana 5:1, 2. Littafi Mai Tsarki ya ce ya kamata ka riƙa yin “kome cikin hankali,” domin Shaiɗan da duniyar nan suna iya ƙoƙarinsu su ga sun gurɓata tunaninmu. (1 Bit. 5:8) Raꞌayin mutane game da ɗabiꞌa, da yadda abubuwa suka soma wanzuwa, da kuma bayanai game wanzuwar Allah, za su iya sa mu soma shakkar abubuwan da Jehobah ya koya mana a Littafi Mai Tsarki. Malaman makarantu sukan yi ƙoƙari su nuna cewa raꞌayoyin da suke koyarwa ne suka fi kyau. Amma gaskiyar ita ce, irin raꞌayoyin nan, “wawanci ne a wurin Allah.”—1 Kor. 3:18-20.
9. Me za ka iya yi don kada ka bar mutane su sa ka yi shakkar abin da ka san cewa gaskiya ne?
9 Abin da za ka iya yi kafin ka soma samun ƙarin ilimi. Ka yi ƙoƙari ka tabbatar wa kanka cewa abin da ke Littafi Mai Tsarki gaskiya ne kafin ka soma samun ƙarin ilimi. Za ka iya yin hakan ta wajen yi wa kanka tambayoyi kamar: ‘Me ya sa na yi imani da Allah? Ta yaya na san cewa Littafi Mai Tsarki Kalmarsa ce? Me ya tabbatar mini cewa bin ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki ne ya fi, maimakon bin raꞌayin mutane?’ Za ka kuma iya tunani a kan lokacin da kake makaranta a dā. Sai ka tambayi kanka: Shin, na taɓa yin shakkar wanzuwar Mahalicci saꞌad da sauran ꞌyan ajinmu suka ce sun yarda da koyarwar juyin halitta? Akwai lokacin da na so yin wasu abubuwa marasa kyau da ꞌyan ajinmu suke yi ne? Idan kana ganin akwai abin da ya kamata ka yi da ba ka yi ba, mene ne za ka iya yi yanzu don ka nuna cewa bin ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki ne ya fi? Ka yi iya ƙoƙarinka kada ka bar mutane su sa ka yi shakkar abin da ka san cewa gaskiya ne.—2 Tim. 2:16-18.b
10. Idan ka riga ka fara samun ƙarin ilimi, me za ka yi don ka tabbatar wa kanka cewa abubuwan da ka yi imani da su gaskiya ne?
10 Ko da ka riga ka fara samun ƙarin ilimi, zai dace ka riƙa tambayar kanka cewa: ‘Shin, na fara gani kamar abubuwa marar kyau da mutane suke yi ba laifi sosai? Ina iya gane koyarwar da ba ta jitu da raꞌayin Jehobah ba? Ina da tabbaci cewa Mulkin Allah ne kawai zai iya warware matsalolin duniyar nan?’ Don ka guji bin raꞌayin mutane, wajibi ne ka riƙa karanta Littafi Mai Tsarki, ka yi tunani a kan abin da ka karanta kuma ka aikata su. Yin hakan zai sa ba za ka yi shakkar duk abin da Littafi Mai Tsarki ya ce ba.—1 Tim. 4:15.
KA YI AMFANI DA LOKACINKA A HANYAR DA TA DACE
11. Saꞌad da kake samun ƙarin ilimi, me ya sa zai iya yi maka wuya ka yi amfani da lokacinka da kyau?
11 Matsalar. Samun ƙarin ilimi yana cin lokaci sosai, musamman a lokacin jarabawa. Idan ba ka yin amfani da lokacinka da kyau, hakan zai sa ka riƙa gajiya sosai. Shi ya sa yake da muhimmanci ka nemi lokaci ka kula da kanka, maimakon ka duƙufa yin ayyukan makaranta kawai.
12. Waɗanne abubuwa ne kake bukatar ka shirya lokaci don ka iya yi? (Afisawa 5:15, 16)
12 Karanta Afisawa 5:15, 16. A wasu lokuta, zai iya yi maka wuya ka yi amfani da lokacinka a hanyar da ta dace. Hakan zai iya faruwa don kana da abubuwa da yawa da kake yi. Alal misali, kana bukatar ka yi karatu sosai a makaranta, amma fiye da hakan ma kana bukatar lokaci don ka riƙa yin cuɗanya da iyalinka da kuma ꞌyanꞌuwa a ikilisiya. (Zab. 133:1; K. Mag. 18:1) Abu mafi muhimmanci shi ne ka riƙa yin abubuwan da za su sa ka kusaci Jehobah. (Mat. 6:33) Ban da haka ma, mai yiwuwa kana da ayyukan da kake yi a gidanku ko kuma kana da aikin albashin da kake yi. Ƙari ga haka, kana bukatar ka kula da kanka ta wajen hutawa da motsa jiki. (M. Wa. 4:6; 1 Tim. 4:8) Don ka iya yin abubuwan nan, wajibi ne ka yi amfani da lokacinka a hanyar da ta dace.
13. Mene ne za ka iya yi don ka yi amfani da lokacinka a hanyar da ta dace?
13 Abin da za ka iya yi kafin ka soma samun ƙarin ilimi. Littafi Mai Tsarki ya ce idan ka yi shiri da kyau, za ka yi nasara. (K. Mag. 21:5) Don haka, kafin ka soma samun ƙarin ilimi, zai dace ka tsara yadda za ka riƙa yin abubuwa. Za ka kuma iya yin tunani a kan lokacin da kake makaranta a dā, sai ka tambayi kanka: ‘Shin, na yi amfani da lokaci na da kyau wajen yin abubuwan da suke da muhimmanci?’ Idan kana ganin akwai abin da ya kamata ka yi da ba ka yi ba, mene ne za ka iya yi yanzu don ka yi abin da ya dace? Ka yi iya ƙoƙarinka ka tsara yadda za ka riƙa yin abubuwa don ka sami lokacin yin duk wani abin da kake so ka yi.
14. Waɗanne tambayoyi ne za su iya taimaka maka ka bincika kanka?
14 Saꞌad da kake samun ƙarin ilimi, zai dace ka riƙa tambayar kanka cewa: ‘Shin, abubuwan da nake yi suna ba ni damar yin hutu ko motsa jiki? Ina samun lokacin yin cuɗanya da ꞌyanꞌuwa a ikilisiya? Zan iya gama ayyukan makaranta da nake da su a kan lokaci? Idan ba ka yin hakan, mene ne dalilin? Kana ganin don ba ka yin amfani da lokacinka a hanyar da ta dace ne? Shin, danginka da abokanka suna ganin kana bukatar ka yi wasu canje-canje?’ Idan kana ganin kana bukatar ka yi wasu canje-canje ko ka yi gyara a kan yadda kake yin abubuwa, ka ɗauki mataki nan da nan. Za ka iya nemi shawara daga waɗanda suke shirya lokacinsu da kyau.—K. Mag. 11:14.
KA CI-GABA DA YIN “TAFIYA TARE DA MASU HIKIMA”
15. Saꞌad da kake samun ƙarin ilimi, wace matsala ce za ka iya fuskanta?
15 Matsalar. Saꞌad da kake samun ƙarin ilimi, wasu ꞌyan ajinku za su iya gayyatar ka ku yi abubuwa tare. Mai yiwuwa za ka so ka bi su. Wataƙila don su tsararka ne kuma don kuna yawan kasancewa tare a aji. Mai yiwuwa kana ji kamar kuna fahimtar juna fiye da wasu ꞌyanꞌuwa a ikilisiya. Amma zai dace ka yi hattara. Ko da yake kuna aji ɗaya, ƙaꞌidodin da kuke bi ba ɗaya ba ne. Kuma idan kana yawan cuɗanya da su, za ka soma kasancewa da irin raꞌayinsu. (1 Kor. 15:33) Wani ɗanꞌuwa mai suna Michael da ya yi shekaru huɗu yana wani makarantar koyar da ilimin wutar lantarki, ya ce: “A kowane mako, nakan yi fiye da awoyi 40 tare da mutanen da muke aiki. Mutanen nan suna da raꞌayin da bai dace ba game da ꞌyan mata, waƙoƙin da suke ji ba masu kyau ba ne, kuma suna maganganun banza. A sannu a hankali na soma gani kamar abubuwan da suke yi ba laifi ba ne sosai.”
16. Mene ne yin “tafiya tare da masu hikima” yake nufi? (Karin Magana 13:20)
16 Karanta Karin Magana 13:20. Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa yin cuɗanya da abokan banza zai iya jawo mana illa. Amma “wanda ya yi tafiya tare da masu hikima zai kasance da hikima.” Darasin shi ne, mutanen da muke yin cuɗanya da su za su iya sa mu zama masu kirki ko marasa kirki. Don haka, bari ka ƙulla abota da waɗanda suke so ka yi farin ciki kuma suna ƙaunar Jehobah kamar yadda kake yi.—Zab. 101:6, 7; 119:63.
17. Mene ne za ka iya yi don ka guji abokan banza?
17 Abin da za ka iya yi kafin ka soma samun ƙarin ilimi. Ka yanke shawara a kan yawan lokacin da za ka riƙa kasancewa tare da ꞌyan ajinku. Wani Mashaidi mai suna Trenton ya ce: “Ina faraꞌa da ꞌyan ajinmu, amma ba na cuɗanya da su bayan an tashi makaranta. Su ꞌyan ajinmu ne kawai ba abokaina na kud da kud ba.” Mene ne za ka iya yi don ka guji ƙulla abota na kud da kud da su, da kuma yawan lokacin da kake cuɗanya da su? Don ka amsa wannan tambayar, za ka iya tambayar kanka cewa: ‘A lokacin da nake makaranta a dā, mene ne na yi don in rage cuɗanya da ꞌyan ajinmu? Idan kana ganin akwai abin da ya kamata ka yi da ba ka yi ba, mene ne za ka iya yi yanzu don ka yi abin da ya dace?’ Ka ƙudura niyyar ci-gaba da yin “tafiya tare da masu hikima,” kuma ka guji abokan banza.c
18. Waɗanne tambayoyi ne za ka iya yi ma kanka? (Ka kuma duba hoton.)
18 Zai dace ka riƙa tambayar kanka cewa: ‘Shin, na soma ƙulla abota na kud da kud da ꞌyan ajinmu? Na soma bin halinsu a yadda suke magana da kuma tunani? Yaya Jehobah yake ji game da dangantakata da ꞌyan ajinmu?’ (Zab. 1:1) Idan kana ganin kana bukatar ka yi wasu canje-canje, ka ɗauki mataki nan da nan. Ka tabbata cewa abokanka na kud da kud masu bauta wa Jehobah ne. Ƙari ga haka, kada ka yi jinkirin yi wa ꞌyan ajinku waꞌazi. Da yake sun san ka kuma kana aji ɗaya tare da su, hakan dama ce na yi musu waꞌazi game da Jehobah.
Kada ka yi jinkirin yi wa ꞌyan ajinku waꞌazi (Ka duba sakin layi na 18)d
KA SHIRYA DA KYAU
19. Ta yaya za ka yi shiri da kyau don ka shawo kan matsalolin da za ka fuskanta saꞌad da kake samun ƙarin ilimi? Ka ba da misali.
19 Alal misali mai hawan dutse yakan yi shiri da kyau kafin ya kama hanya. Ko da yake bai san irin matsalolin da zai fuskanta yayin da yake hawa ba, yana nan a shirye. Yakan saka kayan da ya dace da tafiyar, kuma ya san inda za shi. Hakazalika, za ka iya yin koyi da hakan saꞌad da kake samun ƙarin ilimi. Ka ci-gaba da ƙarfafa dangantakarka da Jehobah, ka saka ‘kayan kāriya na yaƙi wanda Allah ya bayar,’ kuma kada ka manta da dalilin da ya sa kake samun ƙarin ilimi. Maƙasudinka shi ne ka faranta wa Jehobah rai, maimakon tara kayan duniya ko kuma yin suna.—Afis. 6:11-13; 1 Kor. 9:26, 27; 10:31.
20. Ta yaya za ka ci-gaba da gwada kanka don ka san ko kana cikin bangaskiya?
20 Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa: “Ku ci-gaba da gwada kanku don ku san ko kuna cikin bangaskiya; ku ci-gaba da gwada kanku don ku san ko ku waɗanne irin mutane ne.” (2 Kor. 13:5) Za ka iya yin hakan yayin da kake samun ƙarin ilimi. Ta yaya za ka iya yin haka? Ta wajen yi ma kanka irin tambayoyi kamar: Shin, na sa ayyukan ibada farko a rayuwata? Ina guje wa raꞌayoyin mutanen duniyar nan don kada su shafi yadda nake tunani? Ina amfani da lokacina da kyau a hanyar da ta dace? Ina ƙulla abota da ꞌyanꞌuwa a ikilisiya kuma ina guje wa abokan banza? Zai dace ka riƙa yi ma kanka tambayoyin nan, ko kana makaranta ko wurin aiki ko kuma wani wuri dabam. Ka ƙudura niyyar riƙe amincinka ko da wane irin yanayi ne kake ciki. Ka tabbata cewa yayin da kake iya ƙoƙarinka don ka kusaci Jehobah, zai albarkace ka.—K. Mag. 3:5, 6.
WAƘA TA 87 Ku Zo Mu Sami Ƙarfafa!
a Don samun shawarwari a kan yadda za ka ci-gaba da bauta wa Jehobah da ƙwazo, ka karanta talifin nan mai jigo “Matasa Ku Ci Gaba da Manyanta Bayan Kun Yi Baftisma” a Hasumiyar Tsaro ta Agusta, 2022.
b Don samun ƙarin bayani game da yadda za ka riƙa yin kome cikin hankali, ka karanta talifin nan “Kada Ka Bar ‘Hikimar Wannan Duniyar’ ta Yaudare Ka” a Hasumiyar Tsaro ta Mayu, 2019.
c Don samun ƙarin bayani game da yadda za ka ƙulla abota da mutanen kirki, ka karanta darasi na 48, mai jigo “Ka Zaɓi Abokan Kirki,” a littafin nan, Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada!
d BAYANI A KAN HOTO: Wata ꞌyarꞌuwa da take makarantar da ake koyar da yadda ake yin kitso tana yi wa wata ꞌyar ajinsu waꞌazi.