Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w26 Maris pp. 26-31
  • Za Ka Iya Yin Farin Ciki Ko da Ana Tsananta Maka

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Za Ka Iya Yin Farin Ciki Ko da Ana Tsananta Maka
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2026
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • DALILAN DA SUKA SA AKA TSANE MU
  • ZA MU IYA YIN FARIN CIKI KO DA AN TSANE MU
  • Kauna Tana Sa Mu Jimre Kiyayya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2021
  • Wasiƙa da Za Ta Taimake Mu Mu Jimre har Karshe
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
  • Yadda Jehobah Yake Taimaka Mana Mu Jimre
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • “Ku Zaɓi Wanda Za Ku Bauta Masa”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2026
w26 Maris pp. 26-31

1-7 GA YUNI, 2026

WAƘA TA 111 Dalilan da Suke Sa Mu Murna

Za Ka Iya Yin Farin Ciki Ko da Ana Tsananta Maka

“Ku masu farin ciki a duk lokacin da mutane suka tsane ku.”—LUKA 6:22.

ABIN DA ZA MU KOYA

Za mu ga dalilan da suka sa za mu ci-gaba da yin farin ciki ko da mutane sun tsane mu don muna bauta wa Jehobah.

1. Mene ne Yesu ya faɗa, kuma me ya sa abin da ya faɗa yake da ban mamaki?

A HUƊUBAR da Yesu ya yi a kan dutse, ya ce: “Ku masu farin ciki a duk lokacin da mutane suka tsane ku.” (Luka 6:22) Babu shakka, wannan abin da Yesu ya faɗa ya sa mutane mamaki. Domin babu wanda yake farin ciki idan aka tsane shi. Me ya sa Yesu ya yi furucin nan? Wannan tambaya ce da ya kamata mu yi tunani a kai. Domin a yau, mutane da yawa sun tsani mabiyan Yesu. Za mu tattauna dalilin da ya sa aka tsane mu, da kuma dalilin da ya sa za mu ci-gaba da yin farin ciki ko da mutane sun tsane mu.

DALILAN DA SUKA SA AKA TSANE MU

2-3. Waye ne yake sa a tsananta wa bayin Allah, kuma ta yaya sanin hakan zai sa mu ji game da masu tsananta mana? (Yohanna 16:​2, 3)

2 An tsane mu domin muna bauta wa Jehobah. Yesu ya ce waɗanda suke tsananta wa mabiyansa har ma su kashe su ba su san shi ba, kuma “ba su san Uban” ba. (Karanta Yohanna 16:​2, 3.) Waye ne yake sa a tsananta wa bayin Allah? Shaiɗan ne. Shi ne “allah na wannan zamanin.” (2 Kor. 4:​3, 4) Yana iya ƙoƙarinsa don ya hana mutane sanin gaskiya game da Jehobah. Kuma yana sa a tsananta wa waɗanda suka san Allah kuma suna bauta masa. (Yoh. 8:​42-44) Ta yaya sanin hakan zai sa mu ji game da waɗanda suke tsananta mana? Idan muka fahimci cewa Shaiɗan ne yake ruɗinsu, hakan zai sa ba za mu tsane su ba.

3 Bari mu yi laꞌakari da labarin wani ɗanꞌuwa mai suna Pavel,a wanda yake zama a ƙasar da aka hana ayyukan ibadarmu. An kama shi, aka yi masa dukan tsiya, aka kuma ƙulle shi a kurkuku har tsawon watanni don ya ci-gaba da bauta wa Jehobah da aminci. Ɗanꞌuwan ya ce: “Na gano cewa Shaiɗan da aljannunsa ne suke iya ƙoƙarinsu su sa mu daina bauta wa Jehobah. Da alama yawancin masu yin aiki a kurkuku ba tsanan mu suka yi ba, aikinsu su ne kawai suke yi.” Wani ɗanꞌuwa a ƙasar Kuroshiya da iyayensa ba sa bauta wa Jehobah kuma suna tsananta masa, ya ce: “Na gano cewa Shaiɗan ne ainihin maƙiyin, ba iyaye na ba.”—Afis. 6:12.

4. Mene ne za mu iya koya daga labarin Yesu da Istifanus? (Ka kuma duba hoton.)

4 Ba ma tsanan waɗanda suke tsananta mana. Za mu ma iya yin adduꞌa a madadinsu. (Mat. 5:44) Abin da Yesu da kuma Istifanus suka yi ke nan. Saꞌad da sojojin Roma suka rataye Yesu a kan gungumen azaba, Yesu ya yi adduꞌa ya ce: “Uba ka gafarta musu.” (Luka 23:34) Yesu yana roƙan Jehobah ya gafarta wa sojojin da aka ce su kashe shi. Mai yiwuwa a wannan lokacin, Yesu ya yi roƙon ne kuma don jamaꞌar da suke ihu cewa a kashe shi. Yesu ya fahimci cewa waɗannan mutanen ba su san abin da suke yi ba. Abin da Istifanus ma ya yi ke nan. Ya yi adduꞌa ga Allah cewa ya gafarta wa mutanen da suke so su kashe shi. (A. M. 7:​58-60) Shin, Jehobah ya amsa adduꞌar Yesu da na Istifanus? Ƙwarai kuwa. Mutane da yawa da suka so a kashe Yesu sun tuba daga baya, sun ba da gaskiya ga Yesu, kuma sun yi baftisma. (A. M. 2:​36-41) Shawulu wanda ya goyi bayan a kashe Istifanus ya zama Krista daga baya, kuma ya yi nadamar abin da ya yi.—1 Tim. 1:13.

Wani ɗanꞌuwa a kurkuku da ciwo a fuskarsa yana adduꞌa kuma wani mai aiki a kurkukun yana tsaye a bakin ƙofa inda aka kulle shi.

Kamar yadda Yesu da Istifanus suka yi wa waɗanda suke tsananta musu adduꞌa, mu ma za mu iya yi wa waɗanda suke tsananta mana adduꞌa (Ka duba sakin layi na 4)


5. Mene ne muka koya daga labarin César?

5 Mu ma a yau, Jehobah yana amsa adduꞌoꞌin da muke yi a madadin waɗanda suke tsananta mana. Bari mu yi laꞌakari da labarin wani ɗanꞌuwa mai suna César wanda yake zama a ƙasar Venezuela. Mahaifinsa yana tsananta masa sosai domin shi Mashaidin Jehobah ne. César ya ce: “Mahaifiyata uwa ce ta gari. Duk da cewa tana sa bautar Jehobah farko a rayuwarta, ba ta taɓa rena mahaifinmu ba, kuma tana kula da shi sosai. Ta koya wa ni da ꞌyanꞌuwana yadda za mu riƙa girmama mahaifinmu, kuma mu yi masa biyayya. Sai dai in ya ce mu yi abin da Jehobah ba ya so, shi ne za mu ƙi. A kwana a tashi bayan ꞌyan shekaru, mahaifina ya canja raꞌayinsa. César ya ce: “Wata rana bayan da na yi adduꞌa da dukan zuciyata, sai na tambayi mahaifinmu ko zai so in yi nazarin Littafi Mai Tsarki da shi. Na yi farin ciki sosai da ya yarda in yi nazari da shi.” Da shigewar lokaci, mahaifin César ya yi baftisma. Ba dukan masu tsananta mana ne za su canja raꞌayinsu ba. Amma wasu sukan canja raꞌayinsu idan suka ga yadda muke girmama mutane ta wajen halayenmu masu kyau da kuma furucinmu. Muna farin ciki sosai idan suka yi hakan. Fatanmu shi ne, Jehobah “mai shariꞌar dukan duniya” zai taimaka musu su zo su koyi abubuwa game da shi.—Far. 18:25

6. Bisa ga Markus 13:​13, wane dalili ne kuma ya sa aka tsane mu?

6 An tsane mu domin muna daraja Yesu. Yesu ya ce za a tsani mabiyansa saboda sunansa. (Karanta Markus 13:13.) Mene ne sunan Yesu yake wakilta a nan? Yana wakiltar halayensa da kuma ikonsa na zama Sarkin Mulkin Allah. Mutanen da suka tsane mu sun zaɓi gwamnatocin ꞌyanꞌadam maimakon Yesu Kristi wanda Jehobah ya zaɓa. Tun daga shekara ta 1914 ne Yesu Kristi ya soma sarauta. Nan ba da daɗewa ba Yesu zai kawar da dukan gwamnatocin ꞌyanꞌadam.

7-8. Wane dalili ne kuma ya sa aka tsane mu? (Yohanna 15:​18-20) (Ka kuma duba hotunan.)

7 An tsane mu domin mun ƙi mu zama kamar mutanen duniyar nan. Yesu ya ce za a tsani mabiyansa domin su “ba na duniya ba ne.” (Karanta Yohanna 15:​18-20.) Kamar Kristoci a ƙarni na farko, muna guje wa halaye marasa kyau na mutanen duniyar nan. Saboda haka, ana yi wa ꞌyanꞌuwanmu da yawa baꞌa a makaranta, da kuma a wurin aikinsu. (1 Bit. 4:​3, 4) Abin farin ciki shi ne, wasu da suke tsananta mana sun canja raꞌayinsu kuma sun soma daraja mu.

8 Bari mu yi laꞌakari da labarin wani mai suna Ignacio daga Amirka ta Tsakiya. A makaranta, malaminsu ya yi ta yi masa baꞌa domin yana yin rayuwa yadda Jehobah yake so. Amma kafin Ignacio ya gama makarantar, malaminsu ya tambayi shi cewa, me ya taimaka masa ya riƙa bin ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki duk da cewa mutane da yawa suna yi masa baꞌa. Ignacio ya gaya masa cewa ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki suna kāre shi ne. Ignacio ya gayyaci malaminsu zuwa taron ikilisiya, kuma ya yi farin ciki sosai da ya ga malaminsu ya halarci taron. Yadda aka nuna wa malamin ƙauna a taron ya burge shi sosai, har ya ci-gaba da halartan taro. Da shigewar lokaci, an soma tsananta wa malamin, domin ya soma nazarin Littafi Mai Tsarki. Amma bai karaya ba, ya sami ci-gaba har ma ya yi baftisma.

Hotuna: Ana kwatanta abin da ya faru da Ignacio a makaranta. Na 1. Ya zauna shiru a aji yayin da malaminsu yana yi masa baꞌa a gaban ꞌyan ajinsu. Na 2. Daga baya, malamin yana sauraron Ignacio da kyau yayin da yake yi masa magana.

Ko da shekarunmu nawa ne, za mu iya kāre imaninmu da ƙarfin zuciya (Ka duba sakin layi na 8)b


9-10. (a) Wane bambanci ne kuma yake tsakanin Kristoci da mutanen duniya? (b) Ta yaya za mu yi koyi da manzo Bulus?

9 Mun yi dabam da sauran mutane a duniyar Shaiɗan domin ba ma yaƙi, kuma ba ma saka hannu a harkokin siyasa. (Yohanna 18:36) Muna bin abin da ke Romawa 13:1 ta wajen bin dokokin da gwamnati ta kafa. Amma a matsayinmu na Kristoci ba ma saka hannu a harkokin siyasa, ko mu yi takara ko kuma mu yi zaɓe. Me ya sa? Domin muna goyon bayan Jehobah da Mulkinsa wanda Yesu ne Sarkin. An jefa Shaidun Jehobah da yawa a kurkuku saboda imaninsu. Duk da hakan, ꞌyanꞌuwanmu maza da mata sun ci-gaba da yin waꞌazi. Sun yi koyi da manzo Bulus wanda ya yi shekaru a kurkuku. (A. M. 24:27; 28:​16, 30) Bulus ya ci-gaba da yin waꞌazi ga duk wanda ya saurare shi. Ya yi wa masu gadin kurkuku waꞌazi, da maꞌaikatan kotu, da gwamnoni, da sarakuna. Wataƙila har da maꞌaikatan sarkin Roma mai suna Nero.—A. M. 9:15.

10 Hakazalika, ꞌyanꞌuwanmu da aka ƙulle a kurkuku, su ma suna yin waꞌazi ga duk wanda ya saurare su, kamar su alƙalai, da maꞌaikatan gwamnati, da kuma masu gadin kurkuku. Wani ɗanꞌuwa da ya yi fiye da shekara shida a kurkuku don ya ƙi saka hannu a harkokin siyasa ya ce, bai ɗauki lokacin da ya yi kurkuku a matsayin horo ba. A maimakon haka, ya ɗauka a matsayin hidimar da Jehobah ya ba shi na neman masu zuciyar kirki. Muna farin ciki idan Jehobah ya yi amfani da mu wajen yi wa mutanen nan waꞌazi! (Kol. 4:3) Bari mu ga wasu dalilai kuma da suke sa mu farin ciki duk da cewa mutane sun tsane mu don muna bauta wa Jehobah.

ZA MU IYA YIN FARIN CIKI KO DA AN TSANE MU

11. Ta yaya tsanantawa za ta ƙarfafa bangaskiyarmu? Ka ba da misali.

11 Mun san cewa yadda mutane suka tsane mu yana cika annabcin Littafi Mai Tsarki ne. A annabci na farko da aka rubuta a Littafi Mai Tsarki, Jehobah ya ce Shaiɗan da magoyan bayansa za su tsani waɗanda suke ƙauna da kuma bauta wa Jehobah. (Far. 3:15) Sau da yawa Yesu ya ce za a tsani waɗanda suke bauta wa Jehobah. (Mat. 10:22; Mar. 13:​9-12; Luk. 6:​22, 23; Yoh. 15:20) Kuma wasu marubutan Littafi Mai Tsarki ma, sun faɗi hakan. (2 Tim. 3:12; Yak. 1:2; 1 Bit. 4:​12-14; Yahu. 3, 17-19) Saboda haka, ba ma mamaki idan ana tsananta mana. A maimako hakan, muna farin ciki domin annabcin Littafi Mai Tsarki ne yake cika. Wannan yana tabbatar mana da cewa, muna bauta wa Allah na gaskiya. Wata ꞌyarꞌuwa da take zama a ƙasar da aka hana ayyukan ibadarmu ta ce: “Saꞌad da na yi baftisma na san cewa a kwana a tashi za a tsananta mini. Saboda haka, ba na tsoro ko in yi mamaki saꞌad da nake fuskantar matsaloli.” Maigidanta yana ɗaya daga cikin waɗanda suke tsananta mata. Yana wulaƙanta ta, kuma ya ƙona Littafi Mai Tsarki da wasu littattafanta. Amma maimako ta ji tsoro ko kuma ta yi sanyin gwiwa, hakan ya ƙarfafa bangaskiyarta. (Ibran. 10:39) Ta ce: “An annabta cewa za a tsananta mana. Yadda nake fuskantar tsanantawa yana ƙara tabbatar mini cewa, wannan ne addini na gaskiya.”

12. Mene ne ya taimaka ma wani ɗanꞌuwa ya jimre tsanantawa?

12 Ko da yake mun san cewa za a tsananta mana, a wasu lokuta zai iya yi mana wuya mu jimre. Wani ɗanꞌuwa da aka taɓa jefa shi a kurkuku ya ce: “A wasu lokuta nakan yi baƙin ciki, kuma in yi kuka.” Mene ne ya taimaka wa ɗanꞌuwan nan? Ya ce: “Ina yawan yin adduꞌa. Idan na tashi da safe, nakan soma da adduꞌa. A duk lokacin da na fuskanci matsala kuma, nakan yi adduꞌa. A duk lokacin da wasu suka wulaƙanta ni kuma na ji haushi, nakan shiga ban ɗaki in yi adduꞌa.” Ban da haka ma, ɗanꞌuwanmu yakan yi tunani a kan bayin Allah masu aminci da suka jimre tsanantawa a dā da kuma a yau. Abin da ya taimaka masa ya jimre tsanantawar ke nan. Kuma ya sami kwanciyar hankali kamar yadda Yesu ya yi wa mabiyansa alkawari.—Yoh. 14:27; 16:33.

13. Mene ne zai taimaka mana mu jimre tsanantawa?

13 Ƙaunarmu ga Jehobah da kuma junanmu tana taimaka mana mu jimre tsanantawa. Yesu ya ci-gaba da ƙaunar Ubansa da dukan zuciyarsa. Kuma yana ƙaunar dukan abokansa. (Yoh. 13:1; 15:13) Idan mu ma muka ƙaunaci Jehobah da ꞌyanꞌuwanmu da dukan zuciyarmu, hakan zai taimaka mana mu jimre tsanantawa. Labarin manzo Bulus zai taimaka mana mu san yadda za mu yi hakan.

14. Me ya taimaka wa Bulus ya riƙe amincinsa duk da cewa ya san za a kashe shi?

14 Jim kaɗan kafin a kashe manzo Bulus, ya rubuta wa abokinsa Timoti wasiƙa cewa: “Ruhun da Allah ya ba mu bai mai da mu masu tsoro ba, a maimakon haka, ya mai da mu masu iko, da masu ƙauna.” (2 Tim. 1:7) Mene ne Bulus yake nufi? Bulus yana nufin cewa, idan muna ƙaunar Jehobah sosai, hakan zai taimaka mana mu jimre saꞌad da ake tsananta mana. (2 Tim. 1:8) Duk da cewa Bulus ya san za a iya kashe shi, ƙaunar da yake yi wa Jehobah ce ta taimaka masa ya kasance da ƙarfin zuciya kuma ya riƙe amincinsa.—A. M. 20:​22-24.

15. Ta yaya ꞌyanꞌuwanmu maza da mata suke nuna wa juna ƙauna a yau? (Ka kuma duba hoton.)

15 Babu shakka muna ƙaunar ꞌyanꞌuwanmu da suke riƙe amincinsu duk da tsanantawa. ꞌYanꞌuwa da yawa a yau suna nuna wa juna ƙauna har ma su sa rayukansu cikin haɗari, kamar yadda Biriskila da Akila suka yi wa manzo Bulus. (Rom. 16:​3, 4) Alal misali, a Rasha, ꞌyanꞌuwanmu da yawa sun je kotu don su ƙarfafa ꞌyanꞌuwan da hukuma ta kama. Wata ꞌyarꞌuwa da aka kama kuma aka kai ta kotu ta sami ƙarfafa sosai da ta ga ꞌyanꞌuwa da yawa sun zo kotun don su ba ta ƙarfin gwiwa. Ta yi mamaki sosai, har ta ɗan ɗau lokaci kafin ta soma magana. Babu shakka, ƙaunar da ꞌyanꞌuwan nan suka nuna mata shi ne abin da take bukata a wannan lokacin. Muna matukar farin ciki sanin cewa ꞌyanꞌuwanmu za su ci-gaba da ƙaunarmu duk da cewa wasu sun tsane mu!

Wasu mata biyu ꞌyanꞌsanda suna ƙoƙarin saka wata ꞌyarꞌuwa cikin motarsu. Wasu ꞌyanꞌuwa kuma a gefe suna tafa mata.

ꞌYanꞌuwanmu suna nuna wa juna ƙauna marar canjawa har a inda aka hana aikinmu ko aka sa mana taƙunƙumi (Ka duba sakin layi na 15)c


16. Me ya sa manzo Bitrus ya ce waɗanda ake tsananta musu don suna bauta wa Jehobah suna da dalilin yin farin ciki? (1 Bitrus 4:14)

16 Mun san cewa muna sa Jehobah farin ciki idan muka jimre tsanantawa. (Karanta 1 Bitrus 4:14.) Manzo Bitrus ya ce waɗanda suke jimre tsanantawa don suna bauta wa Jehobah suna da dalilin yin farin ciki. Me ya sa? Tsanantawa da ake mana yana nuna cewa ruhun Allah yana “tare da [mu].” Bitrus ya san yadda mutum yake ji idan ya yi abin da Jehobah yake so kuma ya jimre tsanantawa. Jim kaɗan bayan Fentakos na shekara ta 33 bayan haihuwar Yesu, an turo jamiꞌan tsaro na haikalin Yahudawa su je su kama Bitrus da sauran almajiran don suna waꞌazi. Amma Bitrus ya kāre imaninsu da ƙarfin zuciya. (A. M. 5:​24-29) Duk da cewa an yi musu bulala, shi da sauran almajiran ba su daina waꞌazi ba. A maimakon haka, sun yi farin ciki “domin sun cancanci a wulaƙanta su saboda sunan Yesu.” Mu ma za mu iya yin farin ciki idan ana tsananta mana.—A. M. 5:​40-42.

17. Mene ne Yesu ya gaya wa almajiransa da dare kafin a kashe shi?

17 Da dare kafin a kashe Yesu, ya gaya wa almajiransa cewa: “Duk wanda ya ƙaunace ni, Ubana ma zai ƙaunace shi, zan ƙaunace shi kuma.” (Yoh. 14:21) Muna ɗokin ganin lokacin da za mu bauta wa Jehobah ba tare da an tsananta mana ba! (2 Tas. 1:​6-8) Kafin lokacin, zai dace mu ci-gaba da tuna da dalilan da za su sa mu farin ciki idan ana tsananta mana.

MECE CE AMSARKA?

  • Me ya sa aka tsani mabiyan Yesu?

  • Ta yaya ƙaunar da ꞌyanꞌuwanmu suke nuna mana take taimaka mana mu jimre tsanantawa?

  • Ta yaya za mu iya yin farin ciki ko da an tsane mu?

WAƘA TA 149 Waƙar Nasara

a An canja wasu sunayen.

b BAYANI A KAN HOTUNA: Ana kwatanta yadda Ignacio ya yi wa malaminsa waꞌazi.

c BAYANI A KAN HOTO: Ana kwatanta yadda ꞌyanꞌuwa suke ƙarfafa wata ꞌyarꞌuwa saꞌad da ake kai ta kurkuku.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba