LABARIN WANI DAGA LITTAFI MAI TSARKI
Mu Kasance da Ƙarfin Zuciya da Kuma Aminci Kamar Benaya
Benaya soja ne mai ƙarfin zuciya da ya yi yaƙi a lokacin Sarki Dauda da kuma Sarki Sulemanu. Benaya ɗan firist ne, kuma yaƙi ba abu ne da Firistoci da Lawiyawa suka saba yi ba. Amma Benaya ya yi yaƙi, kuma ya kasance da ƙarfin zuciya. Alal misali, akwai lokacin da Benaya ya kashe zaki cikin wani rami, ya kuma kashe wani ƙaton mayaƙi da ke riƙe da mashi. Dauda ya amince da Benaya sosai har ya naɗa shi shugaban masu gadinsa.—2 Sam. 23:20-23.
A lokacin da Absalom da Adonijah suka yi tawaye, Benaya ya kasance da aminci ga Dauda. (2 Sam. 8:18; 15:18; 1 Sar. 1:8) Kuma a lokacin da Dauda ya tsufa sosai, Benaya ya ci-gaba da kasancewa da aminci ga Dauda har ya taimaka a naɗa Sulemanu Sarki. (1 Sar. 1:32-40) Benaya ya riƙe amincinsa ga Jehobah da kuma waɗanda Jehobah ya zaɓa su yi sarauta, duk da cewa wasu ba su yi hakan ba.
Mu ma muna bukatar ƙarfin zuciya don mu yi gāba da Shaiɗan da masu goyon bayansa. Ƙari ga haka, mu ƙuduri niyyar yin irin rayuwar da Jehobah yake so. (Afis. 6:11; 1 Bit. 5:8, 9) Zai dace mu ci-gaba da riƙe amincinmu ga Jehobah ko da wasu sun daina bauta masa. Idan mun yi hakan, za mu kasance da tabbaci cewa Jehobah zai yi mana albarka.—2 Sam. 22:26.