Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu
Yaushe ne alꞌummai za su ce an sami “zaman lafiya da salama”?
Kamar yadda muka gani a talifin Hasumiyar tsaroa na kwanan nan, Jehobah zai sa tunaninsa a zukatan “ƙahoni goma,” (dukan gwamnatocin duniya) nan ba da daɗewa ba, kuma hakan zai sa su ba wa “jar dabbar” wato Majalisar Ɗinkin Duniya ikonsu. Ana kuma kiran dabbar ‘siffar dabba.’ (R. Yar. 13:14, 15; 17:3, 16, 17) “Ƙahoni goma” tare da wannan dabbar da aka ba ta iko, za su haɗa hannu su kawar da addinan ƙarya a dukan faɗin duniya. Shin, alꞌumman duniya za su ce an sami “zaman lafiya da salama”b kafin a hallaka addinan ƙarya ko kuma bayan hakan?—1 Tas. 5:3.
Gaskiyar ita ce, ba mu san lokacin da za a ce an sami “zaman lafiya da salama” ba. Idan mun san kome da kome game da lokacin, ba za mu zama a faɗake ko kuma mu zama a shirye ba. Shi ya sa Yesu ya yi ta gargaɗin mabiyansa cewa, su “ci-gaba da yin tsaro.” (Mat. 24:42; 25:13; 26:41) Bari mu daɗa bincika annabcin da manzo Bulus ya yi a wasiƙar da ya rubuta wa Tasalonikawa.
Bulus ya ce: “Lokacin da mutane suke cewa, ‘muna zaman lafiya da salama’ sai kawai halaka za ta auko musu.” (1 Tas. 5:2, 3) A littattafanmu an saba cewa, za a ce an sami “zaman lafiya da salama” ne kafin a soma ƙunci mai girma. Kuma za a soma ƙunci mai girma da hallaka Babila Babba, wato dukan addinan ƙarya. Mun kuma bayyana cewa, idan aka ce an sami “zaman lafiya da salama,” lokacin ne za mu san cewa ana dab da soma ƙunci mai girma.
Amma bayan da aka yi nazari sosai a kan wannan ayar, an gano cewa, mai yiwuwa akwai wata hanya dabam da za a iya bayyana wannan batun. Wataƙila za a ce an sami “zaman lafiya da salama” ne bayan an hallaka addinan ƙarya. Me ya sa muka ce hakan? Ga wasu dalilai.
Ta yaya addinan ƙarya suke taka rawa a yaƙe-yaƙen da ake yi a duniya? Littafi Mai Tsarki ya ce: “A cikin Babila [“babbar karuwa,” ko Babila Babba] aka sami jinin . . . dukan waɗanda aka kashe a duniya.” (R. Yar. 17:1, 5; 18:24) An daɗe ana ganin yadda addinan ƙarya suke goyon bayan yaƙe-yaƙe da kuma taꞌaddanci a duniya. Saboda haka, addinan ƙarya ne suke haddasa yaƙe-yaƙe da tashe-tashen hankula, ba samun zaman lafiya da salama ba. Wannan ya kawo mu ga wata tambaya. Shin, za a ce an sami “zaman lafiya da salama ne” kawai bayan an kawar da Babila Babba? Za mu iya ce hakan, amma kuma ba mu da tabbaci.
Me zai faru bayan an sanar da “zaman lafiya da salama”? Bulus ya ce: “Sai kawai halaka za ta auko musu.” (1 Tas. 5:3) Idan masu iko da duniya sun ce an sami “zaman lafiya da salama,” bayan an riga an kawar da addinan ƙarya, su ma nan take za a hallaka su.
Mene ne bayin Jehobah za su yi a lokacin da abubuwan nan za su faru? Bulus ya ce: “Ba a cikin duhu kuke ba ꞌyanꞌuwa, har da ranar nan za ta same ku kamar zuwan ɓarawo.” (1 Tas. 5:4) Hakan ya nuna cewa, idan aka ce an sami “zaman lafiya da salama” bayan da aka hallaka addinan ƙarya, bayin Jehobah za su kasance da tabbaci cewa ana dab da hallaka gwamnatocin duniyar nan. Amma ga gwamnatocin kuma, hallakar za ta zo ba zato ba tsammani.
Muna da tabbaci cewa a nan gaba kaɗan, ‘ƙahoni goman’ tare da jar dabbar za su hallaka addinan ƙarya. Kuma ta haka ne za a soma ƙunci mai girma. Mun kuma san cewa akwai lokacin da alꞌummai za su ce an sami “zaman lafiya da salama.” Yaushe ne hakan zai faru? Mun tattauna lokuta biyu da za su iya faɗan hakan. Na ɗaya shi ne: Mai yiwuwa za su ce an sami “zaman lafiya da salama” kafin a hallaka addinan ƙarya. Na biyu kuma shi ne: Mai yiwuwa za su ce an sami zaman lafiya da salama bayan an hallaka addinan ƙarya. A nan gaba ne za mu san yadda kome zai faru. A yawancin lokuta, ana fahimtar annabce-annabcen Littafi Mai Tsarki da kyau saꞌad da suke faruwa ko bayan sun faru.—Ka ga misalin hakan a Yohanna 12:16.
Ba lokacin da abubuwan nan za su faru ne yake da muhimmanci ba, amma riƙe amincinmu ga Jehobah ne ya fi muhimmanci. Don haka, wajibi ne “mu yi zaman tsaro da shiri,” don mu kasance a shirye ko da yaya ne abubuwan za su faru.—1 Tas. 5:6.
a Ka duba “Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu” a Hasumiyar Tsaro ta Nuwamba 2025.
b Irin kalmomin da manzo Bulus ya yi amfani da su sun nuna cewa mai yiwuwa ba abu ɗaya ne za a faɗa ba, amma abubuwa da dama ne.