Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w26 Fabrairu p. 32
  • Mu Zama Masu Tsoron Jehobah Kamar Obadiya

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Mu Zama Masu Tsoron Jehobah Kamar Obadiya
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2026
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Kasance Da Gaba Gaɗi Ta Wurin Bangaskiya Da Tsoron Allah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Me Ya Sa Ya Kamata Mu Ji Tsoron Jehobah?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2023
  • Darussa Daga Littafin Obadiah, Yunana, da Mikah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2026
w26 Fabrairu p. 32

LABARIN WANI DAGA LITTAFI MAI TSARKI

Mu Zama Masu Tsoron Jehobah Kamar Obadiya

Obadiya ne ke kula da gidan mugun Sarki Ahab. Duk da cewa Sarki Ahab ya bar bautar Baal ta yaɗu a ko ina a Israꞌila, Obadiya ya ci-gaba da tsoron Allah tun yana “yaro.” (1Sar 18:​1-13) Shi ya sa a lokacin da Sarauniya Jezebel ta ba da umurni cewa a kakkashe dukan annabawan Jehobah, Obadiya ya nuna ƙarfin zuciya, kuma ya ɗau mataki don ya hana hakan faruwa. Idan mutum ya ɓoye annabi ɗaya, hakan zai iya jefa rayuwar mutumin cikin haɗari. Duk da haka, Obadiya ya ɓoye annabawa guda ɗari, kuma ya ci-gaba da ba su abinci. Yin hakan ba abu mai sauƙi ba ne, domin akwai ɗarurruwan annabawan ƙarya da suke yi wa Sarki Ahab da sarauniyarsa hidima da za su iya ganin sa.—1Sar 18:19.

Wane darasi ne za mu iya koya daga labarin Obadiya? Ko da yake Obadiya yana jin tsoron Ahab, ya fi jin tsoron Jehobah. Shi ya sa ya kasance da ƙarfin zuciya kuma ya sa ransa cikin haɗari don ya kāre ꞌyanꞌuwansa. Mu ma za mu iya nuna cewa mun fi jin tsoron Allah idan aka hana ayyukan ibadarmu a inda muke. Hakan zai ba mu ƙarfin zuciyar taimaka wa ꞌyanꞌuwanmu maza da mata da suke fuskantar matsaloli.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba