Yara “Gādo Ne Daga Wurin Yahweh”
IDAN ka ji kalmar nan “gādo” me ke zuwa zuciyarka? Mai yiwuwa kana tunanin kuɗi, ko fili, ko gida, ko wani abu mai muhimmanci da mutum yakan samu daga wurin iyayensa ko danginsa. Ko da wane irin gādo ne mutum ya samu, yana ɗaukan sa daraja sosai, kuma yana iya ƙoƙarinsa wajen kula da shi.
Littafi Mai Tsarki ya ce yara “gādo ne daga wurin Yahweh.” (Zab. 127:3) Iyayen da suke ƙaunar Jehobah, suna ɗaukan yaransu a matsayin kyauta mai daraja sosai daga wurin Jehobah. Suna iya ƙoƙarinsu don su tanada wa yaransu abinci, da kula da lafiyarsu, da kuma tabbata cewa yaran suna farin ciki. Ƙari ga haka, suna taimaka wa yaransu su ƙulla dangantaka ta kud da kud da Jehobah.
Abin baƙin cikin shi ne, wasu iyaye a yau ba sa ganin cewa yaransu gādo ne daga wurin Allah. (Isha. 49:15; 2 Tim. 3:1-3) Wasu iyaye kuma suna so su kula da yaransu, amma matsaloli dabam-dabam suna hana su yin hakan. Waɗanne matsaloli ne iyaye suke fama da su da ke sa kula da yaransu ya yi musu wuya? Mene ne Jehobah yake so iyaye su yi wa yaransu? Kuma ta yaya iyaye za su yi nasara wajen renon yaransu?
MATSALOLIN
Matsi daga wurin ꞌyanꞌuwa da abokan arziki. A wasu wurare a faɗin duniya, an fi daraja iyaye da suke da yara da yawa. Saboda haka, wasu maꞌaurata suna ganin zai fi kyau su haifi yara da yawa don gudun abin da mutane za su faɗa. Ko da hakan zai fi ƙarfinsu.
Damuwa game da abin da zai faru a nan gaba. A wasu wurare da babu abinci sosai ko asibitoci, kuma akwai cututtuka da dama, wasu iyaye sukan haifi yara da yawa da tunanin cewa ko da wasu sun mutu wasu za su rayu. Wasu iyaye kuma suna haifan yara da yawa don yaran su kula da su saꞌad da suka tsufa. Hakan yana faruwa ne musamman a ƙasashen da gwamnati ba ta taimaka wa tsofaffi.
Tazarar haihuwa. A wasu wurare, wasu maꞌaurata ba su da damar samun magunguna ko wasu hanyoyi dabam-dabam da ake yin tazarar haihuwa. A wasu wurare kuma ana samun magungunan, amma ba su da inganci sosai. Hakan yana sa mutane su ji tsoron yadda magungunan nan za su shafi lafiyar jikinsu. A wasu wurare kuma, mutane ba sa iya sayan magungunan domin suna da tsada sosai.a
MENE NE JEHOBAH YAKE SO IYAYE SU YI WA YARANSU?
Ku nemi lokacin da za ku riƙa kasancewa da kowane cikin yaranku
Ku tanada wa yaranku abubuwan da suke bukata. Jehobah ya ba wa iyaye hakkin tanada wa yaransu abubuwan da suke bukata kamar abinci, da riguna, da kuma wurin zama har sai sun yi girma. Jehobah ya kuma ba wa iyaye hakkin koyar da yaransu. Saboda haka, ꞌyanꞌuwa a ikilisiya ba sa tura yaransu zuwa makarantar kwana (boarding school). A maimakon haka, wajibi ne iyaye su kasance tare da yaransu har su yi girma don su tabbata cewa sun koyi abubuwan da za su taimaka musu a rayuwa. Ƙari ga haka, suna bukatar su nemi lokacin kasancewa da kowane yaronsu, don su riƙa kwantar masa da hankali kuma su tabbatar masa cewa suna ƙaunar sa. Jehobah bai ce dole ne sai iyaye sun zama masu arziki ba. Yana so ne su yi iya ƙoƙarinsu. Alal misali, Jehobah ya zaɓi iyayen da ba su da kuɗi sosai don su reni Ɗansa. Duk da haka, sun yi iya ƙoƙarinsu don su tanada masa abubuwan da yake bukata.—Mat. 13:55, 56; Luk. 2:24.
Ƙaꞌidar Littafi Mai Tsarki: “Duk wanda ba ya kula da danginsa, musamman iyalin gidansa, ya yi mūsun bangaskiyarsa ke nan, ya kuma fi wanda yake marar ba da gaskiya muni.”—1 Tim. 5:8.
Jehobah ya san cewa iyaye suna bukatar a girmama su kuma a taimaka musu yayin da suke tsufa. Hanya ɗaya da yara za su nuna cewa suna girmama iyayensu ita ce ta wajen shirya yadda iyayen za su sami abubuwan da suke bukata idan suka tsufa. (Fit. 20:12; 1 Tim. 5:4) Duk da haka, Jehobah yana farin ciki sosai idan iyaye suka mai da hankali a kan yadda za su kula da yaransu, maimakon a kan yadda yaransu za su kula da su.—2 Kor. 12:14.
Ku taimaka wa yaranku su koya game da Jehobah. Iyaye suna da hakkin taimaka wa yaransu su ƙaunaci Jehobah kuma su bauta masa. A gun Jehobah, babu abin da ya fi hakan muhimmanci.—M. Sha. 6:6, 7.
Ƙaꞌidar Littafi Mai Tsarki: “Ku ubanni, kada ku riƙa sa ꞌyaꞌyanku fushi, amma kuna koyar da kuma yi musu horo yadda Jehobah yake so.”—Afis. 6:4, NWT.
JEHOBAH YANA SO KU YI NASARA
Ku tattauna tun da wuri a kan yara nawa za ku haifa
Ku tattauna game da yawan yaran da kuke so ku haifa. Idan kuna so ku haifi yara, zai dace ku yi tunani sosai game da yanayin ku. Alal misali, idan kuka haifi yara da yawa, za ku iya ciyar da su, da saya musu kaya da kuma koyar da su? Idan ba za ku iya kula da yara da yawa ba, zai dace ku tattauna don ku san yawan yaran da za ku haifa. Yin hakan zai taimaka muku ku iya kula da yaranku yadda Jehobah yake so. Gaskiyar ita ce, Jehobah ya san cewa wasu abubuwa za su iya faruwa a rayuwarku ba zato ba tsammani. (M. Wa. 9:11) Amma, idan kuka yi iya ƙoƙarinku wajen kula da yaranku yadda Jehobah yake so, zai albarkace ku.
Ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki: “Shirye-shirye na mai ƙwazo lallai sukan kai ga yalwata, amma duk mai yin abu da gaggawa lallai ba zai sami biyan bukata ba.”—K. Mag. 21:5.
“Alal misali, wane ne a cikinku da yake so ya gina gidan sama, da ba zai fara zaunawa ya yi lissafin nawa ne zai kashe, don ya san ko yana da isasshen kuɗin da zai gama aikin ba?”—Luk. 14:28.
Ku sa bautar Jehobah farko a iyalinku. Ku tabbata cewa bauta wa Jehobah ce ta fi muhimmanci a rayuwarku. Idan kun riga kun haifi yara, ku yi iya ƙoƙarinku wajen taimaka wa kowannensu ya ƙaunaci Jehobah. Kuma idan kuka halarci taro, ku taimaka musu su riƙa saurarawa don su koyi abubuwa. Ku tabbata cewa kuna yin ibada ta iyali tare kowane mako. Kuma ku koya wa yaranku yadda za su iya yin waꞌazi. Bai kamata ku bar hakkin kula da yaranku a hannun danginku ko yaranku da suka ya yi girma, ko wasu dabam ba. Renon yara yadda za su yi girma su ƙaunaci Jehobah jan aiki ne, kuma yana ɗaukan lokaci. Amma za ku yi farin ciki idan kuka ga yaranku suna jin daɗin bauta wa Jehobah.
Ƙaꞌidar Littafi Mai Tsarki: “Ba abin da ya fi sa ni farin ciki fiye da in ji cewa ꞌyaꞌyana suna bin gaskiya.”—3 Yoh. 4.b
Ku dogara ga Jehobah. Ko da kun riga kun haifi yara, ko kuma kuna tunanin yin hakan, ku riƙa tuna cewa yadda Jehobah yake so ku reni yaranku ya fi raꞌayin da mutane a yankinku suke da shi.
Koya wa yara su ƙaunaci Jehobah kuma su bauta masa jan aiki ne kuma yana ɗaukan lokaci
Idan kun yanke shawara cewa ba za ku haifi yara da yawa ba, ku kasance da tabbaci cewa Jehobah zai tanada muku abubuwan da kuke bukata idan kuka tsufa. Kada ku haifi yara don kawai su kula da ku idan kuka tsufa ko da haka ne raꞌayin mutane a yankinku. Kada ku ji tsoro cewa babu wanda zai kula da ku idan kuka tsufa. Jehobah ya yi alkawarin kula da ku, kuma zai cika alkawarinsa.—Yosh. 23:14.
Ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki: “Dogara ga Yahweh da dukan zuciyarka, kada ka dogara ga ganewarka. A dukan hanyoyin rayuwarka ka girmama shi, shi kuwa zai daidaita hanyoyinka.”—K. Mag. 3:5, 6.
“Dā dai ni yaro ne, yanzu kam na tsufa, amma ban taɓa ganin Yahweh ya yashe mai adalci ba, ko kuwa a ga ꞌyaꞌyansa suna roƙon abinci.”—Zab. 37:25.
“Don haka, ku ci-gaba da sa Mulkin Allah da kuma adalcinsa farko a rayuwarku, kuma za a ƙara muku dukan abubuwan nan.”—Mat. 6:33.
Yara kyauta ne mai daraja sosai da Jehobah ya ba wa iyaye. Jehobah yana farin ciki sosai idan iyaye suka bi raꞌayinsa wajen tanada wa yaransu abubuwan da suke bukata, da taimaka musu su kusace Shi. Don haka, zai dace iyaye su yanke shawara a kan yawan yaran da za su haifa, maimakon bin raꞌayin mutanen yankinsu! Yin hakan zai nuna cewa suna ƙaunar yaransu sosai, kuma suna ɗaukan su a matsayin “gādo . . . daga wurin” Jehobah.
a Mata da miji ne za su yanke shawara ko za su yi tazarar haihuwa ko aꞌa, da kuma yadda za su yi hakan. Su ne za su yanke shawara a kan yara nawa za su haifa, da kuma lokacin da za su yi hakan. Su ne za su san ko za su yi amfani da magungunan tazarar haihuwa ko aꞌa. Ko da wace irin shawara ce suka yanke, bai kamata wani ya shariꞌanta su ba. Mun san cewa maꞌaurata ba za su yi amfani da wani abu ko magani da zai zubar da ciki, ko kuma ya kashe jaririn da ke ciki ba. (Rom. 14:4, 10-13) Ƙari ga haka, a duk lokacin da maꞌaurata suke yanke shawarwarin nan, zai dace su tuna da abin da ke 1 Korintiyawa 7:3-5.
b Yaran da aka ambata a ayar nan ꞌyanꞌuwa ne da Yohanna ya koya musu gaskiya. Amma iyaye za su iya ji kamar yadda Yohanna ya ji idan yaransu suna bauta wa Jehobah.