Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w26 Fabrairu pp. 14-19
  • Ka Kafa Maƙasudin Yin Baftisma

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Kafa Maƙasudin Yin Baftisma
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2026
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • ABIN DA YA SA WASU SUKE JINKIRI
  • MU RIƘA TUNA CEWA ƘARSHEN DUNIYAR NAN YA YI KUSA
  • YADDA ZA MU AMFANA IDAN MUKA ƊAUKI MATAKIN YIN BAFTISMA
  • Abin da Baftisma Take Nufi da Kuma Muhimmancin Yin Hakan
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2026
  • Ka Yi Shirin Yin Alkawarin Bauta wa Jehobah?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
  • Ka Ci-gaba da Bin Yesu Bayan Ka Yi Baftisma
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
  • Kada Ka Yi Jinkirin Yin Baftisma
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2026
w26 Fabrairu pp. 14-19

20-26 GA AFRILU, 2026

WAƘA TA 49 Mu Riƙa Faranta Ran Jehobah

Ka Kafa Maƙasudin Yin Baftisma

“Yanzu ne [lokacin da] Allah ya fi nuna mana alheri.”—2 KOR. 6:2.

ABIN DA ZA MU KOYA

Za mu ga cewa yanzu ne lokacin da muke bukatar mu ƙulla dangantaka mai kyau da Jehobah kuma mu yi baftisma.

1. (a) Ta yaya za mu amfana idan muka yi baftisma? (b) Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

SHIN, ka riga ka yi alkawarin bauta wa Jehobah kuma ka yi baftisma? Idan haka ne babu shakka ka riga ka roƙi Jehobah ya gafarta maka zunubanka, kuma ya ba ka damar bauta masa tare da bayinsa. (1 Bit. 3:21) Ƙari ga haka, saꞌad da ka yi baftisma waɗanda ba su yi baftisma ba za su so su bi misalinka. Saboda haka, wannan shawarar da ka yanke, shawara ce da ta dace! Idan ba ka riga ka yi baftisma kuma ba fa? Babu shakka, kana ƙaunar Jehobah kuma kana so ka bauta masa. Amma, kafin Jehobah ya gafarta maka zunubanka kuma ka zama amininsa, wajibi ne ka yi baftisma. (A. M. 2:​38-40) Ko da yake ka san hakan, wataƙila za ka iya yin jinkirin yin baftisma. Mene ne zai taimaka maka? A wannan talifin, za mu tattauna (1) abin da ya sa wasu suke jinkirin yin baftisma, (2) dalilin da ya sa zai dace mu riƙa tuna cewa ƙarshen duniyar Shaiɗan ya yi kusa, kuma (3) yadda za mu amfana idan muka yi baftisma ba tare da ɓata lokaci ba.

ABIN DA YA SA WASU SUKE JINKIRI

2. Me ya sa wasu suke jinkirin yin baftisma?

2 Wasu suna jinkirin yin baftisma don suna tsoro. Alal misali, ko da yake wasu suna so su bauta wa Jehobah, suna ganin cewa ba za su taɓa iya yin abin da yake so ba. Idan irin raꞌayin da kake da shi ke nan, ka karanta ayoyin da za su taimaka maka ka gane cewa Jehobah ya san mu ajizai ne. Kuma yana jin daɗi idan ka yi iya ƙoƙarinka wajen yin abin da yake so. (Zab. 103:​13, 14; Kol. 3:23) Idan kuma kana tsoron cewa za a tsananta maka bayan ka yi baftisma, ka roƙi Jehobah ya ba ka ƙarfin zuciya kamar marubucin zabura da ya ce: “Yahweh yana tare da ni, ba zan ji tsoro ba, me mutum zai iya yi mini?”—Zab. 118:6.

3. Wane abu ne kuma zai iya sa mutum ya yi jinkirin yin baftisma? (Ka kuma duba hoton.)

3 Wasu da suke ƙaunar Jehobah suna jinkirin yin baftisma domin suna ganin kamar ba su san abubuwa da yawa da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa ba. Amma, wajibi ne mutum ya san kome da kome da ke Littafi Mai Tsarki kafin ya yi baftisma? Aꞌa. Alal misali, bayan an yi girgizar ƙasa a kurkukun da aka jefa Bulus da Sailas, sun yi wa mai tsaron kurkukun da iyalinsa waꞌazi. Mai tsaron kurkukun da iyalinsa sun gane cewa Allah ne ya yi wannan muꞌujizar domin ya cece bayinsa. Ƙari ga haka, sun koyi abubuwa da dama game da Jehobah da kuma Yesu. Abubuwan da suka koya da daren nan sun sa sun yi “baftisma ba tare da ɓata lokaci ba.” (A. M. 16:​25-33) Idan ka san abubuwa game da Jehobah, kana ƙaunar sa da dukan zuciyarka, ka san muhimman koyarwa da ke Littafi Mai Tsarki, ka tuba daga zunubanka, kuma ka ƙudura niyyar yin abubuwan da Jehobah yake so, za ka iya yin baftisma.—Mar. 12:30.

Bulus da Sailas suna yi wa mai tsaron kurkukun da iyalinsa waꞌazi da dare. Kuma shi da iyalinsa suna sauraron su da kyau.

Bulus da Sailas sun yi wa mai tsaron kurkukun da iyalinsa waꞌazi, hakan ya sa suka yi “baftisma ba tare da ɓata lokaci ba” (Ka duba sakin layi na 3)


4. Wane abu ne kuma zai iya sa wasu su yi jinkirin yin baftisma? (Ka kuma duba hoton.)

4 Wasu da suke so su yi canje-canje a rayuwarsu don su yi baftisma, suna ganin kamar zai yi musu wuya sosai su bar wasu abubuwan da suke yi a dā. Gaskiyar ita ce, ba laifi ba ne mu yi tunani a kan yadda shawarar da muke so mu yanke za ta shafi rayuwarmu ba. (Luk. 14:​27-30) Amma wasu sukan damu sosai a kan sadaukarwa da za su yi don su iya bauta wa Jehobah. Alal misali, saꞌad da wata ꞌyarꞌuwa mai suna Candace take ƙarama, ta koyi abubuwan da mutum yake bukatar ya yi don ya sa Jehobah farin ciki. Amma, ba ta yi abubuwan ba. Da ta yi girma, ta sake soma yin nazarin Littafi Mai Tsarki. ꞌYarꞌuwar ta ce: “Ina jin daɗin irin rayuwar da nake yi, duk da cewa na san hakan ba ya faranta wa Jehobah rai. Na san cewa zai yi mini wuya in daina irin rayuwar da nake yi.” Wasu mutane kuma sukan ga kamar bayan sun yi baftisma, ba za su iya yin rayuwar da ta jitu da ƙaꞌidodin Jehobah ba. Suna ganin cewa bayan sun yi baftisma za su yi wani zunubi mai tsanani kuma a cire su daga ikilisiya. Idan kai ma kana irin tunanin nan, me zai taimaka maka?

Wata ꞌyarꞌuwa tana nazarin Littafi Mai Tsarki da wata mata. Yayin da ꞌyarꞌuwar take magana, tana tunanin yadda take shan giya da kuma rawa da abokanta a klub.

Wasu da suke so su bauta wa Jehobah sukan damu sosai a kan sadaukarwa da za su yi (Ka duba sakin layi na 4)


5. Mene ne ya kamata mu mai da hankali a kai idan muna jinkirin yin baftisma? (Matiyu 13:​44-46)

5 Idan muna so mu sayi wani abu, za mu yi tunani a kan yadda abin za amfane mu, ba kawai kuɗin da za mu kashe a kan abin ba. Idan muka ga cewa abin zai amfane mu sosai, za mu sayi abin komen tsadarsa. Haka ma, idan muna so mu yi baftisma, kada mu mai da hankali a kan abubuwan da muke jin daɗinsu da za mu daina. A maimakon haka, mu mai da hankali a kan abin da zai fi amfanarmu, wato zama da dangantaka mai kyau da Jehobah. Yesu ya yi amfani da misalai biyu don ya nuna mana muhimmancin yin hakan. (Karanta Matiyu 13:​44-46.) A misalan, kowannensu ya sayar da dukan dukiyoyinsa don ya sayi wani abu mai daraja da ya samu. Kai ma ka samu wani abu mai daraja sosai, wato gaskiya game da Mulkin Allah. Saboda haka, idan kana jinkirin yin wasu canje-canje don ka yi baftisma, zai dace ka yi tunani a kan misalan nan da Yesu ya bayar. Ka tambayi kanka: ‘Shin gaskiyar da na koya game da Mulkin Allah, abu ne da zai amfane ni kuwa? Shin ina nuna godiya don dangantaka da na ƙulla da Jehobah, da begen yin rayuwa har abada, da kuma ꞌyanꞌuwa da Jehobah ya ba ni a duk faɗi duniya?’ Amsoshin tambayoyin nan za su taimaka maka ka san abin da kake bukatar ka yi don ka yanke shawarar yin baftisma.

6. Mene ne zai taimaka mana mu yi abubuwan da muke koya?

6 A misalin da Yesu ya bayar game da wani mutumin da ya je shuka iri, Yesu ya bayyana cewa wasu da suka ji waꞌazin Mulkin Allah ba za su yi abin da suka koya ba. Amma Yesu ya kuma ce, wasu da suka ji waꞌazin Mulkin Allah za su yi abin da suka koya. (Luk. 8:​5-15) Idan kana ganin kamar ba za ka iya yin abubuwan da kake koya ba, kada ka karaya. Jehobah zai taimaka maka ka kasance da niyyar yin abubuwan da yake so. Ka roƙi Jehobah ya taimaka maka ka so abubuwan da kake koya, kuma ka yi amfani da su a rayuwarka.—Ezek. 18:31; 36:26.

7-8. Mene ne yake hana wasu matasa yin baftisma? (Ka kuma duba hoton.)

7 Wasu matasan da suke ƙaunar Jehobah ba sa yin canje-canjen da suke bukata don su yi baftisma don irin raꞌayin da wasu suke cusa musu. Alal misali, wasu malamai a makaranta za su iya gaya wa ɗalibansu cewa, wasu halayen da Jehobah ba ya so ba laifi ba ne. Irin raꞌayin nan zai jefa mutum cikin matsaloli a rayuwa. (Zab. 1:​1, 2; K. Mag. 7:​1-5) Za ka iya guje wa irin matsalolin nan idan ka yi abin da wani marubucin zabura ya yi. Ya ce: “Ƙaꞌidodinka su ne tunanina.”—Zab. 119:99.

8 Wasu Shaidu suna sa ya yi wa yaransu wuya su yanke shawarar yin baftisma ba tare da saninsu ba. Iyayen suna mai da hankali a kan yawan karatun da yaran za su yi da kuma irin aikin da za su samu. Ko kuma ba sa ƙarfafa yaransu su kafa maƙasudan da za su taimaka musu su kusaci Jehobah. Shin kana ganin iyayenka za su iya taimaka maka ka yanke shawarar yin baftisma? Idan haka ne, ka tattauna batun da su. Ka san cewa ko da shekarunka nawa ne, za ka iya ƙulla dangantaka mai kyau da Jehobah.—K. Mag. 20:11.

Wani matashi yana yi wa iyayensa magana kuma yana nuna musu darasi na 23, a littafin nan “Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada!”

Zai dace ka tattauna batun baftisma tare da iyayenka. (Ka duba sakin layi na 8)


9. Mene ne yake sa wasu su yi jinkirin yin baftisma?

9 Wasu da sun cancanci yin baftisma suna jinkirin yin hakan domin suna so su yi baftisma tare da wani a rana ɗaya. Alal misali, mai yiwuwa suna so su yi baftisma a rana ɗaya da wani abokinsu ko kuma wani danginsu. Gaskiyar ita ce, ba laifi ba ne mu yi baftisma a rana ɗaya tare da wani abokinmu ba. Amma, bai kamata mu yi jinkirin yin baftisma don muna jiran wani abokinmu ko danginmu ba. Ka tuna cewa kai da kanka ne ka yi alkawarin bauta wa Jehobah. Saboda haka, kada ka bar jiran wani ya sa ka yi jinkirin yin baftisma.—Rom. 14:12.

MU RIƘA TUNA CEWA ƘARSHEN DUNIYAR NAN YA YI KUSA

10. Wane abu ne kuma yake sa wasu su yi jinkirin yin baftisma?

10 Wani abu kuma da ke sa wasu su yi jinkirin yin baftisma shi ne, suna ganin cewa akwai sauran lokaci kafin a kawo ƙarshen wannan duniyar Shaiɗan. Amma irin tunanin nan ya dace kuwa? Yesu ya gaya wa mabiyansa cewa: “Ku kasance a shirye, domin Ɗan mutum zai zo a lokacin da ba ku yi tsammani ba.”—Luk. 12:40.

11. Yayin da muke ƙara koya game da Jehobah, mene ne hakan zai sa mu yi, kuma me ya sa? (Zabura 119:60)

11 Ƙaunarmu ga Jehobah ce take sa mu yi alkawarin bauta masa kuma mu yi baftisma. Yayin da muke ƙara koya game da Jehobah, hakan zai sa mu ga cewa Jehobah yana ƙaunar mu, kuma ƙaꞌidodinsa don amfaninmu ne. (Karanta Zabura 119:60.) Yakub ya kuma ambata wani dalili mai muhimmanci da ya sa ya dace mu riƙa bin umurnin Jehobah ba tare da ɓata lokaci ba. Ya nuna cewa babu waninmu da ya san abin da zai faru gobe. Don haka, zai dace mu yi amfani da duk wata dama da muka samu mu yi “abin da ya kamata” mu yi. Wato, mu yi abin da zai faranta ran Jehobah.—Yak. 4:​13-17.

12. Mene ne muka koya daga misalin da Yesu ya bayar game da masu aiki a gonar itatuwan inabi?

12 A misalin da Yesu ya bayar game da mutanen da suka yi aiki a gonar itatuwan inabi, Yesu ya ce an biya waɗanda suka yi aiki na awa ɗaya daidai kuɗin da aka biya waɗanda suka yi aiki tun da safe. To me ya sa waɗanda suka yi aiki na awa ɗaya ba su soma aiki da wuri ba? Sun ce: “Domin babu wanda ya ɗauke mu aiki.” Masu aikin nan ba masu ƙyuya ba ne. Da a ce wani ya ɗauke su aiki, da sun yi aikin. Shi ya sa da zarar an kira su aiki, sai suka soma aikin nan da nan. (Mat. 20:​1-16) A yau ma, Yesu ya kira mu mu zama mabiyinsa kuma mu yi waꞌazin Mulkin. Ya kamata mu amsa kiransa nan da nan da zarar mun ji hakan.

13. Mene ne muka koya daga labarin matar Lutu?

13 Wasu suna ganin cewa za su iya yin canje-canje a rayuwarsu don su iya bauta wa Jehobah gab da lokacin da ƙarshen duniyar nan zai zo. Yesu ya san cewa wasu za su kasance da irin raꞌayin nan, shi ya sa ya gaya wa mabiyansa cewa: “Ku tuna da matar Lutu.” (Luk. 17:​31-35) Babu shakka, ta san cewa Jehobah yana gab da hallaka Sodom da Gomora. Amma barin abubuwan da ta mallaka ya yi mata wuya. (Far. 19:​23-26) Labarin nan ya tuna mana cewa akwai lokacin da mutane ba za su sake samun damar yin canje-canje don su bauta wa Jehobah ba. Idan lokacin ya kai, babu wata dama kuma.—Luk. 13:​24, 25.

14. Me ya sa zai dace mu riƙa mai da hankali ga yadda annabce-annabcen Littafi Mai Tsarki suke cika?

14 Abubuwan da suke faruwa a yau sun nuna cewa annabce-annabcen Littafi Mai Tsarki suna cika. Ko da wasu abubuwan da aka annabta a Littafi Mai Tsarki ba sua faruwa a inda kake, ganin yadda abubuwan nan suke faruwa a wurare da dama a faɗin duniya, zai sa ka yi canje-canjen da kake bukata don ka yi baftisma ba tare da ɓata lokaci ba. Ka yi laꞌakari da abin da manzo Bitrus ya gaya wa Kiristoci a ƙarni na farko. Ya gaya musu cewa: “Ƙarshen dukan abu ya yi kusa. Saboda haka sai ku natsu” wato, su zauna da shiri. (1 Bit. 4:7) Mai yiwuwa, “ƙarshen” da Bitrus yake nufi a nan shi ne lokacin da za a hallaka Urushalima da haikalinta. Waɗanda Bitrus ya rubuta wa wasiƙar nan ba sa zama kusa da Urushalima. Saboda haka, ba za su kasance a Urushalima a lokacin da za a hallaka birnin ba. (1 Bit. 1:1) Amma yayin da suka ga cikar annabcin nan, hakan zai sa su ƙara kasancewa da tabbaci cewa Jehobah zai cika sauran alkawuran da ya yi. Haka ma, yayin da kake ganin cikar annabce-annabcen Littafi Mai Tsarki, hakan zai sa ka yi duk abin da kake bukatar ka yi don ka yi baftisma.

15. Ta yaya za mu zauna da shiri don ƙarshen duniyar nan? (2 Bitrus 3:​10-13)

15 A wasiƙa ta biyu da Bitrus ya rubuta, Bitrus ya bayyana yadda za mu zauna da shiri don ranar Ubangiji, wato ƙarshen duniyar nan. A lokacin da Bitrus ya rubuta wasiƙar nan, za a yi shekaru da yawa kafin ranar Ubangiji ta zo. Duk da haka, Bitrus ya gaya wa Kiristocin cewa, su yi “marmarin zuwan ranar.” (Karanta 2 Bitrus 3:​10-13.) Za mu nuna cewa muna marmarin zuwan ranar ta wurin zama da shiri, da yin “rayuwa mai tsarki,” da kuma kasancewa da “hali iri na Allah.” Hakika, idan muka yi abubuwan da Jehobah yake so, hakan zai sa shi farin ciki. Ƙari ga haka, idan ka yi alkawarin bauta wa Jehobah kuma ka yi baftisma, hakan zai daɗa sa shi farin ciki.

YADDA ZA MU AMFANA IDAN MUKA ƊAUKI MATAKIN YIN BAFTISMA

16. A wane lokaci ne zai dace mu yanke shawarar yin baftisma? (2 Korintiyawa 6:​1, 2) (Ka kuma duba hotunan.)

16 Yanzu ne lokacin da ya dace mu yanke shawarar yin baftisma. (Karanta 2 Korintiyawa 6:​1, 2.) Mutumin Itiyofiya wanda bābā ne da Filibus ya haɗu da shi ya gano cewa, yana bukatar ya yi baftisma ba tare da ɓata lokaci ba. Da aka yi masa waꞌazin Mulkin Allah, kuma ya ga wani wurin da zai iya yin baftisma, bai gaya wa kansa cewa: ‘Bari in ƙara koya game da bisharar Mulkin tukuna ba. Ko kuma, ai zan sake ganin wani ruwa a gaba.’ Bai faɗi hakan ba. A maimakon haka, ya gaya wa Filibus cewa, “Ga ruwa a nan! Me zai hana ni yin baftisma?” (A. M. 8:​26, 27, 35-39) Wannan misali ne mai kyau sosai! Da aka yi wa mutumin baftisma, “sai ya ci-gaba da tafiya yana farin ciki.”

Hotuna: Na 1. Mutumin Itiyofiya wanda bābā ne yana shiga cikin ruwa yayin da Filibus yana so ya yi masa baftisma. Na 2. ꞌYarꞌuwar da ɗalibarta suna magana da dattawa biyu da farin cikin a Majamiꞌar Mulki.

Labarin mutumin Itiyofiya wanda bābā ne ya koya mana cewa: Yanzu ne lokacin da ya dace mu yi baftisma! (Ka duba sakin layi na 16)a


17. Wane tabbaci ne zai dace ka kasance da shi?

17 Idan kana jinkirin yin baftisma, ka kasance da tabbaci cewa Jehobah yana so ya taimaka maka ka ƙulla dangantaka mai kyau da shi. (Rom. 2:4) Jehobah zai iya taimaka maka ka yanke shawarar yin baftisma idan kana jin tsoro, ko kana ganin cewa yin baftisma zai yi maka wuya, ko kuma idan ba wanda yake ƙarfafa ka ka yi baftisma. Idan ka yi baftisma, za ka kasance da farin ciki sanin cewa kana faranta wa Jehobah rai, kuma ba za ka riƙa tunani a kan abubuwan da ka bari a baya ba. (Filib. 3:​8, 13) Ƙari ga haka, za ka kasance da begen ganin cikar alkawuran da Jehobah ya yi wa dukan waɗanda suka yi alkawarin bauta masa kuma suka yi baftisma.—A. M. 3:19.

MECE CE AMSARKA?

  • Mene ne yake sa wasu suke jinkirin yin baftisma?

  • Me ya sa bai kamata mutum ya ɓata lokacin yanke shawarar yin baftisma ba?

  • A wane lokaci ne ya dace mutum yanke shawara yin baftisma?

WAƘA TA 38 Zai Ƙarfafa Ka

a BAYANI A KAN HOTUNA: Kamar yadda mutumin Itiyofiya wanda bābā ne ya je ya sami Filibus ya gaya masa cewa yana son ya yi baftisma, haka ma wata ɗaliba ta je ta sami dattawa ta gaya musu cewa tana so ta yi baftisma.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba