TALIFIN NAZARI NA 9
WAƘA TA 51 Mun Yi Alkawarin Zama Bayin Allah
Kada Ka Yi Jinkirin Yin Baftisma
“Me kake jira? Tashi a yi maka baftisma.”—A. M. 22:16.
ABIN DA ZA MU KOYA
Za mu ga yadda labarin Samariyawa da Shawulu na Tarsus da Koneliyus da kuma Korintiyawa za su taimaka mana mu yi baftisma.
1. Waɗanne dalilai masu kyau ne za su sa mu yi baftisma?
KANA ƙaunar Jehobah, wanda ya ba ka rai da dukan abubuwan da kake da su? Za ka so ka nuna masa cewa kana ƙaunarsa? Muhimmiyar hanyar da za ka nuna cewa kana ƙaunar Jehobah ita ce ta wajen yin alkawarin bauta masa da kuma yin baftisma. Yin hakan zai sa ka kasance a cikin iyalin Jehobah. Daga nan, Allahnka da Abokinka Jehobah zai ci-gaba da lura da kai domin kai nasa ne. (Zab. 73:24; Isha. 43:1, 2) Ban da haka ma, yin alkawarin bauta wa Jehobah da kuma yin baftisma zai ba ka damar samun rai na har abada.—1 Bit. 3:21.
2. Me za mu tattauna a wannan talifin?
2 Shin, akwai abin da yake hana ka yin baftisma? Idan haka ne, ka sani cewa ba kai kaɗai ba ne. Miliyoyin mutane sun bukaci su yi canje-canje a rayuwarsu da kuma tunaninsu don su cancanci yin baftisma. Kuma yanzu suna bauta wa Jehobah da farin ciki da ƙwazo. Mene ne za mu iya koya daga waɗanda suka yi baftisma a ƙarni na farko? Bari mu tattauna matsalolin da suka fuskanta, da kuma darasin da za mu iya koya daga misalansu.
SAMARIYAWA SUN YI BAFTISMA
3. Waɗanne canje-canje ne mai yiwuwa Samariyawa suka yi kafin su yi baftisma?
3 Samariyawa suna da nasu addini a lokacin da Yesu yake duniya. Da yawa daga cikinsu suna zama a arewacin ƙasar Yahudiya. Kafin Samariyawan su yi baftisma, suna bukatar su amince da dukan abubuwan da ke Littafi Mai Tsarki, kuma su ƙara sanin abin da yake koyarwa. Samariyawa sun yi imani cewa littattafai biyar na farko na Littafi Mai Tsarki wato, Farawa zuwa Maimaitawar Shariꞌa, da wataƙila littafin Yoshuwa ne kaɗai hurarru daga Allah. Kuma suna sa rai cewa Almasihu zai zo kamar yadda Allah ya yi alkawari a Maimaitawar Shariꞌa 18:18, 19. (Yoh. 4:25) Idan suna so su yi baftisma, dole su amince cewa Yesu ne Almasihun da aka yi alkawarinsa. Abin da “mutanen Samariya da yawa” suka yi ke nan. (Yoh. 4:39) Ƙari ga haka, da yake Kiristoci da yawa Yahudawa ne, mai yiwuwa wasu Samariyawa sun bukaci su canja raꞌayinsu game da Yahudawa.—Luk. 9:52-54.
4. Bisa ga Ayyukan Manzanni 8:5, 6, 14, mene ne wasu Samariyawa suka yi da suka ji waꞌazin da Filibus ya yi?
4 Me ya taimaka wa Samariyawan su yi baftisma? Da Filibus mai waꞌazi ya yi musu “waꞌazin Almasihu,” waɗansu daga cikinsu sun “karɓi Kalmar Allah.” (Karanta Ayyukan Manzanni 8:5, 6, 14.) Ko da yake Filibus Bayahude ne, sun saurare shi. Mai yiwuwa sun tuna da nassosin da suka ce Allah ba ya nuna bambanci. (M. Sha. 10:17-19) Don haka, sun mai da hankali ga abin da Filibus ya faɗa game da Almasihu, kuma sun ga tabbacin cewa Allah ne ya aiko Filibus. Filibus ya yi abubuwan ban mamaki da yawa, kamar warkar da marasa lafiya da kawar da aljannu.—A. M. 8:7.
5. Waɗanne darussa ne za ka iya koya daga Samariyawa?
5 Ko da yake Filibus Bayahude ne kuma Samariyawan ba su taɓa jin irin koyarwar da yake musu ba, ba su bar hakan ya hana su sauraron sa ba. Samariyawan ba su yi jinkirin yin baftisma ba da suka tabbata cewa abin da Filibus yake koya musu gaskiya ne. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Da suka gaskata labari mai daɗin da Filibus ya yi a kan Mulkin Allah, da kuma sunan Yesu Almasihu, dukansu aka yi musu baftisma, maza da mata.” (A. M. 8:12) Kai kuma fa? Ka tabbata cewa Kalmar Allah gaskiya ne? Kuma ka tabbata cewa Shaidun Jehobah suna iya ƙoƙarinsu don su nuna irin ƙaunar da Yesu ya ce mabiyansa na gaske za su nuna? (Yoh. 13:35) Idan haka ne, kada ka yi jinkiri ko ka ji tsoron yin baftisma. Ka kasance da tabbaci cewa Jehobah zai yi maka albarka.
6. Ta yaya labarin Ruben zai taimaka maka?
6 Wani ɗanꞌuwa mai suna Ruben daga ƙasar Jamus, ya yi girma a iyalin da ke bauta wa Jehobah. Amma saꞌad da yake matashi, ya yi shakka cewa akwai Allah. Me ya taimaka masa ya kawar da shakkar? Ya gano cewa yana bukatar ya ƙara yin bincike game da batun kuma ya yi hakan. Ya ce: “Na yi nazari domin in san gaskiyar batun. Na yi nazari game da juyin halitta sau da yawa.” Ya karanta littafin nan mai jigo, Is There a Creator Who Cares About You? Wannan littafin ya taimaka wa Ruben sosai. Har ya gaya wa kansa cewa: ‘Lallai! Akwai Allah.’ Ƙari ga haka, da ya ziyarci hedkwatarmu, ya gano cewa irin haɗin kai da ke ƙungiyarmu babu kamarsa, kuma hakan ya sa ya daɗa ƙaunar ƙungiyarmu. Da Ruben ya koma ƙasar Jamus, ya yi baftisma saꞌad da yake shekara 17. Idan kana shakka ko akwai Allah, ko game da abin da ka koya daga Littafi Mai Tsarki, ko kuma game da wasu batutuwa dabam, ka yi bincike a littattafanmu. Za mu iya daina yin shakka idan muka san gaskiyar batun. (Afis. 4:13, 14) Yayin da kake jin labarai game da ƙauna da haɗin kai da ke tsakanin mutanen Jehobah a faɗin duniya, kuma kana ganin hakan a ikilisiyarku, babu shakka, za ka ƙara son ƙungiyarmu mai haɗin kai da ke duk faɗin duniya.
SHAWULU NA TARSUS YA YI BAFTISMA
7. Wane irin tunani ne Shawulu yake bukatar ya canja?
7 Bari mu tattauna game da Shawulu mutumin Tarsus. Shi mutum ne da ya san Dokokin Yahudawa sosai kuma shi sananne ne ga Yahudawa. (Gal. 1:13, 14; Filib. 3:5) A lokacin, Yahudawa da yawa suna ganin Kiristoci kamar ꞌyan ridda. Don haka, Shawulu ya tsananta musu sosai. A ganinsa, yana yin nufin Allah ne. (A. M. 8:3; 9:1, 2; 26:9-11) Idan Shawulu ya ba da gaskiya ga Yesu kuma ya yi baftisma, dole ne ya san cewa shi ma za a tsananta masa.
8. (a) Mai ya taimaka wa Shawulu ya yi baftisma? (b) Bisa ga Ayyukan Manzanni 22:12-16, ta yaya Hananiya ya taimaka wa Shawulu? (Ka kuma duba hoton.)
8 Me ya taimaka wa Shawulu ya yi baftisma? Saꞌad da Yesu ya yi magana da Shawulu daga sama, wani haske ya sa shi ya makance. (A. M. 9:3-9) Ya yi kwana uku yana azumi, kuma ba mamaki ya yi tunani sosai game da abin da ya faru da shi. Shawulu ya gane cewa Yesu ne Almasihu kuma mabiyansa ne suke yin bauta ta gaskiya. Babu shakka, Shawulu ya yi baƙin ciki sosai cewa shi ne ya amince a kashe Istifanus! (A. M. 22:20) Bayan kwana uku, Hananiya ya same Shawulu, ya warkar da shi kuma ya ƙarfafa shi ya yi baftisma nan da nan. (Karanta Ayyukan Manzanni 22:12-16.) Shawulu ya kasance da sauƙin kai, ya saurari Hananiya kuma ya yi baftisma.—A. M. 9:17, 18.
Za ka yarda ka yi baftisma kamar yadda Shawulu ya yi? (Ka duba sakin layi na 8)
9. Waɗanne darussa ne za ka iya koya daga Shawulu?
9 Akwai darussa da za mu iya koya daga Shawulu. Bai bar girman kai da tsoron mutane su hana shi yin baftisma ba. Shawulu ya kasance da sauƙin kai kuma ya canja rayuwarsa don ya zama mabiyin Kristi. (A. M. 26:14, 19) Shawulu ya amince ya zama Kirista duk da cewa ya san za a tsananta masa. (A. M. 9:15, 16; 20:22, 23) Bayan da ya yi baftisma, ya ci-gaba da dogara ga Jehobah ya taimaka masa ya iya jimre matsaloli dabam-dabam da ya yi fama da su. (2 Kor. 4:7-10) Idan ka yi baftisma kuma ka zama Mashaidin Jehobah, hakan zai iya sa ka fuskanci tsanantawa ko kuma matsalolin da za su gwada bangaskiyarka. Amma ka kasance da tabbaci cewa Allah da kuma Yesu Kristi za su ci-gaba da taimaka maka don ka iya jimrewa kuma ka riƙe aminci.—Filib. 4:13.
10. Me ka koya daga labarin Anna?
10 Anna ta yi girma a Gabashin Turai. Bayan da mahaifiyarta ta yi baftisma, Anna ta soma nazarin Littafi Mai Tsarki da izinin babanta saꞌad da take shekara 9. Amma, da danginta suka ji cewa tana nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehobah, sun soma tsananta mata. Dangin suna ganin cewa abin kunya ne wani a iyalinsu ya bar addinin kakanninsu. Da Anna ta kai shekara 12, ta nemi izinin babanta don ta yi baftisma. Sai ya tambaye ta ko hakan zaɓinta ne ko wani ne yake tilasta mata. Anna ta amsa ta ce, “Ina ƙaunar Jehobah.” Sai babanta ya amince mata ta yi baftisma. Bayan da ta yi baftisma, danginta sun ci-gaba da wulaƙanta ta. Kakanta ma ya ce: “Zan fi jin daɗi idan aka ce mini kin zama karuwa ko kin soma shaye-shaye, maimakon a ce kin zama Mashaidiyar Jehobah.” Me ya taimaka wa Anna ta jimre? Ta ce, “Jehobah ya taimaka min in jimre, kuma iyayena sun goyi bayana sosai.” Anna tana rubuta yanayoyi dabam-dabam da ta ga taimakon Jehobah a rayuwarta. Kuma a wasu lokuta takan duba su don kada ta manta da yadda Jehobah ya taimaka mata. Idan kana tsoron cewa za a tsananta maka, ka tuna cewa kai ma Jehobah zai taimaka maka.—Ibran. 13:6.
KONELIYUS YA YI BAFTISMA
11. Me zai iya sa Koneliyus ya yi jinkirin yin baftisma?
11 Za mu iya koyan darussa masu kyau daga labarin Koneliyus. Shi komandan sojojin Roma ne, kuma wajen sojoji 100 suna ƙarƙashinsa. (A. M. 10:1) Ba mamaki matsayinsa ya sa ya zama sananne a wurin da yake zama da kuma a tsakanin sojoji. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Yana ƙoƙari sosai wajen ba da sadaka hannu sake ga mutane.” (A. M. 10:2) Jehobah ya ce wa manzo Bitrus ya je ya yi masa waꞌazi. Shin, Koneliyus ya yi jinkirin yin baftisma don yana da babban matsayi ne?
12. Me ya taimaka wa Koneliyus ya yi baftisma?
12 Me ya taimaka wa Koneliyus ya yi baftisma? Littafi Mai Tsarki ya ce shi ‘mai tsoron’ Allah ne, “shi da iyalinsa duka.” Kuma yana yin adduꞌa ga Allah kullum. (A. M. 10:2) Saꞌad da Bitrus ya yi wa Koneliyus waꞌazin labari mai daɗi, shi da iyalinsa sun ba da gaskiya ga Yesu Kristi kuma sun yi baftisma nan da nan. (A. M. 10:47, 48) Babu shakka, Koneliyus ya kasance a shirye ya yi canje-canjen da za su sa ya iya bauta wa Jehobah tare da iyalinsa.—Yosh. 24:15; A. M. 10:24, 33.
13. Waɗanne darussa ne za ka iya koya daga Koneliyus?
13 Kamar Shawulu, Koneliyus bai bar matsayinsa ya hana shi zama Kirista ba. Kai kuma fa? Kana bukatar ka yi canje-canje sosai a rayuwarka don ka cancanci yin baftisma? Idan haka ne, Jehobah zai taimaka maka. Zai albarkace ka idan ka ƙudiri niyyar bin kaꞌidodin Littafi Mai Tsarki don ka bauta masa.
14. Me ka koya daga labarin Tsuyoshi?
14 Wani ɗanꞌuwa mai suna Tsuyoshi daga Japan ya yi wasu canje-canje a aikinsa don ya cancanci yin baftisma. Shi mataimakin hedimasta ne na wata sanannen makarantar da ke koya wa mutane yadda ake shirya furanni. Idan ana janaꞌiza, hedimastan ne yake zuwa ya shirya furanni kuma ya yi wasu abubuwan addinin Budda a wurin. Amma idan ba zai iya zuwa ba, Tsuyoshi ne yake zuwa a madadinsa. Da Tsuyoshi ya koyi gaskiya game da matattu, ya gano cewa ba zai iya yin baftisma ba idan yana yin waɗannan abubuwan. Ya yanke shawara cewa ba zai sake yin abubuwan addinin Budda ba. (2 Kor. 6:15, 16) Tsuyoshi ya yi wa hedimastan magana game da batun. Mene ne sakamakon? Tsuyoshi ya ci-gaba da aikinsa kuma ba ya bukatar ya yi waɗannan abubuwan. Ya yi baftisma wajen shekara ɗaya bayan ya soma nazarin Littafi Mai Tsarki.a Idan kana bukatar ka yi canje-canje game da aikinka don ka faranta wa Jehobah rai, ka kasance da tabbacin cewa Jehobah zai yi wa kai da iyalinka tanadin bukatunku.—Zab. 127:2; Mat. 6:33.
KORINTIYAWA SUN YI BAFTISMA
15. Mene ne zai iya hana Korintiyawa yin baftisma?
15 Abin da mutane a birnin Korinti na dā suka sa a gaba shi ne, neman arziki da kuma yin lalata. Mutane da yawa da ke zama a wurin suna yin abubuwan da Jehobah ba ya so. Don haka, zai yi wa mazaunan birnin wuya sosai su soma bauta wa Jehobah. Duk da haka, saꞌad da manzo Bulus ya je birnin ya yi waꞌazi game da Yesu, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Waɗansu Korintiyawa kuma da yawa da suka ji maganar Bulus, suka ba da gaskiya, aka kuwa yi musu baftisma.” (A. M. 18:7-11) Ana nan, sai Yesu ya nuna wa Bulus ruꞌuya, ya ce masa: “Ina da mutane da yawa a wannan birni.” Don haka Bulus ya ci-gaba da waꞌazi a wurin na shekara ɗaya da rabi.
16. Me ya taimaka ma wasu a Korinti su yi baftisma? (2 Korintiyawa 10:4, 5)
16 Me ya taimaka wa Korintiyawa su yi baftisma? (Karanta 2 Korintiyawa 10:4, 5.) Kalmar Allah da ruhunsa mai tsarki ya taimaka musu su yi canje-canje a rayuwarsu nan da nan. (Ibran. 4:12) Waɗanda suka ba da gaskiya ga labari mai daɗi game da Yesu Kristi, sun daina halayen da ya zama musu jiki, kamar buguwa, da sata, da kuma luwaɗi.—1 Kor. 6:9-11.b
17. Mene ne ka koya daga labarin Korintiyawa?
17 Ko da yake wasu a Korinti suna da halayen da sun zama musu jiki da suke bukatar su canja, ba su ɗauka cewa ba za su iya canja halayen nan ba don su zama Kiristoci. Sun yi iya ƙoƙarinsu don su shiga ta ƙaramar ƙofa da zai kai ga rai na har abada. (Mat. 7:13, 14) Kana iya ƙoƙarinka ka yi canje-canje a rayuwarka don ka iya yin baftisma? Kada ka gaji! Ka roƙi Jehobah ya ba ka ruhu mai tsarki don ya taimaka maka ka daina shaꞌawar yin abin da bai da kyau.
18. Mene ne ka koya daga labarin Monika?
18 Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Monika daga ƙasar Georgia, ta yi iya ƙoƙarinta don ta daina yin maganganun banza da kuma saurarar waƙoƙi da kallon fina-finan banza, don ta cancanci yin baftisma. Ta ce: “Kafin in yi baftisma, yin adduꞌa ga Jehobah yana sa in sami ƙarfin da nake bukata. Jehobah ya san cewa ina so in yi abin da ya dace, shi ya sa ya ci-gaba da taimaka min da kuma kāre ni.” Monika ta yi baftisma tana shekara 16. Akwai abubuwan da kake bukatar ka daina don ka iya bauta wa Jehobah yadda yake so? Idan haka ne, ka ci-gaba da roƙonsa ya taimaka maka ka yi canje-canje. Jehobah yana ba da ruhu mai tsarki hannu sake.—Yoh. 3:34.
BANGASKIYA ZA TA SA KA YI NASARA
19. Mene ne zai taimaka maka ka yi nasara ko da wace irin matsala ce kake fuskanta? (Ka kuma duba hoton.)
19 Ko da mene kake fama da shi a rayuwa da zai iya hana ka yin baftisma, ka tabbata cewa Jehobah yana ƙaunar ka kuma yana so ka kasance cikin iyalinsa. Yesu ya gaya ma wasu mabiyansa a ƙarni na farko cewa: “Idan kuna da bangaskiyar da ta yi ƙanƙanta kamar ƙwayar mastad, za ku iya ce wa tudun nan ya tashi daga nan zuwa can, kuma zai tashi. Ba kuwa abin da zai gagare ku.” (Mat. 17:20) Waɗanda Yesu yake yi wa magana sun yi ꞌyan shekaru ne kawai tare da shi, saboda haka, suna bukatar su ci-gaba da ƙarfafa bangaskiyarsu. Amma Yesu ya tabbatar musu cewa, idan sun kasance da bangaskiya, Jehobah zai taimaka musu su yi nasara, ko da wace irin matsala ce suke fuskanta. Kai ma Jehobah zai taimaka maka ka yi hakan!
Ka tabbata cewa Jehobah yana ƙaunar ka kuma yana so ka kasance cikin iyalinsa (Ka duba sakin layi na 19)c
20. Ta yaya labaran Kiristoci a ƙarni na farko da na zamaninmu da muka tattauna a talifin nan suka ƙarfafa ka?
20 Idan akwai wani abin da zai iya hana ka yin baftisma, ka yi iya ƙoƙarinka ka kawar da shi nan da nan. Bincika labarin Kiristoci na ƙarni na farko da na zamaninmu, zai ba ka ƙarfin da kake bukata. Bari misalinsu ya ƙarfafa ka, ya kuma sa ka yi alkawarin bauta wa Jehobah kuma ka yi baftisma. Wannan ita ce shawara mafi kyau da za ka taɓa yankewa a rayuwa!
WAƘA TA 38 Zai Ƙarfafa Ka
a Tarihin Ɗanꞌuwa Tsuyoshi Fujii na cikin mujallar Awake! ta 8 ga Agusta, 2005, shafi na 20-23.
b Ka kalli bidiyon nan mai jigo ‘Me Ke Hana Ka Yin Baftisma?’ a jw.org/ha
c BAYANI A KAN HOTO: Wasu ꞌyanꞌuwa maza da mata suna marabtar waɗanda suka yi baftisma.