Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w26 Fabrairu pp. 8-13
  • Abin da Baftisma Take Nufi da Kuma Muhimmancin Yin Hakan

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Abin da Baftisma Take Nufi da Kuma Muhimmancin Yin Hakan
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2026
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • MENE NE BAFTISMA TAKE NUFI?
  • YADDA AKE YIN BAFTISMA
  • “A CIKIN SUNAN UBA, DA NA ƊA, DA NA RUHU MAI TSARKI”
  • Za Ka Amfana Sosai Idan Ka Yi Baftisma!
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Baftisma Tana da Muhimmanci ga Kiristoci
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2018
  • Me Ya Sa Za Ka Yi Baftisma?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Ma’anar Baftismarka
    Ka Bauta wa Allah Maƙadaici na Gaskiya
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2026
w26 Fabrairu pp. 8-13

13-19 GA AFRILU, 2026

WAƘA TA 52 Alkawarinmu ga Jehobah

Abin da Baftisma Take Nufi da Kuma Muhimmancin Yin Hakan

“Ku koyar da mutane . . . su zama almajiraina, ku riƙa yi musu baftisma.”—MAT. 28:19.

ABIN DA ZA MU KOYA

Za mu ga abin da baftisma take nufi, da muhimmancin yin hakan, da kuma yadda ake yin baftisma.

1. Ta yaya muka san cewa baftisma na cikin muhimman koyarwar Littafi Mai Tsarki?

MUNA farin ciki sosai idan mutane suka yi baftisma! Haka Kiristoci suka ji saꞌad da mutane da yawa suka yi baftisma a ranar Fentakos ta shekara ta 33, bayan haihuwar Yesu. A ranar, manzo Bitrus ya bayyana cewa yana da muhimmanci sosai mutane su yi baftisma. (A. M. 2:​38, 40, 41) Daga baya manzo Bulus ya rubuta cewa, koyarwar baftisma tana cikin “koyarwar nan ta farko wadda muka karɓa game da Almasihu.” (Ibran. 6:​1, 2) Abin da Bulus ya faɗa ya nuna cewa batun baftisma yana cikin muhimman abubuwan da muke koya saꞌad da muka soma yin nazari. Don haka, muna bukatar mu fahimci batun da kyau. Me ya sa?

2. Me ya sa muke bukatar mu fahimci batun baftisma da kyau?

2 Idan aka yi tushen gini da ƙarfi sosai, hakan zai sa ginin ya tsaya daram. Haka ma, idan muka fahimci batun baftisma da kyau, hakan zai ƙarfafa bangaskiyarmu. Muna bukatar mu fahimci wannan batun da kyau ko da mun daɗe da yin baftisma, ko kuma muna ƙoƙarin yin hakan. Saboda haka, a wannan talifin za mu amsa waɗannan tambayoyin: Mene ne baftisma take nufi? Yaya ake yin baftisma? Kuma me ya sa ake yin baftisma cikin sunan Uba, da na Ɗa, da na ruhu mai tsarki?

MENE NE BAFTISMA TAKE NUFI?

3. Idan mutum ya yi baftisma, mene ne hakan yake nuna wa mutane?

3 Saꞌad da ka yi baftisma, kana nuna wa mutane cewa ka amince da gaskiya game da Jehobah da kuma Yesu Kristi. Ka tuba daga zunubanka. Ka kuma yi canje-canjen da kake bukata don ka iya bauta wa Jehobah. Ƙari ga haka, kana nuna ka amince cewa ta wurin Yesu ne kawai za mu iya samun ceto. Kuma ka yi wa Jehobah alkawari cikin adduꞌa cewa za ka bauta masa tare da bayinsa. Da zarar ka yi wannan alkawarin kuma ka yi baftisma, ka soma rayuwa da za ta kai ga rai na har abada.

4. Idan aka nitsar da mutum cikin ruwa kuma aka fitar da shi, mene ne hakan yake nufi? (Ka kuma duba hoton.)

4 Saꞌad da ake yi wa mutum baftisma, akan nitsar da shi cikin ruwa kuma a fito da shi.a Kamar dai an binne mutumin ne kuma aka ta da shi. (Ka duba Kolosiyawa 2:12.) Me ya sa kwatancin nan ya dace? Saꞌad da aka nitsar da mutum cikin ruwa, hakan na nufin cewa ya bar irin rayuwar da yake yi a dā. Kuma idan aka fitar da mutumin daga ruwan, hakan na nuna cewa ya soma sabuwar rayuwa na yin abubuwan da za su faranta wa Allah rai.

Hotuna: Wani mutum da ake yi masa baftisma bayan ya daina wasu munanan halaye. Na 1. Yana kallon masu dambe a talabijin yana farin ciki. Na 2. Yana shan taba. Na 3. Yana shan giya da yawa. Na 4. Daga baya, ana masa baftisma.

Idan ka yi baftisma, kana nuna cewa ka daina yin rayuwa kamar yadda kake yi a dā kuma daga lokacin za ka riƙa yin abubuwan da za su sa Jehobah farin ciki (Ka duba sakin layi na 4)


5. Ta yaya aikin da muke yi don mu yi baftisma ya yi kama da aikin gina jirgi da Nuhu ya yi? (1 Bit. 3:​18-21)

5 Karanta 1 Bitrus 3:​18-21. Za mu iya kwatanta ayyukan da muke yi kafin mu yi baftisma da aikin da Nuhu ya yi don ya gina jirgi. Idan ka soma nazarin Littafi Mai Tsarki, za ka iya ganin kamar yin abubuwan da za su sa ka cancanci yin baftisma jan aiki ne, kamar gina jirgi da Nuhu ya yi. Shin, muna bukatar yin dukan waɗannan ayyukan ne? Hakika. Me ya sa muka ce hakan? Ka yi tunani game da labarin Nuhu. Jehobah ya gaya masa dalla-dalla yadda zai gina jirgin, kuma Nuhu ya bi daidai umurnin da Jehobah ya ba shi don ya tsira. Jehobah ya taimaka wa Nuhu ya cim ma aikin da ya ba shi domin Nuhu yana da bangaskiya gare shi, kuma ya yi masa biyayya. Kamar Nuhu, kai ma za ka iya yin nasara a bin dukan umurnan Jehobah.—Far. 6:22.

6. Mene ne Bitrus yake nufi saꞌad da ya ce baftisma ta cece ku?

6 A 1 Bitrus 3:​21, manzo Bitrus ya rubuta cewa baftisma ta “cece ku.” Amma, ba yin baftisma ne kawai abin da muke bukatar mu yi don a gafarta mana zunubanmu ba. Hadayar Yesu ce kawai ta sa mu sami gafarar zunubanmu. (1 Yoh. 1:7) Duk da haka, yin baftisma yana da muhimmanci sosai domin Jehobah ya ba da umurni mu yi hakan. Kuma idan muka yi baftisma, muna roƙon Allah ya taimaka mana mu kasance da tabbaci cewa ya yafe mana, kuma zuciyarmu ba za ta ci-gaba da daminmu ba. Jehobah zai yi farin cikin amsa adduꞌarmu. Saboda haka, za mu iya cewa baftisma tana ceton mu, wato, tana sa mu sami begen yin rayuwa har abada.

YADDA AKE YIN BAFTISMA

7. Ta yaya ake yin baftisma?

7 Littafi Mai Tsarki bai gaya mana abubuwa da yawa game da baftisma ba. Amma ya nuna sarai cewa saꞌad da ake yi wa mutum baftisma ana bukatar a nitsar da shi gabaki ɗaya cikin ruwa. Ƙari ga haka, Littafi Mai Tsarki ya taimaka mana mu san abubuwan da ya kamata mu yi a lokacin baftisma. Alal misali, ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki za su taimaka wa waɗanda suke so su yi baftisma su san irin kayan da za su saka a ranar. Za su kuma taimaka wa waɗanda suke kallo saꞌad da ake yin baftisma su yi hakan a hanyar da ta dace. (1 Kor. 14:40; 1 Tim. 2:9) A yau, ana zaɓan wasu dattawa su riƙa yi wa mutane baftisma. Amma hakan ba ya sa mu daraja su fiye da kima. (1 Kor. 1:​14, 15) Ban da haka ma, ko da mutane kaɗan ne, ko da yawa ne suke kallo saꞌad da ake yin baftisma, ba shi ne ya fi muhimmanci ba.—A. M. 8:36.

8. Waɗanne tambayoyi ne ake yi wa waɗanda suke so su yi baftisma, kuma me ya sa? (A. M. 2:​38-42) (Ka kuma duba hoton.)

8 Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa “da baki ne mutum yake shelar samun ceto.” (Rom. 10:​9, 10) Ba kawai lokacin da muke yi wa mutane waꞌazi ne muke yin wannan shelar ba. Muna kuma yin hakan a ranar da muke baftisma. Shi ya sa ake yi wa waɗanda za su yi baftisma tambayoyi biyun nan. Na farkon shi ne, “Kun tuba daga zunubanku, kun yi alkawarin bauta wa Jehobah, kuma kun gaskata da hanyar ceto da Allah ya yi ta wurin Yesu Kristi?” Ana wannan tambayar don a nanata abubuwan da mutumin ya riga ya yi don ya cancanci yin baftisma. Bitrus ya faɗi wani abu makamancin hakan a ranar Fentakos, saꞌad da ya gaya wa mutanen cewa su tuba kuma su yi baftisma. Tambaya ta biyu ita ce, “Kun fahimci cewa yin baftisma zai nuna cewa ku Shaidun Jehobah ne masu tarayya da ƙungiyarsa?” Ana wannan tambayar don mutumin ya san abin da zai yi bayan ya yi baftisma. Mutumin ya yi alkawarin bin ja-gorancin ƙungiyar Jehobah da kuma bauta masa tare da bayinsa. Hakan yana kama da abin da mutane suka yi bayan da suka yi baftisma a ranar Fentakos. (Karanta Ayyukan Manzanni 2:​38-42.) Waɗanda suka amsa waɗannan tambayoyin da babbar murya sun cancanci su yi baftisma.

Waɗanda za su yi baftisma manya da ƙanana a wani taron daꞌira sun tashi tsaye suna amsa tambayoyin da ake musu.

Waɗanda suke so su yi baftisma sukan amsa tambayoyi a gaban jamaꞌa (Ka duba sakin layi na 8)d


9. Waɗanne abubuwa ne muke bukatar mu yi don mu kasance da dangantaka mai kyau da Jehobah?

9 Mai yiwuwa kafin ka koyi gaskiya, kana iya ƙoƙarinka wajen yin abubuwan da suka dace. Kuma ba ka yi zunubi mai tsanani ba. Wataƙila iyayenka Shaidu ne kuma sun taimaka maka ka ƙaunaci Jehobah. Idan haka ne, shin kana bukatar ka tuba kuma ka yi baftisma don ka kasance da dangantaka mai kyau da Allah? Ƙwarai kuwa. Dukanmu mun gāji zunubi. Don haka, muna yin wasu abubuwan da Allah ba ya so. (Zab. 51:5) Amma yayin da muke ƙara koyan game da Jehobah, za mu so mu riƙa yin abubuwan da yake so. Hakan zai sa mu tuba, mu daina yin duk wani abin da Allah ba ya so, kuma mu soma yin rayuwa yadda Ubanmu na sama yake so. Hakan zai sa mu cancanci yin baftisma.—A. M. 3:19.

10. Me kake bukatar ka yi idan ka yi baftisma a wani addinin a dā?

10 Ko da ka yi baftisma a wani addinin a dā, kana bukatar ka sake yin baftisma don ka zama ɗaya daga cikin Shaidun Jehobah. Me ya sa? Domin a dā, ba ka san gaskiya game da Allah da Yesu ba. Kuma ko da ka yi alkawarin bauta wa Allah, ka yi hakan ba tare da sanin ainihin abin da Allah yake bukata a gare ka ba. Saꞌad da manzo Bulus ya haɗu da wasu mutane a Afisa da suka yi baftisma ba tare da sanin koyarwar Yesu ba, ya sa an sake yi musu baftisma.b (A. M. 19:​1-5) A yau ma, Jehobah yana amincewa da baftismar mutanen da suka san gaskiya game da shi, da kuma abubuwan da yake bukata a gare su.

“A CIKIN SUNAN UBA, DA NA ƊA, DA NA RUHU MAI TSARKI”

11. Mene ne yin baftisma “a cikin sunan Uba, da na Ɗa, da na ruhu mai tsarki” yake nufi? (Matiyu 28:​18-20)

11 Yesu ya ce waɗanda suke so su zama mabiyansa suna bukatar su yi baftisma “a cikin sunan Uba, da na Ɗa, da na ruhu mai tsarki.” (Karanta Matiyu 28:​18-20.) Mene ne hakan yake nufi? A Littafi Mai Tsarki, sunan mutum yana nufin yadda mutane suke ɗaukan sa. Yana kuma nufin matsayin mutumin ko kuma ikonsa. Saboda haka, idan aka yi abu a cikin sunan mutum, hakan yana nufin cewa an yi laꞌakari da ikon da mai sunan yake da shi. Bari mu ga yadda za mu nuna cewa muna laꞌakari da matsayi da kuma ikon Uba, da na Ɗa, da na ruhu mai tsarki saꞌad da muka yi baftisma.

12. Mene ne yin baftisma cikin sunan Uba ya ƙunsa? (Ruꞌuyar da Aka Yi wa Yohanna 4:11) (Ka kuma duba hoton.)

12 Yin baftisma a cikin sunan Uba. Hakan ya ƙunshi yin imani cewa Jehobah ne Ubanmu na sama, kuma shi ne ya ba mu rai. Shi ne ya halicci kome da kome, kuma shi ne mai iko duka. (Karanta Ruꞌuyar da Aka Yi wa Yohanna 4:11.) Ya kuma ƙunshi yin imani cewa yana jin adduꞌoꞌinmu. Muna amfani da sunansa saꞌad da muke adduꞌa, kuma muna gaya wa mutane game da shi. (Zab. 65:2) Amma ba shi ke nan ba. Waɗanda Bitrus ya yi musu magana a ranar Fentakos sun riga sun san Jehobah. Amma suna bukatar su fahimci cewa Jehobah ne ya ba su damar yin rayuwa har abada ta wurin fansar Yesu Kristi.—Rom. 5:8.

Ɗaya daga cikin ꞌyanꞌuwa mata da suka yi baftismar tana adduꞌa a gidanta.

Bayan ka yi baftisma, ka ci-gaba da yin biyayya ga Uba da Ɗan, kuma ka bi ja-gorancin ruhu mai tsarki (Ka duba sakin layi na 12)


13. Mene ne yin baftisma cikin sunan Ɗa ya ƙunsa? (Ka kuma duba hoton.)

13 Yin baftisma a cikin sunan Ɗa. Hakan ya ƙunshi yin imani cewa Yesu ne Ɗan Allah makaɗaici. Da kuma yin imani cewa ta wurinsa ne kaɗai za mu iya kasancewa da dangantaka mai kyau da Jehobah. (Yoh. 14:6) Ƙari ga haka, mun yarda cewa Yesu ne wanda ya ba da ransa don mu iya samun rai. Shi ya sa muke so mu bi misalinsa kowace rana a rayuwarmu, ba kawai a ranar da za mu yi baftisma ba. (1 Yoh. 2:6) Kamar Yesu, ba ma barin kome ya hana mu yin waꞌazi. (Luk. 4:43) Muna ma a shirye mu jimre tsanantawa, kuma muna bauta wa Allah da aminci. (2 Tim. 3:12) Ƙari ga haka, yin baftisma cikin sunan Ɗa ya ƙunshi bin ja-gorancin waɗanda Yesu ya naɗa su kula da mabiyansa.—Afis. 4:​8, 11, 12; 5:23.

Ɗaya daga cikin ꞌyanꞌuwa maza da suka yi baftismar yana karanta wa wani mutum wata aya a Littafi Mai Tsarki saꞌad da suke waꞌazi.

Bayan ka yi baftisma, ka ci-gaba da yin biyayya ga Ɗan wato, Yesu Kristi (Ka duba sakin layi na 13)


14. (a) Mene ne yin baftisma a cikin sunan ruhu mai tsarki ya ƙunsa? (Ka kuma duba hoton.) (b) Waɗanne baftisma ne kuma shafaffu suke yi? (Ka kuma duba akwatin nan “Baftismar da Shafaffu Suke Yi.”)

14 Yin baftisma a cikin sunan ruhu mai tsarki. Hakan ya ƙunshi sanin gaskiya game da ruhu mai tsarki. Ruhu mai tsarki ba wata halitta ba ce. Kuma ba ɗaya ne daga cikin allah uku cikin ɗaya da ake koyarwa ba. Ruhu mai tsarki iko ne da Allah yake amfani da shi wajen yin abubuwa. Ƙari ga haka, yin baftisma a cikin sunan ruhu mai tsarki ya ƙunshi yin imani cewa Jehobah ya yi amfani da ruhu mai tsarki wajen taimaka wa annabawansa su san abubuwan da za su faɗa. Da kuma taimaka wa marubutan Littafi Mai Tsarki su rubuta abin da yake so. (2 Bit. 1:​20, 21) Ban da haka ma, za mu guje wa yin zunubi mai tsanani. Domin rashin yin hakan zai iya hana mu da ikilisiya gabaki ɗaya samun ruhu mai tsarki.—Afis. 4:30.

Ɗaya daga cikin ꞌyanꞌuwa mata da suka yi baftismar tana karanta Littafi Mai Tsarki a gidanta.

Bayan ka yi baftisma, ka ci-gaba da bin ja-gorancin ruhu mai tsarki (Ka duba sakin layi na 14)


Baftismar da Shafaffu Suke Yi

Ban da baftismar da ake yi da ruwa, akwai wasu baftisma kuma da shafaffu suke yi.

  • Ana musu baftisma da ruhu mai tsarki lokacin da aka zaɓe su su yi mulki tare da Yesu a sama. (Mat. 3:11)

  • Suna baftisma wadda ta nuna cewa su na Almasihu ne. Hakan yakan sa su ƙulla dangantaka ta kud da kud da Yesu har ana iya kiran su jikin Kristi. (Gal. 3:​27, 28; 1 Kor. 12:27)

  • Suna kuma yin baftisma cikin mutuwar Yesu. Hakan yana nufin cewa suna bukatar su bi misalinsa har lokacin da za su mutu, kuma a ta da su zuwa rayuwa a sama. (Rom. 6:​3-5)

15. Mene ne ka ƙudura niyyar yi?

15 Idan ka riga ka yi baftisma, ka ci-gaba da tuna wa kanka muhimmancin baftismarc da ka yi. Kuma ka yi ƙoƙari ka cika alkawarin da ka yi wa Jehobah. Amma idan ba ka riga ka yi baftisma kuma ba fa? Akwai abin da ya hana ka yin hakan? A talifi na gaba, za mu tattauna abin da za ka iya yi don ka cancanci yin baftisma.

MECE CE AMSARKA?

  • Mene ne nitsar da mutum cikin ruwa da kuma fitar da shi lokacin da ake yi masa baftisma yake nufi?

  • Waɗanne tambayoyi ne ake yi wa waɗanda suke so su yi baftisma, kuma me ya sa?

  • Mene ne yin baftisma “a cikin sunan Uba, da na Ɗa, da naruhu mai tsarki” yake nufi?

WAƘA TA 161 Ina Son Yin Nufinka

a A Littafi Mai Tsarki, kalmar nan “baftisma,” tana nufin “somawa” ko kuma “nitsarwa.” Saboda haka, idan ana yi wa mutum baftisma ana nitsar da shi gabaki ɗaya cikin ruwa, ba kawai yayyafa masa ruwa kamar yadda wasu addinai suke yi ba.

b Waɗannan mutanen da ke Afisa “baftismar Yohanna ce” suka yi. (A. M. 19:3) Yohanna Mai Baftisma ya ƙarfafa Yahudawa su tuba daga rashin bin Dokar Musa. Kuma Yohanna ya yi wa waɗanda suka tuba baftisma. (Mar. 1:​4, 5) Amma bayan da aka daina bin Dokar Musa, Jehobah ya daina amincewa da irin baftismar nan. Daga lokacin, Allah yana amincewa da baftisma ɗaya kawai, wadda take kai ga samun ceto.—Afis. 4:5.

c Ka duba talifin nan mai jigo, “Mene ne Maꞌanar Kalmar Nan Baftisma?” da ke sashen “Amsoshin Tambayoyin Littafi Mai Tsarki” a jw.org/ha da kuma manhajar JW Library.®

d BAYANI A KAN HOTO: Waɗanda suke so su yi baftisma a wani taron yanki sun tashi tsaye suna nuna bangaskiyarsu ta wajen amsa tambayoyin da ake musu.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba