Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w25 Nuwamba pp. 8-9
  • Zai Dace In Daina Yin Tuƙi?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Zai Dace In Daina Yin Tuƙi?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Ƙananan Jigo
  • KA LURA DA YADDA KAKE TUƘI
  • TA YAYA LITTAFI MAI TSARKI ZAI TAIMAKA MAKA KA TSAI DA SHAWARA MAI KYAU
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
w25 Nuwamba pp. 8-9
Wani ɗanꞌuwan da ya tsufa zaune kusa da wundonsa, yana kallon motarsa da ke waje. Ya riƙe maƙullin motar yana tunani.

Zai Dace In Daina Yin Tuƙi?

KA YI shekaru kana tuƙi. Kuma kana jin daɗin tuƙi zuwa duk inda kake so. Amma iyalinka da abokanka suna damuwa kuma suna so ka daina tuƙi. Kai kuma kana mamakin dalilin da ya sa suke irin wannan tunanin.

Irin yanayin da kake ciki ke nan? Idan haka ne, mene ne zai taimaka maka ka san ko za ka ci-gaba da yin tuƙi?

A wasu ƙasashe, idan mutum ya kai wasu shekaru, dole likita ya duba shi kuma ya ba shi izini, kafin ya ci-gaba da yin tuƙi. ꞌYanꞌuwanmu da suke ƙasashen nan suna bin irin wannan dokar. (Rom. 13:1) Amma ko da ba ka zama a irin ƙasashen nan, akwai shawarwarin da za su taimaka maka ka san ko za ka ci-gaba da yin tuƙi.

KA LURA DA YADDA KAKE TUƘI

Wata ƙungiya da ke kula da hakkin waɗanda suka tsufa, ta ce za su iya yi wa kansu waɗannan tambayoyin:

  • Yana mini wuya in ga alamun da ake sa a kan hanya da kyau, ko in ga wuri da dare?

  • Ina iya juya kaina in duba madubi ko kuma wuraren da madubi ba ya iya nunawa da kyau?

  • Saꞌad da nake tuƙi, zan iya ɗaukan mataki da wuri, alal misali, in cire ƙafata daga kan totur in mai da shi kan birki?

  • Ina tuƙi a hankali har ma in jawo go-sulo?

  • Na kusan yin hatsari kwanan nan, ko kuwa akwai wuraren da suka lanƙwashe ko suka goggoge a motata don na bugi wasu abubuwa?

  • ꞌYan sanda sun taɓa tsai da ni don yadda nake tuƙi?

  • Barci ya taɓa ɗauke ni saꞌad da nake tuƙi?

  • Akwai magungunan da nake sha da za su iya shafan yadda nake tuƙi?

  • Iyalina ko kuma abokaina sun taɓa gaya min cewa yadda nake tuƙi yana tayar musu da hankali?

Idan amsarka e ce, ga ɗaya ko biyu daga cikin tambayoyin nan, zai dace ka yi wasu canje-canje. Alal misali, za ka iya rage yin tuƙi musamman da dare. Kuma ka yi laꞌakari da yadda kake tuƙi kowane lokaci. Za ka iya tambayar wani a iyalinka ko abokinka ya gaya maka gaskiya game da yadda kake tuƙi. Ƙari ga haka, za ka iya zuwa wurin da za ka koyi yadda za ka ƙara lura yayin da kake tuƙi. Amma idan amsarka e ce ga tambayoyi da dama da aka yi a sama, zai fi alheri ka daina tuƙi.a

TA YAYA LITTAFI MAI TSARKI ZAI TAIMAKA MAKA KA TSAI DA SHAWARA MAI KYAU

A wasu lokuta, yana da wuya mu gane cewa ba ma iya yin tuƙi da kyau kamar yadda muke yi a dā. Kuma idan aka ce mu daina tuƙi, hakan zai iya ɓata mana rai. Ta yaya Littafi Mai Tsarki zai iya taimaka maka ka kasance da raꞌayin da ya dace kuma ka yanke shawara mai kyau? Ga ƙaꞌidodi biyu.

Ka zama mai sauƙin kai. (K. Mag. 11:2) Yayin da mutum ya soma tsufa, idanunsa, da kunnuwansa, da jikinsa gabaki ɗaya za su soma gajiya. Yawancin mutanen da suka soma tsufa, sukan daina buga wasu irin wasanni don sun san cewa za su iya jin rauni. Haka ma yake da yin tuƙi. Mutum mai sauƙin kai zai daina yin tuƙi idan ya san cewa yin hakan zai sa ransa a cikin hadari. (K. Mag. 22:3) Kuma idan wasu mutane sun soma damuwa game da yadda muke yin tuƙi, mutum mai sauƙin kai yakan saurare su kuma ya bi shawararsu.—Ka duba 2 Samaꞌila 21:​15-17.

Kada ka jawo wa kanka alhakin jini. (M. Sha. 22:8) Idan mutum ba ya tuƙa mota yadda ya dace, zai iya ji wa wasu rauni ko kuma ya kashe su. Idan mutum ya ci-gaba da yin tuƙi duk da cewa ba ya iya tuƙi da kyau kuma, zai iya kashe kansa ko ya kashe wasu. Kuma idan wani ya mutu don yadda muke tuƙi, za mu iya ɗaukan alhakin jinin mutumin.

Kada ka ga kamar wasu ba za su daraja ka ba idan ka daina tuƙi. Jehobah yana ƙaunar ka, kuma yana farin ciki don ka san kasawarka, kana da sauƙin kai, kuma ka damu da lafiyan wasu. Ya yi alkawari cewa zai ci-gaba da taimaka da kuma ƙarfafa ka. (Isha. 46:4) Ba zai taɓa barin ka ba. Saboda haka, idan kana so ka yanke shawara ko za ka daina yin tuƙi, ka roƙe shi ya ba ka hikima kuma ka bi ƙaꞌidodinsa.

Yadda Wasu Za Su Taimaka

ꞌYan iyalin wanda ya tsufa ne za su fi gaya masa gaskiya game da yadda yake tuƙi. Idan kai abokin wani ne da ya tsufa, kuma ka ji mutane suna damuwa da yadda yake tuƙi, kada ka yi watsi da abin da suke faɗa. Za ka ma iya bin sa ya yi tuƙi ka gani. Idan da bukata, ka tattauna da shi game da yadda yake tuƙi. Idan kana masa magana, ka yi tunanin yadda za ka ji da a ce kai ne. Ka gaya masa gaskiya, amma ka yi hakan da alheri. Kar ka yi ta magana game da shekarunsa. Amma ka mai da hankali ga yadda yake tuƙi. Ka gaya masa cewa, “ka damu ne da yadda yake tuƙi,” maimakon ka gaya masa cewa, “bai iya tuƙi da kyau kuma ba.” Ka tuna masa ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki da aka ambata a wannan talifin, kuma ka gaya masa ka san cewa yana so ya bi ƙaꞌidodin nan.

Ya kamata mu yi tunani a kan yadda mutum yake ji a duk lokacin da ya daina tuƙi. Zai ji kamar ya rasa ꞌyancinsa ne kuma bai da amfani. Ta yaya za ka iya taimaka masa? Ka taya shi yin wasu abubuwa kuma ka nuna cewa kana ƙaunar sa. (K. Mag. 17:17) Kada ka jira sai ya roƙe ka ka ɗauke shi a mota don zai ji kamar yana taƙura maka ne. Za ka iya gaya masa cewa, za a shirya yadda za a riƙa kai shi wasu wurare kamar, taro, da waꞌazi, da zuwa kasuwa da kuma asibiti. Ka gaya masa cewa kana so ka taimaka masa kuma kana so ku yi abubuwa tare.—Rom. 1:​11, 12.

a Don ƙarin bayani, ka duba talifin nan, “Automobile Accidents—Are You Safe?” a Awake! na 22 ga Agusta, 2002.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba