TALIFIN NAZARI NA 45
WAƘA TA 111 Dalilan da Suke Sa Mu Murna
Yadda Za Mu Ci-gaba da Farin Ciki Idan Muna Kula da Wanda Ya Tsufa ko Marar Lafiya
“ Masu shuka da hawaye za su yi girbi da waƙoƙin farin ciki.”—ZAB. 126:5.
ABIN DA ZA MU KOYA
Za mu ga wasu shawarwarin da za su taimaka mana mu ci-gaba da yin farin ciki idan muna kula da wani aboki ko danginmu da ya tsufa ko kuma yana ciwo.
1-2. Yaya Jehobah yake ɗaukan waɗanda suke kula da marasa lafiya ko waɗanda suka tsufa? (Karin Magana 19:17) (Ka kuma duba hotunan.)
WANI ɗanꞌuwa mai suna Jin-yeol daga Koriya ya ce: “Ni da matata mun yi fiye da shekaru 32 da aure. Amma a cikin shekaru biyar da suka shige, ina kula da ita don tana fama da wata cuta mai tsanani. Kuma da ƙyar take motsa jikinta. Ina ƙaunar matata sosai kuma ina jin daɗin kula da ita. Kowane dare, tana barci a wani gado na musamman da likita ya ce ta riƙa amfani da shi a gida. Nakan kawo gadona kusa da nata kuma muna riƙe hannun juna saꞌad da muke barci.”
2 Mai yiwuwa kana kula da wani a iyalinku da ya tsufa ko yana rashin lafiya, ko kuma wani abokinka. Idan haka ne, babu shakka kana farin ciki don kana iya taimaka wa mutumin. Ƙari ga haka, kana yin hakan don kana ƙaunar Jehobah. (1 Tim. 5:4, 8; Yak. 1:27) Duk da haka, a wasu lokuta, yin wannan aikin bai da sauƙi. Wataƙila kana ganin kamar ba wanda ya san wahalar da kake sha. Mai yiwuwa kana murmushi idan kana tare da mutane, amma idan kana nan kai kaɗai, kana baƙin ciki har ka zub da hawaye. (Zab. 6:6) Ko da mutane ba su san famar da kake yi ba, Jehobah ya sani. (Ka kuma duba Fitowa 3:7.) Yana ganin hawayen da kake zubarwa, kuma yana ɗaukan sadaukarwa da kake yi da muhimmanci. (Zab. 56:8; 126:5) Yana ganin kome da kake yi don ka kula da wanda kake ƙauna. Jehobah yana ɗaukan komen da kake yi a matsayin bashi ne da kake bin sa. Ya yi alkawari zai biya ka kuma ya albarkace ka.—Karanta Karin Magana 19:17.
ꞌYanꞌuwa maza da mata suna aiki sosai wajen kula da tsofaffi ko marasa lafiya (Ka duba sakin layi na 2)
3. Waɗanne abubuwa ne Ibrahim da Saratu suka yi fama da su saꞌad da suke kula da Tera?
3 A Littafi Mai Tsarki, akwai labaran mutanen da suka kula da marasa lafiya da kuma waɗanda suka tsufa. Ibrahim da Saratu suna cikin irin mutanen nan. A lokacin da suka bar Ur, shekarun mahaifinsu, wato Tera, wajen 200 ne. Duk da haka, ya tafi tare da su. Sun yi tafiya mai nisan wajen kilomita 960 zuwa Haran. (Far. 11:31, 32) Ibrahim da Saratu suna ƙaunar Tera sosai, amma kula da shi saꞌad da suke tafiya, ba zai zama musu da sauƙi ba domin ya tsufa. Mai yiwuwa sun yi tafiyar ne a kan raƙuma ko jakuna, kuma hawan irin dabbobin nan ba zai yi wa Tera sauƙi ba. Mai yiwuwa a wasu lokuta Ibrahim da Saratu sun gaji sosai saꞌad da suke kula da shi. Ko da mene ne dai ya faru, babu shakka Jehobah ya ba su ƙarfin da suke bukata. Kamar yadda Jehobah ya taimaka wa Ibrahim da Saratu, zai taimaka maka kai ma ka sami ƙarfin kula da wanda kake ƙauna.—Zab. 55:22.
4. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?
4 Idan kana farin ciki, zai yi maka sauƙi ka ci-gaba da kula da wanda da ke rashin lafiya, ko wanda ya tsufa. (K. Mag. 15:13) Ka tuna cewa, za ka iya yin farin ciki ko da a wane irin yanayi ne kake ciki. (Yak. 1:2, 3) Mene ne za ka iya yi don ka ci-gaba da yin farin ciki? Ka roƙi Jehobah ya taimaka maka ka ga dalilan da za su sa ka farin ciki. Ƙari ga haka, akwai wasu abubuwa kuma da za su taimaka maka ka ci-gaba da yin farin ciki. A wannan talifin, za mu tattauna wasu daga cikin su. Za mu kuma ga abin da wasu za su iya yi don su taimaka. Da farko, bari mu tattauna dalilin da ya sa masu kula da waɗanda suka tsufa ko suke rashin lafiya suke bukatar su ci-gaba da farin ciki, da kuma dalilin da ya sa yin hakan zai iya yin wuya.
DALILIN DA YA SA YIN FARIN CIKI SAꞌAD DA KAKE KULA DA WANI ZAI IYA YIN WUYA
5. Me ya sa muke bukatar mu ci-gaba da farin ciki saꞌad da muke kula da wani?
5 Idan muna mai da hankali kawai a kan faman da muke yi saꞌad da muke kula da wani, hakan zai iya sa mu sanyin gwiwa. (K. Mag. 24:10) Kuma idan hakan ya faru, ba za mu iya taimaka musu kamar yadda ya kamata ba. Waɗanne abubuwa ne za su iya sa waɗanda suke kula da wani su daina yin farin ciki?
6. Me ya sa waɗanda suke kula da wani suke gajiya sosai?
6 Suna gajiya sosai. Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Leah ta ce: “Ko da a ranar da kome ya tafi daidai, nakan gaji tilis har ma ba na iya yin kome da yamma. A wasu lokuta, ba na ma iya tura saƙo ta waya.” Wasu kuma ba sa samun isashen barci ko su sami lokacin hutawa. Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Inés ta ce: “Ba na samun isashen barci. Kowane awa biyu da dare, nakan tashi don in kula da mamar maigidana. Kuma ni da maigidana mun yi shekaru ba mu taɓa zuwa wani wuri don mu huta ba.” Wasu kuma ba sa iya fita shakatawa da abokai ko yin wasu ayyuka a ƙungiyar Jehobah domin a kowane lokaci, suna bukatar su kasance da wanda suke kula da shi. Hakan zai iya sa su baƙin ciki domin suna ganin yadda rayuwarsu ta canja gabaki ɗaya.
7. Me ya sa waɗanda suke kula da wani suke baƙin ciki ko su ji kamar ba sa iya ƙoƙarinsu?
7 Suna ji kamar ba sa iya ƙoƙarinsu. Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Jessica ta ce: “A yawancin lokuta ina ji kamar ina bukatar in ƙara taimaka wa mahaifina. Kuma ba na jin daɗi idan na bar shi na je ina hutawa.” Wasu da suke kula da wani, suna ganin ba sa iya ƙoƙarinsu wajen taimaka wa mutumin. A wasu lokuta, sukan ji kamar ba za su iya ci-gaba da kula da su ba. Wasu kuma suna baƙin ciki don yadda suka yi wa wanda suke kula da shi baƙar magana saꞌad da suka gaji. (Yak. 3:2) Ƙari ga haka, wasu suna baƙin ciki don yadda yanayin wanda suke kula da shi yake daɗa taɓarɓarewa. Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Barbara ta ce: “Idan na ga cewa jikin wanda nake ƙauna sai ƙara tsanani yake yi, hakan yana sa ni baƙin ciki sosai.”
8. Yaya wasu suka ji saꞌad da waɗanda suke taimaka wa suka gode musu?
8 Wasu suna ganin kamar ba a ganin ƙoƙarinsu. Me ya sa? Domin mutane kaɗan ne suke yaba musu don aiki tuƙuru da kuma sadaukarwar da suke yi. Saboda haka zai dace mu riƙa yaba wa irin mutanen nan. (1 Tas. 5:18) Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Melissa ta ce: “A wasu lokuta, nakan yi kuka domin na karaya ko kuma na gaji sosai. Amma idan waɗanda nake kula da su suka gode min don abin da nake musu, hakan yana ba ni ƙarfi kuma yana sa in so ci-gaba da kula da su.” Wani ɗanꞌuwa mai suna Ahmadu da matarsa, da suke kula da ꞌyar ƙanwar matar da take rashin lafiya sosai, sun faɗi yadda suke ji idan ta gode musu. Ɗanꞌuwa Ahmadu ya ce: “Mai yiwuwa ba za ta fahimci dukan abubuwan da muke yi don mu kula da ita ba, amma muna farin ciki idan ta gaya mana cewa ta gode, ko idan ta ce tana ƙaunar mu.”
YADDA ZA KA CI-GABA DA YIN FARIN CIKI
9. Ta yaya waɗanda suke kula da wani za su nuna cewa sun san kasawarsu?
9 Ka san abin da za ka iya yi da wanda ba za ka iya yi ba. (K. Mag. 11:2) Ba komen da kake so ka yi ba ne za ka iya yi ba. Saboda haka, a wasu lokuta za ka iya ƙin yin wasu abubuwa da mutane suke so ka yi. Hakan ba laifi ba ne, a maimakon haka, kana nuna cewa ka san kasawarka. Idan wasu suna so su taimaka maka, ka ba su damar yin hakan. Wani ɗanꞌuwa mai suna Jay ya ce: “Kowace rana muna aiki iya gwargwadon ƙarfinmu. Idan ba mu yi abin da ya fi ƙarfinmu ba, hakan zai sa mu ci-gaba da yin farin ciki.”
10. Me kake bukatar ka sani idan kana kula da wani? (Karin Magana 19:11)
10 Ka yi ƙoƙari ka san abin da ya sa wanda kake kula da shi yake yin wasu abubuwa. (Karanta Karin Magana 19:11.) Yin hakan zai sa ka kwantar da hankalinka, idan wanda kake taimaka wa ya yi ko faɗi wani abin da ya ɓata maka rai. Gaskiyar ita ce, wasu cututtuka masu tsanani, za su iya sa mutum ya soma yin abubuwan da ba ya yi a dā. (M. Wa. 7:7) Alal misali, mutumin da a dā yana magana a hankali kuma cikin alheri, zai iya soma gardama da kai, ko ya ƙi gamsuwa da abin da kake masa, ko ya zama mai saurin fushi. Idan kana kula da wani da ke fama da ciwo mai tsanani, zai dace ka ɗan yi bincike don ka san yadda cutar take shafan mutum. Yin hakan zai taimaka maka ka san cewa abin da yake yi ko faɗa, ba da saninsa ba ne.—K. Mag. 14:29.
11. Waɗanne abubuwa masu muhimmanci ne waɗanda suke kula da wani suke bukatar su nemi lokacin yi kowace rana? (Zabura 132:4, 5)
11 Ka nemi lokaci don ƙarfafa dangantakarka da Jehobah. A wasu lokuta, kana bukatar ka rage lokacin da kake yin wasu abubuwa don ka sami damar yin abubuwan da suka “fi muhimmanci.” (Filib. 1:10, NWT.) Ɗaya daga cikin abubuwan nan masu muhimmanci shi ne, ƙarfafa dangantakarka da Jehobah. Ko da yake Dauda sarki ne da yake da ayyuka da yawa, ya sa bautar Jehobah farko a rayuwarsa. (Karanta Zabura 132:4, 5.) Haka ma, zai dace ka nemi lokaci kowace rana don ka yi adduꞌa da kuma karatun Littafi Mai Tsarki. Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Elizaa ta ce: “Idan na yi adduꞌa ga Jehobah, na karanta littafin zabura, kuma na yi tunani a kan abubuwa masu ban ƙarfafa da na karanta, hakan yana kwantar mini da hankali kuma yana sa ni farin ciki. Yin adduꞌa ga Jehobah ne ya fi taimaka mini. Sau da yawa kowace rana, nakan roƙi Jehobah ya taimaka min in kasance da kwanciyar hankali.”
12. Me ya sa waɗanda suke kula da wani suke bukatar su nemi lokaci don su kula da lafiyarsu?
12 Ka kula da lafiyar ka. Yana yi wa masu kula da wani wuya su sami lokacin saya ko dafa abincin da zai gina jikinsu. Amma za ka fi kasancewa da ƙoshin lafiya idan kana cin abinci masu gina jiki da kuma motsa jiki a kai a kai. Saboda haka ka nemi lokaci, don cin abinci masu gina jiki kuma ka riƙa motsa jiki. (Afis. 5:15, 16) Ƙari ga haka, ka riƙa samun isashen barci. (M. Wa. 4:6) Bincike ya nuna cewa samun isashen barci yana sa ƙwaƙwalwa ta gyara kanta. Wani talifi mai jigo, “How Sleep Can Affect Stress,” ya ce idan mutum ya sami isashen barci, ba zai riƙa damuwa ba, kuma zai kasance da kwanciyar hankali a yanayi mai wuya. Ƙari ga haka, za ka bukaci ka nemi lokaci don shakatawa. (M. Wa. 8:15) Wata ꞌyarꞌuwa ta faɗi abin da ya sa ta ci-gaba da farin ciki. Ta ce: “Idan ana rana, nakan fita waje in sha ranar. Kuma aƙalla sau ɗaya a wata, nakan shirya yin wani abin da nake jin daɗinsa da abokiyata.”
13. Me ya sa yake da kyau mu riƙa yin dariya? (Karin Magana 17:22)
13 Ka riƙa yin abubuwan da za su sa ka dariya. (Karanta Karin Magana 17:22; M. Wa. 3:1, 4) Yin dariya yana kawo lafiyar jiki da kuma ƙwaƙwalwa. A yawancin lokuta, idan kana kula da wani, abubuwa ba sa tafiya daidai. Amma idan kana ɗaukan yanayin yadda suke, kuma kana dariyar hakan zai rage maka yawan damuwa. Kuma idan kana dariya tare da wanda kake kula da shi, hakan zai ƙara danƙon zumuncin da ke tsakaninku.
14. Ta yaya tattaunawa da wani da ka yarda da shi zai taimake ka?
14 Ka tattauna da wani da ka yarda shi. Ko da kana iya ƙoƙarinka don ka ci-gaba da yin farin ciki, a wasu lokuta za ka iya soma damuwa. Idan hakan ya faru, za ka iya tattaunawa da wani abokinka da ba zai kushe ka ba. (K. Mag. 17:17) A maimakon haka, zai saurare ka, kuma ya ƙarfafa ka. Hakan zai sa ka sake yin farin ciki.—K. Mag. 12:25.
15. Me ya sa zai dace ku riƙa tattaunawa game da rayuwa a aljanna?
15 Ka yi tunani a kan abin da za ku iya yi a aljanna. Ka tuna cewa, ba har abada ba ne za ka dinga kula da waɗanda suka tsufa ko marar lafiya ba. Jehobah bai halicci ꞌyanꞌadam su riƙa irin wannan aikin ba. (2 Kor. 4:16-18) A nan gaba, dukanmu za mu yi rayuwa yadda Jehobah yake so mu yi. (1 Tim. 6:19) Idan kai da wanda kake kula da shi kuna tattaunawa game da yadda za ku yi rayuwa tare a aljanna, hakan zai sa ku farin ciki. (Isha. 33:24; 65:21) Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Heather ta ce: “A yawancin lokuta, ina gaya wa waɗanda nake kula da su cewa, ba da daɗewa ba, za mu yi ɗinki tare, mu yi gudu tare, kuma mu tuƙa keke tare. Za mu yi burodi kuma mu dafa wa wani namu da aka ta da shi daga mutuwa abinci. Bayan mun yi irin wannan tunanin, sai mu gode wa Jehobah tare don wannan begen da ya ba mu.”
YADDA WASU ZA SU IYA TAIMAKAWA
16. Ta yaya za mu iya taimaka wa masu kula da wani? (Ka kuma duba hoton.)
16 Ka taimaka wa masu kula da tsofaffi ko marasa lafiya su ɗan sami lokaci don su huta. ꞌYanꞌuwa a ikilisiya za su iya taimaka wajen kula da wanda ya tsufan ko marar lafiyan. Hakan zai sa mai kula da shi ya sami lokaci ya huta ko kuma lokacin yin wasu abubuwan da yake bukata. (Gal. 6:2) Wasu ꞌyanꞌuwa sun rubuta yadda za su riƙa yin hakan kowane mako. Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Natalya, da take kula da mijinta da ba ya iya tafiya, ta ce: “Wani ɗanꞌuwa a ikilisiyarmu yana zuwa sau ɗaya ko sau biyu a mako don ya kasance tare da mijina. Suna yin waꞌazi tare, su yi hira, kuma su kalli fim tare. Mijina yana jin daɗin hakan sosai. Hakan yana sa ina samun damar yin abubuwan da nake so in yi.” A wasu lokuta, za ka iya zuwa ka kwana a gidan wanda ya tsufa ko marasa lafiyan don ka taimaka. Hakan zai ba wa mai kula da shi damar samun isashen barci.
Ta yaya za ka taimaka wa masu kula da wani da ke ikilisiyarku? (Ka duba sakin layi na 16)b
17. Ta yaya za mu taimaka wa waɗanda suke kula da wani a taro?
17 Ka taimaka musu a lokacin da ake taro. Waɗanda suke kula da wani, ba sa amfana sosai a taron ikilisiya, ko taron daꞌira, ko taron yanki domin hankalinsu yana kan wanda suke kula da shi. Saboda haka, ꞌyanꞌuwa a ikilisiya za su iya taimakawa ta wajen zama da wanda ya tsufan ko marar lafiyan a taro gabaki ɗaya, ko na ɗan lokaci. Idan wanda ya tsufan ko marar lafiyan ba zai iya barin gida ba, za ka iya zuwa wurinsa kuma ku shiga taro ta naꞌura idan zai yiwu. Hakan zai sa mai kula da shi ya iya zuwa taro a Majamiꞌar Mulki.
18. Mene ne kuma za mu iya yi wa masu kula da wani?
18 Ka yaba musu kuma ka yi adduꞌa a madadinsu. Zai dace dattawa su riƙa ƙarfafa waɗanda suke kula da wani kowane lokaci. (K. Mag. 27:23) Zai kuma dace dukanmu, mu riƙa gaya wa waɗanda suke kula da wani cewa muna ƙaunarsu kuma muna jin daɗin komen da suke yi. Ƙari ga haka, za mu iya roƙan Jehobah ya ƙarfafa su kuma ya taimaka musu su ci-gaba da farin ciki.—2 Kor. 1:11.
19. Mene ne muke ɗokin gani a nan gaba?
19 Nan ba da daɗewa ba, Jehobah zai share dukan hawaye daga idanun mutane. Ciwo da mutuwa ba za su sake kasancewa ba. (R. Yar. 21:3, 4) “Guragu za su yi tsalle kamar barewa.” (Isha. 35:5, 6) Babu wanda zai sha wahala don ya tsufa, kuma babu wanda zai sha wahala wajen kula da wani da ke rashin lafiya. Ƙari ga haka, “Ba za a sake tunawa da abubuwan dā ba.” (Isha. 65:17) Ko da yake waɗannan abubuwan za su faru a nan gaba ne, muna da tabbaci cewa Jehobah zai ci-gaba da taimaka mana a yanzu. Idan muka dogara gare shi, zai taimaka mana mu jimre kowane abin da ya faru, mu yi haƙuri, kuma mu yi farin ciki.—Kol. 1:11.
WAƘA TA 155 Jehobah ne Ke Sa Mu Farin Ciki
a An canja sunan.
b BAYANI A KAN HOTO: ꞌYanꞌuwa mata biyu sun zauna tare da wata ꞌyarꞌuwa da ta tsufa don mai kula da ita ta iya fita ta sha iska.