TALIFIN NAZARI NA 44
WAƘA TA 138 Tsofaffi Masu Aminci Suna da Daraja
Yadda Za Ka Kasance da Farin Ciki Idan Ka Tsufa
“ A tsufarsu za su yi ta ba da ꞌyaꞌya.”—ZAB. 92:14.
ABIN DA ZA MU KOYA
Za mu ga abin da ya sa yake da muhimmanci waɗanda suka tsufa su ci-gaba da yin farin ciki, da kuma abin da zai taimaka musu su yi hakan.
1-2. Mene ne raꞌayin Jehobah game da bayinsa masu aminci da suka tsufa? (Zabura 92:12-14; ka kuma duba hoton.)
MUTANE a faɗin duniya suna da raꞌayi dabam-dabam game da tsufa. Wasu suna ganin cewa idan mutum ya tsufa, hakan yana sa ya ƙara zama da daraja. Wasu kuma suna iya ƙoƙarinsu don kada a ga kamar sun tsufa. Alal misali, idan wasu sun ga furfura a kansu, sukan cire shi. Duk da haka, ba za su iya hana furfuran fitowa ba.
2 Amma, mene ne raꞌayin Ubanmu na sama game da bayinsa da suka tsufa? (K. Mag. 16:31) Ya ce suna kama da bishiyar da ke ba da ꞌyaꞌya sosai. (Karanta Zabura 92:12-14.) Me ya sa ya ce hakan? Itatuwan da suka tsufa suna da kyaun gani, domin suna da ganyaye da furanni da yawa. Alal misali, akwai wasu irin itatuwa da ke Japan da sukan yi shekaru da yawa. Wasunsu sun yi shekaru fiye da dubu ɗaya kuma har ila suna da kyau sosai. Haka ma, bayin Jehobah da suka tsufa suna da daraja sosai a wurinsa. Jehobah yana daraja halaye masu kyau da tsofaffin nan suke da shi. Sun yi shekaru da yawa suna bauta masa kuma sun riƙe amincinsu a duk yanayin da suka sami kansu.
Kamar yadda itacen da suka daɗe suke kyau sosai kuma su ba da ꞌyaꞌya, haka ma tsofaffi masu aminci suke da kyau da kuma daraja (Ka duba sakin layi na 2)
3. Ka ba da misalin da ya nuna yadda Jehobah ya yi amfani da waɗanda suka tsufa wajen cim ma nufinsa.
3 Jehobah yana daraja mu ko da mun tsufa.a Jehobah yana amfani da tsofaffi wajen cim ma nufinsa. Alal misali, Saratu ta tsufa a lokacin da Jehobah ya gaya mata cewa za ta haifi ɗa. Kuma ta wurin ɗan, za a sami wata babbar alꞌumma da kuma Almasihu. (Far. 17:15-19) Musa ya tsufa a lokacin da Jehobah ya tura shi ya je ya ceci Israꞌilawa daga Masar. (Fit. 7:6, 7) Ƙari ga haka, manzo Yohanna ma ya tsufa saꞌad da Jehobah ya taimaka masa ya rubuta littattafai biyar a Littafi Mai Tsarki.
4. Bisa ga Karin Magana 15:15, mene ne zai taimaka wa waɗanda suka tsufa su jimre da matsalolin da ke tattare da tsufa? (Ka kuma duba hoton.)
4 Idan mutum ya soma tsufa, hakan yana sa ya yi fama da matsaloli da yawa. Wata ꞌyarꞌuwa ta ce, “Tsufa ba abu mai sauƙi ba ne.” Amma kasancewa da farin cikib zai taimaka wa waɗanda suka tsufa su iya jimre matsalolin da ke tattare da tsufa. (Karanta Karin Magana 15:15.) A wannan talifin, za mu tattauna abubuwan da waɗanda suka tsufa za su iya yi don su ci-gaba da yin farin ciki. Za mu kuma ga yadda wasu za su iya taimaka wa ꞌyanꞌuwa maza da mata da suka tsufa a cikin ikilisiya. Da farko, bari mu tattauna abubuwan da za su iya hana mutum ya ci-gaba da yin farin ciki saꞌad da ya soma tsufa.
Kasancewa da farin ciki zai iya taimaka wa waɗanda suka tsufa su iya jimre matsalolin da ke tattare da tsufa (Ka duba sakin layi na 4)
ABUBUWAN DA SUKE SA YA YI MANA WUYA MU CI-GABA DA FARIN CIKI IDAN MUKA TSUFA
5. Mene ne zai iya sa waɗanda suka tsufa su yi sanyin gwiwa?
5 Mene ne zai iya sa ka yi sanyin gwiwa? Wataƙila kana baƙin ciki domin ba ka iya yin abubuwan da kake yi a dā. Ko kuma kana tuna lokacin da kake matashi, kuma kana da ƙoshin lafiya. (M. Wa. 7:10) Alal misali, wata ꞌyarꞌuwa mai suna Ruby ta ce: “Yana yawan yi min wuya in sa riga domin gaɓaɓuwana ba sa aiki kamar yadda suke yi a dā, kuma jikina yana yi mini ciwo sosai. A wasu lokuta, ɗaga kafa in sa safa ma yana yi min wuya. Hannaye na suna yi mini ciwo, kuma ba na iya amfani da yatsuna da kyau. Hakan ya sa ko ƙananan abubuwa ma ba na iya yi.” Wani ɗanꞌuwa mai suna Harold, da ya taɓa hidima a Bethel ya ce: “A wasu lokuta nakan yi fushi sosai domin ba na iya yin abubuwan da nake jin daɗin yin su a dā. Ina da ƙarfi sosai a lokacin da nake matashi. Ina jin daɗin buga wasanni. Wasu sukan ce a ba ni ƙwallon don sun san zan sha. Amma yanzu, ban tsammani zan iya wurga ƙwallon ba.”
6. (a) Waɗanne abubuwa kuma za su iya sa waɗanda suka tsufa su yi sanyin gwiwa? (b) Mene ne zai taimaka wa waɗanda suka tsufa su san ko za su daina tuƙi? (Ka duba talifin nan mai jigo “Zai Dace In Daina Tuƙi?”)
6 Za ka iya yin sanyin gwiwa domin ba ka iya yin abubuwan da ka saba yi da kanka a dā. Mai yiwuwa kana bukatar wanda zai zo ya riƙa kula da kai, ko kuma kana bukatar ka je ka zauna da yaranka don su kula da kai. Wataƙila kana baƙin ciki domin ba za ka iya yin tuƙi kuma ba. Ko kuma ba za ka iya zuwa wasu wurare da kanka ba, domin ba ka da ƙarfi ko kuma ba ka gani da kyau. Ko da yake ba za ka iya yin abubuwa da yawa kamar yadda ka saba yi ba, ka tuna cewa kana da muhimmanci a wurin Jehobah da kuma mutane. Muna da tabbaci cewa Jehobah ya san abin da ke damin mu. Abin da ya fi muhimmanci ga Jehobah shi ne yadda muke ƙaunar sa da kuma ꞌyanꞌuwanmu maza da mata da dukan zuciyarmu.—1 Sam. 16:7.
7. Mene ne zai iya taimaka wa waɗanda suke ganin kamar za su mutu kafin nan a kawo ƙarshen wannan muguwar duniyar?
7 Wataƙila kana baƙin ciki domin kana ganin kamar za ka mutu kafin Allah ya hallaka wannan muguwar duniyar. Mene ne zai taimaka maka idan haka ne kake ji? Ka tuna cewa Jehobah yana da dalilin da ya sa bai kawo ƙarshen wannan muguwar duniyar ba. (Isha. 30:18) Dalilin shi ne, yana haƙuri ne don yana son miliyoyin mutane su sami damar koya game da shi kuma su bauta masa. (2 Bit. 3:9) Saboda haka, idan ka soma yin sanyin gwiwa, ka yi tunanin yawan mutanen da za su amfana don yadda Jehobah ya kasance da haƙuri. Mai yiwuwa wasu daga cikinsu danginka ne.
8. Idan waɗanda suka tsufa suka soma rashin lafiya ko fama da wasu matsaloli, mene ne hakan zai iya sa su yi?
8 Ko da shekarunmu nawa ne, idan ba mu da lafiya, za mu iya faɗa ko mu yi wani abin da za mu yi da na sani daga baya. (M. Wa. 7:7; Yak. 3:2) Alal misali, lokacin da Ayuba yake fama da matsaloli, ya yi wasu maganganu da ba su dace ba. (Ayu. 6:1-3) Ƙari ga haka, rashin lafiya zai iya sa waɗanda suka tsufa su soma yin wasu abubuwan da ba sa yi a dā. Amma, ko da mun tsufa ko ba mu da lafiya, bai kamata mu riƙa yi wa mutane baƙar magana, ko mu yi ta gani kamar dole ne su yi mana wani abu ba. Kuma idan mun gaya wa wani abin da bai dace ba, zai yi kyau mu roƙi gafararsa nan da nan.—Mat. 5:23, 24.
ABIN DA ZA KA YI DON KA CI-GABA DA FARIN CIKI
Ta yaya za ka ci-gaba da farin ciki duk da cewa ka tsufa? (Ka duba sakin layi na 9-13)
9. Me ya sa zai dace ka yarda wasu su taimaka maka? (Ka kuma duba hotunan.)
9 Ka yarda wasu su taimaka maka. (Gal. 6:2) Da farko, hakan zai iya yi maka wuya. Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Gretl ta ce: “A wasu lokuta yana mini wuya in yarda wasu su taimaka mini, don ina ganin kamar wahala ne kawai nake ba su. Na ɗau lokaci sosai kafin na soma yarda wasu su taimaka mini.” Idan ka bar mutane su taimaka maka, hakan zai sa su farin ciki. (A. M. 20:35) Kuma kai ma za ka yi farin ciki idan ka ga yadda suke ƙaunar ka kuma suke son kula da kai.
(Ka duba sakin layi na 9)
10. Me ya sa zai dace mu riƙa nuna godiya? (Ka kuma duba hotunan.)
10 Ka riƙa nuna godiya. (Kol. 3:15; 1 Tas. 5:18) Idan wasu sun yi mana alheri, mukan ji daɗi sosai. Amma, a wasu lokuta mukan manta mu gode musu. Idan muka yi murmushi kuma muka gode musu, hakan zai sa su san cewa mun ji daɗin abin da suka yi mana. Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Leah, da take kula da tsofaffi a Bethel ta ce: “Ɗaya daga cikin ꞌyanꞌuwa mata da nake kula da su tana gode mini kowane lokaci. Takan rubuta mini saƙo a ɗan ƙaramin fallen takarda. Abubuwa kaɗan ne take rubutawa, amma suna sa ni farin ciki sosai. Ina son karanta abubuwan da take rubuta mini. Ina farin ciki sanin cewa tana jin daɗin yadda nake taimaka mata.”
(Ka duba sakin layi na 10)
11. Ta yaya za ka taimaka wa mutane? (Ka kuma duba hotunan.)
11 Ka yi iya ƙoƙarinka wajen taimaka wa mutane. Idan muka mai da hankalinmu wajen taimaka wa mutane, hakan zai sa mu rage yawan damuwan da muke yi. Za mu iya kwatanta tsofaffi da littattafai da ke ɗauke da darussa masu kyau. Amma idan mutane ba su karanta littattafan ba, ba abin da za su koya. Haka ma, idan ba ka gaya wa waɗanda ba su kai ka shekaru abubuwan da ka sani ba, ba za su koyi kome daga wurinka ba. Saboda haka, ka riƙa musu tambayoyi kuma ka saurare su da kyau. Ƙari ga haka, ka gaya musu yadda Jehobah ya taimaka maka a rayuwa, da yadda yin biyayya ga Jehobah zai sa su farin ciki. Babu shakka, za ka yi farin ciki sosai idan kana ƙarfafa abokanka da ba su kai ka shekaru ba.—Zab. 71:18.
(Ka duba sakin layi na 11)
12. Bisa ga Ishaya 46:4, wane alkawari ne Jehobah ya yi wa waɗanda suka tsufa? (Ka kuma duba hotunan.)
12 Ka roƙi Jehobah ya ba ka ƙarfi. A wasu lokuta, gajiya zai iya sa ka yi sanyin gwiwa. Amma ka tuna cewa Jehobah yana da iko sosai. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ba ya gajiya ko ƙarfi ya kāsa masa.” (Isha. 40:28) Don haka, zai ba ka ƙarfin da kake bukata. (Isha. 40:29-31) Ya yi alkawari cewa zai taimaka maka. (Karanta Ishaya 46:4.) Kuma idan Jehobah ya yi alkawari, babu shakka zai cika alkawarin. (Yosh. 23:14; Isha. 55:10, 11) Idan ka roƙi Jehobah ya taimaka maka, zai taimaka maka. Kuma hakan zai sa ka yi farin ciki sosai sanin cewa yana ƙaunar ka.
(Ka duba sakin layi na 12)
13. Bisa ga 2 Korintiyawa 4:16-18, me ya kamata mu tuna? (Ka kuma duba hotunan.)
13 Ka tuna cewa lokaci yana zuwa da ba za ka tsufa ba. Zai yi mana sauƙi mu jimre wani yanayi mai wuya idan mun san cewa na ɗan lokaci ne. Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa a nan gaba, mutane ba za su ƙara ciwo ko tsufa ba. (Ayu. 33:25; Isha. 33:24) Saboda haka, ka kasance da farin ciki domin a nan gaba za ka zama da koshin lafiya, da ƙarfi, da kuma kyau sosai. (Karanta 2 Korintiyawa 4:16-18.) Mene ne wasu za su iya yi don su taimaka maka?
(Ka duba sakin layi na 13)
YADDA WASU ZA SU IYA TAIMAKAWA
14. Me ya sa yake da muhimmanci mu riƙa kira da kuma ziyartar waɗanda suka tsufa?
14 Ka riƙa kira da kuma ziyartar ꞌyanꞌuwa maza da mata da suka tsufa. (Ibran. 13:16) Waɗanda suka tsufa za su iya yin baƙin ciki don suna zama su kaɗai. Wani ɗanꞌuwa mai suna Camille da yake irin yanayin nan ya ce: “A wasu lokuta ina fushi da kuma damuwa domin ba zan iya barin gida ba kuma ba ni da abin da zan yi.” Idan muna ziyartar waɗanda suka tsufa, muna nuna musu cewa suna da muhimmanci kuma muna ƙaunar su. Shin, ka taɓa ce za ka kira wani da ya tsufa ko ka ziyarce shi amma ba ka yi hakan ba? Hakan yana faruwa da dukanmu. Muna da ayyuka da yawa da muke yi. To, mene ne zai taimaka mana mu “iya zaɓar abin da ya fi kyau,” kamar ziyartar waɗanda suka tsufa? (Filib. 1:10) Za ka iya rubuta sunayen waɗanda suka tsufa da ke ikilisiyarku da kuma ranar da za ka tura musu saƙo ko ka kira su. Ƙari ga haka, ka zaɓi ranar da za ka so ka ziyarce su. Kuma kada ka ce za ka yi hakan a duk lokacin da ka samu zarafi.
15. Waɗanne abubuwa ne matasa da waɗanda suka tsufa za su iya yi tare?
15 Idan kai matashi ne, mai yiwuwa ba za ka san abin da za ka tattauna ko kuma abubuwan da za ka yi tare da waɗanda suka tsufa ba. Idan haka ne, kada ka damu. Ka yi ƙoƙari ka fara zama abokinsu. (K. Mag. 17:17) Kuma ka yi ƙoƙari ka tattauna da waɗanda suka tsufa kafin taro ko bayan taro. Za ka iya ce su gaya maka wani nassin da suka fi so, ko wani abin ban dariyar da ya faru lokacin da suke yara. Za ku iya kallon shirin Tashar JW® tare. Ban da haka, za ka iya yi musu wasu abubuwan da ba za su iya yi da kansu ba. Alal misali, za ka iya taimaka wajen sa naꞌurarsu ta riƙa yin aiki da kyau, ko kuma saukar da sabbin littattafai da muke da su. Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Carol ta ce: “Ka gaya wa waɗanda suka tsufa cewa za ka so ku yi abubuwan da kake jin daɗin yi. Ko da yake na tsufa ina son jin daɗin rayuwa. Ina son zuwa sayayya, da zuwa cin abinci da abokaina a wani wuri, da kuma zuwa yawon buɗe ido.” Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Maira kuma ta ce: “Shekarun wata abokiyata 90 ne. Wato ta girme ni da shekaru 57. Amma ba na tunawa da hakan domin muna wasa da kuma kallon finafinai tare. Kuma idan muna fama da matsaloli, muna taimaka wa juna.”
16. Me ya sa yake da muhimmanci mu riƙa raka waɗanda suka tsufa zuwa asibiti?
16 Ka raka su zuwa asibiti. Za ka iya kai waɗanda suka tsufa asibiti, kuma ka zauna tare da su don ka tabbata cewa likita ko nas da ke kula da su ya yi hakan da kyau. (Isha. 1:17) Za ka iya taimaka wa waɗanda suka tsufa ta wurin rubuta abin da likitan ya ce. Wata ꞌyarꞌuwan da ta tsufa mai suna Ruth ta ce: “A yawancin lokuta idan na je wurin likita ni kaɗai, ba ya ɗaukan abin da na faɗa da muhimmanci. Wasu likitocin sukan ce, ‘Ba abin da ke damun ki, ke ce kawai kike ganin kamar ba ki da lafiya.’ Amma idan wani ya raka ni, likitocin ba sa yi min haka. Ina gode wa ꞌyanꞌuwa maza da mata da suke raka ni zuwa asibiti.”
17. Ta yaya za mu iya yin waꞌazi tare da waɗanda suka tsufa?
17 Ku riƙa yin waꞌazi tare. Wasu da suka tsufa ba za su iya yin waꞌazi gida-gida ba. Saboda haka, za ka iya shirya yin waꞌazi da amalanke tare da wata da ta tsufa. Za ka iya kawo kujera don ta zauna a wurin da kuke waꞌazin. Ban da haka, za ka iya zuwa yin nazari tare da wani ɗanꞌuwan da ya tsufa, ko kuma ka kawo ɗalibinka gidansa. Dattawa za su iya shirya a riƙa yin taron fita waꞌazi a gidan wani ɗanꞌuwan da ya tsufa don ya yi masa sauƙi ya halarta. Jehobah yana farin ciki idan muka yi iya ƙoƙarinmu wajen nuna cewa muna ƙauna da kuma daraja waɗanda suka tsufa.—K. Mag. 3:27; Rom. 12:10.
18. Me za mu tattauna a talifi na gaba?
18 A wannan talifin, an tuna mana cewa Jehobah yana ƙauna da kuma daraja waɗanda suka tsufa. Kuma mu ma muna hakan! Tsufa ba abu mai sauƙi ba ne, amma da taimakon Jehobah, za ka iya ci-gaba da yin farin ciki. (Zab. 37:25) Abin ƙarfafa ne sanin cewa za mu fi yin farin ciki a nan gaba! Amma, ta yaya ꞌyanꞌuwanmu da suke kula da waɗanda suka tsufa ko marasa lafiya za su ci-gaba da yin farin ciki? Abin da za mu tattauna ke nan a talifi na gaba.
WAƘA TA 30 Jehobah Ubana, Allahna da Abokina
a Ka kalli bidiyon nan mai jigo Tsofaffi—Kuna da Matsayi Mai Muhimmanci a jw.org/ha ko a manhajar JW Library®.