RAYUWAR KIRISTA
Ka Guji Yabon Kai, Amma Ka Zama da Sauƙin Kai
Mai girman kai ne yake yabon kansa da cika baki kuma hakan ba ya ƙarfafa waɗanda suke sauraransa. Shi ya sa Littafi Mai Tsarki ya ce: “Bari wani ya yabe ka, ba kai da kanka ba.” —K. Ma 27:2.
KU KALLI BIDIYON NAN KA ZAMA ABOKIN JEHOBAH—KA ZAMA MAI TAWALI’U, SA’AN NAN KU AMSA TAMBAYOYIN NAN:
Waɗanne abubuwa ne suke sa mutane girman kai?
Me Kaleb yake ciccika baki da shi?
Ta yaya baban Kaleb ya taimaka masa?
Ta yaya 1 Bitrus 5:5 za ta taimaka mana mu kasance da sauƙin kai?